× Harshe Turai Rashanci Belarusiyanci Yukreniyanci Yaren mutanen Poland Sabiyanci Bulgaria Slovakiyan Czech Romaniyanci Moldoviyanci Azerbaijan Armeniyanci Jojiyanci Albaniyanci Avar Bashkir Tatar Checheniya Slobaniyanci Kuroshiya Estoniyanci Latvia Lituweniyanci Harshen Hungary Yaren mutanen Finland Yaren mutanen Norway Yaren mutanen Sweden Icelandic Girkanci Macedonia Bajamushe Bavarian Yaren mutanen Holland Danish Welsh Gaelic Irish Faransanci Basque Katalaniyanci Italiyanci Galacian Romani Bosnian Amirka ta Arewa Turanci Kudancin Amurka Sifeniyanci Fotigal Guarani Quechuan Aymara Amurka ta Tsakiya Jamaica Nahuatl Kiche Qeqchi Haiti Gabashin Asiya Sinanci Jafananci Yaren Koriya Mongoliyanci Uyghur Hmong Kudu maso gabashin Asiya Malesiya Burma Chin Nepali Cebuano Tagalog Kambodiyanci Thai Indonesiyanci Vietnam Javanisanci Lao Iban IuMien Kachin Lahu Aceh Balinese Bugis Pampanga Sasak Shan Waray Kudancin Asiya Hindi Оdia Awadhi Mizo Kannada Malayalam Marathi Gujarati Tamil Telugu Harshen Punjabi Kurukh Assamese Maithili Bengali Urdu Sinhala Dogri Haryanvi Meitei Konkani Santali Sindhi Koya Thado Sanskrit Devanagari Adilabad Gondi Ahirani Balochi Bundeli Chhattisgarhi Garhwali Kangri Kumaoni Mewari Munda Sadri Seraiki Shekhawati Sylheti Asiya ta Tsakiya Kirgiziya Uzbek Tajik Turkmen Kazakhstan Karakalpak Gabas ta Tsakiya Baturke Ibrananci Larabci Farisanci Kurdawa Pashto 'Yan Koftik Afirka Afirkaans Xhosa Zulu Ndebele Sotho Amharic Wolaytta Dan Najeriya Mossi Ika Dinka Kabyle Ewe Swahili Maroko Somalian Shona Madagaska Igbo Lingala Baoule Siswati Tsonga Tswana Gambiya Yarbawa Kamba Kinyarwanda Hausa Chewa Luo Makua Dyula Fulfulde Kalenjin Kikuyu Kikwango Kirundi Krio Nigerian Pidgin Oromo Tshiluba Tshivenda Twi Umbundu Lugbara Luguru Pular Gussi Maasai Turkana Moba Nuer Shilluk Tamasheq Makonde Bemba Fon Hadiyya Ibibio Kimbundu Kimiiru Lango Liberian Kreyol Lomwe Mende Morisyen Ndau Nyankole Sena Sidamo Soga Songe Sukuma Tarifit Teso Tiv Zande Nahiyar Australiya New Zealand Papua New Guinea Tsoffin Harsuna Aramaic Latin Esperanto 1 1 1 2020 202020101 1 1 1 Sarakuna FarawaFitowaFiristociƘidayaMaimaitawar ShariʼaYoshuwaMahukuntaRut1 Samaʼila2 Samaʼila1 Sarakuna2 Sarakuna1 Tarihi2 TarihiEzraNehemiyaEstaAyubaZaburaKarin MaganaMai HadishiWaƙar WaƙoƙiIshayaIrmiyaMakokiEzekiyelDaniyelHosiyaYowelAmosObadiyaYunanaMikaNahumHabakkukZefaniyaHaggaiZakariyaMalaki--- --- ---MattiyuMarkusLukaYohannaAyyukan ManzanniRomawa1 Korintiyawa2 KorintiyawaGalatiyawaAfisawaFilibbiyawaKolossiyawa1 Tessalonikawa2 Tessalonikawa1 Timoti2 TimotiTitusFilemonIbraniyawaYaƙub1 Bitrus2 Bitrus1 Yohanna2 Yohanna3 YohannaYahudaRuʼuya ta Yohanna1 1 1 18 123456789101112131415161718192021221 1 1 : 1 123456789101112131415161718192021222324252627282930313233343536373839404142434445461 1 1 Sabon Rai Don Kowa 2020 1 Sarakuna 18 Adana Bayanan kula 1Bayan dogon lokaci, a cikin shekara ta uku, maganar Ubangiji ta zo wa Iliya, ta ce, “Tafi, ka gabatar da kanka ga Ahab, zan kuwa aika da ruwan sama a ƙasar.”2Saboda haka Iliya ya tafi ya gabatar da kansa ga Ahab. Yanzu dai yunwa ta tsananta a Samariya,3Ahab kuma ya aika a kawo Obadiya, sarkin fadansa (Obadiya dai cikakken mai gaskata da Ubangiji ne.4Yayinda Yezebel tana kisan annabawan