× Harshe Turai Rashanci Belarusiyanci Yukreniyanci Yaren mutanen Poland Sabiyanci Bulgaria Slovakiyan Czech Romaniyanci Moldoviyanci Azerbaijan Armeniyanci Jojiyanci Albaniyanci Avar Bashkir Tatar Checheniya Slobaniyanci Kuroshiya Estoniyanci Latvia Lituweniyanci Harshen Hungary Yaren mutanen Finland Yaren mutanen Norway Yaren mutanen Sweden Icelandic Girkanci Macedonia Bajamushe Bavarian Yaren mutanen Holland Danish Welsh Gaelic Irish Faransanci Basque Katalaniyanci Italiyanci Galacian Romani Amirka ta Arewa Turanci Kudancin Amurka Sifeniyanci Fotigal Guarani Quechuan Aymara Amurka ta Tsakiya Jamaica Nahuatl Kiche Qeqchi Haiti Gabashin Asiya Sinanci Jafananci Yaren Koriya Mongoliyanci Uyghur Hmong Kudu maso gabashin Asiya Malesiya Burma Chin Nepali Cebuano Tagalog Kambodiyanci Thai Indonesiyanci Vietnam Javanisanci Lao Iban IuMien Kachin Lahu Kudancin Asiya Hindi Оdia Awadhi Mizo Kannada Malayalam Marathi Gujarati Tamil Telugu Harshen Punjabi Kurukh Assamese Maithili Bengali Urdu Sinhala Dogri Haryanvi Meitei Konkani Santali Sindhi Koya Thado Sanskrit Devanagari Asiya ta Tsakiya Kirgiziya Uzbek Tajik Turkmen Kazakhstan Karakalpak Gabas ta Tsakiya Baturke Ibrananci Larabci Farisanci Kurdawa Pashto 'Yan Koftik Afirka Afirkaans Xhosa Zulu Ndebele Sotho Amharic Wolaytta Dan Najeriya Mossi Ika Dinka Kabyle Ewe Swahili Maroko Somalian Shona Madagaska Igbo Lingala Baoule Siswati Tsonga Tswana Gambiya Yarbawa Kamba Kinyarwanda Hausa Chewa Luo Makua Dyula Fulfulde Kalenjin Kikuyu Kikwango Kirundi Krio Nigerian Pidgin Oromo Tshiluba Tshivenda Twi Umbundu Lugbara Luguru Pular Gussi Maasai Turkana Moba Nuer Shilluk Tamasheq Makonde Nahiyar Australiya New Zealand Papua New Guinea Tsoffin Harsuna Aramaic Latin Esperanto 1 1 1 2020 202020101 1 1 Ayyukan Manzanni FarawaFitowaFiristociƘidayaMaimaitawar ShariʼaYoshuwaMahukuntaRut1 Samaʼila2 Samaʼila1 Sarakuna2 Sarakuna1 Tarihi2 TarihiEzraNehemiyaEstaAyubaZaburaKarin MaganaMai HadishiWaƙar WaƙoƙiIshayaIrmiyaMakokiEzekiyelDaniyelHosiyaYowelAmosObadiyaYunanaMikaNahumHabakkukZefaniyaHaggaiZakariyaMalaki--- --- ---MattiyuMarkusLukaYohannaAyyukan ManzanniRomawa1 Korintiyawa2 KorintiyawaGalatiyawaAfisawaFilibbiyawaKolossiyawa1 Tessalonikawa2 Tessalonikawa1 Timoti2 TimotiTitusFilemonIbraniyawaYaƙub1 Bitrus2 Bitrus1 Yohanna2 Yohanna3 YohannaYahudaRuʼuya ta Yohanna1 1 1 18 123456789101112131415161718192021222324252627281 1 1 : 1 123456789101112131415161718192021222324252627281 1 1 Sabon Rai Don Kowa 2020 Ayyukan Manzanni 18 Adana Bayanan kula 1Bayan haka, Bulus ya bar Atens ya tafi Korint.2A can ya sadu da wani mutumin Yahuda mai suna Akwila, ɗan garin Fontus, wanda ya je can ba da daɗewa ba daga Italiya tare da matarsa Firiskila, gama Kalaudiyus ya umarci dukan Yahudawa su bar Roma. Sai Bulus ya tafi yă gan su,3da yake shi ma mai ɗinkin tenti ne kamar su, sai ya zauna ya yi aiki tare da su.4Kowace Asabbaci kuwa yakan yi muhawwara a majami’a, yana ƙoƙari yă rinjayi Yahudawa da Hellenawa.5Sa’ad da Sila da Timoti suka iso daga Makidoniya, sai Bulus ya ba da kansa ga yin wa’azi kaɗai, yana tabbatar wa Yahudawa cewa Yesu shi ne Kiristi.6Amma sa’ad da Yahudawa suka yi hamayya da Bulus suka kuma shiga zaginsa, sai