Baibul a cikin shekara guda Agusta 6Ayuba 3:1-261. Bayan wannan Ayuba ya buɗe baki ya la’anta ranar da aka haife shi.2. Ayuba ya ce,3. “A hallaka ranar da aka haife ni, da kuma daren da aka ce, ‘An haifi jariri namiji!’4. Bari ranan nan ta zama duhu; kada Allah yă kula da ita; kada rana tă yi haske a wannan rana.5. Bari duhu da inuwa mai duhu ta sāke rufe ta; gizagizai kuma su rufe ta; duhu kuma ya rufe haskenta.6. Bari duhu mai yawa yă rufe daren nan; kada a haɗa ta cikin kwanakin shekara, ko kuma cikin kwanakin watanni.7. Bari daren yă zama marar amfani; kada a ji wata sowa ta farin ciki.8. Bari waɗanda suke la’anta ranaku su la’anta wannan rana su waɗanda suke umartar dodon ruwa.9. Bari taurarinta na safe su zama duhu; bari ranar tă yi ta jiran ganin haske amma kada tă gani,10. gama ba tă hana uwata ɗaukar cikina, don ta hana ni shan wahalan nan ba.11. “Me ya sa ban mutu ba da za a haife ni, ko kuma in mutu sa’ad da ana haihuwata ba?12. Me ya sa aka haife ni, aka tanada nono na sha na rayu?13. Da yanzu ina kwance cikin salama; da ina barcina cikin salama14. tare da sarakuna da mashawarta a cikin ƙasa, waɗanda suka gina wa kansu wuraren da yanzu duk sun rushe,15. da shugabanni waɗanda suke da zinariya, waɗanda suka cika gidajensu da azurfa.16. Ko kuma don me ba a ɓoye ni a cikin ƙasa kamar jaririn da aka haifa ba rai ba, kamar jaririn da bai taɓa ganin hasken rana ba.17. A wurin mugaye za su daina yin mugunta, gajiyayyu kuma za su huta.18. Waɗanda aka daure za su sami jin daɗin; an sake su ba za su sāke jin ana tsawata masu ba.19. Manyan da ƙanana suna a can, bawa kuma ya sami ’yanci daga wurin maigidansa.20. “Don me ake ba da haske ga waɗanda suke cikin ƙunci, rai kuma ga masu ɗacin rai21. ga waɗanda suke neman mutuwa amma ba su samu ba, waɗanda suke nemanta kamar wani abu mai daraja a ɓoye,22. waɗanda suke farin ciki sa’ad da suka kai kabari?23. Don me aka ba mutum rai, mutumin da bai san wani abu game da kansa ba, mutumin da Allah ya kange shi.24. Baƙin ciki ya ishe ni maimakon abinci; ina ta yin nishi ba fasawa;25. Abin da nake tsoro ya faru da ni; abin da ba na so ya same ni.26. Ba ni da salama, ba natsuwa; ba ni da hutu, sai wahala kawai.”Ayuba 4:1-211. Sai Elifaz mutumin Teman ya amsa,2. “In wani ya yi maka magana, za ka ji haushi? Amma wa zai iya yin shiru?3. Ka tuna yadda ka yi wa mutane da yawa magana, yadda ka ƙarfafa hannuwa marasa ƙarfi.4. Maganarka ta ƙarfafa waɗanda suka yi tuntuɓe; ka ƙarfafa gwiwoyin da suka rasa ƙarfinsu.5. Amma yanzu wahala ta zo maka, sai ka karaya; wahala ta sa ka rikice.6. Ashe bai kamata ka dogara ga Allahnka ba, amincinka kuma yă zama begenka?7. “Ka duba ka gani yanzu. Wane marar laifi ne ya taɓa hallaka? Ko an taɓa hallaka masu adalci?8. Na kula cewa waɗanda suke huɗa gonar mugunta, da waɗanda suke shuka mugunta, su ne suke girbe mugunta.9. A sa’a ɗaya Allah yake hallaka su, cikin fushinsa yakan hallaka su.10. Zakoki suna ruri suna gurnani; duk da haka an karya haƙoran manyan zakoki.11. Zakoki suna mutuwa domin ba dabbar da za su kashe su ci, ’ya’yan zakanya kuma sun watse.12. “Asirce aka gaya mini maganan nan, da ƙyar kunnuwana suka iya ji.13. Cikin mafarki da tsakar dare, lokacin kowa yana zurfin barci, na sami saƙon nan.14. Tsoro da fargaba suka kama ni har duk ƙasusuwan jikina suka yi ta rawa.15. Wani iska ya taɓa mini fuska, sai tsigar jikina ta tashi.16. Ya tsaya cik, amma ban iya sani ko mene ne ba. Wani abu ya tsaya a gabana, na kuma ji murya.17. ‘Ko