× Harshe Turai Rashanci Belarusiyanci Yukreniyanci Yaren mutanen Poland Sabiyanci Bulgaria Slovakiyan Czech Romaniyanci Moldoviyanci Azerbaijan Armeniyanci Jojiyanci Albaniyanci Avar Bashkir Tatar Checheniya Slobaniyanci Kuroshiya Estoniyanci Latvia Lituweniyanci Harshen Hungary Yaren mutanen Finland Yaren mutanen Norway Yaren mutanen Sweden Icelandic Girkanci Macedonia Bajamushe Bavarian Yaren mutanen Holland Danish Welsh Gaelic Irish Faransanci Basque Katalaniyanci Italiyanci Galacian Romani Bosnian Kabardian Amirka ta Arewa Turanci Kudancin Amurka Sifeniyanci Fotigal Guarani Quechuan Aymara Amurka ta Tsakiya Jamaica Nahuatl Kiche Qeqchi Haiti Gabashin Asiya Sinanci Jafananci Yaren Koriya Mongoliyanci Uyghur Hmong Tibetian Kudu maso gabashin Asiya Malesiya Burma Chin Nepali Cebuano Tagalog Kambodiyanci Thai Indonesiyanci Sundanese Vietnam Javanisanci Lao Iban IuMien Kachin Lahu Aceh Balinese Bugis Pampanga Sasak Shan Waray Madurese Kudancin Asiya Hindi Оdia Awadhi Mizo Kannada Malayalam Marathi Gujarati Tamil Telugu Harshen Punjabi Kurukh Assamese Maithili Bengali Urdu Sinhala Dogri Haryanvi Meitei Konkani Santali Sindhi Koya Thado Sanskrit Devanagari Adilabad Gondi Ahirani Balochi Bundeli Chhattisgarhi Garhwali Kangri Kumaoni Mewari Munda Sadri Seraiki Shekhawati Sylheti Bagri Bhilali Bodo Braj Tulu Asiya ta Tsakiya Kirgiziya Uzbek Tajik Turkmen Kazakhstan Karakalpak Gabas ta Tsakiya Baturke Ibrananci Larabci Farisanci Kurdawa Mazanderani Pashto 'Yan Koftik Afirka Afirkaans Xhosa Zulu Ndebele Sotho Amharic Wolaytta Dan Najeriya Mossi Ika Dinka Kabyle Ewe Swahili Maroko Somalian Shona Madagaska Igbo Lingala Baoule Siswati Tsonga Tswana Gambiya Yarbawa Kamba Kinyarwanda Hausa Chewa Luo Makua Dyula Fulfulde Kalenjin Kikuyu Kikwango Kirundi Krio Nigerian Pidgin Oromo Tshiluba Tshivenda Twi Umbundu Lugbara Luguru Pular Gussi Maasai Turkana Moba Nuer Shilluk Tamasheq Makonde Bemba Fon Hadiyya Ibibio Kimbundu Kimiiru Lango Liberian Kreyol Lomwe Mende Morisyen Ndau Nyankole Sena Sidamo Soga Songe Sukuma Tarifit Teso Tiv Zande Dagbani Edo Kituba Nahiyar Australiya New Zealand Papua New Guinea Tsoffin Harsuna Aramaic Latin Esperanto 1 1 1 Sabon Rai Don Kowa 2020 Sabon Rai Don Kowa 2020أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا 2020Littafi Mai Tsarki 19791 1 1 1 Sarakuna FarawaFitowaFiristociƘidayaMaimaitawar ShariʼaYoshuwaMahukuntaRut1 Samaʼila2 Samaʼila1 Sarakuna2 Sarakuna1 Tarihi2 TarihiEzraNehemiyaEstaAyubaZaburaKarin MaganaMai HadishiWaƙar WaƙoƙiIshayaIrmiyaMakokiEzekiyelDaniyelHosiyaYowelAmosObadiyaYunanaMikaNahumHabakkukZefaniyaHaggaiZakariyaMalaki--- --- ---MattiyuMarkusLukaYohannaAyyukan ManzanniRomawa1 Korintiyawa2 KorintiyawaGalatiyawaAfisawaFilibbiyawaKolossiyawa1 Tessalonikawa2 Tessalonikawa1 Timoti2 TimotiTitusFilemonIbraniyawaYaƙub1 Bitrus2 Bitrus1 Yohanna2 Yohanna3 YohannaYahudaRuʼuya ta Yohanna1 1 1 10 123456789101112131415161718192021221 1 1 : 1 12345678910111213141516171819202122232425262728291 1 1 Sabon Rai Don Kowa 2020 1 Sarakuna 10 Adana Bayanan kula 1Sa’ad da sarauniyar Sheba ta ji game da sunan da Solomon ya yi, da kuma dangantakarsa da Ubangiji, sai ta zo tă gwada shi da tambayoyi masu wuya.2Ta iso Urushalima da tawaga mai yawa, tare da raƙuma masu ɗauke da kayan yaji, da zinariya masu yawa, da duwatsu masu daraja. Ta zo wurin Solomon ta kuwa yi magana da shi game da dukan abin da take da shi a ranta.3Solomon ya amsa dukan tambayoyinta, ba abin da ya yi wa sarki wuyan bayyanawa mata.4Da sarauniya Sheba ta ga dukan hikimar Solomon da fadan da ya gina.5Da irin abincin da yake kan teburinsa, da irin zaman fadawansa, da irin rigunan masu hidimarsa, da irin masu shayarwarsa, da kuma hadayun ƙonawar da yake yi a haikalin Ubangiji, sai ta yi mamaki ƙwarai.6Ta ce wa