Baibul a cikin shekara guda Maris 19Ƙidaya 35:1-341. A filayen Mowab, wajen Urdun, ɗaura da Yeriko, Ubangiji ya yi magana da Musa ya ce,2. “Ka umarci Isra’ilawa su ba wa Lawiyawa garuruwan da za su zauna a ciki daga cikin gādon da Isra’ilawa za su mallaka. A kuma ba su wurin kiwo kewaye da garuruwan.3. Sa’an nan za su kasance da garuruwan da za su zauna, su sami fili, da kuma za su yi kiwon garkensu na shanu da tumaki da kuma sauran dabbobinsu.4. “Wuraren kiwo a kewayen garuruwan da za a ba wa Lawiyawa, girmansu zai zama mai fāɗin kamu dubu ɗaya daga katangar garin.5. A bayan garin, ka auna kamu dubu biyu a wajen gabas, kamu dubu biyu a wajen yamma, kamu dubu biyu wajen kudu, da kuma kamu dubu uku wajen arewa, a bar garin a tsakiya. Za su kasance da wannan a matsayin wurin kiwo na garuruwan.6. “A cikin biranen da za a ba Lawiyawa, shida daga cikin garuruwan za su zama biranen mafaka, inda wanda ya kashe mutum zai gudu yă je. Ban da wannan, a ba su waɗansu garuruwa arba’in da biyu.7. Duka-duka dai a ba Lawiyawa garuruwa arba’in da takwas, tare da wuraren kiwonsu.8. Garuruwan da za ku ba wa Lawiyawa daga ƙasar da Isra’ilawa suka mallaka, za a ba da su bisa girman gādon kowace kabila. Ka karɓi garuruwa masu yawa daga kabilar da take da garuruwa masu yawa, amma kaɗan daga kabilar da ba ta da garuruwa masu yawa.”9. Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa,10. “Ka yi magana da Isra’ilawa, ka ce musu, ‘Sa’ad da kuka haye Urdun zuwa Kan’ana,11. ku zaɓi waɗansu garuruwan da za su zama biranen mafakarku, inda wanda ya kashe mutum cikin kuskure zai iya gudu zuwa.12. Za su zama wuraren mafaka daga hannun mai bin hakki, don kada a kashe mai kisankai, tun ba a kai shi gaban shari’a, a gaban taron jama’a ba.13. Waɗannan garuruwa shida da aka bayar za su zama biranen mafakarku.14. A ba da uku a wannan gefe na Urdun, a kuma ba da uku a Kan’ana, su zama biranen mafaka.15. Waɗannan garuruwa shida za su zama wurin mafaka wa Isra’ilawa, baƙi da duk sauran mutanen da suke zama a cikinsu, saboda duk wanda ya kashe mutum cikin kuskure yă iya gudu zuwa.16. “ ‘In wani ya bugi wani da makami na ƙarfe har ya mutu, to, shi mai kisankai ne; sai a kashe mai kisankan nan.17. Ko kuwa in wani yana riƙe da dutsen da ya isa yă kashe mutum a hannunsa, ya kuma harbi wani da dutsen har ya mutu, to, shi mai kisankai ne, sai a kashe mai kisankan nan.18. Ko kuwa wani yana da makami na itace a hannunsa da ya isa yă kashe mutum, ya kuma bugi wani da shi har ya mutu, shi ma mai kisankai ne, sai a kashe mai kisankan nan.19. Sai mai bin hakkin jinin yă kashe mai kisankan, sa’ad da ya sadu da mai kisankan, sai yă kashe shi.20. In saboda ƙiyayya, mutum ya laɓe, ya soke wani, ko ya jefe shi da wani abu da gangan har ya mutu,21. ko kuwa saboda ƙiyayya ya naushe shi har ya mutu, sai a kashe wannan mutumin da ya yi haka; shi mai kisankai ne. Sai mai bin hakkin jini yă kashe mai kisankan in ya same shi.22. “ ‘Amma in cikin tsautsayi ne ya soke shi, ba don ƙiyayya ba, ko kuma ya jefe shi, ba da gangan ba,23. ko kuwa bai gan shi ba, ya jefa dutsen da zai kashe shi a kansa, ya kuwa mutu, to, da yake shi ba abokin gābansa ba ne, bai kuma yi nufi yă ji masa ba,24. dole taro su yi hukunci tsakanin mai laifin, da mai bin hakkin jini bisa waɗannan ƙa’idodi.25. Dole taro su kāre wanda ake zargi da kisa, daga mai bin hakkin jini. Su mai da shi birnin mafaka inda ya gudu ya tafi. Dole yă kasance a can sai mutuwar babban firist, wanda aka shafe da mai mai tsarki.26. “ ‘Amma in wanda