× Harshe Turai Rashanci Belarusiyanci Yukreniyanci Yaren mutanen Poland Sabiyanci Bulgaria Slovakiyan Czech Romaniyanci Moldoviyanci Azerbaijan Armeniyanci Jojiyanci Albaniyanci Avar Bashkir Tatar Checheniya Slobaniyanci Kuroshiya Estoniyanci Latvia Lituweniyanci Harshen Hungary Yaren mutanen Finland Yaren mutanen Norway Yaren mutanen Sweden Icelandic Girkanci Macedonia Bajamushe Bavarian Yaren mutanen Holland Danish Welsh Gaelic Irish Faransanci Basque Katalaniyanci Italiyanci Galacian Romani Bosnian Kabardian Amirka ta Arewa Turanci Kudancin Amurka Sifeniyanci Fotigal Guarani Quechuan Aymara Amurka ta Tsakiya Jamaica Nahuatl Kiche Qeqchi Haiti Gabashin Asiya Sinanci Jafananci Yaren Koriya Mongoliyanci Uyghur Hmong Tibetian Kudu maso gabashin Asiya Malesiya Burma Chin Nepali Cebuano Tagalog Kambodiyanci Thai Indonesiyanci Sundanese Vietnam Javanisanci Lao Iban IuMien Kachin Lahu Aceh Balinese Bugis Pampanga Sasak Shan Waray Kudancin Asiya Hindi Оdia Awadhi Mizo Kannada Malayalam Marathi Gujarati Tamil Telugu Harshen Punjabi Kurukh Assamese Maithili Bengali Urdu Sinhala Dogri Haryanvi Meitei Konkani Santali Sindhi Koya Thado Sanskrit Devanagari Adilabad Gondi Ahirani Balochi Bundeli Chhattisgarhi Garhwali Kangri Kumaoni Mewari Munda Sadri Seraiki Shekhawati Sylheti Bagri Bhilali Bodo Braj Tulu Asiya ta Tsakiya Kirgiziya Uzbek Tajik Turkmen Kazakhstan Karakalpak Gabas ta Tsakiya Baturke Ibrananci Larabci Farisanci Kurdawa Mazanderani Pashto 'Yan Koftik Afirka Afirkaans Xhosa Zulu Ndebele Sotho Amharic Wolaytta Dan Najeriya Mossi Ika Dinka Kabyle Ewe Swahili Maroko Somalian Shona Madagaska Igbo Lingala Baoule Siswati Tsonga Tswana Gambiya Yarbawa Kamba Kinyarwanda Hausa Chewa Luo Makua Dyula Fulfulde Kalenjin Kikuyu Kikwango Kirundi Krio Nigerian Pidgin Oromo Tshiluba Tshivenda Twi Umbundu Lugbara Luguru Pular Gussi Maasai Turkana Moba Nuer Shilluk Tamasheq Makonde Bemba Fon Hadiyya Ibibio Kimbundu Kimiiru Lango Liberian Kreyol Lomwe Mende Morisyen Ndau Nyankole Sena Sidamo Soga Songe Sukuma Tarifit Teso Tiv Zande Dagbani Edo Kituba Nahiyar Australiya New Zealand Papua New Guinea Tsoffin Harsuna Aramaic Latin Esperanto 1 1 1 Sabon Rai Don Kowa 2020 Sabon Rai Don Kowa 2020أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا 2020Littafi Mai Tsarki 19791 1 1 Yoshuwa FarawaFitowaFiristociƘidayaMaimaitawar ShariʼaYoshuwaMahukuntaRut1 Samaʼila2 Samaʼila1 Sarakuna2 Sarakuna1 Tarihi2 TarihiEzraNehemiyaEstaAyubaZaburaKarin MaganaMai HadishiWaƙar WaƙoƙiIshayaIrmiyaMakokiEzekiyelDaniyelHosiyaYowelAmosObadiyaYunanaMikaNahumHabakkukZefaniyaHaggaiZakariyaMalaki--- --- ---MattiyuMarkusLukaYohannaAyyukan ManzanniRomawa1 