sarki, “Labarin da na ji a ƙasata game da abin da ka yi da kuma hikimarka gaskiya ne.7Amma ban gaskata waɗannan abubuwa ba sai da na zo na gani da idanuna. Tabbatacce, ba a ma faɗa mini ko rabi ba. Gama cikin hikima da arziki, ka wuce labarin da na ji nesa ba kusa ba.8Abin farin ciki ne ga mutanenka! Abin farin ciki ne ga fadawanka, waɗanda suke cin gaba da tsayawa a gabanka suna kuma jin hikimarka!9Yabo ga Ubangiji Allahnka, wanda ya ji daɗinka, ya kuma sa ka a kujerar sarautar Isra’ila. Ubangiji ya naɗa ka sarki saboda madawwamiyar ƙaunar wa Isra’ila, don ka yi shari’a da adalci.”10Ta kuma ba sarki talenti 120 na zinariya, da kayan yaji masu yawa, da kuma duwatsu masu daraja. Ba a taɓa kawo kayan yaji da yawa haka kamar yadda sarauniyar Sheba ta ba wa Sarki Solomon ba.11(Jiragen ruwan Hiram suka kawo zinariya daga Ofir. Daga can kuma suka kawo kaya masu yawa na katakon almug, da kuma duwatsu masu daraja.12Sarki ya yi amfani da almug don yă yi kayan ado wa haikalin Ubangiji da kuma don fadan sarki, don kuma yă yi molaye, da garayu saboda mawaƙa. Ba a taɓa yin jigilar katakon almug ko a gani irin yawan katakai haka ba har wa yau.)13Sarki Solomon ya ba wa sarauniyar Sheba dukan abin da take so, da kuma duk abin da ta nema, ban da abin da ya ba ta daga yalwar fadan sarki. Sa’an nan ta koma tare da tawagarta zuwa ƙasarta.14Nauyin zinariya da Solomon yake samun kowace shekara, talenti 666 ne.15Ban da haraji daga ’yan kasuwa, da fatake, da kuma daga dukan sarakunan Arabiya, da gwamnonin ƙasar.16Sarki Solomon ya yi manyan garkuwoyi ɗari biyu na zinariya. An yi kowace garkuwa da zinariya bekas ɗari shida.17Ya kuma yi ƙananan garkuwoyi ɗari uku na zinariya. An yi kowane garkuwa da zinariya minas uku. Ya sa su a cikin Fadar Kurmin Lebanon.18Sa’an nan sarki ya yi kujerar sarauta mai nauyin giram na hauren giwa, aka kuma dalaye ta da zinariya zalla.19Kujera sarautar ta kasance da matakai shida, kuma bayanta tana da bisa mai kamannin gammo. A kowane gefen kujerar akwai wurin sa hannu, da kuma zaki tsaye kusa da kowannensu.20Zakoki goma sha biyu suna tsaye a matakai shida, ɗaya a kowane gefen ƙarshen mataki. Babu ƙasar da an taɓa gina irin wannan kujerar mulki.21Dukan kwaf Solomon zinariya ne, kuma dukan kayayyakin gida a Fadan da ake kira Kurmin Lebanon, zinariya ce zalla. Babu wani abin da aka yi da azurfa, domin ba a ɗauki azurfa a bakin kome ba a zamanin Solomon.22Sarki yana da jerin jiragen ruwan kasuwanci a teku, tare da jiragen ruwan Hiram. Sau ɗaya kowace shekara uku jerin jiragen yakan dawo ɗauke da zinariya, da azurfa, da hauren giwa, da birai marasa wutsiya, da kuma gogon biri.23Sarki Solomon ya yi suna a wadata fiye da dukan sarakunan duniya.24Dukan duniya ta nemi su zo wurin Solomon don su ji hikimar da Allah ya sa a zuciyarsa.25Kowace shekara, kowa da ya zo wurinsa yakan kawo kyautai, kayayyakin azurfa da na zinariya, riguna, makamai, da kayan yaji, dawakai da alfadarai.26Solomon ya tara kekunan yaƙi da dawakai; ya kasance da kekunan yaƙi dubu goma sha huɗu, da dawakai dubu goma sha biyu waɗanda ya ajiye a biranen kekunan yaƙi, ya kuma ajiye tare da shi a Urushalima.27Sarki ya mai da azurfa barkatai a cikin Urushalima kamar duwatsu, al’ul kuma da yawa kamar itatuwan fir na jumaiza a gindin tuddai.28An yi jigilar dawakan Solomon daga Masar da kuma daga Kuye, ’yan kasuwan fadan sarki sun sayo su daga Kuye.29Suka yi jigilar kekunan yaƙi daga Masar a bakin shekel ɗari shida na azurfa, doki ɗaya kuma a kan ɗari da hamsin. Sun kuma yi jigilarsu suna sayarwa ga dukan sarakunan Hittiyawa da na Arameyawa.Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Sabon Rai Don Kowa 2020 1 Sarakuna 10 00:00:00 00:00:00 0.5x 2.0x https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/1kings/010.mp3 22 10