Baibul a cikin shekara guda Agusta 10Ayuba 11:1-201. Sa’an nan Zofar mutumin Na’ama ya amsa,2. “Duk surutun nan ba za a amsa maka ba? Ko mai surutun nan marar laifi ne?3. Ko maganganun nan naka marasa amfani za su sa mutane su yi maka shiru? Ba wanda zai kwaɓe ka lokacin da kake faɗar maganar da ba daidai ba?4. Ka ce wa Allah, ‘Abin da na gaskata ba laifi ba ne kuma ni mai tsabta ne a gabanka.’5. Da ma Allah zai yi magana, yă buɗe baki yă faɗi wani abin da ka yi da ba daidai ba6. yă kuma buɗe maka asirin hikima, gama hikima ta gaskiya tana da gefe biyu. Ka san wannan, Allah ya riga ya manta da waɗansu zunubanka.7. “Ko za ka iya gane al’amuran Allah? Ko za ka iya gane girman asirin Maɗaukaki?8. Sun fi nisan sama tudu, me za ka iya yi? Sun fi zurfin kabari zurfi, me za ka sani?9. Tsayinsu ya fi tsawon duniya da kuma fāɗin teku.10. “In ya zo ya kulle ka a kurkuku ya ce kai mai laifi ne, wa zai hana shi?11. Ba shakka yana iya gane mutanen da suke marasa gaskiya; kuma in ya ga abin da yake mugu, ba ya kula ne?12. Amma daƙiƙin mutum ba ya taɓa zama mai hikima kamar dai a ce ba a taɓa haihuwar ɗan aholaki horarre.13. “Duk da haka in ka miƙa masa zuciyarka, ka kuma miƙa hannuwanka gare shi,14. in ka kawar da zunubin da yake hannunka, ba ka bar zunubi ya kasance tare da kai ba15. shi ne za ka iya ɗaga fuskarka ba tare da jin kunya ba; za ka tsaya da ƙarfi kuma ba za ka ji tsoro ba.16. Ba shakka za ka manta da wahalolinka, za ka tuna da su kamar yadda ruwa yake wucewa.17. Rayuwarka za tă fi hasken rana haske, duhu kuma zai zama kamar safiya.18. Za ka zauna lafiya, domin akwai bege; za ka duba kewaye da kai ka huta cikin kwanciyar rai.19. Za ka kwanta, ba wanda zai sa ka ji tsoro, da yawa za su zo neman taimako a wurinka.20. Amma idanun mugaye ba za su iya gani ba, kuma ba za su iya tserewa ba; begensu zai zama na mutuwa.”Ayuba 12:1-251. Sai Ayuba ya amsa,2. “Ba shakka ku ne mutanen nan, hikima za tă mutu tare da ku!3. Amma ni ma ina da hankali kamar ku; ba ku fi ni ba. Wane ne bai san duk waɗannan abubuwan ba?4. “Na zama abin dariya ga abokaina, ko da yake na yi kira ga Allah ya kuwa amsa mini, duk da haka suka yi mini riya ko da yake ni mai adalci ne kuma marar laifi!5. Mutanen da ba su da damuwa suna jin daɗin ganin waɗanda suke dab da fāɗuwa.6. Amma wurin zaman ’yan fashi yana nan ba mai damunsu, waɗanda kuma suke saɓa wa Allah suna zamansu lafiya, har ma da masu ɗaukar allahnsu a hannuwansu.7. “Amma ka tambayi dabbobi, za su kuma koya maka, ko kuma tsuntsayen sararin sama kuma za su gaya maka.8. Ko ka yi magana da duniya, za tă kuma koya maka, ko kuma ka bar kifin teku su sanar da kai.9. Wane ne cikin waɗannan bai san cewa hannun Ubangiji ne ya yi wannan ba?10. Ran kowace halitta yana a hannunsa, haka kuma numfashin dukan ’yan adam.11. Ko kunne ba ya gwada kalmomi kamar yadda harshe yake ɗanɗana abinci?12. Ko ba a wurin tsofaffi ake samun hikima ba? Ba tsawon rai yana kawo ganewa ba?13. “Allah ne mai iko da kuma hikima, shawara da ganewa nasa ne.14. Abin da ya rushe ba a iya ginawa ba; in ya kulle mutum ba a iya buɗe shi a sake shi ba.15. Idan ya hana ruwan sama, za a yi fări; in kuma ya saki ruwa za a yi ambaliya.16. Shi ne mai ƙarfi da kuma mai nasara; mai ruɗi da wanda aka ruɗa, duk nasa ne.17. Yakan sa mashawarta su zama marasa hikima yă kuma sa wawaye su zama masu shari’a.18. Yana cire sarƙar da sarakuna suka ɗaura yă kuma ɗaura musu wata tsumma a kwankwaso.19. Yakan ƙasƙantar da firistoci yă kuma tumɓuke masu ikon da aka kafa tun da daɗewa.20. Yana sa amintattun mashawarta su yi shiru yakan kawar da hikimar dattawa.21. Yakan sa masu iko su ji kunya yă kuma ƙwace ƙarfin masu ƙarfi.22. Yana buɗe abubuwan da suke cikin duhu yă kuma kawo haske a wuraren da ba haske;23. yana sa al’ummai su zama manya, sai kuma yă hallaka su; yana sa al’ummai su