Korintiyawa2 KorintiyawaGalatiyawaAfisawaFilibbiyawaKolossiyawa1 Tessalonikawa2 Tessalonikawa1 Timoti2 TimotiTitusFilemonIbraniyawaYaƙub1 Bitrus2 Bitrus1 Yohanna2 Yohanna3 YohannaYahudaRuʼuya ta Yohanna1 1 1 15 1234567891011121314151617181920212223241 1 1 : 1 1234567891011121314151617181920212223242526272829303132333435363738394041424344454647484950515253545556575859606162631 1 1 Sabon Rai Don Kowa 2020 Yoshuwa 15 Adana Bayanan kula 1An raba wa kabilar Yahuda gādonsu ta wurin yin ƙuri’a, bisa ga iyalansu, rabon ya kai har zuwa sashen Edom, zuwa Jejin Zin can kurewar kudu.2Iyakarsu a kudanci ta tashi tun daga kurewar kudu na Tekun Gishiri,3zuwa kudancin Hanyar Kunama, ta ci gaba har zuwa Zin, zuwa kudancin Kadesh Barneya. Sa’an nan ta kurɗa zuwa Hezron har zuwa Addar, ta kuma karkata zuwa Karka.4Sai ta wuce zuwa Azmon ta haɗu da Rafin Masar, ta ƙarasa a Bahar Rum. Wannan shi ne iyakarsu ta kudu.5Iyakarsu ta gabas kuwa ita ce Tekun Gishiri wadda ta zarce har zuwa gaɓar Urdun. Iyakarsu ta arewa ta fara ne daga Tekun Gishiri a bakin Urdun,6wajen Bet-Hogla ta wuce har zuwa arewancin Bet-Araba, zuwa Dutsen Bohan ɗan Ruben.7Sai iyakar ta haura zuwa Debir daga Kwarin Akor ta juya arewa da Gilgal, wadda take fuskantar hawan Adummim a kudancin kwari, ta ci gaba zuwa ruwan En Shemesh, ta ɓullo ta En Rogel.8Sai kuma ta gangara zuwa Kwarin Ben Hinnom a gangaren kudancin birnin Yebusiyawa (wato, Urushalima). Daga can ta haura zuwa kan tudun a yammancin Kwarin Hinnom, a arewancin ƙarshen Kwarin Refayim.9Daga kan tudun, iyakar ta nufi maɓulɓular ruwa na Neftowa, ta ɓullo a garuruwan da suke a Dutsen Efron, ta gangara zuwa Ba’ala (wato, Kiriyat Yeyarim).10Sa’an nan ta karkata yamma daga Ba’ala zuwa Dutsen Seyir, ta wuce ta gangaren Dutsen Yeyarim (wato, Kesalon), ta ci gaba zuwa Bet-Shemesh, ta bi zuwa Timna.11Ta wuce zuwa gangaren arewancin Ekron, ta juya zuwa Shikkeron, ta wuce zuwa Dutsen Ba’ala, ta kai Yabneyel, iyakarta ta ƙare a teku.12Bakin Bahar Rum nan ne iyakar yammanci. Wannan ita ce iyakar da ta kewaye jama’ar Yahuda bisa ga iyalansu.13Yoshuwa ya ba Kaleb ɗan Yefunne wuri a Yahuda, Kiriyat Arba, wato, Hebron, bisa ga umarnin Ubangiji. (Arba shi ne mahaifin Anak.)14Daga can sai Kaleb ya kori ’ya’yan Anak, maza su uku daga Hebron, wato, Sheshai, Ahiman da Talmai.15Daga can ya nufi Debir ya yi yaƙi da mutanen da suke zama a can (Dā sunan Debir, Kiriyat Sefer ne).16Kaleb ya ce, “Zan ba da ’yata Aksa aure ga wanda zai ci Kiriyat Sefer da yaƙi.”17Otniyel ɗan Kenaz, ɗan’uwan Kaleb, ya ci Kiriyat Sefer da yaƙi; saboda haka Kaleb ya ba wa Aksa ’yarsa, ya kuwa aure ta.18Wata rana da ta zo wurin Otniyel, sai ya zuga ta ta roƙi mahaifinta