Baibul a cikin shekara guda Nuwamba 14Ezekiyel 19:1-141. “Sai ka yi makoki domin hakiman Isra'ila,2. Ka ce, ‘Mahaifiyarka zakanya ce a cikin zakoki, Ta yi zamanta tare da 'yan zakoki, Ta yi renon kwiyakwiyanta.3. Ta goyi ɗaya daga cikin kwiyakwiyanta, Ya zama sagari, Sai ya koyi kamun nama, ya cinye mutane.4. Da al'ummai suka ji labarinsa, Sai suka kama shi cikin wushefensu, Suka ja shi da ƙugiyoyi zuwa Masar.5. Sa'ad da ta ga wanda ta sa zuciya a kansa ya tafi, Sai ta ɗauki ɗaya kuma daga cikin kwiyakwiyanta, Ta goye shi ya zama sagari.6. Sai ya yi ta kai da kawowa a cikin zakoki, Ya zama sagari, Ya koyi kamun nama, ya cinye mutane.7. Ya lalatar da kagaransu, Ya mai da biranensu kufai, Ƙasar da waɗanda suke cikinta suka tsorata da jin rurinsa.8. Sai al'ummai suka kafa masa tarko a kowane waje, Sun kafa masa tarko, Suka kama shi cikin wushefensu.9. Suka sa masa ƙugiyoyi, sa'an nan suka sa shi cikin suru, Suka kai shi wurin Sarkin Babila. Suka sa shi a kurkuku don kada a ƙara jin rurinsa a kan duwatsun Isra'ila.’ ”10. “ ‘Mahaifiyarka tana kama da kurangar inabi, Wadda aka dasa kusa da ruwa, Ta ba da 'ya'ya da rassa da yawa, saboda isasshen ruwa.11. Rassanta masu ƙarfi sun zama sandunan masu mulki, Ta yi tsayi zuwa sama duk da rassan, Ana hangenta daga nesa.12. Amma aka tumɓuke kurangar inabin da fushi, Aka jefar da ita ƙasa. Iskar gabas ta busar da ita, 'Ya'yanta suka kakkaɓe, Rassanta masu ƙarfi sun bushe, wuta kuwa ta cinye su.13. Yanzu na dasa ta a jeji, cikin busasshiyar ƙasa,14. Wuta ta fito daga jikinta Ta cinye rassanta da 'ya'yanta, Don haka ba wani reshe mai ƙarfi da ya ragu, wanda zai zama sandan mulki. Wannan makoki ne, ya kuwa tabbata makoki.’ ”Ezekiyel 20:1-491. A kan rana ta goma ga watan biyar a shekara ta bakwai, sai waɗansu dattawan Isra'ila suka zo don su yi roƙo a wurin Ubangiji. Suka zauna a gabana.2. Ubangiji kuwa ya yi magana da ni ya ce,3. “Ɗan mutum, ka faɗa wa dattawan Isra'ila cewa, ‘Ni Ubangiji Allah na ce kun zo ku yi roƙo a wurina, amma hakika, ba na roƙuwa a gare ku.’4. “Za ka shara'anta su? Ɗan mutum, shara'anta su. To, sai ka sanar da su abubuwa masu banƙyama waɗanda kakanninsu suka yi.5. Ka ce musu, ni Ubangiji Allah, na ce a ranar da na zaɓi Isra'ila na ta da hannuna, na rantse wa zuriyar Yakubu, na kuma bayyana kaina a gare su a ƙasar Masar, cewa ni ne Ubangiji Allahnsu,6. a ran nan na rantse musu, cewa zan fito da su daga ƙasar Masar, zuwa wata ƙasa wadda na samo musu, ƙasar da take da yalwar albarka, wato ƙasa mai albarka duka.7. Sai na ce musu, ‘Bari kowane ɗayanku ya yi watsi da abubuwan banƙyama da kuke jin daɗinsu, kada ku ƙazantar da kanku da gumakan Masarawa, gama ni ne Ubangiji Allahnku.’8. Amma suka tayar mini, ba su ji ni ba, ba su yi watsi da abubuwan banƙyama da suke jin daɗinsu ba, ba su rabu da gumakan Masarawa ba. Sai na ce zan zubo musu