× Harshe Turai Rashanci Belarusiyanci Yukreniyanci Yaren mutanen Poland Sabiyanci Bulgaria Slovakiyan Czech Romaniyanci Moldoviyanci Azerbaijan Armeniyanci Jojiyanci Albaniyanci Avar Bashkir Tatar Checheniya Slobaniyanci Kuroshiya Estoniyanci Latvia Lituweniyanci Harshen Hungary Yaren mutanen Finland Yaren mutanen Norway Yaren mutanen Sweden Icelandic Girkanci Macedonia Bajamushe Bavarian Yaren mutanen Holland Danish Welsh Gaelic Irish Faransanci Basque Katalaniyanci Italiyanci Galacian Romani Bosnian Amirka ta Arewa Turanci Kudancin Amurka Sifeniyanci Fotigal Guarani Quechuan Aymara Amurka ta Tsakiya Jamaica Nahuatl Kiche Qeqchi Haiti Gabashin Asiya Sinanci Jafananci Yaren Koriya Mongoliyanci Uyghur Hmong Kudu maso gabashin Asiya Malesiya Burma Chin Nepali Cebuano Tagalog Kambodiyanci Thai Indonesiyanci Vietnam Javanisanci Lao Iban IuMien Kachin Lahu Aceh Balinese Bugis Pampanga Sasak Shan Waray Kudancin Asiya Hindi Оdia Awadhi Mizo Kannada Malayalam Marathi Gujarati Tamil Telugu Harshen Punjabi Kurukh Assamese Maithili Bengali Urdu Sinhala Dogri Haryanvi Meitei Konkani Santali Sindhi Koya Thado Sanskrit Devanagari Adilabad Gondi Ahirani Balochi Bundeli Chhattisgarhi Garhwali Kangri Kumaoni Mewari Munda Sadri Seraiki Shekhawati Sylheti Asiya ta Tsakiya Kirgiziya Uzbek Tajik Turkmen Kazakhstan Karakalpak Gabas ta Tsakiya Baturke Ibrananci Larabci Farisanci Kurdawa Pashto 'Yan Koftik Afirka Afirkaans Xhosa Zulu Ndebele Sotho Amharic Wolaytta Dan Najeriya Mossi Ika Dinka Kabyle Ewe Swahili Maroko Somalian Shona Madagaska Igbo Lingala Baoule Siswati Tsonga Tswana Gambiya Yarbawa Kamba Kinyarwanda Hausa Chewa Luo Makua Dyula Fulfulde Kalenjin Kikuyu Kikwango Kirundi Krio Nigerian Pidgin Oromo Tshiluba Tshivenda Twi Umbundu Lugbara Luguru Pular Gussi Maasai Turkana Moba Nuer Shilluk Tamasheq Makonde Bemba Fon Hadiyya Ibibio Kimbundu Kimiiru Lango Liberian Kreyol Lomwe Mende Morisyen Ndau Nyankole Sena Sidamo Soga Songe Sukuma Tarifit Teso Tiv Zande Nahiyar Australiya New Zealand Papua New Guinea Tsoffin Harsuna Aramaic Latin Esperanto 1 1 1 2020 202020101 1 1 Zabura FarawaFitowaFiristociƘidayaMaimaitawar ShariʼaYoshuwaMahukuntaRut1 Samaʼila2 Samaʼila1 Sarakuna2 Sarakuna1 Tarihi2 TarihiEzraNehemiyaEstaAyubaZaburaKarin MaganaMai HadishiWaƙar WaƙoƙiIshayaIrmiyaMakokiEzekiyelDaniyelHosiyaYowelAmosObadiyaYunanaMikaNahumHabakkukZefaniyaHaggaiZakariyaMalaki--- --- ---MattiyuMarkusLukaYohannaAyyukan ManzanniRomawa1 Korintiyawa2 KorintiyawaGalatiyawaAfisawaFilibbiyawaKolossiyawa1 Tessalonikawa2 Tessalonikawa1 Timoti2 TimotiTitusFilemonIbraniyawaYaƙub1 Bitrus2 Bitrus1 Yohanna2 Yohanna3 YohannaYahudaRuʼuya ta Yohanna1 1 1 78 1234567891011121314151617181920212223242526272829303132333435363738394041424344454647484950515253545556575859606162636465666768697071727374757677787980818283848586878889909192939495969798991001011021031041051061071081091101111121131141151161171181191201211221231241251261271281291301311321331341351361371381391401411421431441451461471481491501 1 1 : 56 1234567891011121314151617181920212223242526272829303132333435363738394041424344454647484950515253545556575859606162636465666768697071721 