Ubangiji, Obadiya ya ɗauki annabawa ɗari ya ɓoye a kogwanni biyu, hamsin a kowanne, ya kuma tanada musu abinci da kuma ruwa.)5Ahab ya ce wa Obadiya, “Ka ratsa ƙasar zuwa dukan maɓulɓulai da fadamu. Mai yiwuwa ka sami ciyawa mu ba dawakai da alfadarai don su rayu, don kada mu kashe dabbobinmu.”6Saboda haka suka raba ƙasar da za su ratsa, Ahab zai tafi gefe ɗaya, Obadiya kuma yă bi gefe ɗaya.7Yayinda Obadiya yana tafiya, sai Iliya ya sadu da shi. Obadiya ya gane shi, ya rusuna har ƙasa, ya ce, “Kai ne, shugabana, Iliya?”8Iliya ya amsa, ya ce, “I, je ka faɗa wa maigidanka cewa, ‘Iliya yana a nan.’ ”9Obadiya ya yi tambaya, “Me na yi da ba daidai ba, da kake miƙa bawanka ga Ahab don yă kashe?10Na rantse da Ubangiji Allahnka, babu al’umma ko masarauta da mai girma sarki bai aika a nemo ka ba. In suka ce ba ka can, sai yă sa mulkin ko al’ummar su rantse, cewa ai, ba su same ka ba.11Amma yanzu kana faɗa mini in tafi wurin mai girma in ce, ‘Iliya yana a nan.’12Ban san inda Ruhun Ubangiji zai kai ka sa’ad da na bar ka ba. In na tafi na faɗa wa Ahab bai kuma same ka a nan ba, zai sa a kashe ni. Tuna fa, ni bawanka, na yi wa Ubangiji sujada tun ina saurayi.13Ranka yă daɗe, ashe, ba a faɗa maka abin da na yi lokacin da Yezebel ta karkashe annabawan Ubangiji ba? Yadda na ɓoye annabawa ɗari, na sa su hamsin-hamsin a kogwanni biyu, na yi ta ba su abinci da ruwa.14Yanzu fa, kana ce in tafi wurin mai girma sarki, in ce, ‘Iliya yana a nan.’ Ai, zai kashe ni!”15Iliya ya ce, “Na rantse da Ubangiji Maɗaukaki, wanda nake bauta wa, tabbatacce zan gabatar da kaina ga Ahab a yau.”16Saboda haka sai Obadiya ya tafi wurin Ahab ya faɗa masa, Ahab kuwa ya tafi wurin Iliya.17Sa’ad da Ahab ya ga Iliya, sai ya ce masa, “Kai ne wannan, kai mai tā-da-na-zaune-tsaye a Isra’ila?”18Iliya ya amsa, ya ce, “Ban tā-da-na-zaune-tsaye a Isra’ila ba. Amma kai da iyalin mahaifinka, ku kuka tā-da-na-zaune-tsaye. Ka ƙyale umarnai Ubangiji, ka bi Ba’al.19Yanzu ka tara mutane daga dukan Isra’ila su sadu da ni a kan Dutsen Karmel. Ka kuma kawo annabawa ɗari huɗu da hamsin na Ba’al, da kuma annabawa ɗari huɗu na Ashera, waɗanda suke ci a teburin Yezebel.”20Sai Ahab ya aika a duk fāɗin Isra’ila, ya kuma tattara annabawan a kan Dutsen Karmel.21Iliya ya je gaban mutane ya ce, “Har yaushe za ku yi ta yawo tsakanin ra’ayoyi biyu? In Ubangiji ne Allah, ku bi shi; amma in Ba’al Allah ne, ku bi shi.” Mutane dai ba su ce uffam ba.22Sai Iliya ya ce musu, “Ni ne kaɗai annabin Ubangiji da ya rage, amma Ba’al yana da annabawa ɗari huɗu da hamsin.23Ku samo mana bijimai biyu. Bari su zaɓa ɗaya wa kansu, bari kuma su yanka shi kucu-kucu su sa a itace, sai dai, kada su sa wuta a kansa. Ni kuwa zan shirya ɗaya bijimin in sa a kan itace, ni ma, ba zan sa wuta a kansa ba.24Sa’an nan ku kira bisa sunan allahnku, ni kuwa zan kira bisa sunan Ubangiji. Duk allahn da ya amsa ta wurin wuta, shi ne Allah.” Sai dukan jama’a suka ce, “Abin nan da faɗa yana da kyau.”25Iliya ya ce wa annabawan Ba’al, “Ku ku fara zaɓi bijimi ɗaya, ku shirya, da yake kuna da yawa. Ku kira a bisa sunan allahnku, amma kada ku ƙuna wuta.”26Sai suka ɗauki bijimin da aka ba su suka shirya shi. Sa’an nan suka kira bisa sunan Ba’al daga safe har tsakar rana. Suna ihu, “Ya Ba’al, ka amsa mana!” Amma babu