Baibul a cikin shekara guda Janairu 15Farawa 29:1-351. Sa’an nan Yaƙub ya ci gaba da tafiyarsa har ya kai ƙasar mutanen gabashi.2. A can ya ga rijiya a jeji da garkuna uku na tumaki kwance kusa da ita, gama a wannan rijiya ce ake shayar da garkuna. Dutsen da ake rufe bakin rijiyar mai girma ne.3. Sa’ad da dukan garkuna suka taru a can, sai makiyayan su gungurar da dutsen daga bakin rijiyar su shayar da tumaki. Sa’an nan su mai da dutsen a wurinsa a bakin rijiya.4. Yaƙub ya tambayi makiyayan ya ce, “’Yan’uwa, ina kuka fito?” Suka amsa, “Mu daga Haran ne.”5. Sai ya ce musu, “Kun san Laban, jikan Nahor?” Suka amsa, “I, mun san shi.”6. Sa’an nan Yaƙub ya tambaye su, “Yana nan lafiya?” Suka ce, “I, yana lafiya, ga ma ’yarsa Rahila tafe da tumaki.”7. Ya ce, “Duba har yanzu da sauran rana da yawa, lokaci bai kai na tara garkuna ba. Ku shayar da tumaki ku mai da su wurin kiwo.”8. Suka amsa suka ce, “Ba za mu iya ba, sai dukan garkunan sun taru, aka kuma gungurar da dutsen daga bakin rijiyar. Sa’an nan za mu shayar da tumakin.”9. Tun yana cikin magana da su, sai ga Rahila ta zo da tumakin mahaifinta, gama ita makiyayyiya ce.10. Sa’ad da Yaƙub ya ga Rahila ’yar Laban, ɗan’uwan mahaifiyarsa, da tumakin Laban, sai ya tafi ya gungurar da dutsen daga bakin rijiyar, ya kuma shayar da tumakin kawunsa.11. Sa’an nan Yaƙub ya sumbaci Rahila, ya kuma ɗaga murya ya yi kuka.12. Ya riga ya faɗa wa Rahila cewa shi dangin mahaifinta ne kuma ɗan Rebeka. Saboda haka ta ruga da gudu ta faɗa wa mahaifinta.13. Nan da nan, da Laban ya sami labari game da Yaƙub, ɗan ’yar’uwarsa, ya gaggauta yă sadu da shi. Sai ya rungume shi ya sumbace shi, ya kuma kawo shi gidansa, a can kuwa Yaƙub ya faɗa masa dukan waɗannan abubuwa.14. Sa’an nan Laban ya ce masa, “Kai nama da jinina ne.” Bayan Yaƙub ya zauna da shi na wata guda cif,15. sai Laban ya ce masa, “Don kawai kai dangina ne na kusa, sai kawai ka yi mini aiki a banza? Faɗa mini abin da albashinka zai zama.”16. Laban dai yana da ’ya’ya mata biyu; sunan babbar Liyatu, sunan ƙaramar kuwa Rahila.17. Liyatu tana da raunannun idanu, amma Rahila dai tsarinta yana da kyau kuma kyakkyawa ce.18. Yaƙub ya ƙaunaci Rahila, sai ya ce, “Zan yi maka aiki na shekaru bakwai domin ƙaramar ’yarka Rahila.”19. Laban ya ce, “Ya fi kyau in ba ka ita, da in ba wani mutum dabam. Zauna tare da ni.”20. Saboda haka Yaƙub ya yi bauta shekaru bakwai domin a ba shi Rahila, amma shekarun suka zama kamar ’yan kwanaki ne kawai gare shi saboda ƙaunar da yake mata.21. Sa’an nan Yaƙub ya ce wa Laban, “Ba ni matata. Lokacina ya cika, ina kuma so in kwana da ita.”22. Saboda haka Laban ya tara dukan mutanen wurin, ya yi biki.23. Amma da yamma ta yi, sai ya ɗauki ’yarsa Liyatu ya ba da ita ga Yaƙub, sai Yaƙub ya kwana da ita.24. Laban kuma ya ba da baranyarsa Zilfa wa ’yarsa tă zama mai hidimarta.25. Sa’ad da safiya ta yi, sai ga Liyatu! Saboda haka Yaƙub ya ce wa Laban, “Mene ne ke nan ka yi mini? Na yi maka bauta domin Rahila, ba haka na yi ba? Don me ka ruɗe ni?”26. Laban ya amsa, “Ba al’adarmu ba ce a nan a ba da ’ya ƙarama aure kafin ’yar fari.27. Ka gama makon amaryanci na ’yar nan; sa’an nan za mu ba ka ƙaramar ita ma, don ƙarin waɗansu shekaru bakwai na aiki.”28. Haka kuwa Yaƙub ya yi. Ya gama mako guda da Liyatu, sa’an