Baibul a cikin shekara guda Satumba 16Ishaya 23:1-181. Abin da Allah ya faɗa game da Taya. Ku yi kuka mai zafi, ya jiragen ruwan Tarshish! Gama an hallaka Taya aka kuma bar su babu gida ko tasha. Daga ƙasar Saifurus magana ta zo musu.2. Ku yi shiru, ku mutanen tsibiri da ku ’yan kasuwan Sidon waɗanda masu ciniki a teku suka azurta.3. A manyan ruwaye hatsin Shihor suka iso; girbin Nilu ne kuɗin shiga na Taya ta kuma zama kasuwar al’ummai.4. Ki ji kunya, ya ke Sidon, da ke kuma, kagarar teku, gama teku ya yi magana ya ce, “Ban taɓa naƙuda ba balle in haifi ’ya’ya; ban taɓa goyon ’ya’ya maza ba balle in reno ’ya’ya mata.”5. Sa’ad da magana ta kai Masar, za su razana da jin labari daga Taya.6. Ku haye zuwa Tarshish; ku yi kuka mai zafi, ku mutanen tsibiri.7. Wannan ce birnin murnanku, birnin nan na tun dā wadda ƙafafunta suka kai ta zama a ƙasashe masu nesa?8. Wane ne ya ƙulla wannan a kan Taya ita da take ba da rawanin sarauta, wadda ’yan kasuwanta sarakuna ne, wadda masu cinikinta sanannu ne a duniya?9. Ubangiji Maɗaukaki ya ƙulla shi, don yă kawo ƙarshen girman kan dukan darajarta ya kuma ƙasƙantar da dukan waɗanda suke sanannu a duniya.10. Ki nome ƙasarki har zuwa wajen Nilu, Ya Diyar Tarshish, gama ba ki da tashan jirgin ruwa kuma.11. Ubangiji ya miƙa hannunsa a bisa teku ya kuma sa mulkokinsa suka yi rawar jiki. Ya ba da umarni game da Funisiya cewa a hallaka kagararta.12. Ya ce, “Ba za ki ƙara yin murna ba, Ya ke Budurwa Diyar Sidon, yanzu da kike ragargajiya! “Tashi, ki ƙetare zuwa Saifurus; a can ɗin ma ba za ki huta ba.”13. Dubi ƙasar Babiloniyawa, wannan mutanen da yanzu ba su da wani amfani! Assuriyawa sun mai da ita wurin zaman halittun hamada; sun gina hasumiyoyin kwanto, suka ragargaza kagararta ƙaf suka mai da ita kango.14. Ku yi kuka mai zafi, ku jiragen ruwan Tarshish; an rurrushe kagararku!15. A wannan lokaci za a manta da Taya har shekaru saba’in, tsawon rayuwar sarki. Amma a ƙarshen waɗannan shekaru saba’in, zai zama wa Taya kamar yadda yake a waƙar karuwa cewa,16. “Ɗauki garaya, ki ratsa birni, Ya ke karuwar da aka manta da ita; kaɗa garaya da kyau, ki rera waƙoƙi masu yawa, saboda a tuna da ke.”17. A ƙarshen shekaru saba’in, Ubangiji zai magance Taya. Za tă koma ga aikinta na karuwanci za tă kuma yi kasuwancinta da dukan mulkokin duniya.18. Duk da haka za a keɓe ribarta da kuɗin shigarta wa Ubangiji; ba za a yi ajiyarsu ko a ɓoye su. Ribarta za tă tafi ga waɗanda suke yi wa Ubangiji sujada, don su sami yalwataccen abinci da tufafi masu kyau.Ishaya 24:1-231. Duba, Ubangiji zai wofinta duniya ya kuma yi kaca-kaca da ita; zai ɓata fuskarta ya watsar da mazaunanta,2. zai zama abu ɗaya ga firist kamar yadda yake ga mutane, ga maigida kamar yadda yake ga bawa, ga uwargijiya kamar yadda yake ga baiwa, ga mai sayarwa kamar yadda yake ga mai saya, ga mai karɓan rance kamar yadda yake ga mai ba da rance, ga mai karɓan bashi kamar yadda yake ga mai ba da bashi.3. Za a wofinta duniya ƙaƙaf a kuma washe ta sarai. Ubangiji ne ya faɗa haka.4. Duniya