× Harshe Turai Rashanci Belarusiyanci Yukreniyanci Yaren mutanen Poland Sabiyanci Bulgaria Slovakiyan Czech Romaniyanci Moldoviyanci Azerbaijan Armeniyanci Jojiyanci Albaniyanci Avar Bashkir Tatar Checheniya Slobaniyanci Kuroshiya Estoniyanci Latvia Lituweniyanci Harshen Hungary Yaren mutanen Finland Yaren mutanen Norway Yaren mutanen Sweden Icelandic Girkanci Macedonia Bajamushe Bavarian Yaren mutanen Holland Danish Welsh Gaelic Irish Faransanci Basque Katalaniyanci Italiyanci Galacian Romani Bosnian Amirka ta Arewa Turanci Kudancin Amurka Sifeniyanci Fotigal Guarani Quechuan Aymara Amurka ta Tsakiya Jamaica Nahuatl Kiche Qeqchi Haiti Gabashin Asiya Sinanci Jafananci Yaren Koriya Mongoliyanci Uyghur Hmong Kudu maso gabashin Asiya Malesiya Burma Chin Nepali Cebuano Tagalog Kambodiyanci Thai Indonesiyanci Vietnam Javanisanci Lao Iban IuMien Kachin Lahu Aceh Balinese Bugis Pampanga Sasak Shan Waray Kudancin Asiya Hindi Оdia Awadhi Mizo Kannada Malayalam Marathi Gujarati Tamil Telugu Harshen Punjabi Kurukh Assamese Maithili Bengali Urdu Sinhala Dogri Haryanvi Meitei Konkani Santali Sindhi Koya Thado Sanskrit Devanagari Adilabad Gondi Ahirani Balochi Bundeli Chhattisgarhi Garhwali Kangri Kumaoni Mewari Munda Sadri Seraiki Shekhawati Sylheti Asiya ta Tsakiya Kirgiziya Uzbek Tajik Turkmen Kazakhstan Karakalpak Gabas ta Tsakiya Baturke Ibrananci Larabci Farisanci Kurdawa Pashto 'Yan Koftik Afirka Afirkaans Xhosa Zulu Ndebele Sotho Amharic Wolaytta Dan Najeriya Mossi Ika Dinka Kabyle Ewe Swahili Maroko Somalian Shona Madagaska Igbo Lingala Baoule Siswati Tsonga Tswana Gambiya Yarbawa Kamba Kinyarwanda Hausa Chewa Luo Makua Dyula Fulfulde Kalenjin Kikuyu Kikwango Kirundi Krio Nigerian Pidgin Oromo Tshiluba Tshivenda Twi Umbundu Lugbara Luguru Pular Gussi Maasai Turkana Moba Nuer Shilluk Tamasheq Makonde Bemba Fon Hadiyya Ibibio Kimbundu Kimiiru Lango Liberian Kreyol Lomwe Mende Morisyen Ndau Nyankole Sena Sidamo Soga Songe Sukuma Tarifit Teso Tiv Zande Nahiyar Australiya New Zealand Papua New Guinea Tsoffin Harsuna Aramaic Latin Esperanto 1 1 1 2020 202020101 1 1 1 Samaʼila FarawaFitowaFiristociƘidayaMaimaitawar ShariʼaYoshuwaMahukuntaRut1 Samaʼila2 Samaʼila1 Sarakuna2 Sarakuna1 Tarihi2 TarihiEzraNehemiyaEstaAyubaZaburaKarin MaganaMai HadishiWaƙar WaƙoƙiIshayaIrmiyaMakokiEzekiyelDaniyelHosiyaYowelAmosObadiyaYunanaMikaNahumHabakkukZefaniyaHaggaiZakariyaMalaki--- --- ---MattiyuMarkusLukaYohannaAyyukan ManzanniRomawa1 Korintiyawa2 KorintiyawaGalatiyawaAfisawaFilibbiyawaKolossiyawa1 Tessalonikawa2 Tessalonikawa1 Timoti2 TimotiTitusFilemonIbraniyawaYaƙub1 Bitrus2 Bitrus1 Yohanna2 Yohanna3 YohannaYahudaRuʼuya ta Yohanna1 1 1 2 123456789101112131415161718192021222324252627282930311 1 1 : 1 1234567891011121314151617181920212223242526272829303132333435361 1 1 Sabon Rai Don Kowa 2020 1 