ƙasaita, yă kuma watsar da su.24. Yana hana shugabannin duniya ganewa; Ya bar su su yi ta makuwa, su ruɗe, su ɓata.25. Suna lallube cikin duhu ba haske; yă sa su yi ta tangaɗi kamar bugaggu.Zabura 94:1-111. Ya Ubangiji, Allahn da yake ramuwa, Ya Allah wanda yake ramuwa, ka haskaka.2. Ka tashi, ya Alƙalin duniya; ka sāka wa masu girman kai abin da ya dace da su.3. Har yaushe mugaye, ya Ubangiji har yaushe mugaye za su yi ta murna?4. Suna ta yin maganganun fariya; dukan masu aikata mugunta sun cika da fariya.5. Suna murƙushe mutanenka, ya Ubangiji; suna danne gādonka.6. Suna kashe gwauraye da kuma baƙi; suna kisan marayu.7. Suna ce, “ Ubangiji ba ya gani; Allah na Yaƙub bai kula ba.”8. Ku mai da hankali, ku marasa azanci a cikin mutane; ku wawaye, yaushe za ku zama masu hikima?9. Shi da ya sa kunne ba don a ji ba ne? Shi da ya yi ido ba don yă gani ba ne?10. Shi da yake yi wa al’ummai horo ba ya hukunci ne? Shi da yake koya wa mutum ba shi da sani ne?11. Ubangiji ya san tunanin mutum; ya san cewa tunaninsu banza ne.Karin Magana 22:24-2524. Kada ka yi abokantaka da mai zafin rai, kada ka haɗa kai da wanda ba shi da wuya ya yi fushi,25. in ba haka ba za ka koyi hanyoyinsa ka kuma sa kanka a tarko.Romawa 10:1-211. ’Yan’uwa, abin da zuciyata take so da kuma addu’ata ga Allah saboda Isra’ilawa shi ne su sami ceto.2. Gama na shaida su a kan suna da kishi bin Allah, sai dai kishinsu ba a bisa sani ba.3. Da yake ba su san adalcin da yake fitowa daga Allah ba suka kuma nemi su kafa nasu, sai suka ƙi miƙa kai ga adalcin Allah.4. Kiristi shi ne ƙarshen doka domin a sami adalci wa kowane mai bangaskiya.5. Musa ya bayyana adalcin da yake ga Doka cewa, “Mutumin da ya aikata waɗannan abubuwa zai rayu ta wurinsu.”6. Amma adalcin da yake ga bangaskiya yana cewa, “Kada ka faɗa a zuciyarka, ‘Wa zai hau sama?’ ” (wato, don yă sauko da Kiristi),7. “ko kuwa ‘Wa zai gangara can zurfin ƙasa?’ ” (wato, don yă hauro da Kiristi daga matattu).8. Amma mene ne aka ce? “Maganar tana kusa da kai; tana cikin bakinka da kuma cikin zuciyarka,” wato, maganar bangaskiyan nan da muke shela.9. Cewa in ka furta da bakinka, “Yesu Ubangiji ne,” ka kuma gaskata a zuciyarka cewa Allah ya tā da shi daga matattu, za ka sami ceto.10. Gama da zuciyarka ce kakan gaskata a kuma kuɓutar da kai, da bakinka ne kuma kake furta a kuma cece ka.11. Kamar yadda Nassi ya ce, “Duk wanda ya gaskata da shi ba zai taɓa shan kunya ba.”12. Gama ba bambanci tsakanin mutumin Yahuda da mutumin Al’ummai, Ubangijin nan ɗaya shi ne Ubangijin kowa yana kuma ba da albarka a yalwace ga duk masu kira gare shi,13. gama, “Duk wanda ya kira bisa sunan Ubangiji zai sami ceto.”14. To, ta yaya za su kira ga wanda ba su gaskata ba? Ta yaya kuma za su gaskata wanda ba su taɓa ji ba? Ta yaya kuma za su ji ba tare da wani ya yi musu wa’azi ba?15. Kuma ta yaya za su yi wa’azi in ba an aike su ba? Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Isowar masu kawo labari mai daɗi abu mai kyau ne ƙwarai!”16. Amma ba dukan Isra’ilawa ne suka karɓi labari mai daɗin nan ba. Gama Ishaya ya ce, “Ubangiji, wa ya gaskata saƙonmu?”17. Saboda haka, bangaskiya takan zo ne ta wurin jin saƙo, akan ji saƙon kuma ta wurin maganar Kiristi.18. Amma ina tambaya, “Ba su ji ba ne? Tabbatacce sun ji. “Muryarsu ta tafi ko’ina a cikin duniya, kalmominsu kuma har iyakar duniya.”19. Har wa yau, ina da tambaya. Shin, Isra’ila ba su fahimta ba ne? Da farko, Musa ya ce, “Zan sa ku yi kishin waɗanda ba al’umma ba; zan sa ku yi fushin al’ummar da ba ta da fahimta.”20. Ishaya kuma ya fito gabagadi ya ce, “Waɗanda ba su neme ni ba, su suka same ni; Na bayyana kaina ga waɗanda ba su ma taɓa neman sanina ba.”21. Amma game da Isra’ila ya ce, “Dukan yini na miƙa hannuwana ga mutane marasa biyayya da masu taurinkai.” Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.