× Harshe Turai Rashanci Belarusiyanci Yukreniyanci Yaren mutanen Poland Sabiyanci Bulgaria Slovakiyan Czech Romaniyanci Moldoviyanci Azerbaijan Armeniyanci Jojiyanci Albaniyanci Avar Bashkir Tatar Checheniya Slobaniyanci Kuroshiya Estoniyanci Latvia Lituweniyanci Harshen Hungary Yaren mutanen Finland Yaren mutanen Norway Yaren mutanen Sweden Icelandic Girkanci Macedonia Bajamushe Bavarian Yaren mutanen Holland Danish Welsh Gaelic Irish Faransanci Basque Katalaniyanci Italiyanci Galacian Romani Bosnian Amirka ta Arewa Turanci Kudancin Amurka Sifeniyanci Fotigal Guarani Quechuan Aymara Amurka ta Tsakiya Jamaica Nahuatl Kiche Qeqchi Haiti Gabashin Asiya Sinanci Jafananci Yaren Koriya Mongoliyanci Uyghur Hmong Kudu maso gabashin Asiya Malesiya Burma Chin Nepali Cebuano Tagalog Kambodiyanci Thai Indonesiyanci Vietnam Javanisanci Lao Iban IuMien Kachin Lahu Aceh Balinese Bugis Pampanga Sasak Shan Waray Kudancin Asiya Hindi Оdia Awadhi Mizo Kannada Malayalam Marathi Gujarati Tamil Telugu Harshen Punjabi Kurukh Assamese Maithili Bengali Urdu Sinhala Dogri Haryanvi Meitei Konkani Santali Sindhi Koya Thado Sanskrit Devanagari Adilabad Gondi Ahirani Balochi Bundeli Chhattisgarhi Garhwali Kangri Kumaoni Mewari Munda Sadri Seraiki Shekhawati Sylheti Asiya ta Tsakiya Kirgiziya Uzbek Tajik Turkmen Kazakhstan Karakalpak Gabas ta Tsakiya Baturke Ibrananci Larabci Farisanci Kurdawa Pashto 'Yan Koftik Afirka Afirkaans Xhosa Zulu Ndebele Sotho Amharic Wolaytta Dan Najeriya Mossi Ika Dinka Kabyle Ewe Swahili Maroko Somalian Shona Madagaska Igbo Lingala Baoule Siswati Tsonga Tswana Gambiya Yarbawa Kamba Kinyarwanda Hausa Chewa Luo Makua Dyula Fulfulde Kalenjin Kikuyu Kikwango Kirundi Krio Nigerian Pidgin Oromo Tshiluba Tshivenda Twi Umbundu Lugbara Luguru Pular Gussi Maasai Turkana Moba Nuer Shilluk Tamasheq Makonde Bemba Fon Hadiyya Ibibio Kimbundu Kimiiru Lango Liberian Kreyol Lomwe Mende Morisyen Ndau Nyankole Sena Sidamo Soga Songe Sukuma Tarifit Teso Tiv Zande Nahiyar Australiya New Zealand Papua New Guinea Tsoffin Harsuna Aramaic Latin Esperanto 1 1 1 2020 202020101 1 1 Ayyukan Manzanni FarawaFitowaFiristociƘidayaMaimaitawar ShariʼaYoshuwaMahukuntaRut1 Samaʼila2 Samaʼila1 Sarakuna2 Sarakuna1 Tarihi2 TarihiEzraNehemiyaEstaAyubaZaburaKarin MaganaMai HadishiWaƙar WaƙoƙiIshayaIrmiyaMakokiEzekiyelDaniyelHosiyaYowelAmosObadiyaYunanaMikaNahumHabakkukZefaniyaHaggaiZakariyaMalaki--- --- ---MattiyuMarkusLukaYohannaAyyukan ManzanniRomawa1 Korintiyawa2 KorintiyawaGalatiyawaAfisawaFilibbiyawaKolossiyawa1 Tessalonikawa2 Tessalonikawa1 Timoti2 TimotiTitusFilemonIbraniyawaYaƙub1 Bitrus2 Bitrus1 Yohanna2 Yohanna3 YohannaYahudaRuʼuya ta Yohanna1 1 1 25 123456789101112131415161718192021222324252627281 1 1 : 1 1234567891011121314151617181920212223242526271 1 1 Sabon Rai Don Kowa 2020 Ayyukan Manzanni 25 Adana Bayanan kula 1Kwana uku bayan isowa a lardin, sai Festus ya haura daga Kaisariya zuwa Urushalima,2inda manyan firistoci da shugabannin Yahudawa suka bayyana a gabansa suka kuma gabatar da ƙararsu a kan Bulus.3Suka roƙi Festus a gaggauce a matsayin alfarma gare su, da yă sa a mai da Bulus Urushalima, gama sun ’yan kwanto su kashe shi a hanya.4Festus ya amsa ya ce, “Bulus yana tsare a Kaisariya, ni da kaina kuma zan je can ba da daɗewa ba.5Ku sa waɗansu daga cikin shugabanninku su tafi tare da ni su kawo ƙararsu a kan mutumin a can, in ya aikata wani laifi.”6Bayan ya yi kwanaki takwas ko goma tare