× Harshe Turai Rashanci Belarusiyanci Yukreniyanci Yaren mutanen Poland Sabiyanci Bulgaria Slovakiyan Czech Romaniyanci Moldoviyanci Azerbaijan Armeniyanci Jojiyanci Albaniyanci Avar Bashkir Tatar Checheniya Slobaniyanci Kuroshiya Estoniyanci Latvia Lituweniyanci Harshen Hungary Yaren mutanen Finland Yaren mutanen Norway Yaren mutanen Sweden Icelandic Girkanci Macedonia Bajamushe Bavarian Yaren mutanen Holland Danish Welsh Gaelic Irish Faransanci Basque Katalaniyanci Italiyanci Galacian Romani Bosnian Amirka ta Arewa Turanci Kudancin Amurka Sifeniyanci Fotigal Guarani Quechuan Aymara Amurka ta Tsakiya Jamaica Nahuatl Kiche Qeqchi Haiti Gabashin Asiya Sinanci Jafananci Yaren Koriya Mongoliyanci Uyghur Hmong Kudu maso gabashin Asiya Malesiya Burma Chin Nepali Cebuano Tagalog Kambodiyanci Thai Indonesiyanci Vietnam Javanisanci Lao Iban IuMien Kachin Lahu Aceh Balinese Bugis Pampanga Sasak Shan Waray Kudancin Asiya Hindi Оdia Awadhi Mizo Kannada Malayalam Marathi Gujarati Tamil Telugu Harshen Punjabi Kurukh Assamese Maithili Bengali Urdu Sinhala Dogri Haryanvi Meitei Konkani Santali Sindhi Koya Thado Sanskrit Devanagari Adilabad Gondi Ahirani Balochi Bundeli Chhattisgarhi Garhwali Kangri Kumaoni Mewari Munda Sadri Seraiki Shekhawati Sylheti Asiya ta Tsakiya Kirgiziya Uzbek Tajik Turkmen Kazakhstan Karakalpak Gabas ta Tsakiya Baturke Ibrananci Larabci Farisanci Kurdawa Pashto 'Yan Koftik Afirka Afirkaans Xhosa Zulu Ndebele Sotho Amharic Wolaytta Dan Najeriya Mossi Ika Dinka Kabyle Ewe Swahili Maroko Somalian Shona Madagaska Igbo Lingala Baoule Siswati Tsonga Tswana Gambiya Yarbawa Kamba Kinyarwanda Hausa Chewa Luo Makua Dyula Fulfulde Kalenjin Kikuyu Kikwango Kirundi Krio Nigerian Pidgin Oromo Tshiluba Tshivenda Twi Umbundu Lugbara Luguru Pular Gussi Maasai Turkana Moba Nuer Shilluk Tamasheq Makonde Bemba Fon Hadiyya Ibibio Kimbundu Kimiiru Lango Liberian Kreyol Lomwe Mende Morisyen Ndau Nyankole Sena Sidamo Soga Songe Sukuma Tarifit Teso Tiv Zande Dagbani Nahiyar Australiya New Zealand Papua New Guinea Tsoffin Harsuna Aramaic Latin Esperanto 1 1 1 2020 202020101 1 1 Yoshuwa FarawaFitowaFiristociƘidayaMaimaitawar ShariʼaYoshuwaMahukuntaRut1 Samaʼila2 Samaʼila1 Sarakuna2 Sarakuna1 Tarihi2 TarihiEzraNehemiyaEstaAyubaZaburaKarin MaganaMai HadishiWaƙar WaƙoƙiIshayaIrmiyaMakokiEzekiyelDaniyelHosiyaYowelAmosObadiyaYunanaMikaNahumHabakkukZefaniyaHaggaiZakariyaMalaki--- --- ---MattiyuMarkusLukaYohannaAyyukan ManzanniRomawa1 Korintiyawa2 KorintiyawaGalatiyawaAfisawaFilibbiyawaKolossiyawa1 Tessalonikawa2 Tessalonikawa1 Timoti2 TimotiTitusFilemonIbraniyawaYaƙub1 Bitrus2 Bitrus1 Yohanna2 Yohanna3 YohannaYahudaRuʼuya ta Yohanna1 1 1 8 1234567891011121314151617181920212223241 1 1 : 1 