Baibul a cikin shekara guda Mayu 242 Samaʼila 19:1-431. Aka faɗa wa Yowab cewa, “Sarki yana kuka, yana kuma makoki saboda Absalom.”2. Saboda haka sai nasarar da aka yi a ranar ta zama makoki ga dukan sojoji, gama a ranar, rundunoni sun ji an ce, “Sarki yana baƙin ciki domin ɗansa.”3. Mutane fa suka shiga birni shiru, sai ka ce waɗanda sukan sace jiki don kunya sa’ad da suka gudo daga yaƙi.4. Sarki ya rufe fuskarsa ya yi kuka da ƙarfi yana cewa, “Ya ɗana Absalom! Ya Absalom ɗana, ɗana!”5. Sai Yowab ya shiga gidan sarki ya ce, “Yau ka kunyatar da dukan mutanenka, waɗanda ba da daɗewa ba sun ceci ranka, da rayukan ’ya’yanka maza, da na ’ya’yanka mata, da na matanka da kuma na ƙwarƙwaranka.6. Kana ƙaunar maƙiyinka, kana ƙin waɗanda suke ƙaunarka. Ka bayyana a fili cewa komandodi da sojojinsu ba kome ba ne a gare ka. Na ga cewa da za ka yi farin ciki, da a ce Absalom yana da rai a yau, dukanmu kuma mun mutu.7. Yanzu ka fita ka ƙarfafa mutanenka. Na rantse da Ubangiji, in ba ka fita ba, babu mutum guda da za a bari tare da kai a daren nan. Wannan zai fi maka muni fiye da kowace irin masifar da ta auko maka tun ƙuruciyarka har zuwa yanzu.”8. Saboda haka sarki ya tashi, ya zauna a bakin hanyar shiga. Da aka faɗa wa mutane cewa, “Sarki yana zaune a bakin hanyar shiga,” sai duk suka zo gabansa. Ana cikin haka, Isra’ilawa dai sun riga sun tsere zuwa gidajensu.9. Mutane ko’ina a kabilan Isra’ila, suka yi ta gardama da juna, suna cewa, “Sarki ne ya cece mu daga hannun abokan gābanmu, shi ne kuma ya kuɓutar da mu daga hannun Filistiyawa. Amma ga shi ya tsere daga ƙasar saboda Absalom;10. kuma shi Absalom, da muka naɗa yă yi mulkinmu, ya mutu a yaƙi. Saboda haka don me ba kwa ce wani abu game da dawo da sarki?”11. Sai Sarki Dawuda ya aika da saƙo zuwa wurin Zadok da Abiyatar, firistoci, ya ce, “Ku tambayi dattawan Yahuda, ‘Me ya sa ku ne za ku zama na ƙarshe a yin tunanin komar da sarki zuwa fada, da yake abin da ake faɗi ko’ina a Isra’ila ya kai kunnen sarki a mazauninsa?12. Ku ’yan’uwana ne, jikina, jinina kuma. To, don me za ku zama na ƙarshe na yarda a dawo da sarki zuwa fada?’13. Ku kuma ce wa Amasa, ‘Ashe, kai ba jikina ba ne da jinina? Allah yă hukunta ni, da hukunci mai tsanani, idan daga yanzu ba ka zama komandan sojojina a maimakon Yowab ba.’ ”14. Ta haka ya rinjayi zukatan dukan mutane Yahuda, kamar mutum ɗaya. Suka aika da saƙo wurin sarki suka ce, “Ka dawo, kai da dukan mutanenka.”15. Sa’an nan sarki ya dawo, ya kuma tafi har zuwa Urdun. To, mutanen Yahuda suka zo Gilgal don su fita su taryi sarki, su kuma kawo shi ƙetaren Urdun.16. Shimeyi ɗan Gera, mutumin Benyamin daga Bahurim ya gaggauta, ya gangara tare da mutanen Yahuda don su taryi Sarki Dawuda.17. Tare da shi akwai kabilar Benyamin mutum dubu, tare da Ziba, mai hidimar gidan Shawulu, da ’ya’yansa maza goma sha biyar, da bayi ashirin. Suka ruga zuwa Urdun, inda sarki yake.18. Suka haye a mashigin don su ƙetaro da iyalin sarki, su kuma yi duk abin da yake so. Sa’ad da Shimeyi ɗan Gera ya haye Urdun, sai