× Harshe Turai Rashanci Belarusiyanci Yukreniyanci Yaren mutanen Poland Sabiyanci Bulgaria Slovakiyan Czech Romaniyanci Moldoviyanci Azerbaijan Armeniyanci Jojiyanci Albaniyanci Avar Bashkir Tatar Checheniya Slobaniyanci Kuroshiya Estoniyanci Latvia Lituweniyanci Harshen Hungary Yaren mutanen Finland Yaren mutanen Norway Yaren mutanen Sweden Icelandic Girkanci Macedonia Bajamushe Bavarian Yaren mutanen Holland Danish Welsh Gaelic Irish Faransanci Basque Katalaniyanci Italiyanci Galacian Romani Bosnian Kabardian Amirka ta Arewa Turanci Kudancin Amurka Sifeniyanci Fotigal Guarani Quechuan Aymara Amurka ta Tsakiya Jamaica Nahuatl Kiche Qeqchi Haiti Gabashin Asiya Sinanci Jafananci Yaren Koriya Mongoliyanci Uyghur Hmong Tibetian Kudu maso gabashin Asiya Malesiya Burma Chin Nepali Cebuano Tagalog Kambodiyanci Thai Indonesiyanci Sundanese Vietnam Javanisanci Lao Iban IuMien Kachin Lahu Aceh Balinese Bugis Pampanga Sasak Shan Waray Kudancin Asiya Hindi Оdia Awadhi Mizo Kannada Malayalam Marathi Gujarati Tamil Telugu Harshen Punjabi Kurukh Assamese Maithili Bengali Urdu Sinhala Dogri Haryanvi Meitei Konkani Santali Sindhi Koya Thado Sanskrit Devanagari Adilabad Gondi Ahirani Balochi Bundeli Chhattisgarhi Garhwali Kangri Kumaoni Mewari Munda Sadri Seraiki Shekhawati Sylheti Bagri Bhilali Bodo Braj Tulu Asiya ta Tsakiya Kirgiziya Uzbek Tajik Turkmen Kazakhstan Karakalpak Gabas ta Tsakiya Baturke Ibrananci Larabci Farisanci Kurdawa Mazanderani Pashto 'Yan Koftik Afirka Afirkaans Xhosa Zulu Ndebele Sotho Amharic Wolaytta Dan Najeriya Mossi Ika Dinka Kabyle Ewe Swahili Maroko Somalian Shona Madagaska Igbo Lingala Baoule Siswati Tsonga Tswana Gambiya Yarbawa Kamba Kinyarwanda Hausa Chewa Luo Makua Dyula Fulfulde Kalenjin Kikuyu Kikwango Kirundi Krio Nigerian Pidgin Oromo Tshiluba Tshivenda Twi Umbundu Lugbara Luguru Pular Gussi Maasai Turkana Moba Nuer Shilluk Tamasheq Makonde Bemba Fon Hadiyya Ibibio Kimbundu Kimiiru Lango Liberian Kreyol Lomwe Mende Morisyen Ndau Nyankole Sena Sidamo Soga Songe Sukuma Tarifit Teso Tiv Zande Dagbani Edo Kituba Nahiyar Australiya New Zealand Papua New Guinea Tsoffin Harsuna Aramaic Latin Esperanto 1 1 1 Sabon Rai Don Kowa 2020 Sabon Rai Don Kowa 2020أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا 2020Littafi Mai Tsarki 19791 1 1 2 Samaʼila FarawaFitowaFiristociƘidayaMaimaitawar ShariʼaYoshuwaMahukuntaRut1 Samaʼila2 Samaʼila1 Sarakuna2 Sarakuna1 Tarihi2 TarihiEzraNehemiyaEstaAyubaZaburaKarin MaganaMai HadishiWaƙar WaƙoƙiIshayaIrmiyaMakokiEzekiyelDaniyelHosiyaYowelAmosObadiyaYunanaMikaNahumHabakkukZefaniyaHaggaiZakariyaMalaki--- --- ---MattiyuMarkusLukaYohannaAyyukan ManzanniRomawa1 Korintiyawa2 KorintiyawaGalatiyawaAfisawaFilibbiyawaKolossiyawa1 Tessalonikawa2 Tessalonikawa1 Timoti2 TimotiTitusFilemonIbraniyawaYaƙub1 Bitrus2 Bitrus1 Yohanna2 Yohanna3 YohannaYahudaRuʼuya ta Yohanna1 1 1 11 1234567891011121314151617181920212223241 1 1 : 1 1234567891011121314151617181920212223242526271 1 1 Sabon Rai Don Kowa 2020 2 Samaʼila 11 Adana Bayanan kula 1Da bazara, a lokacin da sarakuna sukan fita zuwa yaƙi, sai Dawuda ya aiki Yowab tare da mutanen sarki, da dukan Isra’ila. Suka je suka hallaka Ammonawa, suka kuma yi wa Rabba kwanton ɓauna. Amma Dawuda ya yi zamansa a Urushalima.2Wata rana da yamma, Dawuda ya tashi daga gadonsa, ya zaga kewaye a rufin fadansa. Daga rufin ya ga wata mace tana wanka. Matar kyakkyawa ce ƙwarai.3Sai Dawuda ya aiki wani yă bincika ko wace ce ita, sai mutumin ya dawo ya ce, “Wannan