Baibul a cikin shekara guda Oktoba 12Irmiya 9:1-261. Da ma kaina maɓulɓulan ruwa ne idanuna kuma maɓulɓulan hawaye! Da sai in yi kuka dare da rana saboda mutanena da aka kashe.2. Da ma a hamada ina da wurin da matafiye za su sauka, don in bar mutanena in tafi in bar su; gama dukansu mazinata ne, taron mutane marasa aminci.3. “Sun tanƙwasa harshensu kamar baka, don su harba ƙarya; ba da gaskiya ba ne suke nasara a cikin ƙasar. Sukan tashi daga wannan zunubi zuwa wancan; ba su san ni ba,” in ji Ubangiji.4. “Ka yi hankali da abokanka; kada ka amince da ’yan’uwanka. Gama kowane ɗan’uwa munafuki ne, kowane aboki kuma mai kushe ne.5. Aboki kan ruɗi aboki, ba mai faɗar gaskiya. Sun koya wa harshensu faɗar ƙarya; sun gajiyar da kansu da yin zunubi.6. Kai kana zama a tsakiyar ruɗu; cikin ruɗunsu sun ƙi su san ni,” in ji Ubangiji.7. Saboda haka ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, “Ga shi zan tace in kuma gwada su, gama me kuwa zan yi saboda zunubin mutanena?8. Harshensu kibiya ce mai dafi; yana magana da ruɗu. Da bakinsa kowa yana maganar alheri da maƙwabcinsa, amma a zuciyarsa ya sa masa tarko.9. Bai kamata in hukunta su saboda wannan ba?” In ji Ubangiji. “Bai kamata in ɗau fansa a kan irin al’umma kamar wannan ba?”10. Zan yi kuka in yi kururuwa saboda duwatsu in kuma yi makoki game da wuraren kiwon hamada. Sun zama kango ba wanda yake bi cikinta, ba a kuma jin kukan shanu. Tsuntsaye sararin sama sun gudu namun jeji ma duk sun watse.11. “Zan mai da Urushalima tsibin kufai, wurin zaman diloli; zan kuma lalace garuruwan Yahuda saboda haka ba wanda zai zauna a can.”12. Wane mutum ne yana da isashiyar hikimar fahimtar wannan? Wa Ubangiji ya umarta da zai iya yin bayani? Me ya sa aka lalace ƙasar ta zama kufai kamar hamada da ba wanda zai iya ratsa ta?13. Ubangiji ya ce, “Domin sun bar dokata, wadda na sa a gabansu; ba su yi biyayya da ni ko su bi dokata ba.14. A maimako, sun bi taurin zuciyarsu; suka bi Ba’al, yadda kakanninsu suka koya musu.”15. Saboda haka, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila yana cewa, “Ga shi zan sa wannan mutane su ci abinci mai ɗaci su kuma sha ruwan dafi.16. Zan watsar da su a cikin al’ummai da su da kakanninsu ba su sani ba, zan kuma fafare su da takobi sai na hallaka su.”17. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, “Ku lura yanzu! Ku kira mata masu makoki su zo ku aika wa gwanaye a cikinsu su zo.18. Bari su zo da sauri su yi kuka a kanmu sai idanunmu sun cika da hawaye giranmu kuma su jiƙe sharkaf.19. An ji karar kuka daga Sihiyona cewa, ‘Duba yadda muka lalace! Duba irin babban kunyar da muka sha! Dole mu bar ƙasar domin gidajenmu sun lalace.’ ”20. Yanzu, ya mata, ku ji maganar Ubangiji; ku buɗe kunnuwanku ga maganar bakina. Ku koya wa ’yan matanku yadda za su yi kuka; ku koya wa juna makoki.21. Mutuwa ta haura ta tagoginmu ta kuma shiga katangarmu; ta karkashe ’ya’ya a tituna ta kuma karkashe samari a dandali.22. Ka ce, “Ga abin da Ubangiji ya furta, “ ‘Gawawwakin mutane za su fāɗi kamar juji a fili, kamar hatsin da aka yanka a bayan mai girbi, da ba mai tara su.’ ”23. Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Kada mai hikima ya yi fariya da hikimarsa ko mai ƙarfi ya yi fariya da ƙarfinsa ko mai arziki ya yi fariya da arzikinsa,24. amma bari shi wanda yake taƙama ya yi taƙama da wannan, cewa ya fahimci ya kuma san ni, cewa ni ne Ubangiji, wanda yake yin alheri, gaskiya da kuma adalci a duniya, gama a waɗannan ne nake jin daɗi,” in ji Ubangiji.25. “Kwanaki suna zuwa,” in ji Ubangiji, “sa’ad da zan hukunta dukan waɗanda aka yi musu kaciya kawai a jiki,26. Masar, Yahuda, Edom, Ammon, Mowab da dukan waɗanda suke zaune a hamada a wurare masu nisa. Gama dukan waɗannan al’ummai marasa kaciya ne, har dukan gidan Isra’ila ma marasa kaciya ne a zuciya.”Irmiya 10:1-251. Ku ji abin da Ubangiji yana ce muku, ya gidan Isra’ila.2. Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Kada ku koyi hanyoyin al’ummai ko ku razana game da alamun sararin sama, ko da yake al’ummai sun razana saboda su.3. Gama al’adun mutane banza ne; sukan yanke itace daga kurmi, sai mai sassaƙa yă sassaƙa shi da gizago.4. Sukan yi masa ado da azurfa da kuma zinariya; sukan ɗauki guduma su kafa shi da ƙusoshi, don kada yă fāɗi.5. Kamar dodon gona cikin gonar kabewa, haka gumakansu ba sa iya magana; dole a yi ta ɗaukansu domin ba za su iya tafiya ba. Kada ku ji tsoronsu; ba za su iya yi wa wani lahani ba ba sa iya yin wani abin kirki.”6. Babu wani kamar ka, ya Ubangiji; kai mai girma ne, kuma sunanka yana da girma da kuma iko.7. Wane ne ba zai girmama ka ba, Ya Sarkin al’ummai? Tsoronka wajibi ne. A cikin dukan masu hikima na al’ummai kuma cikin dukan mulkokinsu, babu kamar ka.8. Dukansu marasa azanci ne wawaye; gumakan itacen banza ne suke koya musu.9. An kawo ƙeraren azurfa daga Tarshish zinariya kuma daga Ufaz. Abin da gwani da maƙerin zinariya suka yi sa’an nan aka yi masa ado da mulufi da shunayya dukan aikin gwanaye.10. Amma Ubangiji shi ne Allah na gaskiya; shi ne Allah mai rai, madawwamin sarki. Sa’ad da ya yi fushi, ƙasa takan girgiza; al’ummai ba sa iya jure da hasalarsa.11. “Ka faɗa musu wannan, ‘Waɗannan alloli, waɗanda ba su yi sammai da ƙasa ba, za su hallaka daga duniya da kuma daga ƙarƙashin sammai.’ ”12. Amma Allah ya yi duniya ta wurin ikonsa; ya kafa duniya ta wurin hikimarsa ya shimfiɗa sammai ta wurin fahiminsa.13. Sa’ad da ya yi tsawa, ruwaye a cikin sammai sukan yi ƙugi; yakan sa gizagizai su taso daga iyakokin duniya. Yakan aiki walƙiya da ruwan sama ya fitar da iska daga gidajen ajiyarsa.14. Kowa marar azanci ne, marar ilimi; kowane maƙerin zinariya zai sha kunya saboda gumakansa. Siffofinsa ƙarya ne; ba su da numfashi a cikinsu.15. Su ba kome ba ne, aikin ruɗami ne; Sa’ad da hukuncinsu ya yi za su lalace.16. Shi da yake Rabon Yaƙub ba kamar waɗannan yake ba, gama shi ne Mahaliccin abubuwa duka, har da Isra’ila, kabilar gādonsa Ubangiji Maɗaukaki ne sunansa.17. Ku tattara kayayyakinku don ku bar ƙasar, ku da kuke zaune a wurin da aka kewaye da yaƙi.18. Gama haka Ubangiji ya faɗa, “A wannan lokaci zan jefar da waɗanda suke zaune a ƙasar; zan kawo damuwa a kansu domin a kama su.”19. Tawa ta ƙare, saboda raunin da aka yi mini! Raunina ba mai warkewa ba ne! Duk da haka na ce wa kaina, “Wannan ciwona ne, dole kuma in jure da shi.”20. An lalatar da tentina; dukan igiyoyinsa sun tsintsinke. ’Ya’yana maza sun bar ni ba sa nan; ba wanda aka bari da zai kafa tentina ko ya kafa mini mafaka.21. Makiyaya marasa azanci ne kuma ba sa neman nufin Ubangiji; saboda haka ba sa nasara dukan garkensu kuwa ya watse.22. Ku saurara! Rahoto yana zuwa babban hargitsi daga ƙasar arewa! Zai mai da garuruwan Yahuda kufai, mazaunin diloli.23. Na sani, ya Ubangiji, cewa ran mutum ba nasa ba ne; ba mutum ne yake kiyaye takawarsa ba.24. Ka yi mini gyara, Ubangiji, amma fa da adalci kaɗai ba cikin fushinka ba, don kada ka wofinta ni.25. Ka zuba hasalarka a kan al’umman da ba su san ka ba, a kan mutanen da ba sa kira bisa