wata amsa, babu wani da ya amsa. Suka yi ta rawa kewaye da bagaden da suka yi.27Da tsakar rana, Iliya ya fara yin musu ba’a. Ya ce, “Ku yi ihu da ƙarfi, tabbatacce shi allah ne! Mai yiwuwa yana cikin zurfin tunani, ko dai aiki ya yi masa yawa, ko ya yi tafiya. Mai yiwuwa yana barci ne, dole a tashe shi.”28Sai suka yi ta ihu da ƙarfi suna tsattsaga kansu da takuba da māsu, yadda al’adarsu take, sai da jininsu ya yi ta zuba.29Tsakar rana ta wuce, suka ci gaba da ƙoƙari, suna annabci har lokacin miƙa hadayar yamma ya yi. Amma babu wani da ya tanƙa, babu wani da ya amsa, babu wanda ya kula.30Sa’an nan Iliya ya ce wa dukan mutane, “Ku zo nan wurina.” Suka zo wurinsa, ya kuma shirya bagaden Ubangiji, da ya riga ya zama kufai.31Iliya ya ɗauki duwatsu goma sha biyu, ɗaya don kowace kabila zuriyar Yaƙub, wanda maganar Ubangiji ta zo masa, cewa, “Sunanka zai zama Isra’ila.”32Da waɗannan duwatsun ya gina bagade cikin sunan Ubangiji, ya kuma haƙa wuriya kewaye da shi, isashe da zai ci garwa biyu na irin ƙwayar gyada.33Ya shirya itace, ya yayyanka bijimin kucu-kucu, ya shimfiɗa shi a itacen. Sa’an nan ya ce musu, “Ku cika manyan tuluna da ruwa, ku zuba a kan hadayar da kuma a kan itacen.” Suka zuba.34Ya ce, “Ku sāke yin haka,” sai suka sāke yin haka. Ya umarta, “Ku yi haka sau na uku,” suka kuma yi haka sau na uku.35Ruwan ya gangara kewaye da bagaden har ma ya cika wuriyar.36A lokacin hadaya, sai annabi Iliya ya zo gaba ya yi addu’a, ya ce, “Ya Ubangiji Allah na Ibrahim, na Isra’ila da kuma na Yaƙub, bari a sani a yau cewa kai Allah ne a cikin Isra’ila, a kuma san cewa ni bawanka ne, na kuma yi dukan waɗannan abubuwa bisa umarninka.37Ka amsa mini, ya Ubangiji, ka amsa mini, saboda waɗannan mutane su san cewa kai, ya Ubangiji, kai ne Allah, su kuma san cewa kana sāke juye zukatansu zuwa gare ka.”38Sai wutar Ubangiji ya fāɗo, ya cinye hadayar, itacen, duwatsun da kuma ƙasar, ya lashe ruwan da yake cikin wuriyar.39Sa’ad da mutane suka ga wannan, sai suka rusuna, suka sunkuyar da kai suka ce, “ Ubangiji, shi ne Allah! Ubangiji, shi ne Allah!”40Sa’an nan Iliya ya umarce su, ya ce, “Ku kama annabawan Ba’al, kada ku bar waninsu yă tsere!” Suka kama su, Iliya kuwa ya sa aka gangara da su zuwa Kwarin Kishon, aka yayyanka su a can.41Sai Iliya ya ce wa Ahab, “Ka haura gida, ka ci, ka sha, gama ina jin motsin ruwan sama mai yawa.”42Sai Ahab ya ruga don yă ci, yă sha, amma Iliya ya hau kan ƙwanƙolin Karmel, ya rusuna ƙasa, ya sa fuska a tsakanin gwiwarsa.43Ya ce wa bawansa, “Tafi ka dubi wajen teku.” Sai bawan ya haura ya duba. Ya ce, “Ba kome a can.” Sau bakwai Iliya ya ce, “Koma.”44Sau na bakwai, bawan ya ce, “Wani girgije ƙarami kamar hannun mutum yana tasowa daga teku.” Sai Iliya ya ce, “Je ka faɗa wa Ahab, ‘Shirya keken yaƙinka, ka gangara kafin ruwan sama yă tare ka.’ ”45Ana cikin haka, sarari ya ƙara duhunta da girgije, iska ta taso, sai ruwan sama kamar da bakin kwarya ya sauko, Ahab kuwa ya hau zuwa Yezireyel.46Ikon Ubangiji ya sauko a kan Iliya, ya sha ɗamara, ya ruga a guje a gaban Ahab har zuwa Yezireyel.Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide. Sabon Rai Don Kowa 2020 1 Sarakuna 18 00:00:00 00:00:00 0.5x 2.0x https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/1kings/018.mp3 22 18