× Harshe Turai Rashanci Belarusiyanci Yukreniyanci Yaren mutanen Poland Sabiyanci Bulgaria Slovakiyan Czech Romaniyanci Moldoviyanci Azerbaijan Armeniyanci Jojiyanci Albaniyanci Avar Bashkir Tatar Checheniya Slobaniyanci Kuroshiya Estoniyanci Latvia Lituweniyanci Harshen Hungary Yaren mutanen Finland Yaren mutanen Norway Yaren mutanen Sweden Icelandic Girkanci Macedonia Bajamushe Bavarian Yaren mutanen Holland Danish Welsh Gaelic Irish Faransanci Basque Katalaniyanci Italiyanci Galacian Romani Bosnian Amirka ta Arewa Turanci Kudancin Amurka Sifeniyanci Fotigal Guarani Quechuan Aymara Amurka ta Tsakiya Jamaica Nahuatl Kiche Qeqchi Haiti Gabashin Asiya Sinanci Jafananci Yaren Koriya Mongoliyanci Uyghur Hmong Kudu maso gabashin Asiya Malesiya Burma Chin Nepali Cebuano Tagalog Kambodiyanci Thai Indonesiyanci Vietnam Javanisanci Lao Iban IuMien Kachin Lahu Aceh Balinese Bugis Pampanga Sasak Shan Waray Kudancin Asiya Hindi Оdia Awadhi Mizo Kannada Malayalam Marathi Gujarati Tamil Telugu Harshen Punjabi Kurukh Assamese Maithili Bengali Urdu Sinhala Dogri Haryanvi Meitei Konkani Santali Sindhi Koya Thado Sanskrit Devanagari Adilabad Gondi Ahirani Balochi Bundeli Chhattisgarhi Garhwali Kangri Kumaoni Mewari Munda Sadri Seraiki Shekhawati Sylheti Asiya ta Tsakiya Kirgiziya Uzbek Tajik Turkmen Kazakhstan Karakalpak Gabas ta Tsakiya Baturke Ibrananci Larabci Farisanci Kurdawa Pashto 'Yan Koftik Afirka Afirkaans Xhosa Zulu Ndebele Sotho Amharic Wolaytta Dan Najeriya Mossi Ika Dinka Kabyle Ewe Swahili Maroko Somalian Shona Madagaska Igbo Lingala Baoule Siswati Tsonga Tswana Gambiya Yarbawa Kamba Kinyarwanda Hausa Chewa Luo Makua Dyula Fulfulde Kalenjin Kikuyu Kikwango Kirundi Krio Nigerian Pidgin Oromo Tshiluba Tshivenda Twi Umbundu Lugbara Luguru Pular Gussi Maasai Turkana Moba Nuer Shilluk Tamasheq Makonde Bemba Fon Hadiyya Ibibio Kimbundu Kimiiru Lango Liberian Kreyol Lomwe Mende Morisyen Ndau Nyankole Sena Sidamo Soga Songe Sukuma Tarifit Teso Tiv Zande Dagbani Nahiyar Australiya New Zealand Papua New Guinea Tsoffin Harsuna Aramaic Latin Esperanto 1 1 1 2020 202020101 1 1 Markus FarawaFitowaFiristociƘidayaMaimaitawar ShariʼaYoshuwaMahukuntaRut1 Samaʼila2 Samaʼila1 Sarakuna2 Sarakuna1 Tarihi2 TarihiEzraNehemiyaEstaAyubaZaburaKarin MaganaMai HadishiWaƙar WaƙoƙiIshayaIrmiyaMakokiEzekiyelDaniyelHosiyaYowelAmosObadiyaYunanaMikaNahumHabakkukZefaniyaHaggaiZakariyaMalaki--- --- ---MattiyuMarkusLukaYohannaAyyukan ManzanniRomawa1 Korintiyawa2 KorintiyawaGalatiyawaAfisawaFilibbiyawaKolossiyawa1 Tessalonikawa2 Tessalonikawa1 Timoti2 TimotiTitusFilemonIbraniyawaYaƙub1 Bitrus2 Bitrus1 Yohanna2 Yohanna3 YohannaYahudaRuʼuya ta Yohanna1 1 1 14 123456789101112131415161 1 1 : 55 1234567891011121314151617181920212223242526272829303132333435363738394041424344454647484950515253545556575859606162636465666768697071721 