× Harshe Turai Rashanci Belarusiyanci Yukreniyanci Yaren mutanen Poland Sabiyanci Bulgaria Slovakiyan Czech Romaniyanci Moldoviyanci Azerbaijan Armeniyanci Jojiyanci Albaniyanci Avar Bashkir Tatar Checheniya Slobaniyanci Kuroshiya Estoniyanci Latvia Lituweniyanci Harshen Hungary Yaren mutanen Finland Yaren mutanen Norway Yaren mutanen Sweden Icelandic Girkanci Macedonia Bajamushe Bavarian Yaren mutanen Holland Danish Welsh Gaelic Irish Faransanci Basque Katalaniyanci Italiyanci Galacian Romani Bosnian Kabardian Amirka ta Arewa Turanci Kudancin Amurka Sifeniyanci Fotigal Guarani Quechuan Aymara Amurka ta Tsakiya Jamaica Nahuatl Kiche Qeqchi Haiti Gabashin Asiya Sinanci Jafananci Yaren Koriya Mongoliyanci Uyghur Hmong Tibetian Kudu maso gabashin Asiya Malesiya Burma Chin Nepali Cebuano Tagalog Kambodiyanci Thai Indonesiyanci Sundanese Vietnam Javanisanci Lao Iban IuMien Kachin Lahu Aceh Balinese Bugis Pampanga Sasak Shan Waray Kudancin Asiya Hindi Оdia Awadhi Mizo Kannada Malayalam Marathi Gujarati Tamil Telugu Harshen Punjabi Kurukh Assamese Maithili Bengali Urdu Sinhala Dogri Haryanvi Meitei Konkani Santali Sindhi Koya Thado Sanskrit Devanagari Adilabad Gondi Ahirani Balochi Bundeli Chhattisgarhi Garhwali Kangri Kumaoni Mewari Munda Sadri Seraiki Shekhawati Sylheti Bagri Bhilali Bodo Braj Tulu Asiya ta Tsakiya Kirgiziya Uzbek Tajik Turkmen Kazakhstan Karakalpak Gabas ta Tsakiya Baturke Ibrananci Larabci Farisanci Kurdawa Mazanderani Pashto 'Yan Koftik Afirka Afirkaans Xhosa Zulu Ndebele Sotho Amharic Wolaytta Dan Najeriya Mossi Ika Dinka Kabyle Ewe Swahili Maroko Somalian Shona Madagaska Igbo Lingala Baoule Siswati Tsonga Tswana Gambiya Yarbawa Kamba Kinyarwanda Hausa Chewa Luo Makua Dyula Fulfulde Kalenjin Kikuyu Kikwango Kirundi Krio Nigerian Pidgin Oromo Tshiluba Tshivenda Twi Umbundu Lugbara Luguru Pular Gussi Maasai Turkana Moba Nuer Shilluk Tamasheq Makonde Bemba Fon Hadiyya Ibibio Kimbundu Kimiiru Lango Liberian Kreyol Lomwe Mende Morisyen Ndau Nyankole Sena Sidamo Soga Songe Sukuma Tarifit Teso Tiv Zande Dagbani Edo Kituba Nahiyar Australiya New Zealand Papua New Guinea Tsoffin Harsuna Aramaic Latin Esperanto 1 1 1 Sabon Rai Don Kowa 2020 Sabon Rai Don Kowa 2020أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا 2020Littafi Mai Tsarki 19791 1 1 1 Sarakuna FarawaFitowaFiristociƘidayaMaimaitawar ShariʼaYoshuwaMahukuntaRut1 Samaʼila2 Samaʼila1 Sarakuna2 Sarakuna1 Tarihi2 TarihiEzraNehemiyaEstaAyubaZaburaKarin MaganaMai HadishiWaƙar WaƙoƙiIshayaIrmiyaMakokiEzekiyelDaniyelHosiyaYowelAmosObadiyaYunanaMikaNahumHabakkukZefaniyaHaggaiZakariyaMalaki--- --- ---MattiyuMarkusLukaYohannaAyyukan ManzanniRomawa1 Korintiyawa2 KorintiyawaGalatiyawaAfisawaFilibbiyawaKolossiyawa1 Tessalonikawa2 