Baibul a cikin shekara guda Oktoba 8Irmiya 1:1-191. Kalmomin Irmiya ɗan Hilkiya, ɗaya daga cikin firistoci a Anatot a yankin Benyamin.2. Maganar Ubangiji ta zo gare shi a shekara ta goma sha uku ta sarautar Yosiya ɗan Amon sarkin Yahuda,3. da kuma a zamanin Yehohiyakim ɗan Yosiya sarkin Yahuda, har zuwa watan biyar na shekara goma sha ɗaya na Zedekiya ɗan Yosiya sarkin Yahuda, sa’ad da aka kai mutanen Urushalima zaman bauta.4. Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,5. “Kafin in siffanta ka a cikin ciki na san ka, kafin a haife ka, na keɓe ka; na naɗa ka ka zama annabi ga al’ummai.”6. Sai na ce, “Kayya, Ubangiji Mai Iko Duka, ban iya magana ba; ni ɗan yaro ne kawai.”7. Amma Ubangiji ya ce mini, “Kada ka ce, ‘Ni ɗan yaro ne kawai.’ Dole ka je wurin kowane mutumin da na aike ka ka kuma faɗa abin da na umarce ka.8. Kada ka ji tsoronsu, gama ina tare da kai kuma zan kiyaye ka,” in ji Ubangiji.9. Sai Ubangiji ya miƙa hannunsa ya taɓa bakina ya ce mini, “Yanzu na sa kalmomina a bakinka.10. Duba, yau na naɗa ka a kan al’ummai da mulkoki don ka tumɓuke ka kuma rusar, ka hallaka ka kuma kakkaɓe, ka gina ka kuma shuka.”11. Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Me ka gani, Irmiya?” Sai na amsa na ce, “Na ga reshen itacen almon.”12. Ubangiji ya ce mini, “Daidai ne ka gani, gama ina lura in ga cewa maganata ta cika.”13. Maganar Ubangiji ta sāke zo mini cewa, “Me ka gani?” Na amsa na ce, “Na ga tukunya tana tafasa, tana juyewa daga arewa.”14. Ubangiji ya ce mini, “Daga arewa za a zubo masifa a kan dukan mazaunan ƙasar.15. Ina shirin kiran dukan mutanen masarautar arewanci,” in ji Ubangiji. “Sarakunansu za su zo su kafa kursiyoyinsu a mashigin ƙofofin Urushalima; za su zo su kewaye dukan katangarta su kewaye dukan garuruwan Yahuda.16. Zan furta hukunci a kan mutanena saboda muguntarsu na yashe ni, suna ƙona turare ga waɗansu alloli suna kuma bauta wa abin da hannuwansu suka yi.17. “Ka kintsa kanka! Ka tashi tsaye ka faɗa musu abin da na umarce ka. Kada su firgita ka, in ba haka ba zan firgita ka a gabansu.18. Yau na mai da kai birni mai katanga, ginshiƙin ƙarfe da bangon tagulla don ka tsaya gāba da dukan ƙasar, ya kuma yi gāba da sarakunan Yahuda da fadawan, da firistoci da kuma mutanenta.19. Za su yi yaƙi da kai amma ba za su ci nasara a kanka ba, gama ina tare da kai, zan kuma kiyaye ka,” in ji Ubangiji.Irmiya 2:1-371. Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,2. “Tafi ka yi shela a kunnuwar Urushalima cewa, “ ‘Na tuna da amincin ƙuruciyarki, yadda kamar amarya kika ƙaunace ni kika kuma bi ni cikin hamada, cikin ƙasar da ba a yi shuka ba.3. Isra’ila tsattsarka ce ga Ubangiji, nunan fari na girbinsa; dukan waɗanda suka cinye ta an same su da laifi, masifa kuwa ta same su,’ ” in ji Ubangiji.4. Ka saurari maganar Ubangiji, ya gidan Yaƙub, dukanku zuriyar gidan Isra’ila.5. Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Wane laifi ne kakanninku sun same ni da shi, da suka tsaya nesa da ni? Sun bi gumakan banza su kansu suka kuma zama banza da kansu.6. Ba su yi tambaya, ‘Ina Ubangiji, wanda ya fitar da su daga Masar ya bishe su cikin jeji cikin hamada da kwazazzabai ƙasa mai fări da kuma duhu, ƙasar da ba kowa mai ratsa ta ba kowa kuma mai zama a cikinta?’7. Na kawo ku zuwa ƙasa mai albarka don ku ci amfaninta da abubuwa masu yalwar da take bayarwa. Amma kuka zo kuka ƙazantar da ƙasata kuka kuma mai da gādona abin ƙyama.8. Firistoci ba su yi tambaya, ‘Ina Ubangiji ba.’ Waɗanda suke amfani da doka ba su san ni ba; shugabanni suka yi mini tawaye. Annabawa suka yi annabci ta wurin Ba’al, suna bin gumakan banza.9. “Saboda haka ina sāke tuhumarku,” in ji Ubangiji. “Zan kuma tuhumi ’ya’ya ’ya’yanku.10. Ku ƙetare zuwa tsibiran Kittim ku gani, ku aika zuwa Kedar ku duba da kyau; ku ga ko an taɓa yin wani abu haka.11. Akwai wata al’ummar da ta canja allolinta? (Duk da haka su ba alloli ba ne sam.) Amma mutanena sun musayar da ɗaukakarsu da gumakan banza.12. Ku girgiza saboda wannan, ya sammai, ku kuma razana don tsoro mai girma,” in ji Ubangiji.13. “Mutanena sun aikata zunubai guda biyu. Sun rabu da ni, ni da nake maɓulɓular ruwan rai, sun kuma haƙa tankunan ruwansu, tankuna ruwan da suka fashe da ba za su iya riƙe ruwa ba.14. Isra’ila bawa ne, bawa ne ta wurin haihuwa? Me ya sa ya zama ganima?15. Zakoki sun yi ruri; sun yi masa ruri. Sun lalatar da ƙasarsa; an ƙone garuruwansa aka kuma watse daga ciki.16. Haka ma, mutanen Memfis da Tafanes sun aske rawanin kanka17. Ba kai ne ba ka jawo wa kanka ba ta wurin rabuwa da Ubangiji Allahnka sa’ad da ya bi da kai a hanya?18. To, me ya sa za ka Masar don shan ruwa daga Shihor? Kuma me ya sa za ka Assuriya don shan ruwa daga Kogi?19. Muguntarka za tă hukunta ka; jan bayanka zai tsawata maka. Sai ka lura ka kuma gane yaya mugu da kuma ɗaci suke a gare ka sa’ad da ka rabu da Ubangiji Allahnka kuma ba ka tsorona,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.20. “Tun da daɗewa ka karya karkiyarka ka kuma tsintsinke sarƙoƙinka; sai ka ce, ‘Ba zan bauta maka ba!’ Tabbatacce, a kan kowane tudu mai tsayi da kuma a ƙarƙashin kowane ɗanyen itace ka kwanta kamar karuwa.21. Na shuka ka kamar zaɓaɓɓen inabi iri mai kyau da kuma wanda za a dogara a kai. Yaya kuma ka juya kana gāba da ni ka lalace, ka zama inabin jeji?22. Ko da yake ka wanke kanka da sabulu ka yi amfani da sabulu mai yawa, duk da haka har yanzu tabon laifinka yana nan a gabana,” in ji Ubangiji Mai Iko Duka.23. “Yaya za ka ce, ‘Ban ƙazantu ba; ban bi Ba’al ba’? Duba yadda ka yi a cikin kwari; ka ga abin da ka yi. Kai kamar makwaɗaciyar raƙuma ce mai zafin gudu kana gudu nan da can,24. kamar jakar jejin da ta saba da hamada, mai busar