Samaʼila 2 Adana Bayanan kula 1Sai Hannatu ta yi addu’a ta ce, “Zuciyata tana farin ciki a cikin Ubangiji; a cikin Ubangiji an sa ina jin daɗi ƙwarai. Na buɗe bakina na yi wa abokan gābana dariya. Kai! Ina murna domin ka cece ni!2“Babu wani mai tsarki kamar Ubangiji babu wani, in ban da kai; babu wani dutse kamar Allahnmu.3“Ka daina maganganu na girman kai ka kuma daina faɗin kalmomin ɗaga kai; gama Ubangiji Allah ne masani daga gare shi kuma ana auna ayyuka.4“An kakkarya bakkuna masu yaƙi, amma su da ka raunana an ba su makaman ƙarfi.5Waɗanda a dā suna da abinci sosai; yanzu suna ƙodago saboda abinci, masu fama da yunwa kuwa sun daina jin yunwa. Ita da take bakararriya, ta haifi ’ya’ya bakwai amma ita da tana da ’ya’ya da yawa, ta zama mai baƙin ciki.6“Ubangiji ne ke kawo mutuwa, yă kuma rayar yana kai ga kabari, yă kuma tā da.7Ubangiji ne yakan aika da talauci da kuma dukiya; yakan ƙasƙantar yă kuma ɗaukaka.8Yakan tā da matalauci daga ƙura, yă kuma ɗaga mai bukata daga tarin toka; yă zaunar da su tare da ’ya’yan sarki; yă kuma sa su gāji mulki na ɗaukaka. “Harsashin duniya na Ubangiji ne; a bisansu ne ya kafa duniya.9Zai kiyaye ƙafafun masu tsarki, amma mugaye za su lalace cikin duhu. “Ba bisa ga ƙarfi mutum ba ne mutum ke nasara;10waɗanda suke gāba da Ubangiji za su hallaka. Zai yi musu tsawa daga sama, Ubangiji zai hukunta dukan duniya. “Zai ba wa sarkinsa ƙarfi, yă kuma ɗaukaka shafaffensa.”11Sa’an nan, Elkana ya koma gida a Rama amma yaron ya yi hidima a gaban Ubangiji a ƙarƙashin Eli firist.12’Ya’yan Eli firist, mutane ne masu mugunta. Ba su ɗauki Ubangiji a bakin kome ba.13Al’ada ce ga firistoci da mutane cewa in wani ya miƙa hadaya, yayinda nama yake kan wuta, bawan firist zai zo da babban cokali mai yatsu,14zai soka cokali mai yatsun a tukunyar, ko butar da ake dafan naman. Duk abin da cokali mai yatsun ya cako daga tukunyar, ya zama na firist. Haka aka yi ta yi wa Isra’ilawan da suka zo miƙa hadaya a Shilo.15Tun ma kafin a ƙona kitse, bawan firist yakan zo yă ce wa mutumin da yake miƙa hadaya, “Ka ba wa firist nama domin yă gasa, ba zai karɓi dafaffen nama daga wurinka ba, sai ɗanye.”16In kuwa mutumin ya ce masa, “Bari kitse yă ƙone tukuna, sa’an nan ka ɗiba duk abin da kake so.” Sai bawan yă ce masa, “A’a, ka ba ni yanzu, in ka ƙi kuwa zan ɗiba ƙarfi da yaji.”17Wannan zunubin samarin ya yi muni ƙwarai a gaban Ubangiji, domin sun wulaƙanta hadayar Ubangiji, ƙwarai da gaske.18Amma yaron nan Sama’ila, yana hidima a gaban Ubangiji yana sanye da efod na lilin.19Kowace shekara mahaifiyarsa takan ɗinka ’yar taguwa ta kai masa sa’ad da ita da mijinta suka je miƙa hadaya ta shekara.20Eli yakan sa wa Elkana da matarsa albarka, yă ce, Ubangiji yă ba ka waɗansu ’ya’ya ta wurin matan nan, maimakon wanda ta roƙa daga Ubangiji, ta kuma ba da shi ga Ubangiji. Bayan haka sai