12345678910111213141516171819202122232425262728293031323334351 1 1 Sabon Rai Don Kowa 2020 Yoshuwa 8 Adana Bayanan kula 1Sai Ubangiji ya ce wa Yoshuwa, “Kada ka ji tsoro; kada ka karaya. Ka ɗauki dukan sojojin ku kai wa Ai hari, gama na ba ka nasara a kan sarkin Ai, mutanensa, birninsa da kuma ƙasarsa.2Za ku yi wa Ai yadda kuka yi wa Yeriko da sarkinta, sai dai za ku kwashe ganima da dabbobinta su zama naku. Ku yi kwanto a bayan birnin.”3Yoshuwa da dukan sojojin suka fita su kai wa Ai hari. Sai ya zaɓi sojojinsa waɗanda suka fi saura duka iya yaƙi guda dubu talatin, ya tura su da dad dare4ya ba su umarni ya ce, “Ku ji da kyau, za ku yi kwanto a bayan birnin, kada ku yi nisa da birnin. Kowannenku yă kasance a faɗake.5Ni da waɗanda suke tare da ni za mu nufi birnin, a lokacin da mutanen suka taso mana yadda suka yi dā, sai mu guje musu.6Za su bi mu har su yi nisa da birnin, gama za su ce, ‘Suna gudu kamar yadda suka yi dā.’ Saboda haka lokacin da muka guje musu,7sai ku tashi daga inda kuka yi kwanto, ku ci birnin da yaƙi, Ubangiji Allahnku zai ba da shi a hannunku.8Lokacin da kuka ƙwace birnin, sai ku sa masa wuta. Ku yi abin da Ubangiji ya umarta. Ku tabbata kun yi abubuwan da na ce.”9Sai Yoshuwa ya sallame su, suka kuma tafi wurin da za su yi kwanto, suka kwanta suna fako tsakanin Betel da Ai, yamma da Ai, amma Yoshuwa ya kwana tare da mutanen.10Kashegari da sassafe Yoshuwa ya tattara mutanensa, sai shi da shugabannin Isra’ilawa suka sha gaba suka taka zuwa Ai.11Dukan sojojin da suke tare da shi suka nufi birnin, da suka kai kuwa sai suka kafa sansaninsu a arewancin Ai. Tsakaninsu da Ai akwai kwari.12Yoshuwa ya sa mutum dubu biyar suka yi kwanto tsakanin Betel da Ai, a yammancin birnin.13Mutanen suka kafa sansaninsu arewa da birnin, sansani na ’yan kwanto kuwa yana yamma da birnin, amma Yoshuwa ya kwana a kwarin.14Sa’ad da sarkin Ai ya ga haka, shi da duk mutanen birnin suka hanzarta da sassafe don su gamu da Isra’ilawa, su yi yaƙi da su a wani wurin da yake fuskantar Araba. Amma bai san cewa an yi masa kwanto a bayan birnin ba.15Yoshuwa da duk Isra’ilawa suka bari aka fafare su, sai suka gudu zuwa cikin jeji.16Aka kira duk mazan Ai su fafare su, suka kuwa fafari Yoshuwa, aka yaudare su suka yi nisa da birnin.17Ba namijin da ya rage a Ai ko Betel da bai fita don yă fafari Isra’ilawa ba. Suka bar birnin a buɗe, suka tafi fafarar Isra’ilawa.18Sai Ubangiji ya ce wa Yoshuwa, “Ka riƙe māshin da yake hannunka ka nuna wajen Ai, gama zan ba da birnin a hannunka.” Yoshuwa kuwa ya miƙa māshin ta wajen Ai.19Da yin haka kuwa sai mutanen da suka yi kwanto suka tashi nan da nan daga inda suke, suka nufi birnin a guje, suka shiga suka ci birnin da yaƙi, suka kuma cinna mata wuta da sauri.20Mutanen Ai suka juya suka ga