Baibul a cikin shekara guda Disamba 10Hosiya 11:1-111. “Sa’ad da Isra’ila yake yaro, na ƙaunace shi, daga Masar kuma na kira ɗana.2. Amma yawan kiran da na yi wa Isra’ila haka nesa da ni da suke ta yi. Suka miƙa hadaya ga Ba’al suka kuma ƙona turare ga siffofi.3. Ni ne na koya wa Efraim tafiya ina kama su da hannu; amma ba su gane cewa ni ne na warkar da su ba.4. Na bishe su da linzamin alheri da tausayi, da ragamar ƙauna; Na cire karkiya daga wuyansu na kuma rusuna na ciyar da su.5. “Ba za su koma Masar ba Assuriya kuma ba za tă yi mulki a bisansu ba saboda sun ƙi su tuba ba?6. Takuba za su yi ta wulgawa a biranensu, za su hallaka sandunan ƙarafan ƙofofinsu su kuma kawo ƙarshen ƙulle-ƙullensu.7. Mutanena sun ƙudura su juye daga gare ni. Ko da ma suka yi kira ga Mafi Ɗaukaka, ta ko ƙaƙa ba zai girmama su ba.8. “Yaya zan ba da kai, Efraim? Yaya zan miƙa ka, Isra’ila? Yaya zan yi da kai kamar Adma? Yaya zan yi da kai kamar Zeboyim? Zuciyata ta canja a cikina; dukan tausayina ya huru.9. Ba zan zartar da fushina mai zafi ba, ba kuwa zan juya in ragargaza Efraim ba. Gama ni Allah ne, ba mutum ba, Mai Tsarki a cikinku. Ba zan zo cikin fushi ba.10. Za su bi Ubangiji; zai yi ruri kamar zaki. Sa’ad da ya yi ruri, ’ya’yansa za su zo da rawan jiki daga yamma.11. Za su zo da rawan jiki kamar tsuntsaye daga Masar, kamar kurciyoyi daga Assuriya. Zan zaunar da su a cikin gidajensu,” in ji Ubangiji.Hosiya 12:1-141. Efraim yana kiwo a kan iska; yana fafarar iskar gabas dukan yini yana riɓaɓɓanya ƙarairayi da rikici. Ya yi yarjejjeniya da Assuriya ya kuma aika wa Masar man zaitun.2. Ubangiji yana da ƙarar da zai kawo a kan Yahuda; zai hukunta Yaƙub bisa ga hanyoyinsa zai sāka masa bisa ga ayyukansa.3. A cikin mahaifa ya cafke ɗiɗɗigen ɗan’uwansa; a matsayin mutum ya yi kokawa da Allah.4. Ya yi kokawa da mala’ika ya kuma rinjaye shi; ya yi kuka ya kuma yi roƙo don tagomashi. Ya same shi a Betel ya kuma yi magana da shi a can,5. Ubangiji Allah Maɗaukaki, Ubangiji ne sunansa sananne!6. Amma dole ku koma ga Allahnku; ku ci gaba da ƙauna da yin gaskiya, ku kuma saurari Allahnku kullum.7. Ɗan kasuwa yana amfani da mudu marar gaskiya; yana jin daɗin cuta.8. Efraim yana fariya yana cewa, “Ni mai arziki ne ƙwarai; na azurta. Da dukan wadatata ba za a sami wani laifi ko zunubi a gare ni ba.”9. “Ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar; zan sa ku sāke zauna a tentuna, kamar a kwanakin ƙayyadaddun bukukkuwanku.10. Na yi magana da annabawa, na ba su wahayi da yawa na kuma ba da misalai ta wurinsu.”11. Gileyad mugu ne? Mutanensa mutanen banza ne! Suna miƙa bijimai a Gilgal? Bagadansu za su zama tsibin duwatsu. A gonar da aka nome.12. Yaƙub ya gudu zuwa ƙasar Aram; Isra’ila ya yi bauta don yă sami mata, domin kuma yă biya, sai da ya yi kiwon tumaki.13. Ubangiji ya yi amfani da annabi don yă fitar da Isra’ila daga Masar ta wurin annabi ya lura da shi.14. Amma Efraim ya yi muguwar tsokana da ta sa ya yi fushi; shugabansa zai ɗora musu hakkin jini a kansa kuma zai sāka masa saboda wulaƙancinsa.Zabura 139:17-2417. Tunaninka suna da daraja gare ni, ya Allah! Yawansu ba su da iyaka!18. A ce zan iya ƙirgansu, za su fi yashin teku yawa. Sa’ad da na farka, ina nan tare da kai har yanzu.19. Da kawai za ka kashe mugaye, ya Allah! Ku rabu da ni, ku masu kisankai!20. Suna magana game da kai da mugun nufi; maƙiyanka suna ɗaukan sunanka a banza.21. Ba ina ƙin masu ƙinka ba, ya Ubangiji, ina kuma ƙyamar waɗanda suke tayar maka ba?22. Ba ni da wani abu da nake musu sai kiyaye kawai; na ɗauke su abokan gābana.23. Ka bincike ni, ya Allah ka kuma san zuciyata; ka gwada ni ka kuma san damuwata.24. Duba ko akwai wani laifi a cikina, ka bishe ni a madawwamiyar hanya.Karin Magana 29:22-2222. Mutum mai cika fushi yakan tā da faɗa, mai zafin rai kuma kan yi zunubai masu yawa.Yahuda 1:1-251. Yahuda, bawan Yesu Kiristi, ɗan’uwan Yaƙub, Zuwa ga waɗanda aka kira, waɗanda Allah Uba yake ƙauna, waɗanda kuma Yesu Kiristi ya kiyaye.2. Jinƙai, salama da kuma ƙauna, su kasance tare da ku