Baibul a cikin shekara guda Satumba 20Ishaya 30:1-331. “Kaiton ’ya’ya masu tayarwa,” in ji Ubangiji, “ga waɗanda suke ƙulle-ƙullen da ba nawa ba, suna yin yarjejjeniya, amma ba ta Ruhuna ba, suna jibga zunubi a kan zunubi;2. waɗanda suka gangara zuwa Masar ba tare da sun nemi shawarata; waɗanda suke neman taimakon kāriyar Fir’auna, don neman inuwar mafakar Masar.3. Amma kāriyar Fir’auna za tă zama muku abin kunya, inuwar Masar za tă jawo muku kunya.4. Ko da yake suna da shugabanni a Zowan kuma jakadunsu sun iso Hanes,5. kowa zai sha kunya saboda mutanen da ba su da amfani gare su, waɗanda ba sa taimako ko amfani, sai dai jawo kunya da da-na-sani.”6. Allah ya faɗa game da dabbobin Negeb cewa, Ta cikin ƙasa mai wahala da mai hatsari inda zakoki da zakanya, inda macizai masu dafi da macizai masu tashi sama suke, jakadu na ɗaukan arzikinsu a kan jakuna, dukiyarsu a kan raƙuma, zuwa ƙasan nan marar riba,7. zuwa Masar, wadda taimakonta marar amfani ne. Saboda haka na yi mata laƙabi Rahab Marar Yin Kome.8. Tafi yanzu, ka rubuta musu a kan allo, ka rubuta shi a kan littafi, cewa kwanaki suna zuwa zai zama madawwamin shaida.9. Waɗannan mutane masu tawaye, ’ya’ya masu ruɗu, ’ya’yan da ba sa niyya su saurara ga umarnan Ubangiji.10. Sukan ce wa masu gani, “Kada ku ƙara ganin wahayi!” Ga annabawa kuwa sukan ce, “Kada ku ƙara ba mu wahayin abin da yake daidai! Faɗa mana abubuwan da muke so mu ji ne kawai, ku yi annabcin abin da zai ruɗe mu.11. Ku bar wannan hanya, ku tashi daga wannan hanya, ku kuma daina kalubalantarmu da Mai Tsarkin nan na Isra’ila!”12. Saboda haka, ga abin da Mai Tsarkin nan na Isra’ila yake cewa, “Saboda haka kun ƙi wannan saƙo, kuka dogara ga aikin kama-karya kuka kuma dogara ga yin ruɗu,13. wannan zunubi zai zama muku kamar bango mai tsayi, tsagagge da yake kuma fāɗuwa, da zai rushe nan da nan, ba tsammani.14. Zai rushe kucu-kucu kamar tukunyar yumɓu, ya ragargaje ƙaf har cikin gutsattsarinsa ba za a sami ko ɗan katanga don ɗiba garwashin wuta ko a ɗiba ruwa daga tanki ba.”15. Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka, Mai Tsarkin nan na Isra’ila ya faɗa, “Cikin tuba da hutu ne kaɗai cetonku yake, cikin shiru da dogara gare ni ne za ku sami ƙarfinku, amma ba za ku sami ko ɗaya a cikinsu ba.16. Kun ce, ‘A’a, za mu gudu a kan dawakai.’ Saboda haka za ku gudu! Kun ce, ‘Za mu hau dawakai masu sauri mu gudu.’ Saboda haka masu fafararku za su fi ku gudu!17. Dubu za su gudu don barazanar mutum guda; da jin barazanar mutane biyar dukanku za ku yi ta gudu sai an bar ku kamar sandar tuta a kan dutse, kamar tuta a kan tudu.”18. Duk da haka Ubangiji yana marmari ya yi muku alheri; ya tashi don yă nuna muku jinƙai. Gama Ubangiji Allah ne mai aikata gaskiya. Masu albarka ne dukanku waɗanda suke dogara gare shi!19. Ya mutanen Sihiyona, waɗanda suke zama a Urushalima, ba za ku ƙara kuka ba. Zai zama mai alheri sa’ad da kuka yi kukan neman taimako! Da zarar ya ji, zai amsa muku.20. Ko da yake Ubangiji yakan ba da abincin azaba da ruwan wahala, ba za a ƙara ɓoye malamanku ba; da idanunku za ku gan su.21. Ko kun juye dama ko hagu, kunnuwanku