× Harshe Turai Rashanci Belarusiyanci Yukreniyanci Yaren mutanen Poland Sabiyanci Bulgaria Slovakiyan Czech Romaniyanci Moldoviyanci Azerbaijan Armeniyanci Jojiyanci Albaniyanci Avar Bashkir Tatar Checheniya Slobaniyanci Kuroshiya Estoniyanci Latvia Lituweniyanci Harshen Hungary Yaren mutanen Finland Yaren mutanen Norway Yaren mutanen Sweden Icelandic Girkanci Macedonia Bajamushe Bavarian Yaren mutanen Holland Danish Welsh Gaelic Irish Faransanci Basque Katalaniyanci Italiyanci Galacian Romani Amirka ta Arewa Turanci Kudancin Amurka Sifeniyanci Fotigal Guarani Quechuan Aymara Amurka ta Tsakiya Jamaica Nahuatl Kiche Qeqchi Haiti Gabashin Asiya Sinanci Jafananci Yaren Koriya Mongoliyanci Uyghur Hmong Kudu maso gabashin Asiya Malesiya Burma Chin Nepali Cebuano Tagalog Kambodiyanci Thai Indonesiyanci Vietnam Javanisanci Lao Iban IuMien Kachin Lahu Kudancin Asiya Hindi Оdia Awadhi Mizo Kannada Malayalam Marathi Gujarati Tamil Telugu Harshen Punjabi Kurukh Assamese Maithili Bengali Urdu Sinhala Dogri Haryanvi Meitei Konkani Santali Sindhi Koya Thado Sanskrit Devanagari Asiya ta Tsakiya Kirgiziya Uzbek Tajik Turkmen Kazakhstan Karakalpak Gabas ta Tsakiya Baturke Ibrananci Larabci Farisanci Kurdawa Pashto 'Yan Koftik Afirka Afirkaans Xhosa Zulu Ndebele Sotho Amharic Wolaytta Dan Najeriya Mossi Ika Dinka Kabyle Ewe Swahili Maroko Somalian Shona Madagaska Igbo Lingala Baoule Siswati Tsonga Tswana Gambiya Yarbawa Kamba Kinyarwanda Hausa Chewa Luo Makua Dyula Fulfulde Kalenjin Kikuyu Kikwango Kirundi Krio Nigerian Pidgin Oromo Tshiluba Tshivenda Twi Umbundu Lugbara Luguru Pular Gussi Maasai Turkana Moba Nuer Shilluk Tamasheq Makonde Nahiyar Australiya New Zealand Papua New Guinea Tsoffin Harsuna Aramaic Latin Esperanto 1 1 1 2020 202020101 1 1 Yoshuwa FarawaFitowaFiristociƘidayaMaimaitawar ShariʼaYoshuwaMahukuntaRut1 Samaʼila2 Samaʼila1 Sarakuna2 Sarakuna1 Tarihi2 TarihiEzraNehemiyaEstaAyubaZaburaKarin MaganaMai HadishiWaƙar WaƙoƙiIshayaIrmiyaMakokiEzekiyelDaniyelHosiyaYowelAmosObadiyaYunanaMikaNahumHabakkukZefaniyaHaggaiZakariyaMalaki--- --- ---MattiyuMarkusLukaYohannaAyyukan ManzanniRomawa1 Korintiyawa2 KorintiyawaGalatiyawaAfisawaFilibbiyawaKolossiyawa1 Tessalonikawa2 Tessalonikawa1 Timoti2 TimotiTitusFilemonIbraniyawaYaƙub1 Bitrus2 Bitrus1 Yohanna2 Yohanna3 YohannaYahudaRuʼuya ta Yohanna1 1 1 19 1234567891011121314151617181920212223241 1 1 : 1 1234567891011121314151617181920212223242526272829303132333435363738394041424344454647484950511 1 1 Sabon Rai Don Kowa 2020 Yoshuwa 19 Adana Bayanan kula 1Ƙuri’a ta biyu ta fāɗa a kan kabilar Simeyon, bisa ga iyalansu. Ƙasarsu ta gādo tana cikin yankin Yahuda.2Waɗannan su ne wuraren da suka gāda. Beyersheba (ko Sheba), Molada,3Hazar Shuwal, Bilha, Ezem,4Eltolad, Betul, Horma,5Ziklag, Bet-Markabot, Hazar-Susa,6Bet-Lebayot da Sharuhen, garuruwa goma sha uku ke nan da ƙauyukansu.7Akwai kuma Ayin, Rimmon, Eter da Ashan, garuruwa huɗu ke nan da ƙauyukansu,8da kuma dukan ƙauyukan da suke kewaye da garuruwan nan har zuwa Rama na Negeb (wato, Ba’alat-Beyer). Wannan shi ne gādon kabilar Simeyon bisa ga iyalansu.9Daga cikin gādon mutanen Yahuda ne aka fitar da gādon kabilar Simeyon, bisa ga iyalansu, domin rabon da kabilar Yahuda suka samu ya fi ƙarfin abin da suke bukata. Saboda haka kabilar gādon Simeyon yana cikin harabar Yahuda.10Ƙuri’a ta uku ta fāɗa a kan Zebulun bisa ga iyalansu. Iyakar ƙasarsu ta gādo ta kai har Sarid.11Ta nufi yamma zuwa Marala, ta taɓa Dabbeshet, ta wuce zuwa rafin da yake kusa da Yokneyam.12Daga Sarid, ta juya gabas zuwa harabar