× Harshe Turai Rashanci Belarusiyanci Yukreniyanci Yaren mutanen Poland Sabiyanci Bulgaria Slovakiyan Czech Romaniyanci Moldoviyanci Azerbaijan Armeniyanci Jojiyanci Albaniyanci Avar Bashkir Tatar Checheniya Slobaniyanci Kuroshiya Estoniyanci Latvia Lituweniyanci Harshen Hungary Yaren mutanen Finland Yaren mutanen Norway Yaren mutanen Sweden Icelandic Girkanci Macedonia Bajamushe Bavarian Yaren mutanen Holland Danish Welsh Gaelic Irish Faransanci Basque Katalaniyanci Italiyanci Galacian Romani Bosnian Amirka ta Arewa Turanci Kudancin Amurka Sifeniyanci Fotigal Guarani Quechuan Aymara Amurka ta Tsakiya Jamaica Nahuatl Kiche Qeqchi Haiti Gabashin Asiya Sinanci Jafananci Yaren Koriya Mongoliyanci Uyghur Hmong Kudu maso gabashin Asiya Malesiya Burma Chin Nepali Cebuano Tagalog Kambodiyanci Thai Indonesiyanci Vietnam Javanisanci Lao Iban IuMien Kachin Lahu Aceh Balinese Bugis Pampanga Sasak Shan Waray Kudancin Asiya Hindi Оdia Awadhi Mizo Kannada Malayalam Marathi Gujarati Tamil Telugu Harshen Punjabi Kurukh Assamese Maithili Bengali Urdu Sinhala Dogri Haryanvi Meitei Konkani Santali Sindhi Koya Thado Sanskrit Devanagari Adilabad Gondi Ahirani Balochi Bundeli Chhattisgarhi Garhwali Kangri Kumaoni Mewari Munda Sadri Seraiki Shekhawati Sylheti Asiya ta Tsakiya Kirgiziya Uzbek Tajik Turkmen Kazakhstan Karakalpak Gabas ta Tsakiya Baturke Ibrananci Larabci Farisanci Kurdawa Pashto 'Yan Koftik Afirka Afirkaans Xhosa Zulu Ndebele Sotho Amharic Wolaytta Dan Najeriya Mossi Ika Dinka Kabyle Ewe Swahili Maroko Somalian Shona Madagaska Igbo Lingala Baoule Siswati Tsonga Tswana Gambiya Yarbawa Kamba Kinyarwanda Hausa Chewa Luo Makua Dyula Fulfulde Kalenjin Kikuyu Kikwango Kirundi Krio Nigerian Pidgin Oromo Tshiluba Tshivenda Twi Umbundu Lugbara Luguru Pular Gussi Maasai Turkana Moba Nuer Shilluk Tamasheq Makonde Bemba Fon Hadiyya Ibibio Kimbundu Kimiiru Lango Liberian Kreyol Lomwe Mende Morisyen Ndau Nyankole Sena Sidamo Soga Songe Sukuma Tarifit Teso Tiv Zande Nahiyar Australiya New Zealand Papua New Guinea Tsoffin Harsuna Aramaic Latin Esperanto 1 1 1 2020 202020101 1 1 Markus FarawaFitowaFiristociƘidayaMaimaitawar ShariʼaYoshuwaMahukuntaRut1 Samaʼila2 Samaʼila1 Sarakuna2 Sarakuna1 Tarihi2 TarihiEzraNehemiyaEstaAyubaZaburaKarin MaganaMai HadishiWaƙar WaƙoƙiIshayaIrmiyaMakokiEzekiyelDaniyelHosiyaYowelAmosObadiyaYunanaMikaNahumHabakkukZefaniyaHaggaiZakariyaMalaki--- --- ---MattiyuMarkusLukaYohannaAyyukan ManzanniRomawa1 Korintiyawa2 KorintiyawaGalatiyawaAfisawaFilibbiyawaKolossiyawa1 Tessalonikawa2 Tessalonikawa1 Timoti2 TimotiTitusFilemonIbraniyawaYaƙub1 Bitrus2 Bitrus1 Yohanna2 Yohanna3 YohannaYahudaRuʼuya ta Yohanna1 1 1 6 123456789101112131415161 1 1 : 1 12345678910111213141516171819202122232425262728293031323334353637383940414243444546474849505152535455561 1 1 Sabon Rai Don Kowa 2020 Markus 6 Adana Bayanan kula 1Yesu ya tashi daga can ya tafi garinsa, tare da almajiransa.2Da Asabbaci ya kewayo, sai ya fara koyarwa a cikin majami’a, mutane da yawa da suka saurare shi, suka yi mamaki. Suna tambaya, “Ina mutumin nan ya sami waɗannan abubuwa? Wace hikima ce wannan da aka ba shi, har da yana