nan Laban ya ba shi ’yarsa Rahila tă zama matarsa.29. Laban ya ba da baranyarsa Bilha wa ’yarsa Rahila ta zama mai hidimarta.30. Yaƙub ya kwana da Rahila ita ma, ya kuwa ƙaunaci Rahila fiye da Liyatu. Ya kuma yi wa Laban aiki na ƙarin waɗansu shekaru bakwai.31. Sa’ad da Ubangiji ya ga ba a ƙaunar Liyatu, sai ya buɗe mahaifarta, amma Rahila ta zama bakararriya.32. Sai Liyatu ta yi ciki ta haifi ɗa. Ta sa masa suna Ruben, gama ta ce, “Domin Ubangiji ya ga wahalata. Tabbatacce mijina zai ƙaunace ni yanzu.”33. Ta sāke yin ciki, sa’ad da kuma ta haifi ɗa sai ta ce, “Gama Ubangiji ya ji cewa ba a ƙaunata, ya ba ni wannan shi ma.” Saboda haka ta ba shi suna Simeyon.34. Har yanzu ta yi ciki, sa’ad da kuma ta haifi ɗa sai ta ce, “Yanzu, a ƙarshe mijina zai manne mini, gama na haifa masa ’ya’ya maza uku.” Saboda haka ta ba shi suna Lawi.35. Ta sāke yin ciki, sa’ad da ta haifi ɗa sai ta ce, “A wannan lokaci zan yabi Ubangiji.” Saboda haka ta ba shi suna Yahuda. Sa’an nan ta daina haihuwa.Farawa 30:1-431. Sa’ad da Rahila ta ga cewa ba tă haifa wa Yaƙub ’ya’ya ba, sai ta fara kishin ’yar’uwarta. Saboda haka ta ce wa Yaƙub, “Ka ba ni ’ya’ya, ko kuwa in mutu!”2. Yaƙub ya fusata da ita ya ce, “Ina a matsayin Allah ne wanda ya hana ke samun ’ya’ya?”3. Sa’an nan ta ce, “Ga Bilha, mai baiwata, ka kwana da ita don tă haifa mini ’ya’ya, ta gare ta kuwa ni ma in gina iyali.”4. Saboda haka ta ba shi baranyarta Bilha tă zama matarsa. Yaƙub kuwa ya kwana da ita,5. ta kuwa yi ciki, ta kuma haifi ɗa.6. Sa’an nan Rahila ta ce, “Allah ya baratar da ni; ya saurari roƙona ya kuma ba ni ɗa.” Saboda wannan ta ba shi suna Dan.7. Baranyar Rahila ta sāke yin ciki ta kuma haifi wa Yaƙub ɗa na biyu.8. Sai Rahila ta ce, “Na yi kokawa sosai da ’yar’uwata, na kuwa yi nasara.” Saboda haka ta kira shi Naftali.9. Sa’ad da Liyatu ta ga cewa ta daina haihuwa, sai ta ɗauki mai hidimarta Zilfa ta ba da ita ga Yaƙub tă zama matarsa.10. Baranyar Liyatu, Zilfa ta haifa wa Yaƙub ɗa.11. Sai Liyatu ta ce, “Na yi sa’a!” Saboda haka ta ba shi suna Gad.12. Zilfa baranyar Liyatu ta haifa wa Yaƙub ɗa na biyu.13. Sai Liyatu ta ce, “Ni mai farin ciki ce! Mata za su ce da ni mai farin ciki.” Saboda haka ta sa masa suna Asher.14. A lokacin girbin alkama, sai Ruben ya je jeji ya ɗebo manta-uwa ya kawo wa mahaifiyarsa Liyatu. Sai Rahila ta ce wa Liyatu, “Ina roƙonki ki ɗan sam mini manta-uwa ɗanki.”15. Amma ta ce mata, “Bai ishe ki ba ne da kika ƙwace mijina? Yanzu kuma kina so ki ƙwace manta-uwa na yarona?” Sai Rahila ta ce “Shi ke nan, mijina zai iya kwana da ke yau saboda manta-uwa na ɗanki.”16. Saboda haka sa’ad da Yaƙub ya dawo daga jeji a wannan yamma sai Liyatu ta fito ta tarye shi. Ta ce, “Dole ka kwana da ni, na yi hayarka da manta-uwa na ɗana.” Saboda haka ya kwana da ita a wannan dare.17. Allah ya saurari Liyatu, ta kuwa yi ciki ta kuma haifa wa Yaƙub ɗa na biyar.18. Sai Liyatu ta ce, “Allah ya sāka mini saboda na ba da mai hidimata ga mijina.” Saboda haka ta ba shi suna Issakar.19. Liyatu ta sāke yin ciki ta kuma haifa wa Yaƙub ɗa na shida.20. Sai Liyatu ta ce, “Allah ya ba ni kyauta mai daraja. A wannan lokaci mijina zai darajarta ni, domin na haifa masa ’ya’ya maza shida.” Saboda haka ta ba shi suna Zebulun.21. Daga baya ta haifi ’ya ta kuwa ba