ta bushe ta kuma yanƙwane, duniya tana shan azaba ta kuma raunana, masu daraja na duniya suna shan azaba.5. Duniya ta ƙazantu ta wurin mutanenta sun ƙi yin biyayya da dokoki, sun keta farillai suka kuma karya madawwamin alkawari.6. Saboda haka la’ana za tă auko wa duniya; dole mutanenta su ɗauki hakkin laifinsu. Saboda haka aka ƙone mazaunan duniya, kuma kaɗan ne kurum suka rage.7. Sabon ruwan inabi ya bushe kuringar inabi kuma sun yanƙwane; dukan masu farin ciki suna nishi.8. Kaɗe-kaɗen garayu sun yi shiru, surutun masu murna ya daina, garayan farin ciki ya yi shiru.9. Babu sauran shan ruwan inabi suna rera waƙa; barasa ya zama da ɗaci ga masu shanta.10. Birnin da aka birkice ta zama kango; an kulle ƙofar shiga kowane gida.11. A tituna suna kukan neman ruwan inabi; dukan farin ciki ya dawo baƙin ciki, an hana dukan kaɗe-kaɗe a duniya.12. An bar birnin kango, aka yi kaca-kaca da ƙofofinta.13. Haka zai zama a duniya da kuma a cikin al’ummai, kamar sa’ad da akan karkaɗe itacen zaitun, ko kuma kamar sa’ad da ake barin kala bayan an girbe inabi.14. Sun daga muryoyinsu, sun yi sowa ta farin ciki; daga yamma sun furta darajar Ubangiji.15. Saboda haka a gabas sun ɗaukaka Ubangiji, a ɗaukaka sunan Ubangiji, Allah na Isra’ila, a cikin tsibiran teku.16. Daga iyakokin duniya mun ji waƙoƙi, “Ɗaukaka ga Mai Adalcin nan.” Amma na ce, “Na lalace, na lalace! Kaitona! Munafukai sun ci amana! Da munafunci munafukai sun ci amana!”17. Razana da rami da tarko suna jiranku, Ya mutanen duniya.18. Duk wanda ya yi ƙoƙarin tserewa daga ƙarar razana zai fāɗa cikin rami; wanda kuma ya tsere daga rami za a kama shi a tarko. An buɗe ƙofofin ambaliyar ruwan sama, harsashen ginin duniya suna rawa.19. An tsage duniya, duniya ta farfashe ta wage, an girgiza duniya ƙwarai.20. Duniya tana tangaɗi kamar mashayi, tana lilo kamar rumfa a cikin iska; laifin tayarwarta ya yi nauyi sosai har ta fāɗi ba kuwa za tă ƙara tashi ba.21. A wannan rana Ubangiji zai hukunta ikokin da suke cikin sama da kuma sarakunan da suke a duniya.22. Za a tattara su tare kamar ɗaurarru a kurkuku; za a rufe su a kurkuku a kuma hukunta su bayan kwanaki masu yawa.23. Sa’an nan wata zai ruɗe, rana ta ji kunya; gama Ubangiji Maɗaukaki zai yi mulki a kan Dutsen Sihiyona da kuma a cikin Urushalima, da kuma a gaban dattawanta, da ɗaukaka.Zabura 107:10-2210. Waɗansu sun zauna a cikin duhu da kuma zurfin ɓacin rai, ’yan kurkuku suna wahala cikin sarƙoƙin ƙarfe,11. gama sun yi tayarwa a kan maganar Allah suka ƙi shawarar Mafi Ɗaukaka.12. Saboda haka ya ba da su ga aiki mai wuya; suka yi tuntuɓe, kuma ba mai taimako.13. Sa’an nan suka yi kuka ga Ubangiji cikin wahalarsu, ya kuwa cece su daga damuwarsu.14. Ya fitar da su daga duhu da zurfin ɓaci rai ya tsintsinke sarƙoƙinsu.15. Bari su yi godiya ga Ubangiji saboda ƙaunarsa marar ƙarewa da kuma ayyukansa masu banmamaki saboda mutane,16. gama ya farfashe ƙofofin tagulla ya kuma ragargaza ƙyamaren ƙarfe.17. Waɗansu suka zama wawaye ta wurin hanyoyinsu na tayarwa suka kuwa sha