fili. Da ta sauka daga kan jakinta sai Kaleb ya tambaye ta ya ce, “Me kike so in yi miki?”19Ta amsa ta ce, “Ka yi mini alheri na musamman, tun da ka ba ni wuri a Negeb, ina roƙonka, ka ba ni maɓulɓulan ruwa.” Kaleb kuwa ya ba ta maɓulɓulan ruwa na tuddai da na kwari.20Wannan shi ne gādon kabilar Yahuda bisa ga iyalansu.21Garuruwan kabilar Yahuda da suke kudu cikin Negeb zuwa iyakar Edom su ne. Kabzeyel, Eder, Yagur,22Kina, Dimona, Adada,23Kedesh, Hazor, Itnan,24Zif, Telem, Beyalot,25Hazor-Hadatta, Keriyot Hezron (wato, Hazor),26Amam, Shema, Molada,27Hazar Gadda, Heshmon, Bet-Felet,28Hazar Shuwal, Beyersheba, Biziyotiya,29Ba’ala, Iyim, Ezem,30Eltolad, Kesil, Horma,31Ziklag, Madmanna, Sansanna,32Lebayot, Shilhim, Ayin, Rimmon, jimillarsu, garuruwa da ƙauyukansu duka ashirin da tara ne.33Biranen da suke a filayen kwari su ne, Eshtawol, Zora; Ashna,34Zanowa, En Gannim, Taffuwa, Enam,35Yarmut, Adullam, Soko, Azeka,36Sha’arayim, Aditayim, Gedera (Gederotayim ke nan). Garuruwa goma sha huɗu ke nan da ƙauyukansu.37Zenan, Hadasha, Migdal Gad,38Dileyan, Mizfa, Yokteyel,39Lakish, Bozkat, Eglon,40Kabbon, Lahman, Kitlish,41Gederot, Bet-Dagon, Na’ama, Makkeda, garuruwa goma sha shida ke nan da ƙauyukansu.42Libna, Eter, Ashan,43Yefta, Ashna, Nezib,44Keyila, Akzib, Maresha, garuruwa tara ke nan da ƙauyukansu.45Ekron da ƙauyukan da suke kewaye da ita;46yammancin Ekron da dukan garuruwa da ƙauyukan da suke kusa da Ashdod.47Ashdod da garuruwa da kuma ƙauyukan da suke kewaye da ita, Gaza da garuruwanta da ƙauyukanta har zuwa Rafin Masar da kuma Bahar Rum.48Birane na cikin ƙasar tuddai kuwa, su ne, Shamir, Yattir, Soko,49Danna, Kiriyat Sanna (wato, Debir),50Anab, Eshtemo, Anim,51Goshen, Holon, Gilo, garuruwa goma sha ɗaya ke nan da ƙauyukansu.52Arab, Duma, Eshan,53Yanum, Bet-Taffuwa, Afeka,54Humta, Kiriyat Arba (wato, Hebron) da Ziyor, garuruwa tara ke nan da ƙauyukansu.55Mawon, Karmel, Zif, Yutta56Yezireyel, Yokdeyam, Zanowa,57Kayin, Gibeya, Timna, garuruwa goma ke nan da ƙauyukansu.58Halhul, Bet-Zur, Gedor,59Ma’arat, Bet-Anot, Eltekon, garuruwa shida ke nan da ƙauyukansu.60Kiriyat Ba’al (wato, Kiriyat Yeyarim) da Rabba, garuruwa biyu ke nan da ƙauyukansu.61Biranen da suke a jeji kuwa su ne, Bet-Araba, Middin, Sekaka,62Nibshan, Birnin gishiri da En Gedi, garuruwa shida ke nan da ƙauyukansu.63Kabilar Yahuda kuwa ba su iya korar Yebusiyawa waɗanda suke zama cikin Urushalima ba; har wa yau Yebusiyawa suna nan zaune tare da mutanen Yahuda.Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Sabon Rai Don Kowa 2020 Yoshuwa 15 00:00:00 00:00:00 0.5x 2.0x https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/joshua/015.mp3 24 15