Baibul a cikin shekara guda Nuwamba 3Makoki 1:1-221. Yanzu birnin ya zama babu kowa a ciki, birnin da a dā yake cike da mutane! Yanzu birnin ya zama kamar gwauruwa, wadda a dā babba ce ita a cikin ƙasashe! Ita da take sarauniya a cikin larduna yanzu ta zama baiwa.2. Tana yin kuka mai zafi da dare, hawaye na gangara a kan kumatunta. A cikin masoyanta duka babu wanda ya yi mata ta’aziyya. Duk abokanta sun yashe ta; sun zama abokan gābanta.3. Bayan wahala da baƙin ciki, Yahuda ta tafi bauta. Ta zauna a cikin ƙasashe, ba tă samu wurin hutawa ba. Duk masu fafararta sun same ta sa’ad da take cikin matuƙar ɓacin rai.4. Hanyoyin zuwa Sihiyona suna makoki, gama ba wanda ya zo bikin da ta shirya. Ba kowa a hanyoyin shiganta. Firistocinta suna gurnani, ’yan matana kuma suna wahala, kuma tana cikin shan wahala ƙwarai.5. Maƙiyanta sun zama shugabanninta; Abokan gābanta suna da kwanciyar rai. Ubangiji ya kawo mata ɓacin rai domin yawan zunubanta. ’Ya’yanta sun tafi bauta, a ƙarƙashin maƙiyanta.6. Diyar Sihiyona ba ta da sauran daraja. ’Ya’yan sarakunanta sun zama kamar bareyi waɗanda suka rasa wurin kiwo; cikin rashin ƙarfi suka guje wa masu fafararsu.7. A cikin kwanakin da take shan wahala take kuma yawo Urushalima ta tuna da dukan dukiyar da take da ita a kwanakin dā can. Sa’ad da mutanenta suka faɗa cikin hannun abokan gābanta, ba wanda ya taimake ta. Maƙiyanta suka dube ta suka yi mata dariya don hallakar da ta auko mata.8. Urushalima ta yi zunubi ƙwarai saboda haka ta zama marar tsarki. Dukan masu martaba ta sun raina ta, gama sun ga tsiraicinta; ita ma da kanta tana nishi da ƙyar ta kuma juya baya.9. Ƙazantarta ta manne wa rigunanta; ba tă kula da nan gaba ba, fāɗuwarta kuwa babban abu ne; babu wanda zai yi mata ta’aziyya. “Duba, ya Ubangiji, ka ga wahalata, gama maƙiyi ya yi nasara.”10. Maƙiya ya kwashe dukiyarta duka; ta ga mutanen da ba su san Allah ba sun shiga wuri mai tsarkinta waɗanda ka hana su shiga taron jama’arka.11. Dukan mutanenta suna nishi da ƙyar suna neman burodi; sun sayar da dukiyarsu don su samu abinci don kada su mutu da yunwa. “ Ubangiji, ka duba ka gani, gama an yashe ni.”12. “Ko wannan ba wani abu ba ne a wurinku, dukanku masu wucewa? Ku duba ku gani. Ko akwai wata wahala kamar irin wadda nake sha, wadda Ubangiji ya auko mini a cikin zafin fushinsa?13. “Daga sama ya aiko da wuta, ya aiko ta cikin ƙasusuwana. Ya shimfiɗa raga a ƙafafuna ya juyo da ni. Ya bar ni ni kaɗai, sumamme dukan yini.14. “Ya ɗaura zunubaina a wuyana; aka naɗe su a hannuwansa. Aka rataye su a wuyana Ubangiji ya kwashe ƙarfina. Ya bashe ni ga waɗanda suka fi ni ƙarfi.15. “Ubangiji ya ƙi duk mayaƙan da suke tare da ni; ya sa wata runduna ta tayar mini ta kuma tattake samarina. Ubangiji ya tattake budurwa Diyar Yahuda kamar ’ya’yan inabi a wurin matsewa.16. “Dalilin da ya sa nake kuka ke nan idanuna kuma suna ta zubar da hawaye. Babu wani a kusa da zai yi mini ta’aziyya, ba wanda zai sabunta ruhuna. ’Ya’yana sun zama fakirai domin maƙiyina ya yi nasara.”17. Sihiyona ta miƙa hannunta, amma ba wani da zai yi mata ta’aziyya. Ubangiji ya umarta cewa maƙwabtansa za su zama maƙiyansa; Urushalima ta zama abar ƙyama a cikinsu.18. “ Ubangiji mai adalci ne, duk da haka na yi tawaye da umarninsa. Ku saurara, jama’a duka; ku dubi wahalar da nake sha. Samarina da ’yan matana duka sun tafi bauta.19. “Na kira abokaina amma sun yashe ni. Firistocina da dattawana sun hallaka a cikin birnin yayinda suke neman abinci don kada su mutu da yunwa.20. “Duba, Ubangiji, ka ga ƙuncin da nake ciki! Ina shan azaba a raina, ba ni da