Baibul a cikin shekara guda Janairu 11Farawa 21:1-341. Ana nan sai Ubangiji ya nuna wa Saratu alheri kamar yadda ya ce, Ubangiji kuma ya yi wa Saratu abin da ya yi alkawari.2. Saratu ta yi ciki, ta kuma haifa wa Ibrahim ɗa a tsufansa; a daidai lokacin da Allah ya yi masa alkawari.3. Ibrahim ya sa wa ɗan da Saratu ta haifa masa suna Ishaku.4. Sa’ad da ɗansa Ishaku ya kai kwana takwas da haihuwa, sai Ibrahim ya yi masa kaciya, kamar yadda Allah ya umarce shi.5. Ibrahim yana da shekara ɗari, sa’ad da aka haifa masa ɗansa Ishaku.6. Saratu ta ce, “Allah ya sa na yi dariya, kuma duk wanda ya ji game da wannan, zai yi dariya tare da ni.”7. Ta kuma ƙara da cewa, “Dā, wa zai iya ce wa Ibrahim, Saratu za tă yi renon yara? Duk da haka na haifar masa ɗa cikin tsufansa.”8. Yaron ya yi girma, aka kuma yaye shi, a ranar da aka yaye shi kuwa, Ibrahim ya yi babban biki.9. Amma Saratu ta ga cewa yaron da Hagar, mutuniyar Masar ta haifa wa Ibrahim yana wa ɗanta Ishaku gori,10. sai ta ce wa Ibrahim, “Ka kori baiwan nan tare da ɗanta, saboda ɗan baiwan nan ba zai taɓa raba gādo da ɗana Ishaku ba.”11. Al’amarin ya ɓata wa Ibrahim rai sosai domin zancen ya shafi ɗansa.12. Amma Allah ya ce wa Ibrahim, “Kada hankalinka yă tashi game da yaron nan da kuma baiwarka. Ka saurari duk abin da Saratu ta faɗa maka, saboda ta wurin Ishaku ne za a lissafta zuriyarka.13. Zan ba ɗan baiwan nan al’umma shi ma, domin shi zuriyarka ne.”14. Kashegari da sassafe sai Ibrahim ya ɗauki abinci da salkar ruwa, ya ba wa Hagar. Ya ɗora su a kafaɗunta, sa’an nan ya sallame ta da yaron. Ta kama hanyarta ta kuma yi ta yawo a cikin jejin Beyersheba.15. Sa’ad da ruwan da yake cikin salkan ya ƙare, sai ta ajiye yaron a ƙarƙashin wani ƙaramin itace.16. Sai ta tafi, ta zauna ɗan nesa da yaron, misalin nisan harbin baka, gama ta yi tunani ta ce, “Ba zan iya kallon yaron yana mutuwa ba.” Da ta zauna nesa da yaron, sai ta fara kuka.17. Allah kuwa ya ji yaron yana kuka, sai mala’ikan Allah ya kira Hagar daga sama ya ce mata, “Mene ne damuwarki, Hagar? Kada ki ji tsoro, Allah ya ji yaron yana kuka yayinda yake kwance a can.18. Ki ɗaga yaron ki riƙe shi a hannu, gama zan mai da shi al’umma mai girma.”19. Sa’an nan Allah ya buɗe idanunta ta ga wata rijiyar ruwa. Don haka sai ta tafi ta cika salkan da ruwa, ta kuma ba wa yaron ruwa ya sha.20. Allah ya kasance da yaron, yayinda yake girma. Ya yi zama a jeji, ya kuma zama maharbi.21. Yayinda yake zama a Jejin Faran, sai mahaifiyarsa ta samo masa mata daga Masar.22. A lokacin nan Abimelek da Fikol, komandan rundunoninsa suka zo suka ce wa Ibrahim, “Allah yana tare da kai a ko mene ne kake yi.23. Yanzu ka rantse mini a nan a gaban Allah cewa, ba za ka yaudare ni ko ’ya’yana ko kuma zuriyata ba. Ka nuna mini alheri, kai da ƙasar da kake zama baƙunci kamar yadda na nuna maka.”24. Ibrahim ya ce, “Na rantse.”25. Sa’an nan Ibrahim ya kawo kuka ga Abimelek game da rijiyar ruwan da bayin Abimelek suka ƙwace.26. Sai Abimelek ya ce, “Ban san wanda ya yi wannan ba. Ba ka faɗa mini ba, ban kuwa taɓa ji ba, sai yau.”27. Sai Ibrahim ya kawo tumaki da shanu ya ba wa Abimelek, sai su biyun suka yi