Baibul a cikin shekara guda Agusta 7Ayuba 5:1-271. “Ka yi kira in kana so, amma wa zai amsa maka? Wurin waɗanne tsarkaka za ka juya?2. Fushi yana kashe wawa, ƙyashi kuma yana kashe marar azanci.3. Ni ma na ga wawa yana cin gaba, amma nan da nan gidansa ya zama la’ananne.4. ’Ya’yansa suna cikin hatsari, ba wanda zai tsaya musu a gaban alƙali,5. mayunwata sun kwashe girbinsa, har abubuwan da suke cikin ƙaya, masu jin ƙishirwa kuma suna zuba ido ga dukiyarsa.6. Gama ba daga cikin ƙasa wahala take fitowa ba, ko kuma bala’i daga ƙasa.7. Duk da haka an haifi mutum don wahala ne, kamar yadda ba shakka tartsatsin wuta yake tashi.8. “Amma da a ce ni ne, da zan roƙi Allah; zan gaya masa damuwata.9. Yana yin abubuwan al’ajabi waɗanda ba a ganewa, mu’ujizai waɗanda ba a ƙirgawa.10. Yana zuba ruwan sama a ƙasa; yana zuba ruwa a gonaki.11. Yana ɗaukaka masu sauƙinkai, yana kāre waɗanda suke makoki.12. Yana dagula shirye-shiryen masu wayo don kada su yi nasara cikin abubuwan da suke shirin yi.13. Yana kama masu wayo cikin wayonsu, yana kawar da shirye-shiryensu ba za su yi nasara ba.14. Da rana sukan yi karo da duhu; da rana ma suna lallube kamar a duhun dare suke.15. Yana ceton matalauta daga takobin da za tă kashe su da shi; yana cetonsu daga hannun waɗanda suka fi su ƙarfi.16. Saboda haka matalauta suna da bege, rashin gaskiya kuma ta yi shiru.17. “Mai albarka ne wanda Allah yake yi masa gyara in mutumin ya yi kuskure; saboda haka kada ka guje wa horon Maɗaukaki.18. Ko da yake yana sa ciwo, shi ne kuma yake warkar da ciwon; ciwon da ya ji maka, shi da kansa zai warkar da shi.19. Zai cece ka daga bala’o’i guda shida; har bakwai ma ba abin da zai same ka.20. Lokacin yunwa yana tsare ka daga mutuwa, a cikin yaƙi kuma yana kāre ka daga sarar takobi.21. Zai kāre ka daga ɓata suna, kuma ba ka bukata ka ji tsoro in hallaka ta zo.22. Za ka yi wa hallaka da yunwa dariya; kuma ba ka bukata ka ji tsoron manyan namun jeji.23. Gama za ka zauna lafiya da duwatsu a gonaki, kuma manyan namun jeji za su yi zaman salama da kai.24. Za ka zauna lafiya a cikin tenti naka, za ka ƙirga kayanka za ka samu kome na nan.25. Za ka san cewa ’ya’yanka za su zama da yawa, zuriyarka kuma kamar ciyawa a ƙasa.26. Za ka yi kyakkyawan tsufa kafin ka mutu, kamar yadda ake tara dammuna a lokacin girbi.27. “Mun yi nazarin wannan, kuma gaskiya ne. Saboda haka ka ji, ka kuma yi amfani da shi.”Ayuba 6:1-301. Sa’an nan Ayuba ya amsa,2. “Da kawai za a iya auna wahalata a kuma sa ɓacin raina a ma’auni!3. Ba shakka da sun fi yashin teku nauyi, shi ya sa nake magana haka.4. Kibiyoyin Maɗaukaki suna a kaina, ruhuna yana shan dafinsa; fushin Allah ya sauka a kaina.5. Jaki yakan yi kuka sa’ad da ya sami ciyawar ci, ko saniya takan yi kuka in ta sami abincinta?6. Akan cin abinci marar ɗanɗano ba tare da an sa gishiri ba, ko akwai wani ƙanshin daɗi a cikin farin ruwan ƙwai?7. Na ƙi in taɓa shi; irin wannan abinci zai sa ni rashin lafiya.8. “Kash, da ma Allah zai ba ni abin da nake fatar samu, da ma Allah zai biya mini bukatata,9. wato, Allah yă kashe ni, yă miƙa hannunsa yă yanke raina!10. Da sai in ji daɗi duk zafin da nake sha ban hana maganar Mai Tsarkin nan cika ba.11. “Wane ƙarfi nake da shi, har da zan ci gaba da sa zuciya? Wane sa zuciya ne zai sa in yi haƙuri?12. Da ƙarfin dutse aka yi ni ne? Ko jikina tagulla ne?13. Ina da wani ikon da zan iya taimakon kai na ne, yanzu da aka kore nasara daga gare ni?14. “Duk wanda ya ƙi yă yi alheri ga aboki ya rabu ta tsoron Maɗaukaki.15. Amma ’yan’uwana sun nuna ba zan iya dogara gare su ba, kamar rafin da yakan bushe da rani,16. kamar rafin da yakan cika a lokacin ƙanƙara, yă kuma kumbura kamar ƙanƙarar da ta narke,17. amma da rani sai yă bushe, lokacin zafi ba a samun ruwa yana gudu a wurin.18. Ayari sukan bar hanyarsu; sukan yi ta neman wurin da za su sami ruwa, su kāsa samu har su mutu.19. Ayarin Tema sun nemi ruwa, matafiya ’yan kasuwa Sheba sun nema cike da begen samu.20. Ransu ya ɓace, domin