kwanciyar rai a cikin zuciyata, domin na yi tawaye sosai. A waje takobi na kisa; a ciki kuma akwai mutuwa.21. “Mutane suna ji ina nishi da ƙyar, amma ba wanda zai yi mini ta’aziyya. Dukan maƙiyana sun ji wahalar da nake ciki; suna farin ciki da abin da ka yi. Ka kawo ranan nan da ka sanar domin su ma su zama kamar ni.22. “Bari ka ga muguntarsu duka; ka yi musu yadda ka yi mini domin dukan zunubansu. Nishina da yawa kuma zuciyata ta gaji.”Makoki 2:1-221. Yadda Ubangiji ya rufe Diyar Sihiyona da gizagizan fushi! Ya jefar da darajar Isra’ila daga sama zuwa ƙasa; bai tuna da wurin ɗora ƙafafunsa ba a ranar fushinsa.2. Ubangiji ya hallakar da wurin zaman Yaƙub ba tausayi; A cikin fushinsa kuma zai rurrushe kagaran Diyar Yahuda. Ya ƙasƙantar da mulki da masu mulki.3. A cikin zafin fushi ya fasa kowane ƙaho na Isra’ila. Ya janye hannun damansa sa’ad da maƙiyi ya zo. Ya yi ƙuna a cikin Yaƙub kamar wuta mai ƙone duk abin da yake kusa da ita.4. Kamar abokin gāba, ya ɗana bakansa; hannun damansa na shirye. Kamar maƙiyi, ya kashe duk wanda idonsa ya ji daɗin gani; ya zuba fushinsa kamar wuta a kan tenti na Diyar Sihiyona.5. Ubangiji kamar maƙiyi ne; ya hallaka Isra’ila. Ya hallaka wurarenta duka ya kuma hallaka kagaranta. Ya ƙara yawan makoki da baƙin ciki wa Diyar Yahuda.6. Ya rushe haikalinsa kamar lambu; ya hallaka wurin yi masa sujada. Ubangiji ya sa Sihiyona ta manta da bukukkuwanta da kuma ranakunta na Asabbaci; a cikin zafin fushinsa ya watsar da sarki da firist.7. Ubangiji ya ƙi bagadensa ya kuma yi wofi da haikalinsa. Ya ba maƙiyinta fadodinta; suka yi sowa a cikin gidan Ubangiji kamar a ranar da ake yin biki.8. Ubangiji ya ƙuduri niyya yă rushe bangon da yake kewaye da Diyar Sihiyona. Ya auna da igiyar awo bai fasa hallaka ta ba. Ya sa katanga da katanga duk suka lalace.9. Ƙofofinta sun nutse a cikin ƙasa; ya kakkarya ƙarafanta. Sarakunanta da ’ya’yan sarakunanta duk an kai su bauta cikin waɗansu ƙasashe, babu sauran doka, annabawa kuma ba su samun wahayi daga wurin Ubangiji.10. Dattawan Diyar Sihiyona sun zauna shiru a ƙasa; suka kuma sa rigar buhu. ’Yan matan Urushalima suka sunkuyar da kawunansu ƙasa.11. Idanuna sun dushe don yawan kuka, raina na cike da baƙin ciki; zuciyata ta karaya domin mutanena sun hallaka, domin yara da jarirai suna suma a kan hanyoyi a cikin birni.12. Suna ce wa uwayensu, “Ina burodi da ruwan inabi?” Yayinda suke suma kamar mutanen da aka ji masu ciwo a cikin birni, sa’ad da suke mutuwa a hannuwan uwayensu.13. Me zan ce miki? Da me zan kwatanta ki, ke Diyar Urushalima? Da me zan misalta ki, yadda zan iya yi miki ta’aziyya, Ke Budurwa Diyar Sihiyona? Ciwonki yana da zurfi kamar teku. Wane ne zai iya warkar da ke?14. Wahayin annabawanki ƙarya ne kuma marasa amfani; ba su tona zunubanki ba yadda za su iya ceto ki daga bauta ba. Sun yi miki annabcin ƙarya marar amfani.15. Duk masu wucewa suna yi miki tafi na reni; suna yi wa Diyar Urushalima tsaki suna kaɗa kai suna cewa, “Wannan ne birnin da aka ce kyakkyawa ne, mai farantawa dukan duniya rai?”16. Maƙiyanki duka suna ta surutu game da ke; suna tsaki suna cizon haƙora suna cewa, “Mun hallaka ta. Wannan ce ranar da muke jira; yau mun gan ta.”17. Ubangiji ya yi abin da ya shirya; ya cika maganarsa, wadda ya umarta tun daɗewa. Ya jefar da ke ba tausayi, ya bari maƙiya sun yi nasara da ke, ya ɗaukaka ƙahon maƙiyanki.18. Zuciyar mutane ta yi kuka ga Ubangiji. Ya bangon Diyar Urushalima, bar hawayenki su zuba kamar rafi dare da rana; kada ki huta, kada idanunki su huta.19. Ki tashi, ki yi kuka cikin dare, dare na yi sai ki fara