da hasalata, in aukar musu da fushina a ƙasar Masar.9. Amma saboda sunana ban yi wannan ba, domin kada a saɓi sunana cikin sauran al'umma inda mutanen Isra'ila suke zaune, gama na sanar da kaina ga mutanen Isra'ila, a gaban sauran al'umma kuma, sa'ad da na fito da mutanen Isra'ila, daga ƙasar Masar.10. “Sai na fisshe su daga ƙasar Masar, na kawo su cikin jeji.11. Na ba su dokokina da ka'idodina, waɗanda idan mutum ya kiyaye su, zai rayu.12. Na kuma ba su ranar Asabar don ta zama alama tsakanina da su, don kuma su sani ni ne Ubangiji wanda yake tsarkake su.13. Amma mutanen Isra'ila suka tayar mini a cikin jeji, ba su bi dokokina da ka'idodina ba, waɗanda idan mutum ya kiyaye su, zai rayu. Suka ɓata ranar Asabar ƙwarai. Sai na ce zan zubo musu da hasalata, in aukar da fushina a kansu.14. Amma saboda sunana ban yi wannan ba, domin kada a saɓi sunana a cikin sauran al'umma waɗanda a kan idonsu na fisshe su.15. Na kuma rantse musu a cikin jeji, cewa ba zan kai su ƙasar da na ba su ba, ƙasar da take cike da yalwar albarka, wato ƙasar da take mafi albarka duka,16. domin sun ƙi su bi ka'idodina da dokokina. Suka ɓata ranar Asabar ɗina, gama zuciyarsu ta fi so ta bauta wa gumaka.17. “Duk da haka na yafe musu, ban hallaka su ba, ban kuma shafe su a jeji ba.18. Sai na ce wa 'ya'yansu a jeji, ‘Kada ku bi dokokin ubanninku, ko kuwa ku kiyaye ka'idodinsu, kada kuma ku ɓata kanku da gumakansu.19. Ni ne Ubangiji Allahnku, ku kiyaye dokokina da ka'idodina sosai.20. Ku kiyaye ranar Asabar ɗina domin ta zama alama tsakanina da ku, domin kuma ku sani ni ne Ubangiji Allahnku.’21. “Amma 'ya'yansu suka tayar mini, ba su kiyaye dokokina da ka'idodina ba, waɗanda idan mutum ya kiyaye su, zai rayu. Suka kuma ɓata ranar Asabar ɗina. Sai na yi tunani zan zubo musu da hasalata, in aukar da fushina a kansu a jeji.22. Amma na yi haƙuri saboda sunana, domin kada a saɓi sunana a gaban sauran al'umma waɗanda suka gani na fito da mutanen Isra'ila daga ƙasar Masar.23. Na rantse musu a jeji, cewa zan warwatsar da su cikin sauran al'umma, da sauran ƙasashe24. domin ba su kiyaye ka'idodina da dokokina ba, suka ɓata ranar Asabar ɗina, suka bauta wa gumakan kakanninsu.25. Sai kuma na ba su dokoki da ƙa'idodi marasa amfani, waɗanda ba za su rayu ta wurinsu ba.26. Na kuma bari su ƙazantar da kansu ta wurin hadayunsu, su kuma sa 'ya'yan farinsu su ratsa wuta. Na yi haka don in sa su zama abin ƙyama, don kuma su sani ni ne Ubangiji.27. “Domin haka, ya ɗan mutum, ka yi magana da mutanen Isra'ila ka ce, ‘Ni Ubangiji Allah, na ce kakanninku sun saɓe ni da ba su amince da ni ba.28. Gama sa'ad da na kawo su cikin ƙasar da na rantse zan ba su, sa'ad da suka ga kowane tudu da kowane itace mai ganye, sai suka miƙa hadayunsu a wuraren nan suka tsokane ni da hadayunsu. A wuraren ne suka miƙa hadayunsu na turare mai ƙanshi da hadayu na sha.’29. Sai na ce, ‘Wane ɗakin tsafi kuke tafiya?’ Domin haka aka kira sunan wurin Bama, wato tudu.30. Domin haka ka ce wa mutanen Isra'ila, ‘Ni Ubangiji Allah na ce za ku ƙazantar da kanku kamar yadda kakanninku suka yi? Za ku bi abubuwan da suka yi na banƙyama?31. Sa'ad da kuke miƙa hadaya, kuna miƙa 'ya'yanku hadaya ta ƙonawa, kuna ƙazantar da kanku ta wurin gumakanku har wa yau, to, za ku iya tambayata, ya ku mutanen Isra'ila? Ni Ubangiji Allah ba na tambayuwa gare ku.32. Tunanin nan da kuke yi a zuciyarku, cewa kuna so ku zama kamar sauran al'umma da kabilan ƙasashe, ku bauta wa itace da dutse, ba zai taɓa faruwa ba.’33. “Hakika, ni Ubangiji Allah na ce, zan sarauce ku ƙarfi da yaji, da fushi,34. da ƙarfi da yaji da fushi kuma, zan fito da ku daga cikin mutane, in tattaro ku daga sauran ƙasashe inda aka warwatsa ku.35. Zan kawo ku cikin ruƙuƙin jama'a, in yi muku shari'a fuska da fuska.36. Kamar yadda na yi wa kakanninku shari'a a jejin ƙasar Masar, haka kuma zan yi muku shari'a, ni Ubangiji Allah na faɗa.37. “Zan sa ku wuce ta ƙarƙashin sanda, in ƙulla alkawarina da ku.38. Zan fitar da 'yan tawaye a cikinku, da waɗanda suke yin mini laifi. Zan fito da su daga ƙasar da suke zaune, amma ba za su shiga ƙasar Isra'ila ba. Za ku kuwa sani ni ne Ubangiji Allah.39. “Ya ku, mutanen Isra'ila, ni Ubangiji Allah, na ce, bari kowa ya tafi ya bauta wa gunkinsa daga yanzu zuwa gaba, tun da yake ba za ku kasa kunne gare ni ba, amma kada ku ɓata sunana mai tsarki da hadayunku da gumakanku.40. “Gama a kan dutsena ne mai tsarki, wato a bisa ƙwanƙolin dutsen Isra'ila, dukan mutanen Isra'ila za su bauta mini a ƙasar, a nan ne zan karɓe su. A nan kuma zan nemi sadake-sada-kenku, da hadayunku mafi kyau.41. Zan karɓe ku kamar turare mai ƙanshi sa'ad da na fisshe ku daga cikin sauran mutane, na tattaro ku daga ƙasashen da aka warwatsa ku. Zan nuna tsarkina a cikinku a idon sauran al'umma.42. Za ku sani ni ne Ubangiji sa'ad da na kawo ku ƙasar Isra'ila, ƙasar da na rantse zan ba kakanninku.43. A nan za ku tuna da ayyukanku da dukan abubuwa da kuka ɓata kanku da su. Za ku ji ƙyamar kanku saboda mugayen abubuwa da kuka aikata.44. Za ku sani ni ne Ubangiji sa'ad da na yi muku haka saboda sunana, ba saboda mugayen ayyukanku ba, ya ku mutanen Isra'ila. Ni Ubangiji Allah na faɗa.”45. Ubangiji ya yi magana da ni ya ce,46. “Ɗan mutum, ka fuskanci wajen kudu ka ja kunnen mutanen kudu, ka kuma yi annabci gāba da kurmin ƙasar Negeb.47. Ka ce wa kurmin Negeb, ‘Ka ji maganar Ubangiji, gama Ubangiji Allah ya ce zai kunna wuta a cikinka, za ta kuwa cinye kowane ɗanyen itace, da kowane busasshen itacen da take cikinka. Ba za a kashe harshen wutar ba. Harshen wutar zai babbake kowace fuska daga kudu zuwa arewa.48. Dukan masu rai za su sani ni Ubangiji ne na kunna wutar, ba wanda zai kashe ta.”’49. Sai na ce, “Ya Ubangiji Allah, suna