Baibul a cikin shekara guda Agusta 8Ayuba 7:1-211. “Mutum bai sha wahalar aiki ba a duniya? Rayuwarsa ba kamar ta wanda aka yi hayarsa ba ne?2. Kamar yadda bawa yakan jira yamma ta yi, ko kuma kamar yadda wanda aka yi hayarsa yakan jira a biya shi kuɗin aikin da ya yi.3. Saboda haka rabona shi ne watanni na zama banza, kowane dare kuwa sai ɓacin rai nake samu.4. Lokacin da na kwanta ina tunani, ‘Har sai yaushe zan tashi?’ Gari ya ƙi wayewa, ina ta jujjuyawa har safe.5. Jikina duk tsutsotsi da ƙuraje sun rufe shi, fatar jikina ta ruɓe tana fitar da ruwan miki.6. “Kwanakina suna wucewa da sauri, fiye da yadda ƙoshiyar masaƙa take wucewa da sauri, za su kawo ga ƙarshe ba bege.7. Ka tuna, ya Allah, raina numfashi ne kawai; idanuna ba za su taɓa sāke ganin farin ciki ba.8. Idanun da suke ganina yanzu ba za su sāke ganina ba; za ku neme ni amma ba za ku same ni ba.9. Kamar yadda girgije yakan ɓace yă tafi, haka mutum yake shige zuwa kabari ba kuwa zai dawo ba.10. Ba zai taɓa zuwa gidansa ba; ba za a sāke san da shi ba.11. “Saboda haka ba zan yi shiru ba; zan yi magana cikin ɓacin raina, zan nuna ɓacin raina cikin ruhu, cikin ƙuncin raina.12. Ni teku ne, ko kuwa dodon ruwa, don me kake tsaro na?13. Lokacin da nake zato zan sami salama in na kwanta a gadona don in huta,14. duk da haka kana ba ni tsoro da mafarke-mafarke, kana tsorata ni da wahayi.15. Na gwammace a shaƙe ni in mutu maimakon in kasance cikin wannan jiki.16. Ba na so in zauna da rai; ba zan rayu ba har abada. Ku rabu da ni; rayuwata ba ta da amfani.17. “Mene ne mutum har da ka kula da shi haka, har ka mai da hankali a kansa,18. har kake duba shi kowace safiya, kake kuma gwada shi koyaushe?19. Ba za ka ɗan daina kallo na ba ko ka rabu da ni na ɗan lokaci?20. In na yi zunubi, me na yi maka, kai mai lura da mutane? Don me ka sa ni a gaba? Na zame maka kaya mai nauyi ne?21. Me ya sa ba za ka gafarta mini laifofina ba? Gama na kusa kwantawa cikin ƙasa; za ka neme ni, amma ba za ka same ni ba.”Ayuba 8:1-221. Sai Bildad mutumin Shuwa ya amsa,2. “Har yaushe za ka gama faɗa waɗannan abubuwa? Maganganunka ba su da amfani.3. Allah ba mai shari’ar gaskiya ba ne? Ko Maɗaukaki yakan yi abin da ba daidai ba?4. Lokacin da ’ya’yansa suka yi masa zunubi, yakan bar su su sha wahalar da zunubi yake kawowa.5. Amma in za ka dubi Allah ka roƙi Maɗaukaki,6. in kai mai tsarki ne, kuma mai adalci, ko yanzu ma zai taimake ka, yă mayar maka iyalinka da farin cikinka.7. Ko da yake za ka fara da kaɗan, duk da haka za ka gama da samu mai yawa.8. “Tambayi na gaba da kai ka ji abin da iyayenka suka koya9. gama jiya kaɗai aka haife mu ba mu san kome ba, kuma kwanakinmu a duniya masu wucewa ne.10. Ba za su bishe ka su kuma gaya maka abin da za ka yi ba? Ba za su yi magana daga cikin hikimar da suke da ita ba?11. Ko kyauro zai iya yi girma a wurin da ba ruwa? Ko za tă taɓa iya yin girma ba tare da ruwa ba?12. Yayinda take girma ba a yanka ta, takan mutu da sauri fiye da ciyawa.13. Abin da yake faruwa ke nan da duk wanda yake mantawa da Allah; waɗanda ba su da Allah, ba su da bege.14. Abin da yake dogara a kai ba shi da ƙarfi; abin da yake dogara a kai yanar gizo ce.15. Ya jingina ga yanar gizo, amma ba ta tare shi, sun kama ta, amma ba za tă taimake su tsayawa ba.16. Yana kama da shukar da aka ba ta ruwa sosai lokacin da akwai rana sosai, tana yaɗuwa da kyau;17. shukar tana bin yaɗuwa, jijiyoyinta suna nannaɗe duwatsu, suna neman