Kislot Tabor, ta kuma wuce zuwa Daberat har zuwa Yafiya.13Sa’an nan ta ci gaba, ta yi gabas zuwa Gat-Hefer da Et Kazin; ta ɓulla a Rimmon, ta juya zuwa Neya.14A can ne iyakar ta kewaya zuwa Hannaton, sa’an nan ta ƙarasa a Kwarin Ifta El.15Zebulun ta ƙunshi garuruwa goma sha biyu da ƙauyukansu. Garuruwan sun haɗa da Kattat, Nahalal, Shimron, Idala da Betlehem.16Garuruwan nan da ƙauyukansu su ne gādon da kabilar Zebulun ta samu, bisa ga iyalansu.17Ƙuri’a ta huɗu ta fāɗa a kan kabilar Issakar, bisa ga iyalansu.18Ƙasarsu gādonsu ta haɗa da, Yezireyel, Kessulot, Shunem,19Hafarayim, Anaharat,20Rabbat, Kishiyon, Ebez,21Remet, En Gannim, En Hadda da Bet-Fazez.22Iyakar ta taɓa Tabor Shahazuma da Bet-Shemesh ta kuma ƙarasa a Urdun. Duka-duka garuruwa goma sha shida ke nan da ƙauyukansu.23Waɗannan garuruwa da ƙauyukansu su ne rabon da kabilar Issakar ta samu, bisa ga iyalansu.24Ƙuri’a ta biyar ta fāɗa a kan kabilar Asher, bisa ga iyalansu.25Ƙasarsu gādonsu ta haɗa da, Helkat, Hali, Beten, Akshaf,26Allammelek, Amad da Mishal. A arewanci kuma iyakar ta taɓa Karmel da Shihor Libnat.27Sai ta yi gabas zuwa Bet-Dagon, ta taɓa Zebulun da kuma Kwarin Ifta El, ta wuce arewa zuwa Bet-Emek da Neyiyel, ta wuce Kabul a hagu,28ta kai Abdon, Rehob, Hammon da Kana, har zuwa Sidon Babba.29Daga nan iyakar ta juya baya zuwa Rama, ta bi ta birnin nan mai katanga na Taya, ta juya ta nufi Hosa, sa’an nan ta ɓulla ta Bahar Rum cikin yankin Akzib,30Umma, Afek da Rehob. Garuruwa ashirin da biyu ke nan da ƙauyukansu.31Garuruwan nan da ƙauyukansu su ne gādon da kabilar Asher ta samu bisa ga iyalansu.32Ƙuri’a ta shida ta fāɗa a kan kabilar Naftali, bisa ga iyalansu.33Iyakarsu ta kama daga Helef, daga babban itacen Mamre nan da yake a Za’anannim, ta wuce Adami Nekeb da Yabneyel zuwa Lakkum, ta kuma ƙarasa a Urdun.34Iyakar kuma ta juya yamma ta cikin Aznot-Tabo ta ɓulla a Hukkok. Ta taɓa Zebulun a kudu, Asher a yamma, da kuma Urdun a gabas.35Biranen da suke da katanga su ne Ziddim, Zer, Hammat, Rakkat, Kinneret,36Adama, Rama, Hazor,37Kedesh, Edireyi, En Hazor,38Yiron, Migdal El, Horem, Bet-Anat da Bet-Shemesh. Garuruwa goma sha tara ke nan da ƙauyukansu.39Waɗannan garuruwa da ƙauyukansu su ne rabon da kabilar Naftali ta samu, bisa ga iyalansu.40Ƙuri’a ta bakwai ta fāɗa a kan kabilar Dan, bisa ga iyalansu.41Ƙasarsu ta gādo ta haɗa da, Zora, Eshtawol, Ir Shemesh,42Shalim, Aiyalon, Itla,43Elon, Timna, Ekron,44Elteke, Gibbeton, Ba’alat,45Yehud, Bene-Berak, Gat-Rimmon,46Me Yarkon da Rakkon tare da sashen da yake fuskantar Yaffa.47(Amma ya zama wa mutanen kabilar Dan da wahala su mallaki ƙasar da aka ba su gādo, saboda haka sai suka nufi Leshem suka ci su da yaƙi, suka karkashe mutanen wurin, suka mallake ta, suka zauna a ciki. Suka kuma sa wa Leshem, sunan kakansu, wato, Dan.)48Waɗannan garuruwa da ƙauyukansu su ne gādon kabilar Dan, bisa ga iyalansu.49Sa’ad da aka gama raba gādon ƙasar bisa ga ƙuri’a. Sai Isra’ilawa suka ba Yoshuwa ɗan Nun nasa rabo a cikinsu,50yadda Ubangiji ya umarta, suka ba shi garin da ya ce a ba shi, Timnat Serad a ƙasar tudu ta Efraim. Ya kuma gina garin ya zauna a can.51Waɗannan su ne rabe-raben gādon da Eleyazar firist, Yoshuwa ɗan Nun, da kuma shugabannin kabilan iyalan Isra’ila suka rarraba ta hanyar jefa ƙuri’a a Shilo a gaban Ubangiji a ƙofar Tentin Sujada. Da haka suka yi suka gama rarraba ƙasar.Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide. Sabon Rai Don Kowa 2020 Yoshuwa 19 00:00:00 00:00:00 0.5x 2.0x https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/joshua/019.mp3 24 19