sunanka. Gama sun cinye Yaƙub; sun cinye shi gaba ɗaya suka kuma lalace wurin zamansa.Zabura 118:5-95. Cikin azabata na yi kuka ga Ubangiji, ya kuwa amsa ta wurin ’yantar da ni.6. Ubangiji yana tare da ni; ba zan ji tsoro ba. Me mutum zai yi mini?7. Ubangiji yana tare da ni; shi ne mai taimakona. Zan yi nasara a kan abokan gābana.8. Ya fi kyau in nemi mafaka a wurin Ubangiji da in dogara ga mutum.9. Ya fi kyau in nemi mafaka a wurin Ubangiji da in dogara ga sarakuna.Karin Magana 27:7-77. Duk wanda ya ƙoshi da zuma, ba ya marmarinsa kuma amma wanda yake yunwa ko abin da yake da ɗaci ma zai ji shi da zaƙi.Kolossiyawa 3:1-251. Da yake an tashe ku tare da Kiristi, sai ku sa zukatanku a kan abubuwan da suke sama, inda Kiristi yake zaune a hannun dama na Allah.2. Ku sa hankulanku a kan abubuwan sama, ba kan abubuwan duniya ba.3. Gama kun mutu, ranku yanzu kuwa yana ɓoye tare da Kiristi a cikin Allah.4. Sa’ad da Kiristi, wanda shi ne ranku, ya bayyana, ku ma za ku bayyana tare da shi cikin ɗaukaka.5. Saboda haka, sai ku fid da duk wani abin da yake kawo sha’awa a zukatanku, fasikanci, ƙazanta, sha’awa, muguwar sha’awa, da kuma kwaɗayi wanda shi ma bautar gumaka ne.6. Gama fushin Allah zai sauko a kan masu aikata waɗannan.7. Dā kun yi waɗannan abubuwa, sa’ad da rayuwar tana cikin duniya mai wannan hali.8. Amma yanzu dole ku raba kanku da dukan ire-iren abubuwan nan. Ku daina fushi, ku daina ƙiyayya da ƙeta. Ku bar ɓatan suna da kuma ƙazamar magana daga leɓunanku.9. Kada ku yi wa juna ƙarya, da yake kun tuɓe tsohon halinku tare da ayyukansa10. kun ɗauki sabon halin nan da ake sabuntawa ga sani, bisa ga kamannin Mahaliccinsa.11. A wannan sabuwar rayuwa babu bambanci ko kai mutumin Al’ummai ne ko mutumin Yahuda, mai kaciya ne ko marar kaciya, baƙo, baƙauye, bawa ne ko ’yantacce, gama Kiristi shi ne kome, kuma yana cikin kome.12. Da yake Allah ya mai da ku zaɓaɓɓu, tsarkaka, ƙaunatattu, sai ku dinga jin tausayin juna, kuna yin alheri, kuna nuna tawali’u da sauƙinkai da jimrewa.13. Ku riƙa yin haƙuri da juna kuna kuma gafarta wa juna duk wani laifin da wani ya yi muku. Ku gafarta kamar yadda Ubangiji ya gafarce ku.14. Fiye da waɗannan duka, ku yi ƙaunar juna, gama ƙauna ce take haɗa kome gaba ɗaya.15. Ku bar salamar Kiristi tă yi mulki a zukatanku, da yake a matsayin gaɓoɓin jiki ɗaya an kira ku ga salama. Ku zama masu godiya.16. Ku bar maganar Kiristi ta zauna a cikinku a yalwace yayinda kuke koya, kuna kuma yi wa juna gargaɗi da dukan hikima, da kuma yayinda kuke waƙoƙin zabura, waƙoƙi da waƙoƙin ruhaniya tare da godiya a zukatanku ga Allah.17. Kuma ko mene ne kuke yi, ko cikin magana ko cikin ayyuka, ku yi shi duka a cikin sunan Ubangiji Yesu, kuna yin godiya ga Allah Uba ta wurinsa.18. Mata, ku yi biyayya ga mazanku, yadda ya dace cikin Ubangiji.19. Maza, ku ƙaunaci matanku kada ku nuna musu hali marar tausayi.20. ’Ya’ya, ku yi biyayya ga iyayenku cikin kome, gama wannan yakan gamshi Ubangiji.21. Ubanni, kada ku matsa wa yaranku lamba, don kada su fid da zuciya.22. Bayi, ku yi biyayya ga iyayengijinku na duniya cikin kome; kada ku yi aikin ganin ido kamar masu neman yabon mutane, sai dai ku yi aiki tsakaninku da Allah, kamar masu tsoron Ubangiji.23. Kome kuke yi, ku yi shi da dukan zuciyarku, sai ka ce ga Ubangiji kuke yi, ba ga mutum ba.24. Kun san cewa zai ba ku gādo a matsayin ladanku. Ubangiji Kiristi ne fa kuke bauta wa.25. Duk wanda ya yi laifi, za a sāka masa don laifinsa, babu sonkai. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.