1 1 Sabon Rai Don Kowa 2020 Markus 14 Adana Bayanan kula 1To, saura kwana biyu ne kaɗai a yi Bikin Ƙetarewa da Bikin Burodi Marar Yisti, sai manyan firistoci da malaman dokoki, suka nemi wani dalili su kama Yesu a ɓoye, su kashe.2Suka ce, “Ba a lokacin Biki ba, don kada mutane su yi tawaye.”3Yayinda yake a Betani, a gidan wani mutumin da ake kira Siman Kuturu, yana cin abinci, sai wata mace ta zo da wani ɗan tulu na turaren alabasta da aka yi da nardi zalla, mai tsadan gaske. Ta fasa tulun, ta kuma zuba turaren a kansa.4Waɗansu daga cikin waɗanda suke wurin, suka ji haushi, suka ce wa juna, “Me ya sa za a ɓata turaren nan haka?5Da an sayar da shi, ai, da an sami kuɗi fiye da albashi ma’aikaci na shekara guda, a ba wa matalauta. Sai suka tsawata mata da zafi.”6Yesu ya ce, “Ku ƙyale ta mana. Don me kuke damunta? Ta yi abu mai kyau a gare ni.7Matalauta dai suna tare da ku kullum, za ku kuma iya taimakonsu a duk lokacin da kuke so. Amma ni ba zan kasance da ku kullum ba.8Ta yi abin da ta iya yi. Ta zuba turare a jikina kafin lokaci, don shirin jana’izata.9Gaskiya nake gaya muku, duk inda aka yi wa’azin bishara ko’ina a duniya, za a faɗi abin da ta yi, domin tunawa da ita.”10Sai Yahuda Iskariyot, ɗaya daga cikin Sha Biyun nan, ya je wajen manyan firistoci don yă bashe Yesu a gare su.11Suka yi murna da jin haka, suka yi alkawari za su ba shi kuɗi. Don haka, ya fara neman zarafi yă ba da shi.12A rana ta fari ta Bikin Burodi Marar Yisti, lokacin da akan yanka ɗan ragon hadayar kafara, bisa ga al’ada ta tunawa da Bikin Ƙetarewa, sai almajiran Yesu suka tambaye shi, suka ce, “Ina kake so mu je mu shirya maka wurin da za ka ci Bikin Ƙetarewa?”13Sai ya aiki biyu daga cikin almajiransa ya ce, “Ku shiga cikin birni, za ku sadu da wani ɗauke da tulun ruwa. Ku bi shi.14Gidan da ya shiga, ku gaya wa maigidan cewa, ‘Malam yana tambaya, ina ɗakin baƙina, inda zan ci Bikin Ƙetarewa tare da almajiraina?’15Zai nuna muku wani babban ɗakin sama da aka shirya domin baƙi. Ku yi mana shirin a can.”16Almajiran suka tafi, suka shiga cikin birnin, suka kuwa tarar da kome kamar yadda Yesu ya faɗa musu. Sai suka shirya Bikin Ƙetarewa.17Da yamma ta yi, sai Yesu ya zo tare da Sha Biyun.18Yayinda suke cin abinci a tebur, sai ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, ɗaya daga cikinku zai bashe ni, wani wanda yake ci tare da ni.”19Suka cika da baƙin ciki, da ɗaya-ɗaya suka ce masa, “Tabbatacce, ba ni ba ne, ko?”20Ya ce, “Ɗaya daga cikin Sha Biyun ne, wanda yake ci tare da ni a kwano.21Ɗan Mutum zai tafi kamar yadda yake a rubuce game da shi, amma kaiton mutumin da ya bashe Ɗan Mutum! Zai fi masa, da ba a haife shi ba.”22Yayinda suke cin abinci, sai Yesu ya ɗauki burodi, ya yi godiya, ya kakkarya, ya ba wa almajiransa, yana cewa, “Ku karɓa, wannan jikina ne.”23Sai kuma ya ɗauki kwaf ruwan inabi, ya yi godiya, ya kuma miƙa musu, dukansu suka sha daga ciki.24Sai ya ce musu, “Wannan jinina ne na alkawari, wanda aka zubar da shi saboda mutane da yawa.25Gaskiya nake gaya muku, ‘Ba zan ƙara sha daga ’ya’yan inabi ba, sai ranan nan, da zan sha shi sabo a mulkin Allah.’ ”26Da suka rera waƙa, sai suka fita, suka tafi Dutsen Zaitun.27Yesu ya ce musu, “Dukanku za ku ja da baya ku bar ni, gama yana a rubuce cewa, “ ‘Zan bugi makiyayin tumaki, tumakin kuwa za su warwatse.’28Amma bayan na tashi, zan sha gabanku zuwa Galili.”29Bitrus ya ce, “Ko da duka sun ja da baya suka bar ka, ba zan bar ka ba.”30Yesu ya ce, “Gaskiya nake faɗa maka, yau, tabbatacce, a daren nan, kafin zakara yă yi cara sau biyu kai da kanka za ka yi mūsun sanina sau uku.”31Amma Bitrus ya yi ta nanatawa da ƙarfi ya ce, “Ko da zan mutu tare da kai, ba zan taɓa yin mūsun saninka ba.” Duk sauran ma suka ce haka.32Suka tafi wani wurin da ake kira Getsemane, Yesu ya kuma ce wa almajiransa, “Ku zauna a nan, yayinda ni kuwa in yi addu’a.”33Ya tafi tare da Bitrus, Yaƙub da kuma Yohanna. Sai ya fara baƙin ciki da damuwa ƙwarai.34Sai ya ce musu, “Raina yana cike da baƙin ciki har ma kamar zan mutu. Ku dakata a nan ku yi tsaro.”35Sai ya yi gaba kaɗan, ya fāɗi a ƙasa, ya yi addu’a, ya ce in mai yiwuwa ne, a ɗauke masa wannan sa’a.36Ya ce, “Ya Abba, Uba, kome mai yiwuwa ne a gare ka. Ka ɗauke mini wannan kwaf. Amma ba abin da nake so ba, sai dai abin da kake so.”37Sai ya koma wajen almajiransa, ya same su suna barci. Ya ce wa Bitrus, “Siman, kana barci ne? Ka kāsa yin tsaro na sa’a ɗaya?38Ku yi tsaro, ku kuma yi addu’a, domin kada ku fāɗi cikin jarraba. Ruhu yana so, sai dai jiki raunana ne.”39Ya sāke komawa, ya maimaita addu’ar da ya yi.40Da ya dawo, ya sāke tarar da su suna barci, domin barci ya cika musu ido. Suka rasa abin da za su ce masa.41Da ya koma sau na uku, sai ya ce musu, “Har yanzu kuna barci, kuna hutawa ba? Ya isa! Lokaci ya yi. Duba an ba da Ɗan Mutum a hannun masu zunubi.42Ku tashi! Mu tafi! Ga mai bashe ni ɗin yana zuwa!”43Yana cikin magana ke nan, sai Yahuda, ɗaya daga cikin Sha Biyun ya bayyana. Ya zo tare da taro da suke riƙe da takuba da sanduna. Manyan firistoci da malaman dokoki, da kuma dattawa ne suka turo taron.44Mai bashe shi ɗin ya riga ya shirya alama da su cewa, “Wanda na yi wa sumba, shi ne mutumin, ku kama shi, ku riƙe sosai.”45Nan da nan Yahuda ya je wurin Yesu ya ce, “Rabbi!” Ya kuma yi masa sumba.46Mutanen kuwa suka kama Yesu, suka riƙe shi.47Sai wani cikin waɗanda suke tsattsaye kusa ya zāre takobinsa, ya sare kunnen bawan babban firist.48Yesu ya ce, “Ina jagoran wani tawaye ne da kuka fito da takuba da kuma sanduna domin ku kama ni?49Kowace rana