a yalwace.3. Abokaina ƙaunatattu, ko da yake na yi marmari ƙwarai in rubuta muku game da ceton nan namu, sai na ga ya dace in rubuta, in gargaɗe ku ku tsaya da ƙarfi cikin bangaskiya wadda aka danƙa wa mutane masu tsarki na Allah sau ɗaya tak.4. Na faɗa haka ne domin waɗansu mutanen da aka rubuta hukuncinsu tun dā sun shiga cikinku a ɓoye. Su fa marasa tsoron Allah ne. Su ne waɗanda suka mai da alherin Allahnmu ya zama dalilin yin fasikanci, suna kuma mūsun Yesu Kiristi wanda shi ne Makaɗaici Mai Iko Duka da kuma Ubangijinmu.5. Ko da yake kun riga kun san duk wannan, ina so in tuna muku cewa Ubangiji ya ceci mutanensa daga Masar, duk da haka daga baya ya hallaka waɗanda ba su ba da gaskiya ba.6. Haka ma mala’ikun da ba su riƙe matsayinsu na iko ba, waɗanda suka bar ainihin mazauninsu, su ne ya tsare a duhu daure da dawwammamun sarƙoƙi don hukunci ta babbar Ranan nan.7. Haka ma Sodom da Gomorra da garuruwan da suke kewaye da su, waɗanda su ma suka ba da kansu ga fasikanci da muguwar sha’awar jiki, sun zama misalin waɗanda suke shan hukuncin madawwamiyar wuta.8. Haka yake da masu mafarke-mafarken nan, gama sun ƙazantar da jikunansu, suka ƙi bin masu mulki, suna ɓata sunan talikan sararin sama.9. Kai, ko Mika’ilu babban shugaban mala’iku ma, sa’ad da yake mūsu da Iblis game da gawar Musa, bai yi garajen ɗora masa laifi da baƙar magana ba, sai dai ya ce, “Ubangiji yă tsawata maka!”10. Duk da haka mutanen nan suna maganar banza a kan kome da ba su gane ba; kuma abubuwan da suka fahimta bisa ga jiki, kamar dabbobi marasa hankali, waɗannan abubuwa ne suke hallaka su.11. Kaitonsu! Gama sun kama hanyar Kayinu; sun ruga a guje garin neman riba cikin kuskure kamar Bala’am; aka kuma hallaka su cikin tawayen Kora.12. Waɗannan mutane sun zama kamar ƙazanta a taronku na soyayya, suna ta ciye-ciye a cikinku, ba kunya ba tsoro. Su masu kiwo ne da suke ciyar da kansu kawai. Su kamar hadari ne da babu ruwa da iska take kori. Su kamar itatuwa ne, marasa ’ya’ya da rani, waɗanda aka tumɓuke, ko kamar itatuwan da aka tumɓuke suka kuma mutu ƙurmus.13. Su kamar raƙuman ruwan teku ne masu hauka, suna taƙama da tumbatsan kumfar kunyarsu. Su kamar taurari ne masu yawo barkatai, waɗanda aka ajiye mugun duhu saboda su har abada.14. Enok ma, wanda yake na bakwai daga Adamu, ya yi annabci game da waɗannan mutane cewa, “Duba, Ubangiji yana zuwa da dubu dubban tsarkakansa15. don yă yi wa kowa shari’a, yă kuma hukunta duk marasa tsoron Allah game da dukan ayyukansu na rashin tsoron Allah da suka aikata ta hanyar rashin tsoron Allah, da kuma dukan baƙaƙen kalmomin da masu zunubi marasa tsoron Allah suka faɗa game da shi.”16. Waɗannan mutane dai, gunaguni gare su, kullum ganin laifin waɗansu suke yi. Muguwar sha’awa ce kaɗai tunaninsu. Sun cika da banzar magana ta yabon kansu. Suna ruɗin mutane da zaƙin baki don samun ribar kansu.17. Amma ku abokaina ƙaunatattu, ku tuna da abin da manzannin Ubangijinmu Yesu Kiristi suka faɗa a dā.18. Sun ce muku, “A kwanakin ƙarshe za a kasance da masu ba’a waɗanda za su bi sha’awace-sha’awacensu na rashin tsoron Allah.”19. Waɗannan mutanen ne, suke kawo rabe-rabe, masu bin abin da jiki yake so, marasa Ruhu.20. Amma ku, abokaina ƙaunatattu, ku gina kanku cikin bangaskiyarku mafi tsarki, ku kuma yi addu’a cikin Ruhu Mai Tsarki.21. Ku zauna cikin ƙaunar Allah yayinda kuke jira jinƙan Ubangijinmu Yesu Kiristi don yă kawo ku ga rai madawwami.22. Ku ji tausayin waɗanda suke shakka;23. ku cece waɗansu ta wurin fizge su daga wuta. Ga waɗansu kuma ku ji tausayinsu, amma tare da tsoro, har ma ku yi ƙyamar tufafin da suka ɓata da ayyukansu na jiki.24. To, yabo yă tabbata a gare shi, shi wanda yake da iko yă tsare ku daga fāɗuwa, yă kuma miƙa ku marasa laifi a gaban ɗaukakarsa da matuƙar farin ciki.25. Gare shi kuma, shi da yake kaɗai Allah Mai Cetonmu, ta wurin Yesu Kiristi Ubangijinmu, bari ɗaukaka, daraja, iko da mulki, su tabbata a gare shi, tun farkon zamanai, yanzu, da har abada abadin! Amin. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.