kuka; kina buɗewa Ubangiji zuciyarki. Ki ɗaga hannuwanki gare shi domin rayukan ’ya’yanki, waɗanda suka suma don yunwa a kan kowane titi.20. “Ka duba, ka gani ya Ubangiji. Wane ne ka taɓa yi wa haka? Ko ya kamata uwaye su ci ’ya’yansu, ’ya’yan da suka yi reno? Ko ya kamata a kashe firistoci da annabawa a cikin haikalin Ubangiji?21. “Matasa da tsofaffi duk suna kwanciya a cikin ƙurar tituna; an karkashe matasa da ’yan matana da takobi. Ka kashe su a ranar fushinka; ka kashe su ba tausayi.22. “Kamar yadda kake yin gayyata a ranar biki, haka kake kawo mini tsoro a kowane gefe. A ranar fushin Ubangiji ba mai tserewa ba wanda zai tsira; maƙiyina ya kashe waɗanda na yi renonsu, na kuma lura da su.”Zabura 119:137-144137. Mai adalci ne kai, ya Ubangiji, dokokinka kuma daidai ne.138. Farillan da ka shimfiɗa masu adalci ne; su kuma abin dogara ne ƙwarai.139. Kishina ya cinye ni ɗungum, gama abokan gābana sun yi biris da maganganunka.140. An gwada alkawuranka sarai, bawanka kuwa yana ƙaunarsu.141. Ko da yake ni ba kome ba ne an kuwa rena ni, ba na manta da farillanka.142. Adalcinka dawwammame ne dokar kuma gaskiya ce.143. Wahala da damuwa suna a kaina, amma umarnanka su ne farin cikina.144. Farillanka daidai ne har abada; ka ba ni ganewa don in rayu.Karin Magana 28:9-109. In wani ya yi kunnuwa ƙashi ga doka ko addu’arsa ma abar ƙyama ce.10. Duk wanda ya jagorance masu aikata gaskiya a hanyar mugunta zai fāɗa cikin tarkonsa amma marasa abin zargi za su sami gādo mai kyau.Titus 3:1-151. Ka tuna wa mutane su zama masu biyayya ga masu mulki da kuma hukumomi, su zama masu biyayya suna kuma a shirye su yi kowane abin da yake mai kyau,2. kada su zama masu ɓata sunan kowa, su zama masu salama da kulawa, su kuma zama masu matuƙar tawali’u ga dukan mutane.3. A wani lokaci can baya mu ma wawaye ne, marasa biyayya, aka ruɗe mu, sha’awace-sha’awace da kwaɗayi iri-iri suka daure mu, muka yi zaman ƙiyayya da kishi, aka ƙi mu, mu kuma muka ƙi juna.4. Amma da alheri da kuma ƙaunar Allah Mai Cetonmu suka bayyana,5. sai ya cece mu, ba saboda abubuwan adalcin da muka aikata ba, sai dai saboda jinƙansa. Ya cece mu ta wurin wankan nan na sāke haihuwa da kuma sabuntawan nan ta Ruhu Mai Tsarki,6. wanda ya zubo mana a yalwace ta wurin Yesu Kiristi Mai Cetonmu,7. wannan fa domin an kuɓutar da mu ne ta wurin alherinsa, don mu zama magāda masu begen ga rai madawwami.8. Wannan magana tabbatacciya ce, ina kuma so ka nanata waɗannan abubuwa ƙwarai, domin waɗanda suka dogara ga Allah su himmantu ga aiki mai kyau. Waɗannan abubuwa suna da kyau sosai suna kuma da amfani ga kowane mutum.9. Amma ka guji jayayyar banza da ƙididdigar asali da gardandami da faɗace-faɗace game da Doka, gama ba su da riba kuma aikin banza ne.10. Ka gargaɗe mutumin da yake kawo tsattsaguwa sau ɗaya, ka kuma gargaɗe shi sau na biyu. Bayan haka, kada wani abu yă haɗa ka da shi.11. Ka dai san cewa irin mutumin nan ya taurare kuma mai zunubi ne; ya yanke wa kansa hukunci.12. Da zarar na aika Artemas ko Tikikus zuwa wurinka, sai ka yi iyakacin ƙoƙarinka ka zo wurina a Nikofolis, domin na yanke shawara in ci damina a can.13. Ka yi iyakacin ƙoƙarinka ka taimaki Zenas lauyan nan da Afollos a hanyarsu ka kuma tabbata ba su rasa kome ba.14. Dole mutanenmu su koyi ba da kansu ga aikata abin da yake nagari, domin su iya biyan bukatunsu na yau da kullum kada kuma su yi rayuwar marar amfani.15. Dukan waɗanda suke tare da ni suna gaishe ka. Ka gaggai mini da masoyanmu, masu bangaskiya. Alheri yă kasance tare da ku duka. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.