ake zargin ya kuskura ya fita, ya kai iyakar birnin mafaka wadda ya gudu ya je,27. idan mai bin hakkin jinin ya same shi a bayan gari, mai bin hakkin jinin zai iya kashe mai kisankai ɗin ba tare da wani laifi ba.28. Dole wanda ake zargin, yă kasance a birninsa na mafaka sai bayan mutuwa babban firist; sai bayan mutuwar babban firist ne kawai zai iya komo ga mallakarsa.29. “ ‘Waɗannan su ne za su zama ƙa’idodin da za ku kasance da su, a dukan tsararraki masu zuwa.30. “ ‘Kowa da ya kashe wani, za a kashe shi a matsayin mai kisankai, bisa ga shaidar shaidu. Amma kada a kashe wani bisa ga shaidar mutum ɗaya.31. “ ‘Kada a karɓi fansa don ran wanda ya yi kisankai, wanda ya cancanci mutuwa. Lalle ne a kashe shi.32. “ ‘Kada a karɓi fansa saboda wanda ya tsere zuwa birnin mafaka don yă koma yă zauna gidansa tun babban firist bai rasu ba.33. “ ‘Kada ku ƙazantar da ƙasar da kuke zama a ciki. Zub da jini yakan ƙazantar da ƙasa, ba a kuma iya yin kafara saboda wannan ƙasa da aka zub da jini, sai dai ta wurin jinin mutumin da ya zub da jinin.34. Kada ku ƙazantar da ƙasar da kuke zama, wadda ni kuma nake zama a ciki, gama Ni Ubangiji, ina zama a cikin Isra’ilawa.’ ”Ƙidaya 36:1-131. Sai shugabannin gidajen iyalan Gileyad ɗan Makir, ɗan Manasse, waɗanda suka fito daga kabilar zuriyar Yusuf, suka zo, suka yi magana a gaban Musa da shugabanni, shugabannin iyalan Isra’ilawa.2. Suka ce, “Sa’ad da Ubangiji ya umarce ranka yă daɗe, yă raba ƙasar gādo ga Isra’ilawa ta wurin ƙuri’a, ya umarce ka, ka ba wa ’ya’ya matan nan na Zelofehad ɗan’uwanmu gādonsa.3. To, a ce sun auri mutane daga waɗansu kabilan Isra’ilawa fa; ka ga, za a ɗebe gādonsu daga gādon kakanninmu a ƙara wa gādon kabilan mutanen da suka aura ke nan. Ta haka za a ɗebe sashe daga gādon da aka ba mu ke nan.4. Sa’ad da Shekara ta Murnar Isra’ilawa ta kewayo, za a haɗa gādonsu da na kabilan mutanen da suka aura, a kuma ba su mallakar gādon da aka ɗebe daga kabilar kakanninmu.”5. Ta wurin umarnin Ubangiji, Musa ya ba Isra’ilawa wannan umarni, “Abin da kabilar zuriyar Yusuf suke faɗi, daidai ne.6. Ga abin da Ubangiji ya umarta saboda ’ya’ya matan nan na Zelofehad. Za su iya auri duk wanda suka ga dama, muddin sun yi aure a cikin kabilar kakanninsu.7. Ba gādon Isra’ilan da za a ba wa wata kabila daga wata kabila, gama kowane mutumin Isra’ila zai riƙe gādonsa na kabilar da ya gāda daga kakanninsa.8. Kowace ’ya wadda ta ci gādon ƙasa, a kowace kabilar Isra’ilawa, dole tă auri wani cikin kabilar kakanninta, saboda kowane mutumin Isra’ila yă mallaki gādon kakanninsa.9. Ba gādon da za a ba wa wata kabila daga wata kabila, gama kowace kabilar Isra’ilawa za tă riƙe mallaka da ta gāda.”10. Saboda haka ’ya’yan Zelofehad mata suka yi yadda Ubangiji ya umarci Musa.11. ’Ya’yan Zelofehad mata, Mala, Tirza, Hogla, Milka da Nowa, suka auri ’ya’yan ’yan’uwa na gefen mahaifinsu.12. Suka yi aure cikin kabilar zuriyar Manasse ɗan Yusuf, gādonsu kuwa ya kasance a cikin iyali da kuma kabilar mahaifinsu.13. Waɗannan su ne umarnai da ƙa’idodin da Ubangiji ya ba wa Isra’ilawa ta wurin Musa, a filayen Mowab kusa da Urdun, ɗaura da Yeriko.Zabura 35:17-2817. Ya Ubangiji, har yaushe za ka ci gaba da zuba ido kawai? Ka kuɓutar da raina daga farmakinsu, raina mai daraja daga waɗannan zakoki.18. Zan yi godiya cikin taro mai girma; cikin ɗumbun mutane zan yabe ka.19. Kada ka bar maƙaryatan nan, su yi farin ciki a kaina; kada ka bar waɗanda suke ƙina ba dalili, su ji daɗin baƙin cikina.20. Ba sa maganar salama sukan ƙirƙiro zage-zagen