Baibul a cikin shekara guda Satumba 10Ishaya 11:1-161. Toho zai fito daga kututturen Yesse; daga saiwarsa Reshe zai ba da ’ya’ya.2. Ruhun Ubangiji zai kasance a kansa, Ruhun hikima da na fahimta, Ruhun shawara da na iko, Ruhun sani da na tsoron Ubangiji,3. zai kuwa ji daɗin tsoron Ubangiji. Ba zai yi hukunci ta wurin abin da ya gani da idanunsa ba, ba zai kuwa yanke shawara ta wurin abin da ya ji da kunnuwansa ba;4. amma da adalci zai yi wa masu bukata shari’a, da gaskiya zai yanke shawarwari saboda matalautan duniya. Kamar sanda zai bugi duniya da maganar bakinsa; da numfashin leɓunansa zai yanke mugaye.5. Adalci ne zai zama abin ɗamararsa aminci kuma igiyar da zai ɗaura kewaye da gindinsa.6. Kyarkeci zai zauna tare da ɗan rago damisa za tă kwanta tare da akuya, ɗan maraƙi da zaki da ɗan saniya za su yi kiwo tare; ɗan yaro ne zai lura da su.7. Saniya da beyar za su yi kiwo tare, ƙananansu za su kwanta tare, zaki kuma zai ci ciyawa kamar saniya.8. Jariri zai yi wasa kurkusa da ramin gamsheƙa, ɗan yaro kuma zai sa hannunsa a ramin maciji mai mugun dafi.9. Ba za su yi lahani ko su hallaka wani a dutsena mai tsarki ba, gama duniya za tă cika da sanin Ubangiji kamar yadda ruwaye suka rufe teku.10. A wannan rana Saiwar Yesse zai miƙe kamar tuta don mutanenta; al’ummai za su tattaru wurinsa, wurin hutunsa kuma zai zama mai daraja.11. A wannan rana Ubangiji zai miƙa hannunsa sau na biyu don yă maido da raguwar da ta rage na mutanensa daga Assuriya, daga Masar ta Ƙasa, daga Masar ta Bisa, daga Kush, daga Elam, daga Babiloniya, daga Hamat da kuma daga tsibiran teku.12. Zai tā da tuta saboda al’ummai yă kuma tattara masu zaman bauta na Isra’ila; zai tattara mutanen Yahuda da suke a warwatse kusurwoyi huɗu na duniya.13. Kishin Efraim zai ɓace, za a kuma kau da abokan gāban Yahuda; Efraim ba zai yi kishin Yahuda ba, haka ma Yahuda ba zai yi gāba da Efraim ba.14. Tare za su fāɗa wa Filistiyawa da yaƙi daga yamma; tare za su washe mutane wajen gabas. Za su ɗibiya hannuwa a kan Edom da Mowab, Ammonawa kuma za su yi musu biyayya.15. Ubangiji zai busar da bakin tekun Masar; da iska mai zafi zai share hannunsa a bisa Kogin Yuferites Zai rarraba shi yă zama ƙanana rafuffuka bakwai saboda mutane su iya hayewa da ƙafa.16. Za a yi babbar hanya saboda raguwa mutanensa da ta rage daga Assuriya, kamar yadda ta kasance wa Isra’ila sa’ad da suka fito daga Masar.Ishaya 12:1-61. A wannan rana za ku ce, “Zan yabe ka, ya Ubangiji. Ko da yake a dā ka yi fushi da ni, amma yanzu ka daina fushi da ni ka kuwa ta’azantar da ni.2. Tabbatacce Allah shi ne mai cetona; zan dogara gare shi ba kuwa zan ji tsoro ba. Ubangiji, Ubangiji, ne ƙarfina da waƙata; ya zama mai cetona.”3. Da farin ciki zan ɗebo ruwa daga rijiyoyin ceto.4. A wannan rana za ku ce, “Yi godiya ga Ubangiji, ku kira bisa sunansa; a sanar da wannan abin da ya aikata a cikin al’ummai, a kuma yi shela cewa sunansa mai girma ne.5. Ku rera ga Ubangiji, gama ya aikata manyan abubuwa; bari a sanar da wannan ga dukan duniya.6. Ku tā da murya ku kuma rera don farin ciki, ya ku mutanen Sihiyona, gama Mai Tsarki na Isra’ila da girma yake a cikinku.”Zabura 106:6-186. Mun yi zunubi, kamar yadda kakanninmu suka yi; mun yi ba daidai ba muka kuma aikata mugunta.7. Sa’ad da kakanninmu suke a Masar, ba su damu da