ba Batsheba ba ce, ’yar Eliyam matar Uriya, mutumin Hitti?”4Sa’an nan Dawuda ya aiki manzanni su kawo masa ita. Ta zo wurinsa shi kuma ya kwana da ita (A lokacin kuwa ta gama tsarkake kanta ke nan daga jinin haila.) Sa’an nan ta tafi gida.5Matar ta yi ciki, ta kuwa aika wa Dawuda, tana cewa, “Ina da ciki.”6Saboda haka Dawuda ya aika saƙo wa Yowab ya ce, “Ka aiko mini da Uriya mutumin Hitti.” Yowab kuwa ya aika da shi wajen Dawuda.7Da Uriya ya zo wurinsa, sai Dawuda ya tambaye shi lafiyar Yowab da sojojin, da kuma yaya yaƙin yake tafiya.8Sa’an nan Dawuda ya ce wa Uriya, “Gangara gidanka ka wanke ƙafafunka.” Saboda haka Uriya ya bar fadar, sarki kuma ya aika masa da kyauta.9Amma Uriya ya kwanta a ƙofar fada tare da dukan bayin maigidansa, bai kuwa tafi gidansa ba.10Da aka gaya wa Dawuda, “Uriya bai tafi gida ba,” sai Dawuda ya tambaye shi ya ce, “Ba ka zo daga wuri mai nisa ba? Me ya sa ba ka je gida ba?”11Sai Uriya ya ce wa Dawuda, “Akwatin Alkawari, da Isra’ila, da Yahuda suna zama cikin tentuna, kuma maigidana Yowab da mutanen ranka yă daɗe suna a sansani a fili. Yaya zan je gidana in ci in sha in kuma kwana da matata? Muddin kana a raye, ba zan yi irin wannan abu ba!”12Sai Dawuda ya ce masa, “Ka ƙara dakata a nan kwana ɗaya, gobe kuwa in sallame ka.” Saboda haka Uriya ya dakata a Urushalima a ranar, da kuma ta biye.13Dawuda ya gayyace shi, ya kuwa ci ya sha tare da shi, Dawuda ya sa ya bugu tilis. Amma da yamma Uriya ya koma ya kwanta a tabarmarsa cikin bayin maigidan sarki; bai je gida ba.14Da safe Dawuda ya rubuta wa Yowab wasiƙa ya ba wa Uriya.15A ciki wasiƙar ya rubuta, “Tura Uriya a gaba inda yaƙi ya fi zafi. Sa’an nan ka janye daga gare shi don a buge shi yă mutu.”16Saboda haka yayinda Yowab ya kai yaƙi kusa da birnin, sai tura Uriya a inda ya sani akwai jarumawan Ammon na gaske.17Sa’ad da mutanen garin suka fito suka yaƙi Yowab, sai waɗansu mutane daga sojojin Dawuda suka mutu; Uriya mutumin Hitti ma ya mutu.18Yowab ya aika wa Dawuda cikakken labari batun yaƙin.19Ya umarci manzon ya ce, “Da ka gama yin wa sarki wannan batun yaƙin,20wataƙila sarki yă husata, yă tambaye ka, ‘Me ya sa kuka je kusa da birnin don ku yi yaƙi? Ba ku san cewa za su yi harbi daga katanga ba?21Wane ne ya kashe Abimelek ɗan Yerub-Beshet? Ba mace ce ta jefa dutsen niƙa a kansa daga katanga, ta haka ya mutu a Tebez ba? Me ya sa kuka je kurkusa da katangar?’ In ya tambaye ka wannan, sai ka ce masa, ‘Har bawanka Uriya mutumin Hitti ma ya mutu.’ ”22Manzon ya tashi ya tafi, da ya iso kuwa sai ya gaya wa Dawuda dukan abin da Yowab ya aike shi yă faɗa.23Manzon ya ce wa Dawuda, “Mutanen sun sha kanmu suka fito suka yaƙe mu a fili, amma muka kore su har ƙofar birni.24Sa’an nan maharba suka yi ta harbi daga katanga har waɗansu mutanen sarki suka mutu. Ban da haka ma, Uriya mutumin Hitti bawan sarki ya mutu.”25Dawuda ya ce wa manzon, “Ka gaya wa Yowab, ‘Kada ka bar wannan yă dame ka; yadda takobi ya lamushe wannan, haka zai lamushe wancan ma. Ku ƙara matsa wa garin lamba, ku hallaka shi.’ Ka faɗa haka don ka ƙarfafa Yowab.”26Da matar Uriya ta ji cewa mijinta ya mutu, sai ta yi makoki saboda shi.27Bayan kwanakin makoki suka ƙare, Dawuda ya sa aka kawo ta gidansa, ta kuwa zama matarsa, ta kuma haifa masa ɗa. Sai dai abin da Dawuda ya yi bai gamshi Ubangiji ba.Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Sabon Rai Don Kowa 2020 2 Samaʼila 11 00:00:00 00:00:00 0.5x 2.0x https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/2samuel/011.mp3 24 11