× Harshe Turai Rashanci Belarusiyanci Yukreniyanci Yaren mutanen Poland Sabiyanci Bulgaria Slovakiyan Czech Romaniyanci Moldoviyanci Azerbaijan Armeniyanci Jojiyanci Albaniyanci Avar Bashkir Tatar Checheniya Slobaniyanci Kuroshiya Estoniyanci Latvia Lituweniyanci Harshen Hungary Yaren mutanen Finland Yaren mutanen Norway Yaren mutanen Sweden Icelandic Girkanci Macedonia Bajamushe Bavarian Yaren mutanen Holland Danish Welsh Gaelic Irish Faransanci Basque Katalaniyanci Italiyanci Galacian Romani Bosnian Kabardian Amirka ta Arewa Turanci Kudancin Amurka Sifeniyanci Fotigal Guarani Quechuan Aymara Amurka ta Tsakiya Jamaica Nahuatl Kiche Qeqchi Haiti Gabashin Asiya Sinanci Jafananci Yaren Koriya Mongoliyanci Uyghur Hmong Tibetian Kudu maso gabashin Asiya Malesiya Burma Chin Nepali Cebuano Tagalog Kambodiyanci Thai Indonesiyanci Sundanese Vietnam Javanisanci Lao Iban IuMien Kachin Lahu Aceh Balinese Bugis Pampanga Sasak Shan Waray Madurese Kudancin Asiya Hindi Оdia Awadhi Mizo Kannada Malayalam Marathi Gujarati Tamil Telugu Harshen Punjabi Kurukh Assamese Maithili Bengali Urdu Sinhala Dogri Haryanvi Meitei Konkani Santali Sindhi Koya Thado Sanskrit Devanagari Adilabad Gondi Ahirani Balochi Bundeli Chhattisgarhi Garhwali Kangri Kumaoni Mewari Munda Sadri Seraiki Shekhawati Sylheti Bagri Bhilali Bodo Braj Tulu Asiya ta Tsakiya Kirgiziya Uzbek Tajik Turkmen Kazakhstan Karakalpak Gabas ta Tsakiya Baturke Ibrananci Larabci Farisanci Kurdawa Mazanderani Pashto 'Yan Koftik Afirka Afirkaans Xhosa Zulu Ndebele Sotho Amharic Wolaytta Dan Najeriya Mossi Ika Dinka Kabyle Ewe Swahili Maroko Somalian Shona Madagaska Igbo Lingala Baoule Siswati Tsonga Tswana Gambiya Yarbawa Kamba Kinyarwanda Hausa Chewa Luo Makua Dyula Fulfulde Kalenjin Kikuyu Kikwango Kirundi Krio Nigerian Pidgin Oromo Tshiluba Tshivenda Twi Umbundu Lugbara Luguru Pular Gussi Maasai Turkana Moba Nuer Shilluk Tamasheq Makonde Bemba Fon Hadiyya Ibibio Kimbundu Kimiiru Lango Liberian Kreyol Lomwe Mende Morisyen Ndau Nyankole Sena Sidamo Soga Songe Sukuma Tarifit Teso Tiv Zande Dagbani Edo Kituba Nahiyar Australiya New Zealand Papua New Guinea Tsoffin Harsuna Aramaic Latin Esperanto 1 1 1 Sabon Rai Don Kowa 2020 Sabon Rai Don Kowa 2020أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا 2020Littafi Mai Tsarki 19791 1 1 Yoshuwa FarawaFitowaFiristociƘidayaMaimaitawar ShariʼaYoshuwaMahukuntaRut1 Samaʼila2 Samaʼila1 Sarakuna2 Sarakuna1 Tarihi2 TarihiEzraNehemiyaEstaAyubaZaburaKarin MaganaMai HadishiWaƙar WaƙoƙiIshayaIrmiyaMakokiEzekiyelDaniyelHosiyaYowelAmosObadiyaYunanaMikaNahumHabakkukZefaniyaHaggaiZakariyaMalaki--- --- ---MattiyuMarkusLukaYohannaAyyukan ManzanniRomawa1 Korintiyawa2 KorintiyawaGalatiyawaAfisawaFilibbiyawaKolossiyawa1 Tessalonikawa2 Tessalonikawa1 Timoti2 TimotiTitusFilemonIbraniyawaYaƙub1 Bitrus2 Bitrus1 Yohanna2 Yohanna3 YohannaYahudaRuʼuya ta Yohanna1 1 1 10 1234567891011121314151617181920212223241 1 1 : 1 123456789101112131415161718192021222324252627282930313233343536373839404142431 1 1 Sabon Rai Don Kowa 2020 Yoshuwa 10 Adana Bayanan kula 1Adoni-Zedek sarkin Urushalima ya ji cewa Yoshuwa