iska cikin son barbaranta sa’ad da take son barbara wa zai iya hana ta? Jakin da yake nemanta, ba ya bukatar wahalar da kansa; a lokacin barbara za a same ta.25. Kada ka yi gudu har ƙafafunka su zama ba takalma maƙogwaronka kuma ya bushe. Amma sai ka ce, ‘Ba amfani! Ina ƙaunar baƙin alloli kuma dole in bi su.’26. “Kamar yadda akan kunyatar da ɓarawo sa’ad da aka kama shi, haka gidan Isra’ila zai sha kunya, su, sarakunansu da shugabanninsu, firistocinsu da kuma annabawansu.27. Kuna ce wa itace, ‘Kai ne mahaifina,’ ga dutse kuma, ‘Kai ne ka haife ni.’ Sun juye mini bayansu ba fuskokinsu ba; duk da haka sa’ad da suna cikin wahala, sukan ce, ‘Zo ka cece mu!’28. To ina allolin da kuka yi wa kanku? Bari su zo in suna iya cetonku sa’ad da kuke cikin wahala! Gama kuna da alloli masu yawa kamar yadda kuke da garuruwa, ya Yahuda.29. “Me ya sa kuke tuhumana? Dukanku kun yi mini tawaye,” in ji Ubangiji.30. “A banza na hukunta mutanenku; ba su yi gyara ba. Takobinku ya cinye annabawanku kamar zaki mai jin yunwa.31. “Ku na wannan zamani, ku saurari maganar Ubangiji. “Na zama wa Isra’ila hamada ne ko ƙasa mai babban duhu? Me ya sa mutanena suke cewa, ‘Muna da ’yanci mu yi ta yawo; ba za mu ƙara zuwa wurinka ba’?32. Budurwa za tă manta da kayan adonta amarya ta manta da kayan adon aurenta? Duk da haka mutanena sun manta da ni, kwanaki ba iyaka.33. Kuna da azanci sosai a bin masoya! Kai, ko mafiya muni cikin mata tana iya koya daga hanyoyinku.34. A rigunanku mutane kan sami jinin matalauta marasa laifi, ko da yake ba ku kama su suna fasawa su shiga ba. Duk da haka35. kuna cewa, ‘Ba ni da laifi; ba ya fushi da ni.’ Amma zan zartar da hukunci a kanku domin kun ce, ‘Ban yi zunubi ba.’36. Don me kuke yawo da yawa haka, kuna ta canjin hanyoyinku? Masar za tă kunyata ku yadda kuka sha kunya a wurin Assuriya.37. Za ku kuma bar wurin da hannuwanku a kanku, gama Ubangiji ya ƙi waɗanda kuka amince da su; ba za ku zama abin taimako a gare su ba.Zabura 116:5-145. Ubangiji mai alheri ne da kuma mai adalci; Allahnmu yana cike da tausayi.6. Ubangiji yana tsare masu tawali’u; sa’ad da nake cikin tsananin bukata, ya cece ni.7. Ka kwantar da hankali, ya raina, gama Ubangiji mai alheri ne a gare ka.8. Gama kai, ya Ubangiji, ka ceci raina daga mutuwa, idanuna daga hawaye, ƙafafuna daga tuntuɓe,9. don in iya tafiya a gaban Ubangiji a ƙasar masu rai.10. Na gaskata, saboda haka na ce, “An azabtar da ni ƙwarai.”11. Kuma cikin rikicewana na ce, “Dukan mutane maƙaryata ne.”12. Yaya zan sāka wa Ubangiji saboda dukan alherinsa gare ni?13. Zan daga kwaf na ceto in kuma kira ga sunan Ubangiji.14. Zan cika alkawurana ga Ubangiji a gaban dukan mutanensa.Karin Magana 27:1-11. Kada ka yi fariya a kan gobe gama ba san abin da ranar za tă kawo ba.Filibbiyawa 3:1-211. A ƙarshe, ’yan’uwana, ku yi farin ciki a cikin Ubangiji! Ba abin