Baibul a cikin shekara guda Janairu 18Farawa 35:1-291. Sa’an nan Allah ya ce wa Yaƙub, “Haura zuwa Betel ka yi zama a can, ka kuma gina bagade a can wa Allah wanda ya bayyana gare ka sa’ad da kake gudu daga ɗan’uwanka Isuwa.”2. Saboda haka Yaƙub ya ce wa gidansa da kuma dukan waɗanda suke tare da shi, “Ku zubar da baƙin allolin da kuke da su, ku tsarkake kanku, ku kuma canja tufafinku.3. Sa’an nan ku zo, mu haura zuwa Betel, inda zan gina bagade wa Allah wanda ya amsa mini a ranar wahalata, wanda kuma ya kasance tare da ni a dukan inda na tafi.”4. Saboda haka suka ba Yaƙub dukan baƙin allolin da suke da su, da zoban da suke kunnuwansu, sai Yaƙub ya binne su a ƙarƙashin itacen oak a Shekem.5. Sa’an nan suka kama hanya, tsoron Allah kuwa ya kama dukan garuruwan da suke kewayensu har babu wanda ya iya bin su.6. Yaƙub da dukan mutanen da suke tare da shi suka zo Luz (wato, Betel) a ƙasar Kan’ana.7. A can ya gina bagade, ya kuma kira wurin El Betel, gama a can ne Allah ya bayyana kansa gare shi sa’ad da yake gudu daga ɗan’uwansa.8. To, Debora, ungozomar Rebeka ta rasu aka kuma binne ta a ƙarƙashin itacen oak, ƙasa da Betel. Saboda haka aka kira wurin Allon Bakut.9. Bayan Yaƙub ya komo daga Faddan Aram, sai Allah ya bayyana gare shi, ya kuma albarkace shi.10. Allah ya ce masa, “Sunanka Yaƙub ne, amma ba za a ƙara kira ka Yaƙub ba; sunanka zai zama Isra’ila.” Saboda haka ya ba shi suna Isra’ila.11. Sai Allah ya ce masa, “Ni ne Allah Maɗaukaki, ka yi ta haihuwa, ka kuma riɓaɓɓanya. Al’umma da tarin al’ummai za su fito daga gare ka, sarakuna kuma za su fito daga jikinka.12. Ƙasar da na ba wa Ibrahim da Ishaku, zan kuma ba ka, zan kuma ba da wannan ƙasa ga zuriyarka a bayanka.”13. Sa’an nan Allah ya tashi sama daga gare shi a wurin da ya yi magana da shi.14. Yaƙub kuwa ya kafa al’amudin dutse a inda Allah ya yi magana da shi, ya zuba hadaya ta sha a kansa; ya kuma zuba mai a kansa.15. Yaƙub ya kira inda Allah ya yi magana da shi, Betel.16. Sa’an nan suka tashi daga Betel. Yayinda suna da ɗan nisa da Efrat, sai Rahila ta fara naƙuda ta kuwa sha wahala sosai.17. Sa’ad da take cikin zafin haihuwa, sai macen da ta karɓi haihuwar ta ce mata, “Kada ki ji tsoro, gama yanzu kin sami wani ɗa.”18. Yayinda take jan numfashinta na ƙarshe, sai ta ba wa ɗanta suna Ben-Oni. Amma mahaifinsa ya kira shi Benyamin.19. Ta haka Rahila ta rasu, aka kuma binne ta a hanya zuwa Efrata (wato, Betlehem).20. Yaƙub ya kafa al’amudi bisa kabarinta, al’amudin kabarin Rahila ke nan, wanda yake can har wa yau.21. Isra’ila ya yi gaba, ya kafa tentinsa gaba da Migdal Eder.22. Yayinda Isra’ila yana zama a wancan yanki, Ruben ya shiga ya kwana da Bilha ƙwarƙwarar mahaifinsa, Isra’ila kuwa ya ji labari. Yaƙub ya haifi ’ya’ya maza goma sha biyu.23. ’Ya’yan Liyatu maza, Ruben shi ne ɗan fari na Yaƙub. Sauran su ne, Simeyon, Lawi, Yahuda, Issakar da Zebulun.24. ’Ya’yan Rahila maza su ne, Yusuf da Benyamin.25. ’Ya’yan Bilha maza, mai hidimar Rahila su ne, Dan da Naftali.26. ’Ya’yan Zilfa maza, mai hidimar Liyatu su ne, Gad da Asher. Waɗannan su ne ’ya’yan Yaƙub maza, waɗanda aka haifa masa a Faddan Aram.27. Yaƙub ya dawo gida wurin mahaifinsa Ishaku a Mamre, kusa da Kiriyat Arba (wato, Hebron), inda Ibrahim da Ishaku suka zauna.28. Ishaku ya rayu shekaru ɗari da tamanin,29. sa’an nan ya ja numfashinsa na ƙarshe, ya kuwa mutu, aka kuma tara shi ga mutanensa da kyakkyawan tsufa da kuma cikakken shekaru. ’Ya’yansa maza, Isuwa da Yaƙub suka binne shi.Farawa 36:1-431. Waɗannan su ne zuriyar Isuwa (wato, Edom).2. Isuwa ya ɗauko matansa daga cikin matan Kan’ana, ya ɗauko Ada ’yar Elon mutumin Hitti, da Oholibama ’yar Ana wadda take jikanyar Zibeyon Bahiwiye3. ya kuma auri Basemat ’yar Ishmayel wadda take ’yar’uwar Nebayiwot.4. Ada ta haifi wa Isuwa, Elifaz. Basemat kuma ta haifa masa