Baibul a cikin shekara guda Disamba 10Hosiya 11:1-111. “A lokacin da Isra'ila yake yaro, na ƙaunace shi, Daga cikin Masar na kirawo ɗana.2. Yawan kiransu, yawan tayarwar da suke yi mini, Sai ƙara miƙa wa Ba'al sadaka suke yi, Suna ƙona turare ga gumaka.3. Ko da yake ni ne na koya wa Ifraimu tafiya. Na ɗauke su a hannuna, Amma ba su sani ni ne na lura da su ba.4. Na bishe su da linzamin alheri da ragamar ƙauna, Na zama musu kamar wanda yake ɗauke musu karkiya daga muƙamuƙansu. Na sunkuya, na ciyar da su.5. “Ba su koma ƙasar Masar ba, Amma Assuriya za ta zama sarkinsu Gama sun ƙi yarda su koma wurina.6. Takobi zai ragargaje biranensu, Zai lalatar da sandunan ƙarafan ƙofofinsu, Zai cinye su domin muguwar shawararsu.7. Mutanena sun himmantu su rabu da ni, Ko da yake an kira su ga Ubangiji, Ba wanda ya girmama shi.8. “Ƙaƙa zan iya rabuwa da ke, ya Ifraimu? Ƙaƙa zan miƙa ki, ya Isra'ila? Ƙaƙa zan maishe ki kamar Adma? Ƙaƙa zan yi da ke kamar Zeboyim? Zuciyata tana motsawa a cikina, Juyayina ya huru.9. Ba zan aikata fushina mai zafi ba, Ba zan ƙara hallaka Ifraimu ba, Gama ni Allah ne, ba mutum ba, Maitsarki wanda yake tsakiyarku, Ba zan zo wurinku da hasala ba.10. “Za su bi Ubangiji, Zai yi ruri kamar zaki, hakika zai yi ruri 'Ya'yansa za su zo da rawar jiki da yamma.11. Da sauri za su zo kamar tsuntsaye daga Masar, Kamar kurciyoyi daga ƙasar Assuriya, Zan komar da su gidajensu, ni Ubangiji na faɗa.”Hosiya 12:1-141. Ifraimu tana kiwon iska, Tana ta bin iskar gabas dukan yini. Tana riɓaɓɓanya ƙarya da kamakarya. Tana ƙulla yarjejeniya da Assuriya, Tana kai mai a Masar.”2. Ubangiji yana da magana game da mutanen Yahuza, Zai hukunta Isra'ila saboda hanyoyinta, Zai sāka mata gwargwadon ayyukanta.3. A cikin mahaifa kakansu Yakubu ya kama diddigen ɗan'uwansa, Sa'ad da ya zama baligi ya yi kokawa da Allah.4. Ya yi kokawa da mala'ika ya yi rinjaye. Ya yi kuka, ya roƙi albarka. Ya sadu da Allah a Betel, A can Allah ya yi magana da shi.5. Ubangiji Allah Mai Runduna, Sunansa Ubangiji,6. Sai ku koma wurin Allahnku, Ku yi alheri, ku yi adalci, Ku saurari Allahnku kullayaumin.7. Ubangiji ya ce, “Ɗan kasuwa wanda yake da ma'aunin algus a hannunsa. Yana jin daɗin yin zalunci.8. Mutanen Ifraimu sun ce, ‘Hakika, mun zama attajirai, Mun samar wa kanmu dukiya. A cikin harkokinmu ba za a sami wata mugunta ba.’9. Ni ne Ubangiji Allahnku tun daga ƙasar Masar, Zan kuma sa ku zauna cikin alfarwai, Kamar lokatan ƙayyadaddun idodi.10. “Na yi magana da annabawa, Ni ne na ba da wahayi da yawa, Da misalai kuma ta wurin annabawa.11. Idan akwai laifi a Gileyad, Hakika za su zama wofi. A Gilgal ana sadaka da bijimai, Bagadansu za su zama kamar tsibin duwatsu A gyaffan kunyoyin gona.”12. Kakanmu Yakubu ya gudu zuwa ƙasar Aram, A can Isra'ila ya yi barantaka saboda mace, Saboda mace ya yi kiwon tumaki.13. Ta wurin annabi Ubangiji ya fito da mutanen Isra'ila daga Masar, Ta wurin annabi kuma ya kiyaye su.14. Mutanen Ifraimu sun yi muguwar tsokana mai ta da fushi, Domin haka Ubangiji zai ɗora musu hakkin jini a kansu, Zai saka musu cin mutuncin da suka yi.Zabura 139:17-2417. Ya Allah, tunaninka suna da wuyar ganewa a gare ni, Ba su da iyaka!18. In na ƙirga su, za su fi tsabar yashi, Sa'ad da na farka, har yanzu ina tare da kai.19. Ya Allah, da yadda nake so ne, da sai ka karkashe mugaye! 