mu’ujizanka ba; ba su tuna yawan alheranka ba, suka kuma yi tayarwa a teku, Jan Teku.8. Duk da haka ya cece su saboda sunansa, don yă sanar da ikonsa mai girma.9. Ya tsawata wa Jan Teku, ya kuwa bushe; ya bi da su ta cikin zurfafa sai ka ce a hamada.10. Ya cece su daga hannun maƙiyi; daga hannun abokin gāba ya fanshe su.11. Ruwaye suka rufe abokan gābansu; babu ko ɗaya da ya tsira.12. Sa’an nan suka gaskata alkawarinsa suka kuma rera yabonsa.13. Amma nan da nan suka manta abin da ya yi ba su kuwa jira shawararsa ba.14. A cikin hamada suka bar sha’awarsu ta mamaye su a ƙasar da babu kome suka gwada Allah.15. Sai ya ba su abin da suka roƙa, amma ya aika musu da muguwar cuta.16. A sansani suka ji kishin Musa da kuma Haruna, wanda Ubangiji ya keɓe.17. Ƙasa ta buɗe ta haɗiye Datan ta binne iyalin Abiram.18. Wuta ta ƙuno a cikin mabiyansu; harshen wuta ya cinye mugaye.Karin Magana 25:3-53. Kamar yadda sammai suna can bisa duniya kuma tana da zurfi, haka zukatan sarakuna suka wuce a bincika.4. Ka tace azurfa sai kayan su fito don maƙerin azurfa;5. ka cire mugaye daga gaban sarki, kursiyinsa kuwa zai kahu ta wurin adalci.2 Korintiyawa 2:1-171. Saboda haka na yanke shawara ba zan sāke kawo muku ziyara ta ɓacin rai ba.2. Gama in na sa ku baƙin ciki, wa ya rage yă faranta mini zuciya, in ba ku waɗanda na sa baƙin cikin ba?3. Na rubuta yadda na yi ne saboda sa’ad da na iso kada waɗanda ya kamata su faranta mini rai, su sa ni baƙin ciki. Na amince da ku duka a kan farin cikina naku ne ku duka.4. Gama na rubuta muku ne cikin baƙin ciki mai yawa da ɓacin zuciya har ma da hawaye mai yawa, ba don in sa ku baƙin ciki ba ne, a’a, sai dai domin in nuna muku zurfin ƙaunar da nake yi muku.5. In wani ya jawo baƙin ciki, ba ni kaɗai ya jawo wa ba, amma a wani fanni, sai in ce dukanku ne ya jawo wa, ba na faɗa haka don in matsa muku lamba ba ne.6. Irin wannan mutum, horon da yawancin mutane suka yi masa ya isa haka.7. Yanzu fa, a maimako, gara ku yafe masa, ku kuma ta’azantar da shi, don kada baƙin ciki mai yawa yă sha kansa.8. Saboda haka, ina roƙonku, ku sāke nuna masa ƙaunarku.9. Abin da ya sa na rubuta muku shi ne don in ga ko za ku jimre da gwajin nan, kuna kuma yin biyayya ta kowace hanya.10. In kuka gafarta wa wani, ni ma na gafarta masa. Abin da na gafarta kuwa, in har ma da abin gafartawa, saboda ku ne na gafarta masa, albarkacin Kiristi,11. don kada Shaiɗan yă rinjaye mu. Da yake muna sane da dabarunsa.12. To, sa’ad da na tafi Toruwas don in yi wa’azin bisharar Kiristi, ko da yake na tarar cewa Ubangiji ya buɗe mini ƙofa,13. duk da haka, ban sami salama a zuciyata ba domin ban sami ɗan’uwana Titus a can ba. Sai na yi bankwana da su na wuce zuwa Makidoniya.14. Amma godiya ga Allah, wanda kullum yake bi da mu da nasara cikin Kiristi, kuma ta wurinmu, yana baza ƙanshin nan na sanin Kiristi a ko’ina.15. Don kuwa, a wurin Allah mu ƙanshin Kiristi ne cikin waɗanda ake ceto, da kuma waɗanda suke hanyar hallaka.16. Ga wani, mu warin mutuwa ne, amma ga wani kuwa, mu ƙanshin rai ne. Wa ya isa yă yi irin wannan aikin?17. Ba ma tallar maganar Allah don riba yadda waɗansu mutane da yawa suke yi. A maimakon haka, muna magana cikin Kiristi a gaban Allah da gaskiya, kamar mutanen da aka aika daga Allah. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.