Tessalonikawa1 Timoti2 TimotiTitusFilemonIbraniyawaYaƙub1 Bitrus2 Bitrus1 Yohanna2 Yohanna3 YohannaYahudaRuʼuya ta Yohanna1 1 1 13 123456789101112131415161718192021221 1 1 : 1 123456789101112131415161718192021222324252627282930313233341 1 1 Sabon Rai Don Kowa 2020 1 Sarakuna 13 Adana Bayanan kula 1Bisa ga umarnin Ubangiji, sai wani mutumin Allah ya zo daga Yahuda zuwa Betel, yayinda Yerobowam yake tsaye kusa da bagade don yă miƙa hadaya.2Sai mutumin Allah ya tā da murya a kan bagade bisa ga umarnin Ubangiji ya ce, “Ya bagade, bagade! Ubangiji ya ce, ‘Za a haifi ɗa mai suna Yosiya wa gidan Dawuda. A kanka zai miƙa firistoci na masujadai kan tuddai masu miƙa hadayu a nan, za a kuma ƙone ƙasusuwan mutane a kanka.’ ”3A wannan rana mutumin Allah ya ba da alama, “Ga alamar da Ubangiji ya furta. Wannan bagade zai tsage yă rabu kashi biyu, tokar da yake a kansa za tă zuba a ƙasa.”4Sa’ad da Yerobowam ya ji abin da mutumin Allah ya tā da murya ya faɗa game da bagaden Betel, sai ya miƙa hannunsa daga bagaden ya ce, “Ku kama shi!” Amma sai hannun da ya miƙa ya yanƙwane, har bai iya janye shi ba.5Haka ma, bagaden ya rabu, tokarsa kuma ya zuba, bisa ga alamar da mutumin Allah ya bayar, ta wurin kalmar Ubangiji.6Sai sarki ya ce wa mutumin Allah, “Ka roƙi Ubangiji Allahnka, ka kuma yi addu’a domina don hannuna ya warke.” Saboda haka mutumin Allah ya yi roƙo ga Ubangiji, hannun sarki kuwa ya warke, ya kuma zama kamar yadda yake a dā.7Sai sarki ya ce wa mutumin Allah, “Zo gida tare da ni, ka sami wani abu ka ci, zan kuwa yi maka kyauta.”8Amma mutumin Allah ya amsa wa sarki, “Ko da za ka ba rabin mallakarka, ba zan tafi tare da kai ba, ba kuwa zan ci abinci, ko in sha ruwa a can ba.9Gama an umarce ni ta wurin kalmar Ubangiji, aka ce, ‘Kada ka ci abinci, ko ka sha ruwa, ko ka koma ta hanyar da ka zo.’ ”10Saboda haka ya ɗauki wata hanya, bai kuwa koma ta hanyar da ya zo Betel ba.11To, fa, akwai wani tsohon annabi yana zama a Betel, wanda ’ya’yansa suka zo suka faɗa masa dukan abin da mutumin Allah ya yi a can, a ranar. Suka kuma faɗa wa mahaifinsu abin da ya faɗa wa sarki.12Mahaifinsu ya tambaye su ya ce, “Wace hanya ce ya bi?” Sai ’ya’yansa suka nuna masa hanyar da mutumin Allah daga Yahuda ya bi.13Sai ya ce wa ’ya’yansa, “Ku yi wa jakina shimfiɗa.” Da suka yi wa jakin shimfiɗa, sai ya hau.14Ya bi bayan mutumin Allah. Ya same shi yana zama a ƙarƙashin itace oak, sai ya tambaye shi ya ce, “Kai ne mutumin Allah wanda ya zo daga Yahuda?” Ya amsa, “Ni ne.”15Saboda haka annabin ya ce masa, “Zo gida tare da ni ka ci abinci.”16Mutumin Allah ya ce, “Ba zan koma tare da kai ba, ko in ci abinci, ko in sha ruwa tare da kai a can ba.17An faɗa mini ta wurin maganar Ubangiji, ‘Kada ka ci abinci, ko ka sha ruwa a can, ko ka koma ta hanyar da ka zo.’ ”18Sai annabin ya amsa, “Ni ma annabi ne, kamar ka. Kuma mala’ika ya ce mini ta wurin kalmar Ubangiji, ‘Dawo da shi zuwa gidanka saboda yă ci abinci, yă kuma sha ruwa.’ ” (Amma yana masa ƙarya ne.)19Sai mutumin Allah ya koma tare da shi ya kuma ci ya sha a gidansa.20Yayinda suke zaune a teburi, sai maganar Ubangiji ta zo wa tsohon annabin da ya dawo da mutumin Allah.21Sai tsohon annabin ya tā da murya wa mutumin Allah wanda ya zo daga Yahuda, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Ka ƙazantar da maganar Ubangiji, ba ka kuma kiyaye umarnin Ubangiji Allahnka ba.22Ka dawo ka ci abinci, ka kuma sha ruwa a wurin da na faɗa maka kada ka ci, ko ka sha. Saboda haka ba za a binne jikinka a kabarin kakanninka ba.’ ”23Sa’ad da mutumin Allah ya gama ci da sha, sai annabin da ya dawo da shi ya yi wa jakin mutumin Allah shimfiɗa.24Yayinda yake kan hanyarsa, sai wani zaki ya sadu da shi ya kashe shi, aka kuma jefar da jikinsa a kan hanya, jakin da zakin suka tsaya kusa da gawar.25Waɗansu mutane masu wucewa suka ga an yar da gawar a can, zaki yana tsaye kusa da gawar, sai suka tafi suka ba da labarin a birni inda tsohon annabin nan yake zama.26Sa’ad da annabin da ya dawo da mutumin Allah ya ji, sai ya ce, “Mutumin Allah ne, wanda ya ƙazantar da maganar Ubangiji. Ubangiji ya bashe shi ga zaki, wanda ya yayyage shi ya kuma kashe shi, kamar yadda maganar Ubangiji ta gargaɗe shi.”27Sai annabin ya ce wa ’ya’yansa, “Ku yi wa jakina shimfiɗa.” Sai suka yi.28Sai ya fita ya sami an jefar da gawar a hanya, jakin da zakin suna tsaye kusa da shi. Zakin bai ci gawar ko yă yayyage jakin ba.29Saboda haka annabin ya ɗauki gawar mutumin Allah, ya shimfiɗa shi a kan jaki, ya koma da shi cikin birninsa don yă yi makokinsa yă kuma binne shi.30Sai ya kwantar da gawar a kabarinsa, suka yi makoki a kansa, ya kuma ce, “Ayya, abokina!”31Bayan an binne shi, sai ya ce wa ’ya’yansa, “Sa’ad da na mutu, ku binne ni a kabarin da aka binne mutumin Allah; ku kwantar da ƙasusuwana kusa da ƙasusuwansa.32Gama annabcin da ya yi ta maganar Ubangiji gāba da bagaden da yake cikin Betel da kuma wuraren sujada a tuddan da suke a biranen Samariya, ba shakka zai cika.”33Har ma bayan wannan, Yerobowam bai canja daga mugayen hanyoyinsa ba, amma ya ƙara naɗa firistoci domin masujadai da suke kan tuddai daga kowane irin mutane. Duk wanda ya so yă zama firist sai yă naɗa shi don aiki a masujadai da suke kan tuddai.34Wannan ne zunubin gidan Yerobowam da ya kai ga fāɗuwarsa da kuma hallakarsa daga fuskar duniya.Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Sabon Rai Don Kowa 2020 1 Sarakuna 13 00:00:00 00:00:00 0.5x 2.0x https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/1kings/013.mp3 22 13