wurin da za su kama sosai a cikin duwatsu.18. Amma lokacin da aka tuge shukar daga wurin da take, wurin ba zai san da ita kuma ba, wurin zai ce, ‘Ban taɓa ganin ki ba.’19. Ba shakka shukar ta mutu ke nan, kuma waɗansu za su tsiro a wurin.20. “Ba shakka, Allah ba ya ƙin marar laifi, ko kuma yă ƙarfafa masu aikata mugunta.21. Sai dai yă cika bakinka da dariya, yă sa ka yi sowa ta murna.22. Maƙiyanka za su sha kunya, za a kawar da tentin mugaye.”Zabura 92:8-158. Amma kai, ya Ubangiji, za a ɗaukaka har abada.9. Gama tabbatacce abokan gābanka, ya Ubangiji, tabbatacce abokan gābanka za su hallaka; za a watsar da dukan masu aikata mugunta.10. Ka ɗaukaka ƙahona kamar na ɓauna; an zubo mai masu kyau a kaina.11. Idanuna sun ga fāɗuwar maƙiyana; kunnuwana sun ji kukan mugayen maƙiyana.12. Adalai za su haɓaka kamar itacen dabino, za su yi girma kama al’ul na Lebanon;13. da aka daddasa a gidan Ubangiji, za su haɓaka a filayen gidan Allahnmu.14. Za su ci gaba da ba da ’ya’ya a tsufansu, za su kasance ɗanye kuma kore shar,15. suna shela cewa, “ Ubangiji adali ne; shi ne Dutsena, kuma babu mugunta a cikinsa.”Karin Magana 22:17-2117. Ka kasa kunne ka kuma saurara ga maganganu masu hikima; ka yi amfani da abin da nake koyarwa,18. gama yana da daɗi sa’ad da ka kiyaye su a zuciyarka ka kuma kasance da su a shirye a leɓunanka.19. Domin dogarawarka ta kasance ga Ubangiji, ina koya maka yau, har kai ma.20. Ban rubuta maka maganganu talatin ba, maganganun shawara da sani,21. ina koya maka gaskiya da kalmomin da za ka dogara a kai, saboda ka iya ba da amsa daidai ga duk wanda ya aike ka?Romawa 9:1-151. Ina faɗin gaskiya a cikin Kiristi ba ƙarya nake yi ba, lamirina ya tabbatar da wannan a cikin Ruhu Mai Tsarki.2. Ina da baƙin ciki mai yawa da kuma rashin kwanciyar rai marar ƙarewa a zuciyata.3. Gama da so na ne, sai a la’anta ni a kuma raba ni da Kiristi saboda ’yan’uwana, waɗannan na kabilata,4. mutanen Isra’ila. Su ne Allah ya mai da su ’ya’yansa, ya bayyana musu ɗaukakarsa, ya ba su alkawarinsa da Dokarsa, ya nuna musu hanyar sujada ta gaske, ya kuma ba su sauran alkawura.5. Kakannin-kakannin nan kuma nasu ne, Kiristi kuma, ta wurin zamansa mutum, na kabilarsu ne. Yabo ya tabbata ga Allah har abada, shi da yake bisa kome! Amin.6. Ba cewa maganar Allah ta kāsa ba ne. Gama ba duk waɗanda suke zuriyar Isra’ila ne suke Isra’ila na gaske ba.7. Ba kuwa don su zuriyarsa ne dukansu suka zama ’ya’yan Ibrahim ba. A maimako, “Ta wurin Ishaku ne za a lissafta zuriyarka.”8. Ana iya cewa zaman zuriyar Ibrahim, ba shi ne zama ’ya’yan Allah ba, a’a, zuriya ta alkawarin nan su ne ake lasaftawa zuriyar Ibrahim.9. Ga yadda aka yi alkawarin nan, “A ƙayyadadden lokaci zan dawo, Saratu kuma za tă haifi ɗa.”10. Ba ma haka kaɗai ba, ’ya’yan Rifkatu suna da mahaifi guda ne, wato, mahaifinmu Ishaku.11. Duk da haka, tun ba a haifi tagwayen nan ba, balle su yi wani abu mai kyau ko marar kyau don nufin Allah bisa ga zaɓensa ya tabbata, ba ga aikin lada ba, sai dai ga kiransa,12. ba ta wurin ayyuka ba sai dai ta wurin shi wanda ya kira, aka faɗa mata cewa, “Babban zai bauta wa ƙaramin.”13. Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Yaƙub ne na so, amma Isuwa ne na ƙi.”14. Me za mu ce ke nan? Allah marar adalci ne? Sam, ko kaɗan!15. Gama ya ce wa Musa, “Zan nuna jinƙai ga wanda zan nuna jinƙai, zan kuma ji tausayin wanda zan ji tausayi.” Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.