Baibul a cikin shekara guda Fabrairu 10Fitowa 31:1-181. Sai Ubangiji ya ce wa Musa,2. “Duba, na zaɓi Bezalel ɗan Uri, ɗan Hur, na kabilar Yahuda,3. na kuma cika shi da Ruhun Allah, fasaha, azanci, da kuma sani cikin kowace irin sana’a,4. don yin zāne-zāne na aikin zinariya, azurfa da tagulla,5. don yanka da shirya duwatsu, yin aikin katako, da kuma yin kowane irin aikin sana’ar hannu.6. Ban da haka, na zaɓi Oholiyab ɗan Ahisamak, na kabilar Dan, don yă taimake shi. Na kuma ba da fasaha ga dukan masu aikin sana’ar hannu, don yin duk abin da na umarce ka.7. Tentin Sujada, akwatin Alkawari tare da murfin kafara a bisansa, da dukan kayan aiki na tentin,8. tebur da kayansa, wurin ajiye fitila na zinariya zalla, da dukan kayansa, bagaden ƙona turare,9. bagaden hadaya ta ƙonawa da dukan kayansa, daro tare da mazauninsa,10. da kuma saƙaƙƙun riguna, tsarkakan riguna don Haruna firist da rigunan ’ya’yansa maza, sa’ad da suke hidima a matsayin firistoci,11. da man shafewa, da turare mai ƙanshi don Wuri Mai Tsarki. Za a yi su kamar yadda na umarce ka.”12. Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa,13. “Ka faɗa wa Isra’ilawa, ‘Dole ku kiyaye Asabbataina. Wannan zai zama alama tsakanina da ku daga tsara zuwa tsara, saboda ku sani ni ne Ubangiji, wanda ya mai da ku masu tsarki.14. “ ‘Ku kiyaye Asabbaci, domin yă zama mai tsarki a gare ku. Duk wanda ya ƙazantar da shi, za a kashe shi; duk wanda ya yi wani aiki a ranar, za a ware shi daga mutane.15. Kwana shida, za a yi aiki, amma a rana ta bakwai, Asabbaci ne na hutu, mai tsarki ga Ubangiji. Duk wanda ya yi wani aiki a Asabbaci, za a kashe shi.16. Isra’ilawa za su kiyaye Asabbaci, suna bikinsa daga tsara zuwa tsara a matsayin madawwamin alkawari.17. Zai zama alama tsakanina da Isra’ilawa har abada, gama cikin kwana shida Ubangiji ya yi sama da ƙasa, a rana ta bakwai kuma ya daina aiki, ya kuma huta.’ ”18. Sa’ad da Ubangiji ya gama yin wa Musa magana a kan Dutsen Sinai, sai ya ba shi alluna biyu na Alkawari, allunan duwatsu rubutattu da yatsan Allah.Fitowa 32:1-351. Sa’ad da mutane suka ga Musa ya daɗe bai sauko daga dutse ba, sai suka taru kewaye da Haruna suka ce, “Zo, ka yi mana alloli waɗanda za su yi mana jagora. Game da wannan Musa wanda ya fitar da mu daga Masar dai, ba mu san abin da ya faru da shi ba.”2. Haruna ya amsa musu ya ce, “Ku tuttuɓe zoban zinariya waɗanda suke kunnuwan matanku, da na ’ya’yanku maza da mata, ku kawo mini.”3. Saboda haka dukan mutane suka tuttuɓe ’yan kunnensu suka kawo wa Haruna.4. Sai ya karɓi abubuwan da suka ba shi, ya yi gunki na siffar ɗan maraƙi, ya sassaƙa shi da kayan aiki. Sa’ad da mutane suka gani, sai suka tā da murya suka ce, “Waɗannan su ne allolinku, ya Isra’ila, waɗanda suka fitar da ku daga Masar.”5. Da Haruna ya ga haka, sai ya gina bagade a gaban ɗan maraƙi, ya yi shela ya ce, “Gobe akwai biki ga Ubangiji.”6. Saboda haka kashegari, mutane suka tashi da sassafe suka miƙa hadaya ta ƙonawa, da hadaya ta salama. Bayan haka suka zauna suka ci, suka sha, suka kuma tashi suka yi rawa.7. Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Sauka, gama mutanenka, waɗanda ka fitar da su daga Masar sun ƙazantu.8. Sun yi saurin juyawa daga abin da na umarce su, sun kuma yi wa kansu gunki na siffar ɗan maraƙi. Sun yi sujada ga ɗan maraƙi, suka yi hadaya gare shi, suka kuma ce, waɗannan su ne allolinka ya Isra’ila, waɗanda suka fito da kai daga Masar.”9. Ubangiji ya ce wa Musa, “Na ga waɗannan mutane, mutane ne masu taurinkai.”10. Yanzu ka bar ni kurum fushina yă yi ƙuna a kansu, in hallaka su. Sa’an nan in maishe ka al’umma mai girma.11. Amma Musa ya nemi tagomashin Ubangiji, Allahnsa ya ce, “Ya Ubangiji don me fushinka zai yi ƙuna a kan mutanenka, waɗanda ka fisshe su daga Masar da ikon hannunka mai girma?12. Don me za ka sa Masarawa su ce, ‘Ai, da mugun nufi ne ya fito da su don yă shafe su daga fuskar duniya’? Ka juya daga fushinka mai zafi, ka ji tausayi, kada ka kawo masifa a kan mutanenka.13. Ka tuna da bayinka Ibrahim, Ishaku da Isra’ila, waɗanda ka rantse da kanka cewa, ‘Zan mai da zuriyarka kamar taurarin sama kuma zan ba wa zuriyarka wannan ƙasa wadda na yi musu alkawari, za tă kuma zama abin gādonsu har abada.’ ”14. Sai Ubangiji ya yi juyayi, bai kuwa kawo wa mutanensa bala’in da ya yi niyya ba.15. Musa ya juya, ya sauka daga kan dutsen da alluna biyu na Alkawari a hannuwansa. An yi rubutun a kowane gefe, gaba da baya.16. Allunan aikin Allah ne; rubutun kuma rubutun Allah ne, da ya zāna a kan alluna.17. Sa’ad da Yoshuwa ya ji surutun mutane suna ihu, sai ya ce wa Musa, “Kamar akwai ƙarar yaƙi a sansani.”18. Musa ya amsa ya ce, “Ba ƙarar nasara ba ce, ba ƙarar wanda yaƙi ya ci ba ne; ƙarar waƙa ce nake ji.”19. Da Musa ya kusato sansanin, sai ya ga ɗan maraƙin da kuma mutane suna rawa. Sai fushinsa ya yi ƙuna, ya kuwa jefar da allunan da suke hannuwansa, allunan kuwa suka farfashe a gindin dutsen.20. Sai ya ɗauki ɗan maraƙin da suka yi, ya ƙone a wuta; sa’an nan ya niƙa shi ya zama gari, ya barbaɗa garin a ruwa, ya sa Isra’ilawa suka sha.21. Ya ce wa Haruna, “Mene ne waɗannan mutane suka yi maka da ka kai su ga wannan zunubi mai girma?”22. Haruna ya amsa ya ce, “Kada ka yi fushi da ni ranka yă daɗe, ka san yadda mutanen nan suke da saurin yin mugunta.23. Sun ce mini, ‘Ka yi mana alloli waɗanda za su yi mana jagora, game da wannan Musa dai, wanda ya fito da mu daga Masar, ba mu san abin da ya faru da shi ba.’24. Sai na gaya musu, ‘Duk wanda yana da kayan ado na zinariya, ya cire?’ Sa’an nan suka ba ni zinariya, sai na jefa cikin wuta, wannan ɗan maraƙi ya fito.”25. Musa ya duba ya ga mutane sun kauce gaba ɗaya domin Haruna ya sa suka kauce, har suka zama abin dariya ga abokan gābansu.26. Saboda haka sai ya tsaya a ƙofar sansani ya ce, “Duk wanda yake na Ubangiji yă zo wurina.” Sai dukan Lawiyawa suka taru wurinsa.27. Sa’an nan ya ce musu, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, ‘Kowane mutum yă rataya takobinsa, yă kai yă kawo daga wannan gefe zuwa wancan cikin sansani, kowa yă kashe ɗan’uwansa, da abokinsa, da kuma maƙwabcinsa.’ ”28. Lawiyawa suka yi yadda Musa ya umarta, a ranar, mutane wajen dubu uku suka mutu.29. Sa’an nan Musa ya ce, “An keɓe ku ga Ubangiji a yau, gama kun yi gāba da ’ya’yanku da ’yan’uwanku, ya kuma albarkace ku a wannan rana.”30. Kashegari Musa ya ce wa mutane, “Kun yi zunubi mai girma. Amma yanzu zan hau wurin Ubangiji; wataƙila zan iya yin kafara domin zunubinku.”31. Don haka Musa ya koma wurin Ubangiji ya ce, “Kaito, mutanen nan sun yi zunubi mai girma! Sun yi wa kansu allolin zinariya.32. Amma yanzu, ina roƙonka ka gafarta zunubinsu, in ba haka ba, to, ka shafe ni daga littafin da ka rubuta.”33. Ubangiji ya