ya fāɗi rubda ciki a gaban sarki19. ya ce masa, “Ranka yă daɗe, ina roƙonka kada ka riƙe laifina a zuciya. Kada ka tuna da laifin da na yi maka ranka yă daɗe, ranan nan da kake gudu daga Urushalima. Kada ka tuna da shi ko kaɗan.20. Na sani ni bawanka na yi maka laifi. Shi ya sa na zama na farko daga dukan Gidan Yusuf, da mutanen Isra’ila wanda ya fito don yă tarye ka yau, ranka yă daɗe, sarki.”21. Sai Abishai ɗan Zeruhiya ya ce, “Bai kamata a kashe Shimeyi saboda wannan ba? Ya la’anci shafaffe na Ubangiji.”22. Dawuda ya ce, “Me ya haɗa ni da ku, ku ’ya’yan Zeruhiya? Yau ɗin nan kun zama maƙiyana! Ya kamata a kashe wani a Isra’ila a yau? Ban san cewa yau ni sarki ne a bisa Isra’ila ba?”23. Saboda haka sarki ya ce wa Shimeyi, “Ba za ka mutu ba.” Sarki kuwa ya yi alkawari har da rantsuwa.24. Mefiboshet, jikan Shawulu, shi ma ya gangara don yă taryi sarki. Tun daga ranar da sarki ya gudu har ran da ya komo lafiya, Mefiboshet bai lura da ƙafafunsa, ko yă aske gemunsa, ko yă wanke tufafinsa ba.25. Sa’ad da ya zo daga Urushalima don yă taryi sarki, sai sarki ya ce masa, “Me ya sa ba ka tafi tare da ni ba Mefiboshet?”26. Sai ya ce, “Ranka yă daɗe sarki, da yake bawanka gurgu ne, na ce, ‘A sa mini sirdi a kan jakina don in hau in tafi tare da sarki.’ Amma Ziba bawana ya bashe ni.27. Ya kuwa ɓata suna bawanka a gaban ranka yă daɗe, sarki. Ranka yă daɗe, sarki yana kama da mala’ikan Allah, ka yi abin da ka ga ya fi maka kyau.28. Duk zuriyar kakana ba su cancanci kome ba sai mutuwa daga ranka yă daɗe, amma ka ba wa bawanka wuri cikin mutanen da suke ci a teburinka. Saboda haka, wanda ’yanci nake da shi da zan yi wani ƙarin roƙo a wurin sarki?”29. Sarki ya ce masa, “Me ya sa kake zancen nan? Ai, na riga na umarta, da kai, da Ziba ku raba filayen.”30. Mefiboshet ya ce wa sarki, “Bari yă ɗauki kome, yanzu da ranka yă daɗe, sarki ya dawo gida lafiya.”31. Barzillai mutumin Gileyad shi ma ya zo daga Rogelim don yă ƙetare Urdun tare da sarki, yă kuma sallame shi daga can.32. To, Barzillai fa tsoho ne, mai shekara tamanin. Ya tanada wa sarki a lokaci da yake Mahanayim, gama shi attajiri ne.33. Sarki ya ce wa Barzillai, “Ka ƙetaro tare da ni ka zauna tare da ni a Urushalima, zan kuwa tanada maka.”34. Amma Barzillai ya ce wa sarki, “Shekara nawa ya rage mini har da zan tafi Urushalima da sarki?35. Yanzu ina da shekara tamanin. Zan iya bambanta abu mai daɗi da marar daɗi kuma ne? Bawanka zai iya jin ɗanɗano abin da yake ci, ko yake sha ne? Har yanzu zan iya jin muryoyin mawaƙan maza da mata? Don me bawanka zai zama ƙari kaya ga ranka yă daɗe?36. Bawanka zai ƙetare Urdun tare da sarki, yă ɗan yi maka rakiya kaɗan. Me ya sa ranka yă daɗe zai ba ni irin wannan lada.37. Ka bar bawanka yă koma, don in mutu a garina, kusa da kabarin mahaifina da mahaifiyata. Amma ga bawanka Kimham. Bari yă ƙetare tare da ranka yă daɗe, sarki. Ka yi abin da ka ga dama da shi.”38. Sarki ya ce, “Kimham zai ƙetare tare da ni, zan kuwa yi masa abin da ya gamshe ka. Kuma duk abin da kake bukata a wurina, zan yi