damuwa ba ne a gare ni in sāke rubuta muku irin waɗannan abubuwa, domin lafiyarku ne.2. Ku yi hankali da waɗancan karnuka, waɗancan mutane masu aikata mugunta, waɗancan masu yankan jiki.3. Gama mu ne masu kaciya, mu da muke yi sujada ta wurin Ruhun Allah, mu da muke taƙama a cikin Kiristi Yesu, mu da ba mu dogara da ayyukan da ake gani ba,4. ko da yake ni kaina ina da dalilan dogara da haka. In kuwa akwai wani wanda yake tsammani yana da dalilan dogara ga jiki, ni fa na fi shi,5. an yi mini kaciya a rana ta takwas, asalina Isra’ila ne, na kabilar Benyamin, mutumin Ibraniyawa ɗan Ibraniyawa; bisa ga doka kuwa ni Bafarisiye ne;6. wajen himma kuwa, ni mai tsananta wa ikkilisiya ne, wajen aikin adalci bisa ga hanyar doka, ni marar laifi ne.7. Amma abin da dā ya zama mini riba yanzu, na ɗauka hasara ce saboda Kiristi.8. Me kuma ya fi, na ɗauki dukan abubuwa hasara ne in aka kwatanta da mafificiyar girman sanin Kiristi Yesu Ubangijina, wanda saboda shi ne na yi hasarar kome. Na mai da su kayan wofi, domin in sami Kiristi9. a kuma same ni a cikinsa, ba da wani adalcin kaina wanda yake zuwa daga bin doka ba, sai dai adalcin da yake samuwa ta wurin bangaskiya a cikin Kiristi, adalcin da yake fitowa daga Allah da kuma yake zuwa ta wurin bangaskiya.10. Ina so in san Kiristi da ikon tashinsa daga matattu da kuma zumuncin tarayya cikin shan wahalarsa, in kuma zama kamar sa a cikin mutuwarsa,11. yadda kuma ko ta yaya, in kai ga tashin nan daga matattu.12. Ba cewa na riga na sami dukan wannan ba ne, ko kuma an riga an mai da ni cikakke ba, sai dai ina nacewa don in kai ga samun abin da Kiristi Yesu ya riƙe ni saboda shi.13. ’Yan’uwa, ban ɗauki kaina a kan cewa na riga na sami abin ba. Sai dai abu guda nake yi. Ina mantawa da abin da yake baya, ina kuma nacewa zuwa ga samun abin da yake gaba,14. ina nacewa gaba zuwa ga manufar, don in sami ladar da Allah ya yi mini na kiran nan zuwa sama a cikin Kiristi Yesu.15. Dukanmu da muka balaga ya kamata mu yi wannan irin ganin abubuwa. In kuwa saboda wani dalili tunaninku ya yi dabam, Allah zai bayyana muku wannan ma.16. Sai dai a duk inda muka kai, mu ci gaba da haka.17. Ku haɗa kai da waɗansu cikin bin gurbina, ku kuma lura da waɗanda suke rayuwa bisa ga ƙa’idar da muka ba ku.18. Gama kamar yadda na sha gaya muku yanzu kuma ina sāke gaya muku har ma da hawaye, waɗansu da yawa suna rayuwa kamar abokan gāban gicciyen Kiristi.19. Ƙaddararsu hallaka ce, allahnsu cikinsu ne, rashin kunyarsu shi ne abin fahariyarsu. Hankalinsu yana kan kayan duniya.20. Amma mu ’yan mulkin sama ne. Muna kuma jira zuwan Mai Ceto daga can, Ubangiji Yesu Kiristi,21. shi ne mai ikon kawo dukan abubuwa ƙarƙashin mulkinsa. Ta wurin ikon nan nasa zai sāke jikin nan namu na ƙasƙanci, yă mai da shi kamar jikin nan nasa na ɗaukaka. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.