za su ji murya a bayanku tana cewa, “Ga hanya; ku yi tafiya a kai.”22. Sa’an nan za ku ƙazantar da gumakanku da kuka dalaye da zinariya; za ku zubar da su kamar rigar al’adar mace ku kuma ce musu, “Ku ɓace mana da gani!”23. Zai kuma aiko muku da ruwan sama don shuki a ƙasa, kuma abincin da zai fito daga gona zai zama mai albarka da kuma mai yawa. A wannan rana shanu za su yi kiwo a wadatacciyar makiyaya.24. Shanunku da jakunanku da suke huɗar gonakinku za su ci harawa mafi kyau, wanda an sheƙe shi da babban cokali mai yatsu da kuma babban cokali.25. A ranar babban kisa, sa’ad da hasumiyoyi za su fāɗi, rafuffukan ruwa za su malalo a kan kowane dutse da kowane tudu mai tsawo.26. Wata zai yi haske kamar rana, kuma hasken rana zai ma yi sau bakwai na haskenta, kamar hasken cikakku ranaku bakwai, sa’ad da Ubangiji zai ɗaura raunukan mutanensa ya kuma warkar da raunukan da ya yi musu.27. Duba, Sunan Ubangiji yana zuwa daga nesa, tare da fushi mai ƙuna da kuma baƙin hayaƙi; leɓunansa sun cika da fushi, harshensa kuma wuta ce mai cinyewa.28. Numfashinsa kamar raƙuman ruwa masu gudu yana tashi har zuwa wuya. Yakan tankaɗe al’ummai cikin lariyar hallaka; yakan sa a muƙamuƙan mutane linzamin da zai jagorance su su kauce.29. Za ku kuma rera kamar a daren da kuke shagalin biki mai tsarki; zukatanku za su yi farin ciki kamar sa’ad da mutane sukan haura da busa zuwa dutsen Ubangiji, zuwa Dutse na Isra’ila.30. Ubangiji zai sa mutane su ji muryarsa mai daraja ya kuma sa su ga hannunsa na saukowa tare da fushi mai ƙuna da kuma wuta mai cinyewa, gizagizai za su ɓarke, za a yi hadarin tsawa da ƙanƙara.31. Muryar Ubangiji za tă firgita Assuriya da sandar mulkinsa zai kashe su.32. Kowane bugun da Ubangiji zai yi musu da bulalarsa na hukunci zai zama kiɗi ga ganguna da garaya, yayinda yake yaƙi da su da naushin hannunsa.33. An riga an shirya wurin ƙonawa; an shirya shi saboda sarki. An haƙa ramin wutarsa da zurfi da kuma fāɗi, da isashen wuta da itacen wuta; numfashin Ubangiji, yana kamar kibiritu mai ƙuna, da aka sa masa wuta.Ishaya 31:1-91. Kaiton waɗanda suka gangara zuwa Masar don neman taimako, waɗanda suke dogara ga dawakai, waɗanda suke dogara ga yawan kekunan yaƙinsu da kuma a girman ƙarfin mahayan dawakansu, amma ba sa dogara ga Mai Tsarkin nan na Isra’ila, ko ya nemi taimako daga Ubangiji.2. Shi ma yana da hikima kuma zai iya kawo masifa; ba ya janye kalmominsa. Zai yi gāba da gidan mugu, gāba da waɗanda suke taimakon masu aikata mugunta.3. Amma Masarawa mutane ne ba Allah ba; dawakansu nama da jini ne ba ruhu ba. Sa’ad da Ubangiji ya miƙa hannunsa, shi da yake taimako zai yi tuntuɓe shi da aka taimaka zai fāɗi; dukansu biyu za su hallaka tare.4. Ga abin da Ubangiji ya faɗa mini, “Kamar yadda zaki kan yi ruri babban zaki a kan abin da ya yi farauta, kuma ko da yake dukan ƙungiyar makiyaya sun taru wuri ɗaya a kansa, ba zai jijjigu ta wurin ihunsu ba ko ya damu da kiraye-kirayensu, ta haka Ubangiji Maɗaukaki zai sauko don yă yi yaƙi a kan Dutsen Sihiyona da kuma a kan ƙwanƙolinsa.5. Kamar tsuntsaye masu shawagi a sama haka Ubangiji Maɗaukaki zai kiyaye