maka.”39. Saboda haka dukan mutane suka ƙetare Urdun, sa’an nan kuma sarki ma ya ƙetare. Sarki ya yi wa Barzillai sumba ya albarkace shi, sa’an nan Barzillai ya koma gidansa.40. Sa’ad da sarki ya ƙetare zuwa Gilgal, Kimham ma ya ƙetare tare da shi. Dukan sojojin Yahuda da rabin sojojin Isra’ila suka ƙetare da sarki.41. Nan take sai ga mutane Isra’ila suna zuwa wurin sarki, suna cewa, “Don me ’yan’uwanmu, mutanen Yahuda, suka saci sarki, suka kawo shi da iyalinsa a ƙetaren Urdun, tare da dukan mutanensa?”42. Dukan mutanen Yahuda suka ce wa mutanen Isra’ila, “Mun yi haka domin sarki danginmu na kurkusa ne. Don me kuke fushi game da wannan? Mun ci wani abu daga cikin kayan sarki ne? Mun ɗauki wani abu wa kanmu ne?”43. Sa’an nan mutanen Isra’ila suka ce wa mutanen Yahuda, “Muna da rabo goma a wurin sarki; ban da haka ma, muna da hakki mafi yawa a wurin Dawuda fiye da ku. Don me kuke mana reni? Ba mu ne ma muka fara magana dawowa da sarki ba?” Amma mutanen Yahuda suka ɗauka maganar da zafi fiye da mutanen Isra’ila.2 Samaʼila 20:1-261. Akwai wani mai tā-da-na-zaune-tsaye, sunansa Sheba, ɗan Bikri, daga kabilar Benyamin, a wurin. Sai ya busa ƙaho, ya yi ihu ya ce, “Ba mu da rabo a wurin Dawuda, ba mu da sashe a wurin ɗan Yesse! Kowa yă nufi tentinsa, ya Isra’ila!”2. Saboda haka dukan mutane Isra’ila suka bar Dawuda don su bi Sheba ɗan Bikri. Amma mutanen Yahuda suka kasance a wurin sarki tun daga Urdun har zuwa Urushalima.3. Da Dawuda ya komo fadarsa a Urushalima, sai ya ɗauko ƙwarƙwaran goma nan da ya bari su lura da fada, ya keɓe su a wani gida inda za a yi tsaronsu. Ya tanada musu, amma bai kwana da su ba. Aka sa su a keɓe har iyakar rayuwarsu, suka yi zama kamar gwauraye.4. Sa’an nan sarki ya ce wa Amasa, “Ka tattaro mutanen Yahuda su zo wurina cikin kwana uku, kai kuwa ka kasance a can kai kanka.”5. Amma da Amasa ya tafi kiran mutanen Yahuda, ya ɗauki lokaci fiye da lokacin da sarki ya ba shi.6. Dawuda ya ce wa Abishai, “Ina gani Sheba ɗan Bikri zai ba mu wuya fiye da Absalom. Ka ɗauki mutanen maigidanka ka fafare shi, don kada yă sami garuruwa masu katanga yă tsere mana.”7. Saboda haka mutanen Yowab da Keretawa da Feletiyawa da dukan jarumawa suka fita a ƙarƙashin Abishai. Suka fita daga Urushalima don su fafari Sheba ɗan Bikri.8. Yayinda suke a babban dutse a Gibeyon, Amasa ya zo don yă tarye su. Yowab kuwa yana sanye da doguwar rigar soja, a ɗamarar da ya sha kuwa akwai wuƙa a cikin kube. Da ya zo gaba sai wuƙar ta zāre daga kube ta fāɗi.9. Yowab ya ce wa Amasa, “Yaya kake, ɗan’uwana?” Sai Yowab ya kama gemun Amasa da hannun dama don yă yi masa sumba.10. Amasa kuwa bai lura da wuƙar da take hannun Yowab ba, Yowab kuwa ya soke shi da wuƙar a ciki, hanjinsa suka zube ƙasa. Ba tare da ƙarin suƙa ba, Amasa ya mutu. Sa’an nan Yowab da ɗan’uwansa Abishai suka fafari Sheba ɗan Bikri.11. Ɗaya daga cikin mutanen Yowab ya tsaya kusa da Amasa ya ce, “Duk mai son Yowab, kuma duk mai son Dawuda, yă bi Yowab!”12. Amasa kuwa yana kwance cikin tafkin jininsa a kan hanya, sai