su koma gida.21Hannatu kuwa ta sami alfarma daga Ubangiji. Ta yi ciki. Ana cikin haka Sama’ila kuwa sai girma yake ta yi a gaban Ubangiji.22To, Eli kuwa ya tsufa ƙwarai, yana kuma jin labari duk abin da ’ya’yansa suke yi wa dukan Isra’ila, da yadda suke lalata da matan da suke hidima a bakin ƙofar Tentin Sujada.23Saboda haka ya ce musu, “Don me kuke yin waɗannan abubuwa? Na sami labari daga wurin mutane a kan duk ayyukan muguntanku.24A’a, ’ya’yana ba labari mai kyau nake ji cikin mutanen Ubangiji ba.25In mutum ya yi wa wani laifi Allah yakan kāre shi; amma in mutum ya yi wa Ubangiji zunubi wa zai kāre shi?” Duk da haka, ’ya’yansa ba su kula da gargaɗin mahaifinsu ba, domin nufin Ubangiji ne yă hallaka su.26Yaron nan Sama’ila ya dinga girma cikin kwarjini da cikin tagomashi a gaba Ubangiji da mutane.27Wani mutum ya zo wurin Eli ya ce masa, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Ashe ban bayana kaina sosai ga mahaifinka lokacin da yake a Masar a ƙarƙashin Fir’auna ba?28Na zaɓi mahaifinka daga cikin dukan kabilar Isra’ila yă zama firist nawa don yă yi hidima a bagade, don yă ƙona turare mai ƙanshi, don kuma yă sanya doguwar riga a gabana. Na kuma ba wa iyalin mahaifinka dukan hadaya ta ƙonawa da Isra’ila suka miƙa.29Don me kuke rena hadayata da sadakokina da na ƙayyade domin mazaunina? Don me kake girmama ’ya’yanka fiye da ni ta wurin cinye sashe mafi kyau na kowane hadayar da mutanena Isra’ila suka miƙa?’30“Saboda haka Ubangiji Allah na Isra’ila ya ce, ‘Na yi alkawari cewa gidanka da gidan mahaifinka za su yi mini hidima a gabana har abada.’ Amma, yanzu Allah ya ce, ba zai yiwu ba; waɗanda suke girmama ni; Ni ma zan girmama su. Amma waɗanda suke ƙasƙantar da ni, haka za a ƙasƙantar da su.31Lokaci yana zuwa sa’ad da zan rage ƙarfinka da ƙarfin iyalin gidan mahaifinka. Domin kada a sāke samun tsohon mutum a zuriyarka.32Za ka zama da ɓacin rai a mazaunina ko da yake za a yi wa Isra’ila alheri. A zuriyarka ba za a taɓa samun tsohon mutum ba.33Kowannenku da ban kashe daga hidima a bagadena ba, za a bar shi don yă cika idanunka da hawaye da kuma baƙin ciki, dukan sauran zuriyarka kuwa za su mutu a ƙuruciyarsu.34“ ‘Abin da kuma ya faru da ’ya’yanka biyu Hofni da Finehas zai zama alama a gare ka; saboda mutuwarsu za tă zama a rana ɗaya.35Zan tayar wa kaina amintaccen firist wanda zai aikata abin da nake so yă yi, zan kuwa ba shi zuriya da koyaushe za su yi aiki a gaban zaɓaɓɓen sarkina.36Sa’an nan duk wanda ya rage a zuriyarka zai zo yă durƙusa a gabansa yă roƙi kuɗi da abinci, zai kuma roƙa a yardar masa yă taimaki firistoci da aiki domin yă sami abin da zai ci.’ ”Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide. Sabon Rai Don Kowa 2020 1 Samaʼila 2 00:00:00 00:00:00 0.5x 2.0x https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/1samuel/002.mp3 31 2