1 1 Sabon Rai Don Kowa 2020 Zabura 78 Adana Bayanan kula 1Ya mutanena, ku ji koyarwata; ku saurari kalmomin bakina.2Zan buɗe bakina da misalai, zan faɗi ɓoyayyun abubuwa, abubuwan dā,3abin da muka ji muka kuma sani, abubuwan da kakanninmu suka faɗa mana.4Ba za mu ɓoye su wa ’ya’yanmu ba; za mu faɗa wa tsara mai zuwa ayyukan da suka zama yabo na Ubangiji, ikonsa, da abubuwan banmamakin da ya aikata.5Ya kafa ƙa’idodi wa Yaƙub ya kuma kafa doka a cikin Isra’ila, wadda ya umarce kakanni-kakanninmu su koya wa ’ya’yansu,6don tsara na biye su san su, har da ’ya’yan da ba a riga an haifa ba, su kuma su faɗa wa ’ya’yansu.7Ta haka za su dogara ga Allah ba kuwa za su manta da ayyukansa ba amma za su kiyaye umarnansa.8Ba za su zama kamar kakanni kakanninsu ba, masu taurinkai da kuma tsara masu tayarwa, waɗanda zukatansu ba su yi biyayya ga Allah ba, waɗanda zukatansu ba su yi aminci ga Allah ba.9Mutanen Efraim, ko da yake suna da bakkuna, suka juya da baya a ranar yaƙi;10ba su kiyaye alkawarin Allah ba suka kuma ƙi su yi rayuwa ta wurin dokarsa.11Suka manta da abin da ya aikata, abubuwan banmamakin da ya nuna musu.12Ya yi mu’ujizai a idanun kakanninsu a ƙasar Masar, a yankin Zowan.13Ya raba teku ya kuma bi da su ciki; ya sa ruwa ya tsaya daram kamar bango.14Ya bishe su da girgije da rana da kuma haske daga wuta dukan dare.15Ya tsage duwatsu a cikin hamada ya kuma ba su ruwaye a yalwace kamar tekuna;16ya fid da rafuffuka daga dutsen da ya tsaga ya sa ruwa ya gudu kamar koguna.17Amma suka ci gaba da yin masa zunubi, suna tayarwa a cikin hamada a kan Mafi Ɗaukaka.18Da gangan suka gwada Allah ta wurin neman abincin da suke kwaɗayi.19Suka yi magana a kan Allah, suna cewa, “Allah zai iya shimfiɗa tebur a cikin hamada?20Sa’ad da ya bugi dutse, ruwa ya ɓulɓulo, rafuffuka suka yi gudu a yalwace. Amma zai iya ba mu abinci? Zai iya tanada wa mutanensa nama?”21Sa’ad da Ubangiji ya ji su, ya yi fushi ƙwarai; wutarsa ta ɓarke a kan Yaƙub, hasalarsa kuwa ta tashi a kan Isra’ila,22gama ba su gaskata ga Allah ba ko su dogara ga cetonsa.23Duk da haka ya ba da umarni ga sarari a bisa ya kuma buɗe ƙofofin sammai;24ya sauko da Manna wa mutanensa don su ci, ya ba su hatsin sama.25Mutane suka ci burodin mala’iku; ya aika musu dukan abincin da za su iya ci.26Ya saki iskar gabas daga sammai ya kuma saki iskar yamma ta wurin ikonsa.27Ya sauko da nama a kansu kamar ƙura, tsuntsaye masu firiya kamar yashi a bakin teku.28Ya sa suka sauka a cikin sansaninsu, ko’ina kewaye da tentunansu.29Suka ci har suka sami fiye da abin da ya ishe su, gama ya ba su abin da suka yi kwaɗayi.30Amma kafin su juyo daga abincin da suka yi kwaɗayi, kai tun ma yana a bakunansu,31fushin Allah ya ƙuna a kansu; ya karkashe waɗanda suka fi ƙiba a cikinsu, yana yankan matasan Isra’ila.32Duk da haka, suka ci gaba da yin zunubi; duk da abubuwan banmamakinsa, ba su gaskata ba.33Saboda haka ya sa kwanakinsu suka ƙare a banza shekarunsu kuma cikin masifa.34A duk sa’ad da Allah ya kashe su, sai su neme shi; sukan juyo a natse gare shi.35Sun tuna cewa Allah ne Dutsensu, cewa Allah Mafi Ɗaukaka ne Mai fansarsu.36Amma