mutumin ya ga dukan sojoji suka zo suka tsaya cik a can. Da ya gane cewa duk wanda ya haura zuwa wurin Amasa sai ya tsaya, sai ya ja gawar Amasa daga hanyar ya kai can cikin wani fili ya rufe shi da zane.13. Bayan an ɗauke Amasa daga hanya, sai dukan mutane suka bi Yowab don fafaran Sheba ɗan Bikri.14. Sheba ya bi ta dukan kabilan Isra’ila zuwa Abel da kuma ta dukan yankin Beriyawa, waɗanda suka taru suka bi shi.15. Sai dukan rundunonin da suke tare da Yowab suka zo suka yi wa Sheba kwanton ɓauna a Abel-Bet-Ma’aka. Suka tara ƙasa kewaye da jikin katangar birnin daidai da tsayinta. Sa’an nan waɗansu kuma suna ƙoƙarin rushe katangar.16. Sai wata mata mai hikima ta yi kira daga ciki birnin ta ce, “Ku saurara! Ku saurara! Ku gaya wa Yowab yă zo nan ina so in yi magana da shi.”17. Ya tafi wurinta, sai ta ce, “Kai ne Yowab?” Ya ce, “Ni ne”. Ta ce, “Ka ji abin da zan ce maka.” Ya ce, “Ina jinki.”18. Ta ci gaba ta ce, “A dā can, akan ce, ‘Sami amsarka a Abel,’ shi ke nan an gama.19. Mu ne masu salama da kuma amintattu na Isra’ila. Kana ƙoƙari ka hallaka birnin da yake uwa a Isra’ila. Don me kake so ka hallakar da gādon Ubangiji?”20. Yowab ya ce, “Allah yă sawwaƙe! Allah yă sawwaƙe in hallaka, ko in lalace gādon Ubangiji.21. Ba haka ba ne batun. Wani mai suna Sheba ɗan Bikri ne, daga ƙasar tudun Efraim, ya tayar wa sarki, yana gāba da Dawuda. Ki ba mu wannan mutum, zan kuwa janye daga birnin.” Matar ta ce wa Yowab, “Za a jefa maka kansa daga katanga.”22. Sa’an nan matar ta tafi wurin dukan mutane da shawararta mai hikima, sai suka datse kan Sheba ɗan Bikri suka jefa wa Yowab. Saboda haka sai ya busa ƙaho, mutanensa kuwa suka watse daga birnin, kowa ya koma gidansa. Yowab kuma ya koma wurin sarki a Urushalima.23. Yowab ne yake shugabancin dukan rundunoni; Benahiya ɗan Yehohiyada ne yake shugabancin Keretawa da Feletiyawa;24. Adoniram kuwa shi ne shugaban aikin gandu; Yehoshafat ɗan Ahilud shi ne marubucin tarihi;25. Shewa kuwa magatakarda; Zadok da Abiyatar su ne firistoci;26. Ira mutumin Yayir kuwa shi ne firist na Dawuda.Zabura 67:1-71. Bari Allah yă yi mana alheri yă kuma albarkace mu yă kuma sa fuskarsa ta haskaka a kanmu,2. don a san hanyoyinka a duniya, cetonka kuma a cikin dukan al’ummai.3. Bari mutane su yabe ka, ya Allah; bari dukan mutane su yabe ka.4. Bari al’ummai su yi murna su kuma rera don farin ciki, gama kana mulkin mutanenka da adalci kana kuma bi da al’umman duniya.5. Bari mutane su yabe ka, ya Allah; bari dukan mutane su yabe.6. Sa’an nan ƙasa za tă ba da girbinta Allah kuma, Allahnmu, zai albarkace mu.7. Allah yă sa mana albarka, dukan iyakar duniya kuma su ji tsoronsa.Karin Magana 16:33-3333. Akan jefa ƙuri’a a kan cinya, amma kowace shawara mai kyau daga Ubangiji ne.Karin Magana 17:1-11. Gara ka ci busasshen burodi da kwanciyar rai kuma shiru da ka je cin abinci a gidan da ke cike da biki amma da ɓacin rai.Yohanna 8:1-271. Amma Yesu ya tafi Dutsen Zaitun.2. Da sassafe ya sāke bayyana a filin haikali, inda dukan mutane suka taru kewaye da shi, sai