zai yiwu mutum yă fi Allah adalci, ko kuma mutum yă fi wanda ya halicce shi tsarki?18. In Allah bai yarda da bayinsa ba, in ya sami mala’ikunsa da laifi,19. to, su wane ne mutane masu zama a gidan da aka yi da laka, waɗanda da ƙura aka yi harsashensu, waɗanda za a iya murƙushe su kamar asu!20. Tsakanin safe da yamma mai yiwuwa ne ragargaza su; farat ɗaya, su mutu har abada.21. Ba a tuge igiyar tentinsu, don su mutu ba tare da hikima ba?’Zabura 91:14-1614. Ubangiji ya ce, “Domin ya ƙaunace ni, zan kuɓutar da shi; zan kiyaye shi, gama ya yarda da sunana.15. Zai kira bisa sunana, zan kuma amsa masa; zan kasance tare da shi a lokacin wahala, zan kuɓutar da shi in kuma girmama shi.16. Da tsawon rai zan ƙosar da shi in kuma nuna masa cetona.”Karin Magana 22:15-1515. Wauta tana da yawa a zuciyar yara, amma sandar horo zai kore ta nesa da su.Romawa 8:1-211. Saboda haka, yanzu babu hukunci don waɗanda suke cikin Kiristi Yesu,2. gama ta wurin Kiristi Yesu dokar Ruhu mai ba da rai ta ’yantar da ni daga Dokar Musa.3. Gama abin da dokar ba tă iya yi saboda kāsawar mutuntaka ba, Allah ya yi shi sa’ad da ya aiko da Ɗansa a kamannin mutum mai zunubi, don yă zama hadaya ta zunubi. Ta haka, ya hukunta zunubi a cikin mutum mai zunubi.4. Ya yi haka domin yă cika bukatun adalcin doka a cikinmu, mu da ba ma rayuwa bisa ga mutuntaka, sai dai bisa ga Ruhu.5. Waɗanda suke rayuwa bisa ga mutuntaka sun kafa hankulansu a kan sha’awace-shawa’acen jiki; amma waɗanda suke rayuwa bisa ga Ruhu sun kafa hankulansu a kan abubuwan da Ruhu yake so.6. Ƙwallafa rai ga al’amuran halin mutuntaka ƙarshensa mutuwa ne, ƙwallafa rai ga al’amuran Ruhu kuwa rai ne da salama;7. hankalin mai zunubi na gāba da Allah. Ba ya biyayya da dokar Allah, ba kuwa zai iya yin haka ba.8. Waɗanda mutuntaka yake mulkinsu ba za su iya su gamshi Allah ba.9. Ku kam, ana mulkinku ba ta wurin mutuntaka ba, sai dai ta wurin Ruhu, in Ruhun Allah yana zaune a cikinku. In kuma wani ba shi da Ruhun Kiristi, shi ba na Kiristi ba ne.10. Amma in Kiristi yana a cikinku, jikinku matacce ne saboda zunubi, duk da haka ruhunku yana a raye saboda adalci.11. In kuwa Ruhu wannan da ya tā da Yesu daga matattu yana zama a cikinku, shi wanda ya tā da Kiristi daga matattu zai ba da rai ga jikunanku masu mutuwa ta wurin Ruhunsa, wanda yake zama a cikinku.12. Saboda haka ’yan’uwa, muna da hakki, amma ba na wanda za mu yi rayuwar mutuntaka da yake so ba.13. Gama in kuna rayuwa bisa ga mutuntaka, za ku mutu; amma in ta wurin Ruhu kuka kashe ayyukan jikin nan, za ku rayu.14. Domin waɗanda Ruhun Allah yake bi da su ne ’ya’yan Allah.15. Gama ba ku karɓi ruhun da ya mai da ku bayi da za ku sāke jin tsoro ba ne, sai dai kun karɓi Ruhun zaman ɗa. Ta wurinsa kuwa muke kira, “ Abba, Uba.”16. Ruhu kansa yana ba da shaida tare da ruhunmu cewa mu ’ya’yan Allah ne.17. In kuwa mu ’ya’ya ne, to, mu magāda ne, magādan Allah da kuma abokan gādo tare da Kiristi, in kuwa muna tarayya a cikin shan wuyarsa to, za mu yi tarayya a cikin ɗaukakarsa.18. A ganina, wuyar da muke sha a wannan lokaci ba su isa a kwatanta da ɗaukakar da za a bayyana a cikinmu ba.19. Halitta tana jira da marmari ta ƙosa ta ga bayyanuwar ’ya’yan Allah.20. Gama an sa halitta a cikin wulaƙanci, ba da son ta ba, sai dai ta wurin nufin wannan da ya mai da ita haka, da bege21. cewa za a ’yantar da halitta kanta daga bautarta ga ruɓewa a kuma kawo ta cikin ’yancin ɗaukakar ’ya’yan Allah. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.