ya karkaɗe tufafinsa a cikin rashin yarda, ya ce musu, “Alhakinku yana a kanku! Ba ni da wani laifi. Daga yanzu zan tafi wajen Al’ummai.”7Sai Bulus ya bar majami’ar ya kuma tafi ƙofar da take kusa da gidan Titus Yustus, mai yi wa Allah sujada.8Kirisbus, shugaban majami’a, da dukan iyalinsa suka gaskata Ubangiji; Korintiyawa masu yawa kuwa da suka ji shi suka gaskata, aka kuwa yi musu baftisma.9Wata rana da dad dare, Ubangiji ya yi magana da Bulus a cikin wahayi ya ce, “Kada ka ji tsoro; ka ci gaba da yin magana, kada ka yi shiru.10Gama ina tare da kai, ba kuma wanda zai fāɗa maka ya cuce ka, domin ina da mutane da yawa a wannan birni.”11Saboda haka Bulus ya zauna a nan har shekara ɗaya da rabi, yana koya musu maganar Allah.12Yayinda Galliyo yake muƙaddas Akayya, Yahudawa suka haɗa kai suka tasar wa Bulus, suka kuwa kawo shi cikin kotu.13Suka yi zarge cewa, “Wannan mutum yana rarrashin mutane su yi wa Allah sujada a hanyoyin da suka saɓa wa doka.”14A daidai sa’ad da Bulus yana shirin yin magana, sai Galliyo ya ce wa Yahudawan, “Da a ce ku Yahudawa kuna gunaguni game da munafunci, ko kuma wani babban laifi, da sai in iya sauraronku.15Amma da yake ya shafi gardama ce game da kalmomi da sunaye da kuma dokarku, sai ku ji da ita da kanku. Ni ba zan zama mai shari’a kan irin waɗannan abubuwa ba.”16Saboda haka ya kore su.17Sai duk suka juya kan Sostenes shugaban majami’a suka yi masa dūka a gaban kotun. Amma Galliyo ko yă kula.18Bulus kuwa ya ci gaba da zama a Korint na ’yan kwanaki. Sa’an nan ya bar ’yan’uwa ya shiga jirgin ruwa zuwa Suriya tare da Firiskila da Akwila. Kafin ya tashi, ya aske kansa a Kenkireya saboda alkawarin da ya yi.19Suka isa Afisa, inda Bulus ya bar Firiskila da Akwila. Shi kansa ya shiga majami’a ya kuma yi muhawwara da Yahudawa.20Sa’ad da suka roƙe shi ya ƙara ’yan kwanaki da su, bai yarda ba.21Amma da yake barin wurin, ya yi alkawari cewa, “Zan dawo in Allah ya yarda.” Sa’an nan ya tashi daga Afisa a jirgin ruwa.22Sa’ad da ya sauka a Kaisariya, sai ya haura ya gai da ikkilisiya sa’an nan ya gangara zuwa Antiyok.23Bayan ya yi ’yan kwanaki a Antiyok, Bulus ya tashi daga can ya zaga ko’ina a yankin Galatiya da Firjiya, yana ƙarfafa dukan almajirai.24Ana cikin haka sai wani mutumin Yahuda mai suna Afollos, ɗan ƙasar Alekzandariya, ya zo Afisa. Shi masani ne, yana da cikakken sani na Nassosi.25An horar da shi a hanyar Ubangiji, ya kuma himma ƙwarai a magana, ya kuma yi koyarwa game da Yesu, daidai, ko da yake baftismar Yohanna ce kaɗai ya sani.26Sai ya fara magana gabagadi a majami’a. Sa’ad da Firiskila da Akwila suka ji shi, sai suka gayyace shi gidansu suka ƙara bayyana masa hanyar Allah sosai.27Sa’ad da Afollos ya so ya tafi Akayya, sai ’yan’uwa suka ƙarfafa shi suka kuma rubuta wa almajiran da suke can da su marabce shi. Da isowarsa, ya zama da taimako ƙwarai ga waɗanda ta wurin alheri suka gaskata.28Gama da ƙwazo ya ƙaryata Yahudawa a muhawwara a fili, yana tabbatar daga Nassosi cewa Yesu shi ne Kiristi.Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide. Sabon Rai Don Kowa 2020 Ayyukan Manzanni 18 00:00:00 00:00:00 0.5x 2.0x https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/acts/018.mp3 28 18