wahala saboda laifofinsu.18. Ba su so su ga abinci ba suka kuwa kai bakin mutuwa.19. Sa’an nan suka yi kuka ga Ubangiji cikin wahalarsu, ya kuwa cece su daga damuwarsu.20. Ya ba da umarninsa ya kuma warkar da su ya kuɓutar da su daga kabari.21. Bari su yi godiya ga Ubangiji saboda ƙaunarsa marar ƙarewa da kuma ayyukansa masu banmamaki saboda mutane.22. Bari su miƙa hadaya ta godiya su kuma ba da labarin ayyukansa da waƙoƙin farin ciki.Karin Magana 25:17-1717. Kada ka cika ziyarar gidan maƙwabcinka yawan ganinka zai sa ya ƙi ka.2 Korintiyawa 1:8-248. ’Yan’uwa, ba ma so ku zama da rashin sani, a kan wahalolin da muka sha a lardin Asiya. Mun sha wahaloli sosai, har abin ya fi ƙarfinmu, ya sa muka fid da tsammanin rayuwa.9. Ba shakka, a zuciyarmu mun ji kamar hukuncin kisa ne aka yi mana. Wannan kuwa ya faru ne domin kada mu dogara da kanmu, sai dai ga Allah, wanda yake tā da matattu.10. Shi ya cece mu daga irin wannan hatsari na mutuwa, zai kuwa cece mu. A kansa muka kafa bege cewa zai ci gaba da cetonmu,11. yayinda kuke taimakonmu ta wurin addu’o’inku. Mutane da yawa kuwa za su yi godiya ta dalilinmu, saboda albarkar da aka yi mana, ta amsa addu’o’i masu yawa.12. Wannan shi ne taƙamarmu. Lamirinmu yana ba da shaida cewa mun yi zamanmu a duniya, musamman a dangantakarmu da ku cikin tsarki, tsakani da Allah. Mun yi haka ta wurin bishewar alherin Allah, ba bisa ga hikimar duniya ba.13. Gama ba mu rubuta muku abin da ba za ku iya karatu ko ku kāsa fahimta ba. Ina kuma fata cewa,14. kamar yadda kuka ɗan fahimce mu, za ku kai ga cikakkiyar fahimta cewa za ku iya yin taƙama da mu, kamar yadda mu ma za mu yi taƙama da ku a ranar da Ubangiji Yesu zai dawo.15. Saboda na amince da haka, shi ya sa na so zuwa wurinku da fari, domin ku sami albarka riɓi biyu.16. Na yi shiri in ziyarce ku a kan hanyata zuwa Makidoniya, in kuma sāke dawo wurinku a kan hanyata daga Makidoniya, sa’an nan ku yi mini rakiya a hanyata zuwa Yahudiya.17. Kuna gani na yi wannan shirin ba da sanin abin da nake yi ba ne? Ko kuwa, kuna gani na yi shirin nan da halin mutuntaka ne, don in ce, “I” in koma in ce, “A’a”?18. Kamar dai yadda ba shakka Allah yake mai aminci, haka ma maganar da muka yi muku, ba “I” da kuma “A’a” ba ce.19. Gama Ɗan Allah, Yesu Kiristi, wanda ni da Sila da Timoti muka yi muku wa’azinsa, ai, ba “I” da “A’a” ba ne, amma a cikin Kiristi, “I” ne kullum.20. Domin dukan alkawaran Allah cikarsu a gare shi suke, ta wurinsa ne kuma muke faɗar “Amin”, domin a ɗaukaka Allah.21. Allah ne fa yake sa mu da ku mu tsaya daram cikin Kiristi. Shi ne ya shafe mu,22. ya buga mana hatiminsa a kan mu nasa ne, ya kuma sa mana Ruhunsa a cikin zukatanmu, domin yă tabbatar da abin da yake zuwa nan gaba.23. Labudda, Allah shi ne shaidata cewa don kada in ƙara muku wahala ne ya sa ban koma Korint ba.24. Ba nuna muku iko a kan bangaskiyarku muke yi ba, sai dai muna aiki tare da ku ne saboda farin cikinku, domin bisa ga bangaskiya ce kuke tsaye da ƙarfi. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.