'Yan ta da zaune tsaye kuma sai su rabu da ni!20. Suna ambaton mugayen abubuwa a kanka, Suna faɗar mugayen abubuwa gāba da sunanka.21. Ya Ubangiji, ga yadda nake ƙin waɗanda suke ƙinka, Da yadda nake raina waɗanda suke tayar maka!22. Ƙiyayyar da nake yi musu ta kai intaha, Na ɗauke su, su abokan gābana ne.23. Jarraba ni, ya Allah, ka san tunanina, Gwada ni, ka gane damuwata.24. Ka bincike, ko akwai wani rashin gaskiya a gare ni, Ka bi da ni a madawwamiyar hanya.Karin Magana 29:22-2222. Mutum mai saurin fushi yakan ta da faɗa, mai zafin rai kuma yakan aikata laifi da yawa.Yahuda 1:1-251. Daga Yahuza bawan Yesu Almasihu, ɗan'uwan Yakubu zuwa ga kirayayyu, ƙaunatattun Allah Uba, keɓaɓɓu ga Yesu Almasihu.2. Jinƙai, da salama, da ƙauna su yawaita a gare ku.3. Ya ku ƙaunatattuna, da yake dā ma ina ɗokin rubuto muku zancen ceton nan namu, mu duka, sai na ga wajibi ne in rubuto muku in gargaɗe ku, ku dage ƙwarai a kan bangaskiyar nan da aka danƙa wa tsarkaka sau ɗaya tak, ba ƙari.4. Gama waɗansu mutane sun saɗaɗo a cikinku, waɗanda tun zamanin dā aka ƙaddara ga hukuncin nan, marasa bin Allah ne, masu mai da alherin Allah dalilin aikata fajirci, suna kuma ƙin makaɗaicin Ubangijinmu Yesu Almasihu.5. Sai dai ina so in tuna muku, ko da yake kun riga kun san kome sosai, cewa Ubangiji ya ceci jama'a daga ƙasar Masar, duk da haka daga baya ya hallaka waɗanda ba su ba da gaskiya ba.6. Har ma mala'ikun da ba su kiyaye girmansu ba, amma suka bar ainihin mazauninsu, ya tsare su cikin sarƙa madawwamiya a baƙin duhu, har ya zuwa shari'ar babbar ranar nan.7. Haka kuma Saduma da Gwamrata, da birane kewayensu, waɗanda su ma suka dulmuya cikin fasikanci da muguwar sha'awa ta jiki, an nuna su domin ishara, suna shan hukuncin madawwamiyar wuta.8. Haka kuma masu mafarke-mafarken nan, sukan ƙazantar da jikinsu, su ƙi bin mulki, su kuma yi wa masu ɗaukaka baƙar magana.9. Amma lokacin da babban mala'ika, Mika'ilu yake fama da Iblis, suna mūsu a kan gawar Musa, shi Mika'ilu bai yi garajen ɗora masa laifi da baƙar magana ba, sai dai ya ce, “Ubangiji yă tsawata maka.”10. Amma mutanen nan sukan kushe duk abin da ba su fahinta ba, saboda abubuwan da suka sani bisa ga jiki suna kamar dabbobi marasa hankali, su ne kuwa sanadin halakarsu.11. Kaitonsu! Don sun bi halin Kayinu, sun ɗunguma cikin bauɗewar Bal'amu don kwaɗayi, sun kuma hallaka ta irin tawayen Kora.12. Waɗannan mutane kamar aibobi ne a taronku na soyayya, suna ta shagulgulan ciye-ciye a cikinku, ba kunya ba tsoro, suna kula da kansu kawai. Su kamar holoƙon hadiri ne, wanda iska take korawa. Su kamar itatuwa ne, marasa 'ya'ya da kaka, matattu murus, tumɓukakku.13. Su kamar raƙuman ruwan teku ne masu hauka, suna taƙama da kumfar kunyarsu. Su kamar taurari ne masu kai da kawowa, waɗanda aka tanada wa matsanancin duhu har abada.14. Anuhu ma wanda yake na bakwai daga Adamu, shi ma ya yi annabci a kan waɗannan mutane cewa, “Ga shi, Ubangiji ya zo da dubban tsarkakansa,15. don ya zartar da hukunci kan kowa, yă kuma tabbatar wa marasa bin Allah dukan aikinsu na rashin bin Allah, da suka aikata ta hanyar rashin bin Allah, da kuma baƙaƙen maganganu da masu zunubi marasa bin Allah suka yi game da shi.”16. Waɗannan su ne masu gunaguni, masu ƙunƙuni, masu biye wa muguwar sha'awa, marubata, masu yi wa mutane bambaɗanci don samun wata fa'ida.17. Ya ku ƙaunatattuna, lalle ku tuna da maganar da manzannin Ubangijinmu Yesu Almasihu suka faɗa a dā,18. da suka ce da ku, “A zamanin ƙarshe za a yi waɗansu mutane masu ba'a, masu biye wa muguwar sha'awarsu ta rashin bin Allah.”19. Waɗannan su ne masu raba tsakani, masu son zuciya, marasa Ruhu.20. Amma ya ku ƙaunatattuna, ku riƙa inganta kanku ga bangaskiyarku mafi tsarki, kuna addu'a da ikon Ruhu Mai Tsarki.21. Ku tsaya a kan ƙaunar da Allah yake yi mana, kuna sauraron jinƙan Ubangijinmu Yesu Almasihu mai kaiwa ga rai madawwami.22. Ku ji tausayin waɗanda suke shakka,23. kuna ceton waɗansu kuna fizgo su daga wuta. Waɗansu kuma ku ji tausayinsu, amma tare da tsoro kuna ƙyamar ko da tufafin da halinsu na mutuntaka ya ƙazantar.24. Ga wanda yake da iko yă tsare ku daga faɗuwa, yă kuma miƙa ku marasa aibi a gaban ɗaukakarsa da matuƙar farin ciki,25. ga Allah makaɗaici Mai Cetonmu ta wurin Yesu Almasihu Ubangijinmu, ɗaukaka, da fifiko, da mulki, da iko su tabbata gare shi, tun fil'azal, da yanzu, da kuma har abada abadin. Amin, amin. Hausa Bible 2010 Bible Society of Nigeria © 1932/2010