hayaƙin birninsu yana tashi sama, amma ba yadda za su iya tsira ta ko’ina, gama Isra’ilawan da suke gudu zuwa cikin jeji suka juya suka fara fafarar waɗanda suke fafararsu.21Lokacin da Yoshuwa da dukan Isra’ilawa suka ga waɗanda suka yi kwanto sun ci birnin da yaƙi, hayaƙi kuwa ya cika birnin, sai suka juya suka kai wa mutanen Ai hari.22Mutanen da suka yi kwanto su ma suka fito daga birnin suka tasar musu, ya zama an kama su a tsakiya, ga Isra’ilawa daga kowane gefe. Isra’ilawa kuwa suka karkashe su duka ba su bar wani da rai ba, ba kuma wanda ya tsere.23Amma suka tafi da sarkin Ai da rai suka kawo shi wurin Yoshuwa.24Da Isra’ilawa suka gama kashe duk mutanen Ai a filaye da kuma a cikin jeji inda suka fafare su, kuma da aka karkashe kowane mutumin Ai da takobi sai dukan Isra’ilawa suka koma Ai suka karkashe duk waɗanda suke cikinsa.25A ranan nan, dukan mutanen Ai da aka kashe, mutum dubu goma sha biyu ne maza da mata.26Gama Yoshuwa bai janye hannunsa da yake riƙe da māshinsa ba har sai da ya hallaka dukan mazaunan Ai.27Amma Isra’ilawa suka kwashe ganima da dabbobin birnin nan yadda Ubangiji ya umarci Yoshuwa.28Yoshuwa kuwa ya ƙone Ai, ya mai da ita tarin ƙasa, ta zama kufai har wa yau.29Ya rataye sarkin Ai a kan itace, ya bar shi a can har yamma. Da rana ta fāɗi, Yoshuwa ya umarta a ɗauke gawar sarkin a jefa a gaban ƙofar birnin. Suka kuma tara manyan duwatsu a kan gawar, tsibin na nan har wa yau.30Yoshuwa kuwa ya yi wa Ubangiji, Allah na Isra’ila bagade a Dutsen Ebal,31kamar yadda Musa bawan Ubangiji ya umarci Isra’ilawa. Ya gina bisa ga abin da yake a rubuce a cikin Littafin Dokoki na Musa, bagade na duwatsun da ba a sassaƙa su ba, waɗanda ba wani ƙarfen da ya taɓa su. Suka miƙa wa Ubangiji hadayu na ƙonawa da hadayu na salama a kai.32A can, a gaban Isra’ilawa, Yoshuwa ya rubuta dokokin Musa a kan duwatsun.33Sai Isra’ilawa duka, da baƙi, da haifaffun gida, da dattawansu, da shugabanninsu, da alƙalansu, suka tsaya a gefe-gefen akwatin alkawarin Ubangiji, suna fuskantar waɗanda suke ɗauke da shi, wato, firistoci waɗanda su ne Lawiyawa. Rabin mutanen suka tsaya a gaban Dutsen Gerizim, rabinsu kuma suka tsaya a gaban Dutsen Ebal, kamar yadda Musa bawan Ubangiji ya riga ya umarta, cewa su sa wa mutanen Isra’ilawa albarka.34Bayan haka, Yoshuwa ya karanta duk abin da yake a cikin Dokoki, albarku da la’anoni, kamar yadda suke a rubuce a cikin Littafin Dokoki.35Babu wata kalmar da Musa ya umarta da Yoshuwa bai karanta wa dukan taron Isra’ilawa ba, haɗe da mata, da yara, da baƙin da suke zama tare da su.Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide. Sabon Rai Don Kowa 2020 Yoshuwa 8 00:00:00 00:00:00 0.5x 2.0x https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/joshua/008.mp3 24 8