yarjejjeniya.28. Ibrahim ya ware ’yan raguna bakwai daga cikin garke,29. sai Abimelek ya ce wa Ibrahim, “Mene ne ma’anar ’yan raguna bakwai da ka keɓe?”30. Ibrahim ya amsa ya ce, “Ka karɓi waɗannan ’yan tumaki bakwai daga hannuna a matsayin shaida cewa ni ne na haƙa wannan rijiya.”31. Saboda haka aka kira wurin Beyersheba, domin a nan ne su biyun suka yi rantsuwa.32. Bayan da aka yi yarjejjeniya a Beyersheba, sai Abimelek da Fikol, komandan rundunoninsa suka koma ƙasar Filistiyawa.33. Sai Ibrahim ya shuka itacen tsamiya a Beyersheba, a can kuma ya kira bisa sunan Ubangiji, Allah Madawwami.34. Ibrahim kuwa ya zauna a ƙasar Filistiyawa na dogon lokaci.Farawa 22:1-241. Bayan abubuwan nan suka faru, sai Allah ya gwada Ibrahim. Ya ce masa, “Ibrahim!” Ibrahim ya amsa ya ce, “Ga ni.”2. Sai Allah ya ce, “Ka ɗauki ɗanka, makaɗaicin ɗanka Ishaku, wanda kake ƙauna, ka tafi yankin Moriya, ka miƙa shi hadaya ta ƙonawa a can a kan ɗaya daga cikin duwatsun da zan nuna maka.”3. Kashegari da sassafe, Ibrahim ya tashi ya ɗaura wa jakinsa sirdi. Ya ɗauki bayinsa biyu, da ɗansa Ishaku. Bayan ya faskare isashen itace saboda hadaya ta ƙonawa sai ya kama hanya zuwa wurin da Allah ya faɗa masa.4. A rana ta uku Ibrahim ya ɗaga ido sai ya ga wurin daga nesa.5. Ibrahim ya ce wa bayinsa, “Ku tsaya a nan da jakin, ni da yaron kuwa mu haura can. Za mu yi sujada sa’an nan mu komo wurinku.”6. Ibrahim ya ɗauki itace saboda hadaya ta ƙonawa ya ɗora wa ɗansa Ishaku, shi kuwa ya riƙe wuƙa da wutar. Yayinda su biyun suke tafiya,7. sai Ishaku ya yi tambaya, ya ce wa mahaifinsa Ibrahim, “Baba?” Ibrahim ya ce masa, “Na’am ɗana!” Ishaku ya ce, “Ga dai wuta, ga kuma itace, amma ina ɗan ragon hadaya ta ƙonawa?”8. Ibrahim ya amsa ya ce, “Ɗana, Allah kansa zai tanada ɗan ragon hadayar ƙonawa.” Sai su biyu suka ci gaba da tafiya.9. Sa’ad da suka isa wurin da Allah ya faɗa masa, sai Ibrahim ya gina bagade a can, ya kuma shisshirya itacen a kai. Ya ɗaura ɗansa Ishaku, ya kwantar da shi a kan itacen, a bisa bagaden.10. Sa’an nan Ibrahim ya miƙa hannunsa ya ɗauki wuƙar don yă yanka ɗansa.11. Amma mala’ikan Ubangiji ya kira shi daga sama ya ce, “Ibrahim, Ibrahim!” Sai Ibrahim ya amsa ya ce, “Ga ni.”12. Mala’ikan ya ce, “Kada ka yi wa yaron nan rauni. Kada kuma ka ji masa ciwo. Yanzu na san cewa kana tsoron Allah, gama ba ka hana ni ɗanka, makaɗaicin ɗanka ba.”13. Ibrahim ya ɗaga ido, ya duba, sai ya ga rago da ƙahoninsa a kafe a wani ɗan kurmi. Sai Ibrahim ya tafi ya kamo ragon ya miƙa shi hadaya ta ƙonawa a maimakon ɗansa.14. Ibrahim kuwa ya ba wa wurin suna, Ubangiji Zai Tanada. Gama kamar yadda ake ce har yă zuwa yau, “A bisan dutsen Ubangiji, za a tanada.”15. Mala’ikan Ubangiji ya kira Ibrahim daga sama sau na biyu16. ya ce, “Na rantse da kaina, in ji Ubangiji, domin ka yi wannan, ba ka kuwa hana ni ɗanka, makaɗaicin ɗanka ba,17. tabbatacce zan albarkace ka, zan kuma sa zuriyarka su yi yawa kamar taurari a sararin sama, kamar kuma yashi a bakin teku. Zuriyarka za su mallaki biranen abokan gābansu,18. ta wurin zuriyarka kuma dukan al’umman duniya za su sami albarka, domin ka yi mini biyayya.”19. Sa’an nan Ibrahim ya koma wurin