× Harshe Turai Rashanci Belarusiyanci Yukreniyanci Yaren mutanen Poland Sabiyanci Bulgaria Slovakiyan Czech Romaniyanci Moldoviyanci Azerbaijan Armeniyanci Jojiyanci Albaniyanci Avar Bashkir Tatar Checheniya Slobaniyanci Kuroshiya Estoniyanci Latvia Lituweniyanci Harshen Hungary Yaren mutanen Finland Yaren mutanen Norway Yaren mutanen Sweden Icelandic Girkanci Macedonia Bajamushe Bavarian Yaren mutanen Holland Danish Welsh Gaelic Irish Faransanci Basque Katalaniyanci Italiyanci Galacian Romani Bosnian Kabardian Amirka ta Arewa Turanci Kudancin Amurka Sifeniyanci Fotigal Guarani Quechuan Aymara Amurka ta Tsakiya Jamaica Nahuatl Kiche Qeqchi Haiti Gabashin Asiya Sinanci Jafananci Yaren Koriya Mongoliyanci Uyghur Hmong Tibetian Kudu maso gabashin Asiya Malesiya Burma Chin Nepali Cebuano Tagalog Kambodiyanci Thai Indonesiyanci Sundanese Vietnam Javanisanci Lao Iban IuMien Kachin Lahu Aceh Balinese Bugis Pampanga Sasak Shan Waray Madurese Kudancin Asiya Hindi Оdia Awadhi Mizo Kannada Malayalam Marathi Gujarati Tamil Telugu Harshen Punjabi Kurukh Assamese Maithili Bengali Urdu Sinhala Dogri Haryanvi Meitei Konkani Santali Sindhi Koya Thado Sanskrit Devanagari Adilabad Gondi Ahirani Balochi Bundeli Chhattisgarhi Garhwali Kangri Kumaoni Mewari Munda Sadri Seraiki Shekhawati Sylheti Bagri Bhilali Bodo Braj Tulu Asiya ta Tsakiya Kirgiziya Uzbek Tajik Turkmen Kazakhstan Karakalpak Gabas ta Tsakiya Baturke Ibrananci Larabci Farisanci Kurdawa Mazanderani Pashto 'Yan Koftik Afirka Afirkaans Xhosa Zulu Ndebele Sotho Amharic Wolaytta Dan Najeriya Mossi Ika Dinka Kabyle Ewe Swahili Maroko Somalian Shona Madagaska Igbo Lingala Baoule Siswati Tsonga Tswana Gambiya Yarbawa Kamba Kinyarwanda Hausa Chewa Luo Makua Dyula Fulfulde Kalenjin Kikuyu Kikwango Kirundi Krio Nigerian Pidgin Oromo Tshiluba Tshivenda Twi Umbundu Lugbara Luguru Pular Gussi Maasai Turkana Moba Nuer Shilluk Tamasheq Makonde Bemba Fon Hadiyya Ibibio Kimbundu Kimiiru Lango Liberian Kreyol Lomwe Mende Morisyen Ndau Nyankole Sena Sidamo Soga Songe Sukuma Tarifit Teso Tiv Zande Dagbani Edo Kituba Nahiyar Australiya New Zealand Papua New Guinea Tsoffin Harsuna Aramaic Latin Esperanto 1 1 1 Sabon Rai Don Kowa 2020 Sabon Rai Don Kowa 2020أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا 2020Littafi Mai Tsarki 19791 1 1 Fitowa FarawaFitowaFiristociƘidayaMaimaitawar ShariʼaYoshuwaMahukuntaRut1 Samaʼila2 Samaʼila1 Sarakuna2 Sarakuna1 Tarihi2 TarihiEzraNehemiyaEstaAyubaZaburaKarin MaganaMai HadishiWaƙar WaƙoƙiIshayaIrmiyaMakokiEzekiyelDaniyelHosiyaYowelAmosObadiyaYunanaMikaNahumHabakkukZefaniyaHaggaiZakariyaMalaki--- --- ---MattiyuMarkusLukaYohannaAyyukan ManzanniRomawa1 Korintiyawa2 KorintiyawaGalatiyawaAfisawaFilibbiyawaKolossiyawa1 Tessalonikawa2 Tessalonikawa1 Timoti2 TimotiTitusFilemonIbraniyawaYaƙub1 Bitrus2 Bitrus1 Yohanna2 Yohanna3 YohannaYahudaRuʼuya ta Yohanna1 1 1 19 123456789101112131415161718192021222324252627282930313233343536373839401 1 1 : 1 123456789101112131415161718192021222324251 1 1 Sabon Rai Don Kowa 2020 Fitowa 19 Adana Bayanan kula 1A rana ta farko a cikin watan uku bayan da Isra’ilawa suka bar Masar, a wannan rana, suka iso Hamadar Sinai.2Bayan da suka tashi daga Refidim, suka shiga Hamadar Sinai, sai Isra’ilawa suka yi sansani a gaban dutsen.3Sai Musa ya hau kan dutsen don yă sadu