cewa misalai kawai, nake yi.”Zabura 125:1-51. Waɗanda suke dogara ga Ubangiji, Suna kama da Dutsen Sihiyona, Wanda ba zai jijjigu ba, faufau. Faufau kuma ba za a kawar da shi ba.2. Kamar yadda duwatsu suka kewaye Urushalima, Haka nan Ubangiji zai kewaye jama'arsa, Daga yanzu har abada.3. Ba a koyaushe mugaye za su yi mulki a ƙasar jama'ar Allah ba, Idan kuwa suka yi, to, ya yiwu jama'ar Allah su yi laifi.4. Ya Ubangiji, ka yi wa mutanen kirki alheri, Su waɗanda suke biyayya da umarnanka!5. Amma ka hukunta waɗanda suke bin mugayen al'amuransu, Sa'ad da kake hukunta wa masu aikata mugunta! Salama ta kasance tare da Isra'ila!Karin Magana 28:22-2222. Mutum mai haɗama yana gaggawar samun dukiya, bai kuwa sani ba, ashe, fatara ce za ta same shi.Ibraniyawa 10:1-181. To, tun da yake Shari'a ishara ce kawai ta kyawawan abubuwan da suke a gaba, ba ainihin siffarsu ba, ashe, har abada ba za ta iya kammala waɗanda suke kusatar Allah ta wurin waɗannan hadayu ba, waɗanda ake yi a kai a kai kowace shekara.2. In haka ne kuwa, ashe, ba sai a daina yin hadayar ba? Da an taɓa tsarkake masu ibadar nan sarai, ai, da ba su ƙara damuwa da zunubai ba.3. Amma a game da irin waɗannan hadayu, akan tuna da zunubai a kowace shekara,4. domin ba mai yiwuwa ba ne jinin bijimai da na awaki ya ɗauke zunubi.5. Shi ya sa da Almasihu zai shigo duniya, sai ya ce, “Hadaya da sadaka kam, ba ka so, Amma kā tanadar mini jiki.6. Ba ka farin ciki da hadayar ƙonewa, da kuma hadayar kawar da zunnbai.7. Sa'an nan na ce, ‘Ga ni, na zo in aikata nufinka, ya Allah,’ Kamar yadda yake a rubuce a game da ni a Littafi.”8. Sa'ad da ɗazu ya ce, “Ba ka son hadaya, da sadaka, da hadayar ƙonewa, da hadayar kawar da zunubai, ba ka kuwa jin daɗinsu,” wato, irin waɗanda ake miƙawa ta hanyar Shari'a,9. sai kuma ya ƙara da cewa, “Ga ni, na zo in aikata nufinka.” Ya kawar da na farkon ne, don yă kafa na biyun.10. Ta nufin nan ne aka tsarkake mu, ta wurin miƙa jikin Yesu Almasihu hadaya sau ɗaya tak, ba ƙari.11. Har wa yau kuma, kowane firist yakan tsaya a kan hidimarsa kowace rana, yana miƙa hadaya iri ɗaya a kai a kai, waɗanda har abada ba za su iya ɗauke zunubai ba.12. Amma shi Almasihu da ya miƙa hadaya guda ta har abada domin kawar da zunubai, sai ya zauna a dama ga Allah,13. tun daga lokacin nan yana jira, sai an sa ya take maƙiyansa.14. Gama ta hadaya guda kawai ya kammala waɗanda aka tsarkake har abada.15. Ruhu Mai Tsarki ma yana yi mana shaida haka, domin bayan ya ce,16. “Wannan shi ne alkawarin da zan yi da su, Bayan kwanakin nan, in ji Ubangiji, Zan sa shari'una a birnin zuciyarsu, In kuma rubuta su a allon zuciyarsu,”17. sai kuma ya ƙara cewa, “Ba kuma zan ƙara tunawa da zunubansu da laifofinsu ba.”18. To, a inda aka sami gafarar waɗannan, ba sauran wata hadaya domin kawar da zunubi. Hausa Bible 2010 Bible Society of Nigeria © 1932/2010