Urushalima; zai kāre ta ya kuma fanshe ta, zai ‘ƙetare’ ta ya kuma kuɓutar da ita.”6. Ku dawo gare shi ku da kuka yi masa babban tayarwa, ya Isra’ilawa.7. Gama a wannan rana kowannenku zai ƙi gumakan azurfa da zinariya da hannuwanku masu zunubi suka yi.8. “Za a karkashe Assuriyawa da takobin da ba na yin mutum ba; takobi, da ba na yin mutum ba, zai cinye. Za su gudu daga takobi za a kuma sa samarinsu aikin dole.9. Kagararsu za tă fāɗi saboda razana; da ganin matsayin yaƙin, shugabannin yaƙinsu za su firgita,” in ji Ubangiji, wanda wutarsa tana a Sihiyona, wanda matoyarsa tana a Urushalima.Ishaya 32:1-201. Duba, sarki zai yi mulki cikin adalci masu mulki kuma su yi mulki da adalci.2. Kowane mutum zai zama kamar wurin fakewa daga iska mafaka kuma daga hadari, kamar rafuffukan ruwa a hamada da kuma inuwar babban dutse a ƙeƙasasshiyar ƙasa.3. Sa’an nan idanun waɗanda suka gani ba za su ƙara rufewa ba, kunnuwan waɗanda suka ji kuma za su saurara.4. Zuciya marasa haƙuri za su sani su kuma fahimta, harshen masu ana’ana kuma zai sāke su yi magana sosai.5. Ba za a ƙara ce da wawa mai girma ba ko kuwa a ɗaukaka mazambaci.6. Gama wawa maganar wauta yakan yi, zuciyarsa ta cika da mugunta, yana aikata abubuwan rashin sanin Allah yana baza kurakurai game da Ubangiji; yana barin mayunwata da yunwa ya kuma hana masu ƙishirwa ruwan sha.7. Matakan mazambaci mugaye ne, yana ƙulla mugayen shirye-shirye don yă hallaka talakawa da ƙarairayi, ko sa’ad da roƙon mai bukata da gaskiya ne.8. Amma mutumin kirki kan yi shirye-shirye masu kirki, kuma yakan tsaya a kan ayyukan kirki.9. Ku matan da kuke zaman jin daɗi, ku tashi ku saurare ni; ku ’yan matan da kuke tsammani kuna da kāriya, ku ji abin da zan faɗa!10. Cikin ɗan lokaci ƙasa da shekara guda ku da kuke tsammani kuna da kāriya za ku yi rawar jiki; girbin ’ya’yan inabi zai kāsa, girbin ’ya’yan itatuwa kuma ba zai zo ba.11. Ku yi rawar jiki, ku mata masu jin daɗi, ku sha wahala, ku ’yan matan da kuke tsammani kuna da kāriya! Ku tuɓe rigunanku, ku ɗaura tsummoki a kwankwasonku.12. Ku bugi ƙirjinku don gonaki masu kyau don ’ya’yan inabi13. da kuma don ƙasar mutanena, da ƙasar da ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya ne suka yi girma, I, ku yi kuka saboda dukan gidajen da dā ake biki da kuma domin wannan birnin da dā ake murna a ciki.14. Za a ƙyale kagarar, a gudu a bar birnin da dā ake hayaniya; mafaka da hasumiyar tsaro za su zama kango har abada, jin daɗin jakuna, makiyaya don garkuna,15. sai an zubo Ruhu a kanmu daga sama, hamada kuma ta zama ƙasar mai taƙi, gona mai taƙi kuma ta zama kamar kurmi.16. Aikin gaskiya zai zauna a hamada adalci kuma zai zauna a ƙasa mai taƙi.17. Aikin adalci zai zama salama; tasirin adalci zai zama natsuwa da tabbaci har abada.18. Mutanena za su zauna lafiya a wuraren salama, a gidaje masu kāriya, a wuraren hutun da babu fitina.19. Ko da yake ƙanƙara za tă fāɗo a jeji, a kuma rurrushe birni gaba ɗaya,20. zai zama muku da albarka, ku da kuke shuki iri kusa da kowane rafi, kuna kuma barin lafiyayyiyar makiyaya domin shanu da jakunanku.Zabura 108:7-137. Allah ya yi magana daga wurinsa