da su, sai ya gangara zuwa Kaisariya, kashegari kuma ya kira a yi zaman kotu ya kuma umarta a kawo Bulus a gabansa.7Da Bulus ya bayyana, sai Yahudawan da suka gangaro daga Urushalima suka tsaya kewaye shi, suna kawo ƙarar masu tsanani da yawa a kansa, waɗanda ba su iya tabbatarwa ba.8Sa’an nan Bulus ya kāre kansa ya ce, “Ban aikata wani laifi game da dokokin Yahudawa ko game da haikali ko kuma game da Kaisar ba.”9Festus, da yake yana so yă yi wa Yahudawa alfarma, sai ya ce wa Bulus, “Ka yarda ka je Urushalima a yi maka shari’a a can a gabana a kan waɗannan zarge?”10Bulus ya amsa ya ce, “Yanzu ina tsaye a gaban kotun Kaisar, inda ya kamata a yi mini shari’a. Ban yi wani laifi ga Yahudawa ba, kai da kanka ma ka san da haka sarai.11In kuwa ina da wani laifin da ya isa kisa, ban ƙi in mutu ba. Amma in ƙarar da waɗannan Yahudawa suka kawo a kaina ba gaskiya ba ne, ba wanda yake da iko ya ba da ni a gare su. Na ɗaukaka ƙara zuwa gaban Kaisar!”12Bayan Festus ya yi shawara da majalisarsa sai ya ce, “Ka ɗaukaka ƙara zuwa gaban Kaisar. To, ga Kaisar kuwa za ka tafi!”13Bayan ’yan kwanaki sai Sarki Agiriffa da Bernis suka iso Kaisariya don su yi wa Festus gaisuwar bangirma.14Da yake za su yi kwanaki da dama a can, sai Festus ya tattauna batun Bulus da sarki. Ya ce, “Akwai mutumin da Felis ya bari a daure.15Sa’ad da na je Urushalima, manyan firistoci da dattawan Yahudawa suka kawo ƙara game da shi suka kuma nema a hukunta shi.16“Na gaya musu cewa ba al’adar Romawa ba ce a hukunta mutum kafin ya fuskanci masu ƙararsa ya kuma sami damar kāre kansa game da ƙararsu.17Da suka zo nan tare da ni, ban yi wani jinkiri ba, na kira zaman kotu kashegari kuma na umarta a kawo mutumin.18Sa’ad da masu zarginsa suka tashi tsaye don su yi magana, ba su zarge shi da wani laifin da na yi tsammani ba.19A maimako haka, sai suka kawo waɗansu ’yan maganganu game da addininsu da ba su yarda da shi ba da kuma game da wani Yesu da ya mutu wanda Bulus ya ce yana da rai.20Na rasa yadda zan bincike irin abubuwan nan; saboda haka na yi tambaya ko zai yarda ya tafi Urushalima a yi masa shari’a a can game da waɗannan zargi.21Da Bulus ya ɗaukaka ƙara zuwa gaban Babban Sarki sai na umarta a tsare shi har kafin in aika shi zuwa ga Kaisar.”22Sai Agiriffa ya ce wa Festus, “Ni ma zan so in saurari mutumin da kaina.” Sai ya amsa ya ce, “Za ka kuwa ji shi gobe.”23Kashegari Agiriffa da Bernis suka yi shiga irin ta sarauta suka shiga ɗakin jama’a tare da manyan sojoji da manyan mutanen birni. Da umarnin Festus, sai aka shigo da Bulus.24Sai Festus ya ce, “Sarki Agiriffa, da kuma dukan waɗanda suke tare da mu, kun ga wannan mutum! Dukan jama’ar Yahudawa sun kawo mini kararsa a Urushalima da kuma a nan Kaisariya, suna kururuwa suna cewa bai kamata a bar shi da rai ba.25Ban same shi da wani laifin da ya isa kisa ba, amma saboda ya ɗaukaka ƙararsa zuwa gaban Babban Sarki sai na yanke shawara in aika da shi Roma.26Ba ni da wata tabbatacciyar maganar da zan rubuta wa Mai Girma game da shi. Saboda haka na kawo shi a gabanku duka, musamman a gabanka, Sarki Agiriffa, saboda a sakamakon wannan bincike zan iya samun abin da zan rubuta.27Don a ganina wauta ce a aika da ɗan kurkuku ba tare da an nuna zargin da ake yi a kansa ba.”Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide. Sabon Rai Don Kowa 2020 Ayyukan Manzanni 25 00:00:00 00:00:00 0.5x 2.0x https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/acts/025.mp3 28 25