sai su yi ta yin masa zaƙin baki, suna masa ƙarya da harsunansu;37zukatansu ba sa biyayya gare shi, ba su da aminci ga alkawarinsa.38Duk da haka ya kasance mai jinƙai; ya gafarta laifofinsu bai kuwa hallaka su ba. Sau da sau ya janye fushinsa bai kuwa sa fushinsa yă ƙuna ba.39Ya tuna cewa su naman jiki ne kawai, iska mai wucewa da ba ta dawowa.40Sau da yawa sun tayar masa a cikin hamada suka kuma ɓata masa rai a jeji!41Sau da sau suka riƙa gwada Allah; suka tsokane Mai Tsarki na Isra’ila.42Ba su tuna da ikonsa, a ranar da ya fanshe su daga mai danniya,43ranar da ya nuna mu’ujizansa a Masar abubuwan banmamakinsa a yankin Zowan ba.44Ya mai da kogunansu suka zama jini; ba su iya sha daga rafuffuka ba.45Ya aika da tarin ƙudajen da suka cinye su, da kwaɗin da suka wahalshe su.46Ya ba da hatsinsu ga fāra, amfanin gonakinsu ga ɗango.47Ya lalace inabinsu da ƙanƙara itatuwan al’ul nasu kuma da jaura.48Ya miƙa shanunsu ga ƙanƙara, tumakinsu ga aradun tsawa.49Ya saki musu fushinsa mai zafi, hasalarsa, zafin rai da kuma ɓacin ransa, ƙungiyar mala’iku masu hallakarwa.50Ya shirya hanya wa fushinsa; bai tsare ransu daga mutuwa ba amma ya miƙa su ga annoba.51Ya bugi kowane ɗan fari na Masar, mafari ƙarfin mazantakansu a tentunan Ham.52Amma ya fitar da mutanensa kamar garke; ya bi da su kamar tumaki ta cikin hamada.53Ya bi da su lafiya ƙalau, don kada su ji tsoro; amma teku ya cinye abokan gābansu.54Ta haka ya kawo su iyakar ƙasa mai tsarki, zuwa ƙasar tudun da hannunsa na dama ya kame.55Ya kori al’ummai a gabansu ya rarraba ƙasashensu gare su a matsayin gādo; ya zaunar da kabilan Isra’ila a gidajensu.56Amma suka gwada Allah suka tayar wa Mafi Ɗaukaka; ba su kiyaye ƙa’idodinsa ba.57Kamar kakanninsu suka zama marasa biyayya da marasa aminci, marar tabbas kamar tanƙwararren baka.58Suka ba shi haushi da masujadansu na kan tudu; suka tayar da kishinsa da gumakansu.59Sa’ad da Allah ya ji su, ya yi fushi ƙwarai; ya ƙi Isra’ila gaba ɗaya.60Ya yashe tabanakul na Shilo, tentin da ya kafa a cikin mutane.61Ya aika da akwatin alkawarin ƙarfinsa zuwa bauta, darajarsa zuwa cikin hannuwan abokin gāba.62Ya ba da mutanensa ga takobi; ya yi fushi ƙwarai da gādonsa.63Wuta ta cinye matasansu maza, ’yan matansu kuma ba su da waƙoƙin aure;64aka karkashe firistocinsu, gwaurayensu kuwa ba su iya makoki ba.65Sa’an nan Ubangiji ya farka sai ka ce daga barcinsa, kamar yadda mutum kan farka daga buguwar ruwan inabi.66Ya kori abokan gābansa; ya sa suka sha madawwamiyar kunya.67Sa’an nan ya ƙi tentunan Yusuf, bai zaɓi kabilar Efraim ba;68amma ya zaɓi kabilar Yahuda, Dutsen Sihiyona, wanda ya ƙaunaci.69Ya gina wurinsa mai tsarki kamar bisa, kamar duniyar da ya kafa har abada.70Ya zaɓi Dawuda bawansa ya kuma ɗauke shi daga ɗakin tumaki;71daga kiwon tumaki ya kawo shi don yă kuma zama makiyayin mutanensa Yaƙub, na Isra’ila gādonsa.72Dawuda kuwa ya zama makiyayinsu da mutuncin zuciya; da hannuwa masu gwaninta ya bi da su.Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide. Sabon Rai Don Kowa 2020 Zabura 78 00:00:00 00:00:00 0.5x 2.0x https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/psalms/078.mp3 150 78