ya ci Ai da yaƙi ya kuma hallaka ta sarai, ya yi wa Ai da sarkinta abin da ya yi wa Yeriko da sarkinta, mutanen Gibeyon kuwa sun yi yarjejjeniya ta salama da Isra’ilawa, suna kuma zama kusa da su.2Shi da mutanensa suka ji tsoron wannan sosai, gama Gibeyon muhimmiyar birni ce, har ma kamar ɗaya daga cikin biranen sarauta, ya ma fi Ai girma, mazanta duka kuwa mayaƙa ne na ƙwarai.3Saboda haka sai Adoni-Zedek sarkin Urushalima ya roƙi Hoham sarkin Hebron, Firam sarkin Yarmut, Yafiya sarkin Lakish da Debir sarki Eglon ya ce,4“Ku zo ku taimake ni in kai wa Gibeyon hari. Domin sun yi yarjejjeniya ta salama da Yoshuwa da Isra’ilawa.”5Sai sarakunan nan biyar na Amoriyawa, sarakunan Urushalima, Hebron, Yarmut, Lakish da Eglon suka haɗa sojojinsu. Suka je dukansu suka yi shirin kai wa Gibeyon hari.6Sai mutanen Gibeyon suka aika zuwa wurin Yoshuwa a sansani a Gilgal, “Kada ka juya wa bayinka baya, ka zo da sauri ka cece mu! Ka taimake mu domin sarakunan Amoriyawa duka daga kan tudu sun haɗa ƙarfinsu tare za su tasar mana.”7Saboda haka Yoshuwa ya tashi da rundunarsa duka, tare da dukan jarumawansa.8Ubangiji ya ce wa Yoshuwa, “Kada ka ji tsoronsu; na ba ka su a hannunka. Ba waninsu da zai iya tsayayya da kai.”9Bayan sun yi tafiya dukan dare daga Gilgal, Yoshuwa ya auko musu ba labari.10Ubangiji ya sa suka ruɗe a gaban Isra’ilawa, Isra’ilawa kuwa suka yi babbar nasara a kansu a Gibeyon. Isra’ilawa suka fafare su a kan hanyar zuwa Bet-Horon suka karkashe su duka har zuwa Azeka da Makkeda.11Suna guje wa Isra’ilawa suna gangarawa a kan hanyar Bet-Horon har zuwa Azeka, sai Ubangiji ya turo manyan duwatsu daga sararin sama suka karkashe su, waɗanda manyan duwatsun suka kashe sun fi waɗanda Isra’ilawa suka kashe da takobi.12A ranar da Ubangiji ya ba da Amoriyawa a hannun Isra’ilawa, Yoshuwa ya ce wa Ubangiji a gaban Isra’ilawa, “Ke rana, ki tsaya cik a Gibeyon Kai wata, ka je Kwarin Aiyalon.”13Sai rana ta tsaya cik, wata kuma ya tsaya, har sai da al’ummar ta ɗauki fansa a kan abokan gābanta, kamar yadda aka rubuta a cikin littafin Yashar. Rana ta tsaya a sararin sama, ba tă fāɗi ba har kusan yini guda.14Ba a taɓa ganin abu haka ba ko dā can, ranar da Ubangiji ya saurari mutum. Ba shakka Ubangiji yana yaƙi domin Isra’ilawa.15Sai Yoshuwa ya koma sansanin Gilgal tare da dukan Isra’ilawa.16Sarakunan guda biyar suka gudu, suka ɓuya a cikin kogo a Makkeda.17Lokacin da aka gaya wa Yoshuwa cewa an sami sarakunan nan biyar a ɓoye a cikin kogo a Makkeda.18Sai ya ce, “Ku mirgina manyan duwatsu ku rufe bakin kogon, sai ku sa waɗannan mutane su yi tsaron kogon.19Amma kada ku tsaya a can! Ku fafari abokan gābanku, ku kai musu hari ta baya, kada ku bari su kai biranensu, gama Ubangiji Allahnku ya ba da su a hannunku.”20Saboda haka Yoshuwa da Isra’ilawa suka hallaka su da yawa ƙwarai, amma ’yan kaɗan ɗin da suka rage suka tsere zuwa cikin biranensu masu kāriya.21Dukan rundunar kuma suka dawo sansanin Makkeda tare da Yoshuwa, ba abin da ya same su. Ba wanda ya sāke tsokanar Isra’ilawa.22Yoshuwa ya ce, “Ku buɗe bakin kogon ku kawo mini sarakunan nan guda biyar.”23Sai suka kawo sarakunan