ya zauna don yă koya musu.3. Sai malaman dokoki da Farisiyawa suka kawo wata macen da aka kama a zina. Suka sa ta tsaya a gaban taron4. suka kuma ce wa Yesu, “Malam, an kama wannan mace tana zina.5. A cikin Doka Musa ya umarce mu, mu jajjefe irin waɗannan mata. To, me ka ce?”6. Sun yi wannan tambaya ce don su sa masa tarko, don su sami hanyar zarge shi. Amma Yesu ya sunkuya ya fara rubutu a ƙasa da yatsarsa.7. Da suka ci gaba da yin masa tambayoyi, sai ya miƙe tsaye ya ce musu, “In da wani a cikinku da ba shi da zunubi, sai yă fara jifanta da dutse.”8. Sai ya sāke sunkuyawa ya kuma yi rubutu a ƙasa.9. Da jin haka, waɗanda suka ji sai suka fara tashi daga wurin ɗaya-ɗaya, tun daga babbansu har ya zuwa ƙaraminsu, sai da aka bar Yesu kaɗai, tare da macen tsaye a wurin.10. Sai Yesu ya miƙe tsaye ya tambaye ta ya ce, “Mace, ina suke? Ba wanda ya hukunta ki?”11. Ta ce, “Ba kowa, ranka yă daɗe.” Sai Yesu ya ce, “Haka ni ma ban hukunta ki ba. Ki tafi, ki daina rayuwar zunubi.”12. Sa’ad da Yesu ya sāke magana da mutanen, sai ya ce, “Ni ne hasken duniya. Duk wanda ya bi ni ba zai yi tafiya cikin duhu ba, sai dai yă sami hasken rayuwa.”13. Sai Farisiyawa suka tambaye shi suka ce, “Ga kai dai, kana yi wa kanka shaida, shaidarka kuwa ba tabbatacciya ba ce.”14. Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ko na shaidi kaina, ai, shaidata tabbatacciya ce, gama na san inda na fito da kuma inda za ni. Amma ku ba ku san inda na fito ko inda za ni ba.15. Kuna shari’a bisa ga ma’aunin mutane; ni kuwa ba na yin wa kowa shari’a.16. Amma ko da zan yi shari’a, shari’ata daidai ce, don ba ni kaɗai ba ne. Ina tare da Uba da ya aiko ni.17. A cikin Dokarku a rubuce yake cewa shaidar mutum biyu tabbatacciya ce.18. Ni ne nake shaidar kaina, Uba da ya aiko ni kuma yana shaidata.”19. Suka tambaye shi suka ce, “Ina Uban nan naka?” Sai Yesu ya ce, “Ba ku san ni ko Ubana ba. Da kun san ni, da za ku san Ubana ma.”20. Ya faɗi waɗannan kalmomi ne yayinda yake koyarwa a filin haikali, kusa da inda ake ajiye baye-baye. Duk da haka ba wanda ya kama shi, domin lokacinsa bai yi ba tukuna.21. Har wa yau Yesu ya sāke ce musu, “Zan tafi, za ku kuwa neme ni, za ku kuma mutu cikin zunubinku. Inda za ni, ba za ku iya zuwa ba.”22. Wannan ya sa Yahudawa suka yi tambaya suka ce, “Zai kashe kansa ne? Shi ya sa yake cewa, ‘Inda za ni, ba za ku iya zuwa ba’?”23. Amma ya ci gaba da cewa, “Ku daga ƙasa kuke; ni kuwa daga bisa ne. Ku na duniyan nan ne; ni kuwa ba na duniyan nan ba ne.24. Na gaya muku cewa za ku mutu cikin zunubanku; in ba ku gaskata cewa ni ne wanda na ce nake ba, lalle za ku mutu cikin zunubanku.”25. Suka ce, “Wane ne kai?” Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ni ne wannan da na sha faɗi muku.26. Ina da abubuwa masu yawa da zan faɗa game ku in kuma yi muku shari’a. Amma wanda ya aiko ni mai aminci ne, abin da kuma na ji daga gare shi, shi nake gaya wa duniya.”27. Ba su gane cewa yana yin musu magana game da Ubansa ba ne. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.