da Allah, Ubangiji kuwa ya kira shi daga dutsen ya ce, “Wannan shi ne abin da za ka faɗa wa gidan Yaƙub, da kuma abin da za ka faɗa wa mutanen Isra’ila.4‘Ku da kanku kun ga abin da na yi wa Masar, da yadda na ɗauko ku a kan fikafikan gaggafa na kawo ku wurina.5Yanzu, in kuka yi mini cikakken biyayya, kuka kuma kiyaye yarjejjeniyata, to, za ku zama keɓeɓɓiyar taska a gare ni a cikin dukan al’ummai. Ko da yake duk duniya tawa ce,6za ku zama firistoci masu tsarki da kuma al’umma keɓaɓɓiya a gare ni.’ Waɗannan su ne kalmomin da za ka faɗa wa Isra’ilawa.”7Sai Musa ya koma ya aika a kira dukan dattawan mutane, ya bayyana dukan kalmomin da Ubangiji ya umarta, ya faɗa.8Dukan mutane suka amsa gaba ɗaya suka ce, “Za mu yi duk abin da Ubangiji ya faɗa.” Sai Musa ya mayar wa Ubangiji amsar da mutane suka bayar.9Ubangiji kuwa ya ce wa Musa, “Ina zuwa wurinka a cikin baƙin hadari, domin mutane su ji ni ina maganar da kai, domin su amince da kai koyaushe.” Sa’an nan Musa ya faɗa wa Ubangiji abin da mutane suka ce.10Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Tafi wurin mutanen, ka tsarkake su yau da gobe, ka sa su wanke tufafinsu.11Su zama da shiri a rana ta uku, gama a ranar ce Ubangiji zai sauko a kan Dutsen Sinai a idon dukan mutane.12Sai ka yi wa jama’a iyaka kewaye da dutsen, ka kuma faɗa musu cewa, ‘Ku mai da hankali, kada ku hau dutsen ko ku taɓa gefensa. Duk wanda ya taɓa dutsen, lalle za a kashe shi.13Za a jajjefe shi da duwatsu, ko a harbe shi da kibiyoyi, ba hannun da zai taɓa shi. Mutum ko dabbar da ya taɓa, ba za a bar shi da rai ba.’ Lokacin da aka ji muryar ƙaho ne kawai za su iya taru a gindin dutsen.”14Bayan da Musa ya gangara wurin mutane, ya tsarkake su, sai suka wanke tufafinsu.15Sa’an nan ya ce wa mutane, “Ku shirya kanku domin rana ta uku. Ku ƙame kanku daga yin jima’i.”16A safiyar rana ta uku, aka yi tsawa, da walƙiyoyi, sai ga girgije mai duhu a bisa dutsen, aka tsananta busar ƙaho, sai dukan jama’ar da suke cikin sansani suka yi rawar jiki.17Sa’an nan Musa ya jagoranci mutane daga sansani domin su sadu da Allah, sai suka tsaya a gefen dutsen.18Dutsen Sinai kuwa ya tunnuƙe duka da hayaƙi, gama Ubangiji ya sauko a bisan dutsen cikin wuta. Hayaƙin ya hau kamar hayaƙin da yake fitowa daga matoya, duk dutsen ya yi rawa da ƙarfi,19sai karar ƙaho ya yi ta ƙaruwa. Sa’an nan Musa ya yi magana, murya Allah kuwa ta amsa masa.20Ubangiji ya sauko a kan ƙwanƙolin Dutsen Sinai, ya kira Musa zuwa ƙwanƙolin dutsen. Musa kuwa ya haura21sai Ubangiji ya ce masa, “Ka sauka ka faɗa wa jama’a, kada su kuskura su ƙetare layin iyakan nan, garin son zuwa don ganin Ubangiji, gama duk waɗanda suka yi haka za su mutu.22Ko firistocin da za su kusato Ubangiji sai su tsarkake kansu, don kada in hallaka su.”23Musa ya ce wa Ubangiji, “Mutanen ba za su hau Dutsen Sinai ba, gama kai da kanka ka gargaɗe mu, ‘Ku sa iyaka kewaye da dutsen ku kuma tsarkake shi.’ ”24Ubangiji ya amsa, “Sauka ka kawo Haruna tare da kai. Amma kada firistoci da mutane su zarce iyakan nan, a kan za su zo wurin Ubangiji, don kada in hallaka su.”25Saboda haka Musa ya sauka wurin mutane ya kuma faɗa musu.Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Sabon Rai Don Kowa 2020 Fitowa 19 00:00:00 00:00:00 0.5x 2.0x https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/exodus/019.mp3 40 19