sun sa zuciya sosai; sa’ad da suka kai wurin kuwa ba su sami abin da suka sa zuciyar samu ba.21. Yanzu kuma kun nuna mini ba ku iya taimako; kun ga abin bantsoro kuka tsorata.22. Ko na taɓa cewa, ‘Ku ba da wani abu a madadina, ko na roƙe ku, ku ba da wani abu domina daga cikin dukiyarku,23. ko kuma kun taɓa kuɓutar da ni daga hannun maƙiyina, ko kun taɓa ƙwato ni daga hannun marasa kirki’?24. “Ku koya mini, zan yi shiru; ku nuna mini inda ban yi daidai ba.25. Faɗar gaskiya tana da zafi! Amma ina amfanin gardamar da kuke yi?26. Ko kuna so ku gyara abin da na faɗi ne, ku mai da magana wanda yake cikin wahala ta zama ta wofi?27. Kukan yi ƙuri’a a kan marayu ku kuma sayar da abokinku.28. “Amma yanzu ku dube ni da kyau, zan yi muku ƙarya ne?29. Ku bi a hankali, kada ku ɗora mini laifi; ku sāke dubawa, gama ba ni da laifi.30. Ko akwai wata mugunta a bakina? Bakina ba zai iya rarrabewa tsakanin gaskiya da ƙarya ba?Zabura 92:1-71. Yana da kyau a yabi Ubangiji a kuma yi kiɗi ga sunanka, ya Mafi Ɗaukaka,2. don a yi shelar ƙaunarka da safe amincinka kuma da dare,3. da kiɗin molo mai tsirkiya goma da kuma ƙarar garaya.4. Gama ka sa na yi murna ta wurin ayyukanka, ya Ubangiji; na rera don farin ciki saboda ayyukan hannuwanka.5. Ina misalin ayyukanka, ya Ubangiji, tunaninka da zurfi suke ƙwarai!6. Mutum marar azanci ba zai sani ba, wawa ba zai gane ba,7. cewa ko da yake mugaye suna girma kamar ciyawa kuma dukan masu aikata mugunta suna haɓaka, za a hallaka su har abada.Karin Magana 22:16-1616. Duk wanda yake danne matalauta don yă azurta kuma duk wanda yake kyauta ga mawadata, dukansu kan talauta.Romawa 8:22-3922. Mun san cewa dukan halitta tana nishi sai ka ce mace mai naƙuda har yă zuwa wannan lokaci.23. Ba haka kaɗai ba ma, mu kanmu da muke da nunan fari na Ruhu, muna nishi a ciki-cikinmu yayinda muke jira da marmari a maishe mu ’ya’yan riƙo na Allah, fansar jikunanmu.24. Gama a wannan begen ne muka sami ceto. Amma begen da ake gani ba bege ba ne sam. Wa yake begen abin da ya riga ya samu?25. Amma in muna begen abin da ba mu riga mun samu tukuna ba, mukan jira da haƙuri.26. Haka nan ma, Ruhu yana taimakonmu cikin rashin ƙarfinmu. Ba mu san abin da ya kamata mu roƙa cikin addu’a ba, amma Ruhu kansa yana roƙo a madadinmu da nishe-nishen da kalmomi ba sa iya bayyanawa.27. Shi kuma wanda yake binciken zukatanmu ya san halin Ruhu, domin Ruhu yana roƙo a madadin tsarkaka bisa ga nufin Allah.28. Mun kuma san cewa a cikin dukan abubuwa Allah yana aikata alheri ga waɗanda suke ƙaunarsa, yana waɗanda aka kira bisa ga nufinsa.29. Gama waɗanda Allah ya rigyasani ya kuma ƙaddara su dace da kamannin Ɗansa, don yă zama ɗan fari cikin ’yan’uwa masu yawa.30. Waɗanda kuwa ya ƙaddara, su ne ya kira; waɗanda ya kira kuwa, su ne ya kuɓutar; waɗanda ya kuɓutar kuwa, su ne ya ɗaukaka.31. Me za mu ce ke nan game da wannan abu? In Allah yana goyon bayanmu, wa kuwa zai iya gāba da mu?32. Shi da bai hana Ɗansa ba, sai ma ya ba da shi saboda mu duka, ashe, ba zai kuma ba mu, tare da shi, dukan abubuwa cikin alherinsa ba?33. Wa zai kawo wani zargi a kan waɗanda Allah ya zaɓa? Allah ne mai kuɓutarwa.34. Wa zai yi hukunci? Yesu Kiristi ne, wanda ya mutu, fiye da haka ma, shi da aka tā da zuwa rai, yana zaune a hannun dama na Allah yana kuma yin roƙo a madadinmu.35. Wane ne zai raba mu da ƙaunar Kiristi? Masifa ce ko wahala ko tsanani ko yunwa ko tsiraici ko hatsari ko takobi?36. Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Saboda kai ne muke fuskantar mutuwa dukan yini; an ɗauke mu kamar tumakin da za a yanka.”37. A’a, cikin dukan waɗannan abubuwa mun ma fi masu nasara ta wurin shi wanda ya ƙaunace mu.38. Gama na tabbata cewa ko mutuwa ko rai, ko mala’iku ko aljanu, ko abubuwa na yanzu ko abubuwa masu zuwa nan gaba, ko ikoki,39. ko tsayi ko zurfi, ko wani abu dabam cikin dukan halitta da zai iya raba mu da ƙaunar Allah wadda take cikin Kiristi Yesu Ubangijinmu. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.