biyar daga cikin kogo; sarakunan Urushalima, Hebron, Yarmut, Lakish da Eglon.24Sa’ad da aka kawo sarakunan nan wurin Yoshuwa, ya kira dukan Isra’ilawa ya ce wa shugabannin rundunoni waɗanda suke tare da shi, “Ku zo nan ku taka wuyan sarakunan nan.” Sai suka zo suka taka wuyansu.25Yoshuwa ya ce musu, “Kada ku ji tsoro, ko kuwa ku razana, amma ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali. Haka Ubangiji zai yi da duk abokan gāban da za ku yi yaƙi da su.”26Sai Yoshuwa ya karkashe waɗannan sarakuna guda biyar, ya kuma rataye kowannensu a bisa itace inda jikunansu suka kasance har yamma.27Da yamma Yoshuwa ya ba da umarni a sauko da su daga itatuwan a jefa su cikin kogon da suka ɓuya. Aka sa manyan duwatsu aka rufe bakin kogon, suna a can har wa yau.28A ranan nan Yoshuwa ya ci Makkeda da yaƙi. Ya karkashe mutanen tare da sarkinta. Bai bar wani da rai ba. Ya yi wa sarkin Makkeda yadda ya yi wa sarkin Yeriko.29Sai Yoshuwa da dukan Isra’ilawa suka tashi daga Makkeda zuwa Libna, suka kai mata hari.30Ubangiji kuma ya ba da ƙasar da sarkinta a hannun Yoshuwa. Yoshuwa ya karkashe kowa ya hallaka birnin, bai bar wani da rai ba. Ya kuma yi wa sarkin yadda ya yi wa sarkin Yeriko.31Sai Yoshuwa da dukan Isra’ilawa suka tashi daga Libna zuwa Lakish; suka yi shiri suka kai mata hari.32Ubangiji ya ba da Lakish a hannun Isra’ilawa, a rana ta biyu kuwa Yoshuwa ya ci nasara a kansu. Ya karkashe duk mutanen birnin ya kuma hallaka birnin, kamar yadda ya yi a Libna.33Horam sarkin Gezer kuwa ya zo don yă taimaki Lakish, amma Yoshuwa ya haɗa duk da shi da rundunarsa ya ci su da yaƙi, har bai bar waninsu da rai ba.34Yoshuwa kuwa da dukan Isra’ilawa suka tashi daga Lakish zuwa Eglon; suka yi shiri suka kai mata hari.35A ranan nan suka ci ƙasar da yaƙi, suka buge ta, suka karkashe kowa da takobi kamar dai yadda suka yi a Lakish.36Sai Yoshuwa da dukan Isra’ilawa suka tashi daga Eglon zuwa Hebron suka kai hari a can.37Suka ci birnin da yaƙi, suka karkashe mazaunanta, da sarkin, har da ƙauyukan, ba wanda ya tsira kamar yadda ya yi wa Eglon. Ya hallakar da ita sarai duk da kowane mutum da yake cikinta.38Yoshuwa da Isra’ilawa duka suka juya suka kai wa Debir hari,39suka hallaka birnin, da sarkinta da ƙauyukanta, suka karkashe dukan mazaunan wurin, ba su bar wani da rai ba. Suka yi wa Debir da sarkinta yadda suka yi wa Libna da sarkinta da kuma Hebron.40Yoshuwa ya cinye yankin duka da yaƙi, haɗe da na kan tudu, da Negeb, da kwarin yamma, da filayen cikin duwatsu tare da sarakunansu duka. Bai bar wani da rai ba, ya kashe duk wani mai numfashi, yadda Ubangiji, Allah na Isra’ilawa ya umarta.41Yoshuwa ya ci su da yaƙi daga Kadesh Barneya zuwa Gaza, da kuma daga dukan yankin Goshen zuwa Gibeyon.42Yoshuwa kuwa ya cinye sarakunan nan duka da ƙasashensu gaba ɗaya gama Ubangiji, Allah na Isra’ila ne ya yi yaƙi domin Isra’ilawa.43Yoshuwa kuwa ya dawo da dukan Isra’ilawa zuwa sansani a Gilgal.Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Sabon Rai Don Kowa 2020 Yoshuwa 10 00:00:00 00:00:00 0.5x 2.0x https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/joshua/010.mp3 24 10