ta suna Dina.22. Sai Allah ya tuna da Rahila; ya saurare ta ya kuma buɗe mahaifarta.23. Sai ta yi ciki ta kuma haifi ɗa ta ce, “Allah ya ɗauke mini kunyata.”24. Ta ba shi suna Yusuf, ta kuma ce, “Bari Ubangiji yă ƙara mini wani ɗa.”25. Bayan Rahila ta haifi Yusuf, sai Yaƙub ya ce wa Laban, “Ka sallame ni don in koma ƙasata.26. Ba ni matana da ’ya’yana, waɗanda na bauta maka dominsu, zan kuwa tafi. Ka dai san yadda na bauta maka.”27. Amma Laban ya ce masa, “In na sami tagomashi daga gare ka, ina roƙonka ka zauna. Na gane ta wurin duba cewa Ubangiji ya albarkace ni saboda kai.”28. Ya ƙara da cewa, “Faɗa albashinka, zan kuwa biya shi.”29. Yaƙub ya ce masa, “Ka dai san yadda na yi maka aiki da kuma yadda dabbobinka suka yi yawa a hannuna.30. Kaɗan da kake da shi kafin zuwata ya ƙaru sosai, kuma Ubangiji ya albarkace ka a duk inda na tafi. Amma yanzu, yaushe zan yi wani abu domin gidana ni ma?”31. Sai Laban ya yi tambaya, “Me zan ba ka?” Yaƙub ya amsa ya ce, “Kada ka ba ni wani abu. Amma in za ka yi mini abu guda ɗaya, zan ci gaba da kiwon garkunanka, ina kuma lura da su.32. Bari in ratsa cikin dukan garkunanka yau in fid da masu dabbare-dabbare da tumaki babare-babare, da kowane ɗan rago baƙi, da dabbare-dabbare da babare-babare na awaki daga ciki, waɗannan ne za su zama ladana.33. Gaskiyata kuwa za tă zama mini shaida nan gaba, duk sa’ad da ka bincika a kan albashin da ka biya ni. Duk akuyar da take tawa da ba dabbare-dabbare ko babare-babare, ko ɗan ragon da ba baƙi ba, zai kasance sata na yi.”34. Sai Laban ya ce, “Na yarda. Bari yă zama yadda ka faɗa.”35. A wannan rana ya ware dukan bunsurai da suke dabbare-dabbare da masu zāne-zāne, da dukan awakin da suke dabbare-dabbare (duka da suke da fari-fari a jikinsu), da dukan baƙaƙen tumaki, ya sa su a hannun ’ya’yansa maza.36. Sa’an nan ya sa nisan tafiya kwana uku tsakaninsa da Yaƙub, yayinda Yaƙub ya ci gaba da lura da sauran garkunan Laban Yaƙub.37. Yaƙub ya samo ɗanyen reshen itatuwan aduruku, da na katambiri, da na durumi, ya ɓare ya bar fararen cikin katakon rassan.38. Sa’an nan ya zuba ɓararre rassan cikin dukan kwamame na banruwa saboda su kasance a gaban garkunan sa’ad da suka zo shan ruwa. A sa’ad da garkunan suke barbara suka kuma zo shan ruwa,39. sai su yi barbara a gaban rassan. Sai kuwa su haifi ƙanana masu zāne dabbare-dabbare, ko babare-babare ko masu zāne-zāne.40. Sai Yaƙub yă ware ƙananan garken dabam, amma sai yă sa sauran su fuskanci dabbobin da suke dabbare-dabbare da kuma baƙaƙe da suke na Laban. Ta haka ya ware garkuna dabam domin kansa bai kuwa haɗa su da dabbobin Laban ba.41. A duk sa’ad da ƙarfafa dabbobi mata suke barbara, Yaƙub yakan zuba rassan a kwamame a gaban dabbobin saboda su yi barbara kusa da rassan,42. amma in dabbobin raunana ne, ba ya sa su a can. Saboda haka raunanan dabbobi suka zama na Laban, ƙarfafan kuma suka zama na Yaƙub.43. Ta haka mutumin ya zama riƙaƙƙe mai arziki, ya kasance mai manya-manyan garkuna, da bayi mata da maza, da raƙuma da kuma jakuna.Zabura 8:1-51. Ya Ubangiji, shugabanmu, sunanka da girma take a cikin dukan duniya! Ka kafa ɗaukakarka bisa sammai.2. Daga leɓunan yara da jarirai ka kafa yabo domin su sa abokan gābanka da masu ɗaukan fansa su yi shiru.3. Sa’ad da na dubi sammai, aikin yatsotsinka, wata