ƙarya a kan waɗanda suka zama shiru a ƙasar.21. Sukan wage mini bakinsu suna cewa, “Allah yă ƙara! Da idanunmu mun gani.”22. Ya Ubangiji, ka ga wannan; kada ka yi shiru. Kada ka yi nisa da ni, ya Ubangiji.23. Ka farka, ka kuma tashi ka kāre ni! Ka yi mini faɗa, ya Allahna da shugabana.24. Ka nuna ni marar laifi ne ciki adalcinka, Ya Ubangiji Allahna; kada ka bari su yi farin ciki a kaina.25. Kada ka bari su ce wa kansu, “Allah yă ƙara, dā ma abin da mun so ke nan!” Ko su ce, “Mun haɗiye shi.”26. Bari dukan waɗanda suke farin ciki a kaina a wahalata su sha kunya su kuma ruɗe; bari dukan waɗanda suke ɗaukar kansu sun fi ni su sha kunya da wulaƙanci.27. Bari waɗanda suke murna saboda nasarata su yi sowa don farin ciki da murna; bari kullum su riƙa cewa, “A ɗaukaka Ubangiji, wanda yake farin ciki da zaman lafiyar bawansa.”28. Harshena zai yi zancen adalcinka da kuma yabonka dukan yini.Karin Magana 12:3-33. Ba yadda mutum zai kahu ta wurin aikata mugunta, amma ba za a tumɓuke adali ba.Markus 15:25-4725. Sa’a ta uku na safe ce kuwa aka gicciye shi.26. Akwai rubutu na zarginsa, da ya ce, Sarkin Yahudawa.27. Suka gicciye ’yan fashi biyu tare da shi, ɗaya a damansa, ɗayan kuma a hagunsa.28. 29. Masu wucewa suka zazzage shi. Suka kaɗa kai suna cewa, “To, kai da za ka rushe haikali ka kuma gina shi a kwana uku,30. sai ka sauko daga gicciyen, ka ceci kanka!”31. Haka kuma, manyan firistoci da malaman dokoki suka yi masa ba’a a junansu, suna cewa, “Ya ceci waɗansu, amma ya kāsa ceton kansa!32. Bari wannan Kiristi, wannan Sarkin Isra’ila, yă sauko yanzu daga gicciye, don mu ga mu kuma gaskata.” Waɗanda aka gicciye tare da shi ma suka zazzage shi.33. Daga sa’a ta shida har zuwa sa’a ta tara na rana, duhu ya rufe dukan ƙasar.34. A daidai sa’a ta tara na rana, sai Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Eloi, Eloi, lama sabaktani?” (Wato, “Ya Allahna, ya Allahna, don me ka yashe ni?” ).35. Da waɗansu cikin waɗanda suke tsattsaye kusa da wurin suka ji haka, suka ce, “Ku saurara, yana kiran Iliya.”36. Wani mutum ya ruga ya je ya jiƙo soso da ruwan tsami, ya soka a sanda ya miƙa wa Yesu yă sha. Ya ce, “Ku ƙyale shi. Bari mu ga ko Iliya zai zo yă saukar da shi.”37. Da murya mai ƙarfi, Yesu ya ja numfashinsa na ƙarshe.38. Labulen haikali kuwa ya yage kashi biyu, daga sama har ƙasa.39. Da jarumin da yake tsaye a gaban Yesu ya ji muryarsa, ya kuma ga yadda ya mutu, sai ya ce, “Gaskiya, wannan mutum Ɗan Allah ne!”40. Waɗansu mata suna kallo daga nesa. A cikinsu kuwa akwai Maryamu Magdalin, Maryamu mahaifiyar Yaƙub ƙarami da Yusuf, da kuma Salome.41. A Galili waɗannan mata ne suka riƙa bin sa suna yin masa hidima. Waɗansu mata da yawa da suka zo tare da shi daga Urushalima, su ma suna nan a can.42. Ranar kuwa ita ce ranar Shirye-shirye (wato, ana kashegari Asabbaci). Saboda haka, da yamma ta yi, sai43. Yusuf daga Arimateya, wani sanannen ɗan Majalisa, wanda dā ma yake jiran zuwan mulkin Allah, ya je wajen Bilatus ba tsoro, ya roƙa a ba shi jikin Yesu.44. Bilatus ya yi mamaki da ya ji cewa Yesu ya riga ya mutu. Sai ya kira jarumin ya tambaye shi ko Yesu ya riga ya mutu.45. Da ya ji ta bakin jarumin cewa haka ne, sai ya ba wa Yusuf jikin.46. Sai Yusuf ya kawo zanen lilin, ya saukar da jikin, ya nannaɗe shi da lilin ɗin, sa’an nan ya sa shi a kabarin da aka fafe a cikin dutse. Sai ya gungura wani dutse ya rufe bakin kabarin.47. Maryamu Magdalin da Maryamu uwar Yusuf sun ga inda aka kwantar da shi. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.