ina tare da ku, ina koyarwa a filin haikali, ba ku kama ni ba. Amma dole a cika Nassi.”50Sai kowa ya yashe shi ya gudu.51Wani saurayin da ba ya sanye da kome sai rigar lilin, yana bin Yesu. Da suka yi ƙoƙarin kama shi,52sai ya gudu ya bar rigarsa, ya gudu tsirara.53Suka kai Yesu wajen babban firist, sai dukan manyan firistoci, dattawa da kuma malaman dokoki suka taru.54Bitrus ya bi shi daga nesa, har cikin filin gidan babban firist. A can, ya zauna tare da masu gadi, yana jin ɗumin wuta.55Manyan firistoci da dukan ’yan Majalisa, suka shiga neman shaidar laifin da za a tabbatar a kan Yesu, domin su kashe shi. Amma ba su sami ko ɗaya ba.56Da yawa suka ba da shaidar ƙarya a kansa, amma shaidarsu ba tă zo ɗaya ba.57Sai waɗansu suka miƙe tsaye, suka ba da wannan shaida ƙarya a kansa, suka ce,58“Mun ji shi ya ce, ‘Zan rushe wannan haikali da mutum ya gina, cikin kwana uku, in sāke gina wani wanda ba ginin mutum ba.’ ”59Duk da haka ma, shaidarsu ba tă zo ɗaya ba.60Sai babban firist ya tashi a gabansu, ya tambayi Yesu ya ce, “Ba za ka amsa ba? Wane shaida ke nan waɗannan mutane suke kawowa a kanka?”61Amma Yesu ya yi shiru, bai kuwa amsa ba. Babban firist ya sāke tambayarsa ya ce, “Kai ne Kiristi, Ɗan Mai Albarka?”62Yesu ya ce, “Ni ne. Za ku kuwa ga Ɗan Mutum yana zaune a hannun dama na Mai Iko, yana kuma zuwa a cikin gizagizan sama.”63Babban firist ya yage tufafinsa, ya yi ce, “Ina dalilin neman waɗansu shaidu kuma?64Kun dai ji saɓon. Me kuka gani?” Duka suka yanke masa hukuncin kisa.65Sai waɗansu suka fara tattofa masa miyau, suka rufe masa idanu, suka bubbuge shi da hannuwansu, suka ce, “Yi annabci!” Masu gadin kuma suka ɗauke shi, suka yi masa duka.66Yayinda Bitrus yake ƙasa a filin gidan, sai wata yarinya, baiwa, ɗaya daga cikin ma’aikatan babban firist, ta zo can.67Da ta ga Bitrus yana jin ɗumi, sai ta dube shi da kyau. Ta ce, “Kai ma kana tare da Yesu, Banazare.”68Amma ya yi mūsu ya ce, “Ban san abin da kike magana ba, balle ma in fahimce ki.” Sai ya fita zuwa zaure.69Da baiwar ta gan shi a can, sai ta sāke gaya wa waɗanda suke tsattsaye a wurin, ta ce, “Wannan mutum yana ɗaya daga cikinsu.”70Sai ya sāke yin musu. Bayan ɗan lokaci kaɗan, sai waɗanda suke tsattsaye kusa suka ce wa Bitrus, “Lalle, kana ɗaya daga cikinsu, gama kai mutumin Galili ne.”71Sai ya fara la’antar kansa, yana rantsuwa musu, yana cewa, “Ban san wannan mutumin da kuke magana a kai ba.”72Nan da nan zakara ya yi cara sau na biyu. Sai Bitrus ya tuna da maganar da Yesu ya yi masa cewa, “Kafin zakara yă yi cara sau biyu, za ka yi mūsun sanina sau uku.” Sai ya fashe da kuka.Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide. Sabon Rai Don Kowa 2020 Markus 14 00:00:00 00:00:00 0.5x 2.0x https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/mark/014.mp3 16 14