da taurari waɗanda ka ajiye a wurarensu,4. wane ne mutum da kake tunawa da shi, ɗan mutum da kake lura da shi?5. Ka yi shi ƙasa kaɗan da Allah ka yi masa rawani da ɗaukaka da girma.Karin Magana 3:13-1813. Mai albarka ne mutumin da ya sami hikima, mutumin da ya sami fahimi,14. gama ta fi azurfa riba tana kuma da amfani fiye da zinariya.15. Ta fi lu’ulu’u daraja; ba a kwatanta abin da ka fi sha’awa da ita.16. Tsawon rai yana a cikin hannunta na dama; a hannunta na hagu kuwa akwai arziki da bangirma.17. Hanyoyinta hanyoyi ne masu daɗi, dukan hanyoyinta kuma salama ne.18. Ita itacen rai ne ga waɗanda suka rungume ta; waɗanda suke riƙe da ta za su zama masu albarka.Mattiyu 10:21-4221. “Ɗan’uwa zai ci amanar ɗan’uwansa, a kuma kashe shi, Uba ma zai yi haka da ɗansa; ’ya’ya za su tayar wa iyayensu, su kuma sa a kashe su.22. Dukan mutane za su ƙi ku saboda ni, amma wanda ya jure har ƙarshe zai sami ceto.23. Sa’ad da aka tsananta muku a wannan wuri, ku gudu zuwa wancan. Gaskiya nake gaya muku, kafin ku gama zazzaga dukan biranen Isra’ila, Ɗan Mutum zai zo.24. “Ɗalibi ba ya fin malaminsa, haka ma, bawa ba ya fin maigidansa.25. Ya isa wa ɗalibi yă zama kamar malaminsa, haka ma bawa kamar maigidansa. In har an kira wanda yake kan gida Be’elzebub, me za su ce game da mutanen gidansa?26. “Saboda haka kada ku ji tsoronsu. Ba abin da yake a rufe da ba za a tone ba, ko kuwa a ɓoye da ba za a bayyana ba.27. Abin da na faɗa muku a asirce, ku faɗe shi a sarari; abin da aka faɗa muku a kunne, ku yi shelarsa daga kan rufin ɗaki.28. Kada ku ji tsoron masu kashe jiki amma ba sa iya kashe rai. A maimakon haka, ku ji tsoron Wannan wanda yake da iko yă hallaka rai duk da jiki a jahannama ta wuta.29. Ba akan sayar da kanari biyu kobo ɗaya ba? Duk da haka ba ɗayansu da zai fāɗi ƙasa ba da yardar Ubanku.30. Kai, ko gashin kanku ma duk an ƙidaya su.31. Saboda haka kada ku ji tsoro; kun fi kanari masu yawa, daraja nesa.32. “Duk wanda ya bayyana yarda a gare ni a gaban mutane, ni ma zan bayyana yarda a gare shi a gaban Ubana da yake cikin sama.33. Amma duk wanda ya yi mūsun sani na a gaban mutane, ni ma zan yi mūsun saninsa a gaban Ubana da yake cikin sama.34. “Kada fa ku ɗauka na zo ne don in kawo salama a duniya. A’a, ban zo don in kawo salama ba, sai dai takobi.35. Gama na zo ne in sa, “ ‘gāba tsakanin mutum da mahaifinsa, ’ya da mahaifiyarta, matar ɗa da surukarta,36. abokan gāban mutum, za su zama mutanen gidansa ne.’37. “Duk wanda ya fi ƙaunar mahaifinsa ko mahaifiyarsa fiye da ni, bai dace yă zama nawa ba; duk kuwa wanda yake ƙaunar ɗansa ko diyarsa fiye da ni, bai dace yă zama nawa ba;38. duk wanda kuma bai ɗauki gicciyensa ya bi ni ba, bai dace yă zama nawa ba.39. Duk mai son adana ransa zai rasa shi, duk wanda kuwa ya rasa ransa saboda ni zai same shi.40. “Wanda ya karɓe ku, ya karɓe ni ne, wanda kuma ya karɓe ni, ya karɓi wanda ya aiko ni ne.41. Duk wanda ya karɓi annabi don shi annabi ne, zai sami ladar annabi, duk kuwa wanda ya karɓi mutum mai adalci don shi mai adalci ne, zai sami ladar mai adalci.42. In kuma wani ya ba wa ɗaya daga cikin ƙananan nan ko da kwaf ruwan sanyi ne kan shi almajirina ne, gaskiya nake gaya muku, ba shakka ba zai rasa ladarsa ba.” Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.