mai tsarki, “Ciki nasara zan raba Shekem in kuma auna Kwarin Sukkot.8. Gileyad nawa ne, Manasse nawa ne; Efraim shi hulan kwanona, Yahuda ne sandana na sarauta.9. Mowab shi ne kwanon wankina, a kan Edom zan jefa takalmina; a bisa Filistiya zan yi kirari cikin nasara.”10. Wa zai kawo ni birni mai katanga? Wa zai jagorance ni zuwa Edom?11. Ba kai ba ne, ya Allah, kai da ka ƙi mu ba ka kuwa fita tare da mayaƙanmu?12. Ka ba mu taimako a kan abokin gāba, gama taimakon mutum banza ne.13. Tare da Allah za mu yi nasara, zai kuma tattaka abokan gābanmu.Karin Magana 25:23-2423. Kamar yadda iskar arewa kan kawo ruwan sama, haka jita-jita kan kawo fushi.24. Gara a zauna a kusurwar rufin ɗaki da a zauna a gida ɗaya da mace mai fitina.2 Korintiyawa 11:16-3316. Ina sāke faɗa, kada wani yă ɗauka ni wawa ne. Amma in kun ɗauke ni haka, to, sai ku karɓe ni kamar yadda kuke karɓan wawa, domin in ɗan in yi taƙama.17. A wannan taƙamata ba na magana yadda Ubangiji zai yi ba ne, sai dai magana ce irin ta wawa.18. Da yake mutane da yawa suna taƙama irin ta duniya, ni ma haka zan yi.19. Ku kam kuna da wayo sosai, har kuna jimre wa wawaye da murna!20. Gaskiyar ita ce, kuna haƙuri da duk wanda ya sa ku bauta ko ya cuce ku ko ya more ku ko ya nuna muku isa ko kuma ya mare ku a fuska.21. Ina jin kunya in ce mun nuna kāsawa da ba mu yi waɗannan abubuwan ba! Abin da wani yake da ƙarfin hali yin taƙama a kai, shi ne ni ma nake ƙarfin hali yin taƙama a kai. Ina magana kamar wawa ne.22. In su Ibraniyawa ne, ni ma haka. In su Isra’ilawa ne, ni ma haka. In su zuriyar Ibrahim ne, ni ma haka.23. In su bayin Kiristi ne, ni na fi su ma, ina magana kamar ruɗaɗɗe ne fa! Ai, na fi su shan fama ƙwarai da gaske, da shan dauri, na sha dūka marar iyaka, na sha hatsarin mutuwa iri-iri.24. Sau biyar Yahudawa suka yi mini bulala arba’in ɗaya babu.25. Sau uku aka bulale ni da bulalar ƙarfe, sau ɗaya aka jajjefe ni da duwatsu, sau uku jirgin ruwa ya ragargaje ina ciki, na kwana na kuma yini ruwan teku yana tafiya da ni.26. Na yi tafiye-tafiye da yawa, na sha hatsari a koguna, na sha hatsarin ’yan fashi, na sha hatsari a hannun kabilarmu, na sha hatsari a hannun al’ummai, na sha hatsari a birane, na sha hatsari a jeji, na sha hatsari a teku, na kuma sha hatsarin ’yan’uwa na ƙarya.27. Na yi fama, na shan wuya, ga kuma rashin barci sau da yawa. Na san abin da ake nufin da jin yunwa da ƙishirwa, sau da yawa kuwa na kasance da rashin abinci, na sha sanyi da zaman tsirara.28. Ban da waɗannan abubuwa, kowace rana ina ɗauke da nauyin kula da dukan ikkilisiyoyi.29. Wane ne ya rasa ƙarfi, da ban ji shi a jikina ba? Wane ne ya fāɗi cikin zunubi, da ban ji zafin wannan ba?30. In ma lalle ne in yi taƙama, to, sai in yi taƙama da abubuwan da suka nuna rashin ƙarfina.31. Allah Uban Ubangiji Yesu Kiristi, wanda yabo ta tabbata a gare shi har abada, ya san cewa ba ƙarya nake yi ba.32. A Damaskus, gwamnan da yake ƙarƙashin Sarki Aretas, ya sa tsare ƙofofin birnin Damaskus, don yă kama ni.33. Amma aka saukar da ni cikin kwando ta tagar katanga, na kuɓuce masa. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.