amsa wa Musa, “Duk wanda ya yi mini zunubi, shi zan shafe daga littafina.34. Yanzu tafi, ka jagoranci mutanen zuwa inda na yi zance, mala’ikana kuma zai sha gabanku. Duk da haka sa’ad da lokaci ya yi da zan yi horo, zan hore su domin zunubinsu.”35. Ubangiji kuwa ya bugi mutanen da annoba, saboda abin da suka yi da ɗan maraƙin da Haruna ya yi.Zabura 21:1-71. Ya Ubangiji, sarki yana farin ciki cikin ƙarfinka. Yana farin cikinsa ƙwarai cikin nasarorin da ka ba shi!2. Ka biya masa bukatar zuciyarsa ba ka kuwa hana masa roƙon da ya yi da leɓunansa ba.3. Ka marabce shi da yalwar albarka ka kuma sa masa rawanin zallan zinariya a kansa.4. Ya nemi ka ba shi rai, ka kuwa ba shi, tsawo kwanaki, har abada abadin5. Ta wurin nasarorin da ka ba shi, ɗaukakarsa mai girma ce; ka mayar masa ɗaukaka da kuma suna.6. Tabbatacce ka ba shi madawwamiyar albarka ka kuma sa shi murna da farin cikin kasancewarka.7. Gama sarki ya dogara gare ka Ubangiji ta wurin ƙauna marar ƙarewa ta Mafi Ɗaukaka ba zai jijjigu ba.Karin Magana 7:24-2724. Yanzu fa, ’ya’yana, ku saurare ni; ku kasa kunne ga abin da nake faɗa.25. Kada ku bar zuciyarku ta juya zuwa hanyoyinta ko ku kauce zuwa hanyoyinta.26. Ta zama sanadin fāɗuwar yawanci; kisan da ta yi ba ta ƙidayuwa.27. Gidanta babbar hanya ce zuwa kabari mai yin jagora zuwa ɗakunan lahira.Mattiyu 25:31-4631. “Sa’ad da Ɗan Mutum ya zo cikin ɗaukakarsa, tare da dukan mala’iku, zai zauna a kursiyinsa cikin ɗaukakar sama.32. Za a tara dukan al’ummai a gabansa, zai kuma raba mutane dabam-dabam yadda makiyayi yakan ware tumaki daga awaki.33. Zai sa tumaki a damansa, awaki kuma a hagunsa.34. “Sa’an nan Sarki zai ce wa waɗanda suke damansa, ‘Ku zo, ku da Ubana ya yi wa albarka; ku karɓi gādonku, mulkin da aka shirya muku tun halittar duniya.35. Gama da nake jin yunwa, kun ciyar da ni, da nake jin ƙishirwa, kun ba ni abin sha, da nake baƙunci, kun karɓe ni,36. da nake bukatar tufafi, kun yi mini sutura, da na yi rashin lafiya, kun lura da ni, da nake kurkuku, kun ziyarce ni.’37. “Sa’an nan masu adalci za su amsa masa, su ce, ‘Ubangiji, yaushe muka gan ka da yunwa muka ciyar da kai, ko da ƙishirwa muka ba ka abin sha?38. Yaushe kuma muka gan ka baƙo muka karɓe ka, ko cikin bukatar tufafi muka yi maka sutura?39. Yaushe kuma muka gan ka cikin rashin lafiya ko a kurkuku muka ziyarce ka?’40. “Sarkin zai amsa ya ce, ‘Gaskiya nake gaya muku, duk abin da kuka yi wa ɗaya daga cikin waɗannan ’yan’uwana mafi ƙanƙanta, ni kuka yi wa.’41. “Sa’an nan zai ce wa waɗanda suke a hagunsa, ‘Ku rabu da ni, la’anannu, zuwa cikin madawwamiyar wutar da aka shirya don Iblis da mala’ikunsa.42. Gama da nake jin yunwa, ba ku ba ni abinci ba, da nake jin ƙishirwa, ba ku ba ni abin sha ba,43. da na yi baƙunci, ba ku karɓe ni ba, da nake bukatar tufafi, ba ku yi mini sutura ba, da na yi rashin lafiya kuma ina a kurkuku, ba ku lura da ni ba.’44. “Su ma za su amsa, su ce, ‘Ubangiji, yaushe muka gan ka cikin yunwa ko ƙishirwa ko baƙo ko cikin bukatar tufafi ko cikin rashin lafiya ko cikin kurkuku, ba mu taimake ka ba?’45. “Zai amsa, yă ce, ‘Gaskiya nake gaya muku, duk abin da ba ku yi wa ɗaya daga cikin waɗannan mafi ƙanƙanta ba, ba ku yi mini ba ke nan.’46. “Sa’an nan za su tafi cikin madawwamiyar hukunci, amma masu adalci kuwa za su shiga rai madawwami.” Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.