yin ayyukan banmamaki haka!3Ashe, wannan ba shi ne kafinta nan ba? Shin, ba shi ne ɗan Maryamu ba, ba shi ne ɗan’uwan su Yaƙub, Yusuf, Yahuda da kuma Siman ba? Ashe, ’yan’uwansa mata kuma ba suna nan tare da mu ba?” Sai suka ji haushinsa.4Yesu ya ce musu, “Sai a garinsa kaɗai, da kuma cikin ’yan’uwansa, da cikin gidansa ne, annabi ba shi da daraja.”5Bai iya yin ayyukan banmamaki a wurin ba, sai dai ɗibiya hannuwansa da ya yi a kan mutane kima da suke da cututtuka, ya kuwa warkar da su.6Ya kuwa yi mamaki ƙwarai don rashin bangaskiyarsu. Sai ya Yesu zazzaga ƙauyuka yana koyarwa.7Ya kira Sha Biyun nan wurinsa, ya aike su biyu-biyu, ya kuma ba su iko bisa mugayen ruhohi.8Ga dai umarnansa, “Kada ku ɗauki kome don tafiyar, sai dai sanda ba burodi, ba jaka, ba kuɗi a ɗamararku.9Ku sa takalma, amma ban da riga fiye da waɗanda kuka sa.10Duk sa’ad da kuka shiga wani gida, ku zauna nan sai kun bar garin.11In kuwa a wani wuri ba a karɓe ku, ba a kuwa saurare ku ba, sai ku karkaɗe ƙurar ƙafafunku sa’ad da kuka fita, a matsayin shaida a kansu.”12Suka fita, suna yi wa’azi, suna ce wa mutane su tuba.13Suka fitar da aljanu da yawa, suka shafa wa marasa lafiya da yawa mai, suka kuwa warkar da su.14Sarki Hiridus ya ji wannan labari, gama sunan Yesu ya bazu a ko’ina. Waɗansu suna cewa, “An tashe Yohanna Mai Baftisma daga matattu ne, shi ya sa yana da ikon yin ayyukan banmamakin nan.”15Waɗansu suka ce, “Ai, Iliya ne.” Har wa yau waɗansu suka ce, “Ai, annabi ne, kamar ɗaya daga cikin annabawan dā.”16Amma da Hiridus ya ji haka, sai ya ce, “Ai, Yohanna ne, mutumin da na yanke masa kai, shi ne ya tashi daga matattu!”17Gama Hiridus da kansa ya ba da umarni a kama Yohanna, ya kuma sa aka daure shi, aka sa shi a kurkuku. Ya yi haka saboda Hiridiyas, matar ɗan’uwansa Filibus, wadda ya aura.18Gama Yohanna ya yi ta ce wa Hiridus, “Ba daidai ba ne bisa ga doka, ka ɗauki matar ɗan’uwanka.”19Saboda haka, Hiridiyas ta ƙulla munafunci game da Yohanna, ta kuma so ta kashe shi. Amma ba tă iya ba,20domin Hiridus yana jin tsoron Yohanna, ya kuma kāre shi sosai, da sanin cewa shi mutum ne mai adalci da kuma mai tsarki. Duk sa’ad da Hiridus ya saurari Yohanna, yakan damu ƙwarai, duk da haka, yakan so yă ji shi.21A ƙarshe, ta sami zarafi. A ranar murnar haihuwar Hiridus, ya yi biki domin hakimansa, da shugabannin sojojinsa, da kuma manyan mutanen Galili.22Sa’ad da diyar Hiridiyas ta shigo, ta kuma yi rawa, sai ta gamshi Hiridus tare da baƙinsa. Sai Sarkin ya ce wa yarinyar, “Ki tambaye ni kome da kike so, ni kuwa zan ba ki.”23Ya yi mata alkawari da rantsuwa cewa, “Duk abin da kika roƙa, zan ba ki, ko da rabin mulkina ne.”24Sai ta fita ta ce wa mahaifiyarta, “Me zan roƙa?” Ta ce, “Kan Yohanna Mai Baftisma.”25Nan da nan, sai yarinyar ta yi hanzari zuwa wajen sarki da roƙon, “Ina so ka ba ni kan Yohanna Mai Baftisma a cikin tasa, yanzu-yanzu nan.”26Sai sarki ya yi baƙin ciki ƙwarai, amma saboda rantsuwar da kuma baƙinsa, bai so yă hana ta ba.27Nan take, sai ya aiki mai aiwatar da kisa da umarni ya kawo kan Yohanna. Mutumin ya je ya yanke kan Yohanna a kurkuku.28Ya kuma kawo kan a tasa ya ba yarinyar. Ita kuma ta ba wa