bayinsa, suka kuma kama hanya tare zuwa Beyersheba. Ibrahim kuwa ya yi zamansa a Beyersheba.20. Bayan wani ɗan lokaci, sai aka faɗa wa Ibrahim cewa, “Ga shi, Milka ita ma ta haifa wa Nahor ɗan’uwanka, ’ya’ya maza;21. ɗan fari shi ne Uz, ɗan’uwansa kuma Buz, Kemuwel (shi ne mahaifin Aram),22. Kesed, Hazo, Fildash; Yidlaf, da kuma Betuwel.”23. Betuwel ya haifi Rebeka. Milka ta haifa wa Nahor ɗan’uwan Ibrahim waɗannan ’ya’ya maza takwas.24. Ban da haka ma, ƙwarƙwararsa, mai suna Reyuma, ta haifa masa ’ya’ya maza, Teba, Gaham, Tahash da kuma Ma’aka.Zabura 6:6-106. Na gaji tiƙis daga nishi. Dukan dare na jiƙe gadona da kuka na jiƙe kujerata da hawaye.7. Idanuna sun rasa ƙarfi da baƙin ciki; sun rasa ƙarfi saboda dukan abokan gābana.8. Ku tafi daga gare ni, dukanku masu aikata mugunta, gama Ubangiji ya ji kukata.9. Ubangiji ya ji kukata saboda jinƙansa; Ubangiji ya karɓi addu’ata.10. Dukan abokan gābana za su sha kunya su kuma karaya; za su juya da kunya nan da nan.Karin Magana 3:5-65. Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka kada kuma ka dangana ga ganewarka;6. cikin dukan hanyoyinka ka amince da shi, zai kuwa sa hanyoyinka su miƙe.Mattiyu 8:18-3418. Da Yesu ya ga taron mutane kewaye da shi, sai ya ba da umarni a ƙetare zuwa ɗayan hayin tafkin.19. Sai wani malamin dokoki ya zo wurinsa ya ce, “Malam, zan bi ka duk inda za ka.”20. Sai Yesu ya amsa ya ce, “Yanyawa suna da ramummuka, tsuntsayen sararin sama suna da sheƙuna, amma Ɗan Mutum ba shi da wurin da zai sa kansa.”21. Sai wani almajiri ya ce masa, “Ubangiji, da farko bari in je in binne mahaifina.”22. Amma Yesu ya ce masa, “Ka bi ni, ka bar matattu su binne matattunsu.”23. Sai ya shiga jirgin ruwa, almajiransa kuwa suka bi shi.24. Ba zato ba tsammani, sai wani babban hadari ya taso a tafkin, har raƙuman ruwan suka sha kan jirgin. Amma Yesu yana barci.25. Almajiran suka je suka tashe shi, suna cewa, “Ubangiji, ka cece mu! Za mu nutse!”26. Ya amsa ya ce, “Ku masu ƙarancin bangaskiya, me ya sa kuke tsoro haka?” Sa’an nan ya tashi ya tsawata wa iskar da kuma raƙuman ruwan, sai wuri ya yi tsit gaba ɗaya.27. Mutanen suka yi mamaki suka ce, “Wane irin mutum ne wannan? Har iska da raƙuman ruwa suna masa biyayya!”28. Da ya isa ɗayan gefen a yankin Gadarenawa (ko kuwa Gerasenawa), sai ga mutum biyu masu aljanu suna fitowa daga kaburbura suka tarye shi. Su abin tsoro ne ƙwarai, har ba mai iya bin wannan hanya.29. Suka yi ihu suka ce, “Me ya haɗa ka da mu, Ɗan Allah?” Ka zo ne nan don ka ji mana kafin lokaci yă yi?30. Nesa kaɗan da su kuwa akwai babban garken aladu da yake kiwo.31. Aljanun suka roƙi Yesu suka ce, “In ka fitar da mu, tura mu cikin garken aladun nan.”32. Ya ce musu, “Ku tafi!” Sai suka fita suka shiga cikin aladun, dukan garken kuwa ya gangara a guje daga kan tudun zuwa cikin tafkin aladun kuma suka mutu a cikin ruwa.33. Masu kiwon aladun suka ruga, suka je cikin gari suka ba da labarin dukan wannan, haɗe da abin da ya faru da mutanen nan masu aljanu.34. Sai dukan garin suka fito don su taryi Yesu. Da suka kuwa gan shi, sai suka roƙe shi yă bar musu yanki. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.