mahaifiyarta.29Da almajiran Yohanna suka sami labari, sai suka zo suka ɗauki jikinsa suka binne a kabari.30Manzannin suka taru kewaye da Yesu, suka ba shi rahoton duk abin da suka yi, da kuma suka koyar.31To, saboda mutane da yawa suna kai da kawowa, har ma ba su sami damar cin abinci ba, sai ya ce musu, “Ku zo mu kaɗaita inda ba kowa don ku ɗan huta.”32Sai suka tafi a jirgin ruwa su kaɗai, inda ba kowa.33Amma mutane da yawa waɗanda suka ga tashinsu, sun gane su, sai suka ruga da gudu a ƙafa daga dukan birane, suka riga su kaiwa can.34Da Yesu ya sauka, ya ga taro mai yawa, sai ya ji tausayinsu, gama kamar tumaki suke waɗanda ba su da makiyayi. Sai ya fara koya musu abubuwa da yawa.35A lokacin nan yamma ta yi, sai almajiransa suka zo wurinsa suka ce masa, “Wurin nan ƙauye ne, ga shi kuma lokaci ya ƙure.36Ka sallami mutanen su shiga ƙauyukan da suke kurkusa, su sayi wa kansu wani abu, su ci.”37Sai ya amsa ya ce, “Ku, ku ba su wani abu su ci.” Suka ce masa, “Ai, wannan zai ɗauki albashin wata takwas na mutum! Mu je mu kashe yawan kuɗin nan a burodi mu ba su su ci?”38Sai ya yi tambaya ya ce, “Burodi nawa kuke da su? Je ku duba.” Da suka duba, sai suka ce, “Biyar da kifi biyu.”39Sa’an nan Yesu ya umarce su su sa dukan mutanen su zazzauna ƙungiya-ƙungiya a kan ɗanyar ciyawa.40Haka suka zazzauna a ƙungiyar ɗari-ɗari, da kuma hamsin-hamsin.41Ya ɗauki burodi guda biyar da kifin nan biyu, ya ɗaga kai sama, ya yi godiya, ya kakkarya burodin. Sai ya ba wa almajiransa su rarraba wa mutane. Ya kuma rarraba kifi biyun a tsakaninsu duka.42Kowa ya ci, ya ƙoshi,43almajiran suka kwashe gutsattsarin burodin da na kifin cike da kwanduna goma sha biyu.44Yawan mutanen da suka ci kuwa maza dubu biyar ne.45Nan da nan Yesu ya sa almajiransa su shiga jirgin ruwa, su sha gabansa zuwa Betsaida, shi kuma yă sallami taron.46Bayan ya bar su, sai ya hau kan dutse don yă yi addu’a.47Da yamma ta yi, jirgin ruwan yana tsakiyar tafkin, Yesu kuma yana can a ƙasa shi kaɗai.48Ya ga almajiran suna fama da tuƙi saboda iska tana gāba da su. Wajen tsara ta huɗu na dare, sai ya tafi wurinsu, yana takawa a kan tafkin. Ya yi kamar zai wuce su,49amma da suka gan shi yana takawa a kan tafkin, sai suka yi tsammani fatalwa ce. Sai suka yi ihu,50domin dukansu sun gan shi, suka kuma tsorata. Nan da nan ya yi magana da su ya ce, “Ku yi ƙarfin hali! Ni ne. Kada ku ji tsoro.”51Sai ya shiga jirgin ruwan tare da su, iskar kuma ta kwanta. Dukansu suka yi mamaki,52gama ba su fahimci al’amarin burodin nan ba, don zuciyarsu ta taurare.53Da suka haye, sai suka sauka a Gennesaret, suka daure jirgin a ƙugiya.54Da fitowarsu daga jirgin, sai mutane suka gane Yesu.55Suka gama yankin da gudu, suna ɗaukan marasa lafiya a kan tabarmai zuwa duk inda suka ji yake.56Duk inda ya shiga, cikin ƙauyuka, birane ko karkara, sai su kwantar da marasa lafiya a bakin kasuwa. Suka roƙe shi yă bari su taɓa gefen rigarsa kawai, kuma duk waɗanda suka taɓa shi kuwa, suka warke.Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide. Sabon Rai Don Kowa 2020 Markus 6 00:00:00 00:00:00 0.5x 2.0x https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/mark/006.mp3 16 6