Reyuwel.5. Oholibama kuwa ta haifa masa Yewush, Yalam da Kora. Waɗannan su ne ’ya’yan Isuwa maza, waɗanda aka haifa masa a Kan’ana.6. Isuwa ya ɗauki matansa da ’ya’yansa maza da mata da kuma dukan membobin gidansa, ya kuma ɗauki shanunsa da dukan sauran dabbobinsa, da dukan dukiyarsa da ya samu a ƙasar Kan’ana zuwa wata ƙasa nesa da ɗan’uwansa Yaƙub.7. Mallakarsu ta yi yawa ƙwarai da ba za su iya zauna tare ba; gama ƙasar da suke zaune a ciki ba za tă ishe su su biyu ba saboda dabbobinsu.8. Saboda haka Isuwa (wato, Edom) ya zauna a ƙasar tuddai na Seyir.9. Wannan shi ne zuriyar Isuwa, kakan mutanen Edom, a ƙasar tuddai na Seyir.10. Waɗannan su ne sunayen ’ya’yan Isuwa maza, Elifaz, ɗan Ada matar Isuwa, da Reyuwel ɗan Basemat matar Isuwa.11. ’Ya’yan Elifaz maza su ne, Teman, Omar, Zefo, Gatam da Kenaz.12. Elifaz ɗan Isuwa kuma yana da ƙwarƙwara mai suna Timna, wadda ta haifa masa Amalek. Waɗannan su ne jikokin Ada matar Isuwa.13. ’Ya’yan Reyuwel maza su ne, Nahat, Zera, Shamma da Mizza. Waɗannan su ne jikokin Basemat matar Isuwa.14. ’Ya’yan Oholibama maza ’yar Ana wadda take jikanyar Zibeyon, matar Isuwa, waɗanda ta haifa wa Isuwa su ne, Yewush, Yalam da Kora.15. Waɗannan su ne manya a cikin zuriyar Isuwa, ’Ya’ya Elifaz maza ɗan farin Isuwa, Shugabannin su ne; Teman, Omar, Zefo, Kenaz,16. Kora, Gatam da kuma Amalek. Waɗannan ne manya da suka fito daga dangin Elifaz a Edom; su ne jikokin Ada.17. ’Ya’yan Reyuwel maza, Shugabannin su ne; Nahat, Zera, Shamma da Mizza. Waɗannan su ne manya da suka fito daga dangin Reyuwel a Edom; su ne jikokin Basemat matar Isuwa.18. ’Ya’yan Oholibama maza matar Isuwa, Shugabannin su ne; Yewush, Yalam da Kora. Waɗannan su ne manya da suka fito daga dangin Oholibama ’yar Ana matar Isuwa.19. Waɗannan su ne ’ya’yan Isuwa maza (wato, Edom), waɗannan ne manyansu.20. Waɗannan su ne ’ya’yan Seyir Bahore maza, waɗanda suke zaune a yankin, Lotan, Shobal, Zibeyon, Ana,21. Dishon, Ezer da Dishan. Waɗannan su ne manyan Horiyawa, ’ya’yan Seyir, maza, a ƙasar Edom.22. ’Ya’yan Lotan maza su ne, Hori da Homam. Timna ’yar’uwar Lotan ce.23. ’Ya’yan Shobal maza su ne, Alwan, Manahat, Ebal, Shefo da Onam.24. ’Ya’yan Zibeyon maza su ne, Aiya da Ana. Wannan shi ne Ana wanda ya sami maɓulɓulan ruwan zafi a hamada yayinda yake kiwon jakuna na mahaifinsa Zibeyon.25. ’Ya’yan Ana su ne, Dishon da Oholibama ’yar Ana.26. ’Ya’yan Dishon maza su ne, Hemdan, Eshban, Itran da Keran.27. ’Ya’yan Ezer maza su ne, Bilhan, Za’aban da Akan.28. ’Ya’yan Dishan maza su ne, Uz da Aran.29. Waɗannan su ne manyan Horiyawa, Lotan, Shobal, Zibeyon, Ana,30. Dishon, Ezer da Dishan. Waɗannan su ne manyan Horiyawa, bisa ga ɓangarorinsu, a ƙasar Seyir.31. Waɗannan su ne sarakunan da suka yi mulki a Edom kafin wani sarki mutumin Isra’ila yă yi mulki,32. Bela ɗan Beyor ya zama sarkin Edom. Sunan birninsa shi ne Dinhaba.33. Sa’ad da Bela ya rasu, Yobab ɗan Zera daga Bozra ya gāje shi.34. Sa’ad da Yobab ya rasu, Husham daga ƙasar Temaniyawa ya gāje shi.35. Sa’ad da Husham ya rasu, Hadad ɗan Bedad, wanda ya ci Midiyan da yaƙi a ƙasar Mowab, ya gāje shi. Sunan birninsa shi ne Awit.36. Sa’ad da Hadad ya rasu, Samla daga Masreka ya gāje shi.37. Sa’ad da Samla ya rasu, Sha’ul daga Rehobot na ta kogi ya gāje shi.38. Sa’ad da Sha’ul ya rasu, Ba’al-Hanan ɗan Akbor ya gāje shi.39. Sa’ad da Ba’al-Hanan ɗan Akbor ya rasu, Hadad ya gāje shi. Sunan birninsa shi ne Fau, kuma sunan matarsa Mehetabel ce ’yar Matired, jikanyar Me-Zahab.40. Waɗannan su ne manya da suka fito daga zuriyar Isuwa, bisa ga danginsu, bisa kuma ga kabilansu da yankunansu. Sunayensu su ne, Timna, Alwa, Yetet.41. Oholibama, Ela, Finon.42. Kenaz, Teman, Mibzar.43. Magdiyel da Iram. Waɗannan su ne manyan Edom bisa ga mazauninsu cikin ƙasar da suka zauna. Wannan shi ne zuriyar Isuwa, kakan mutanen Edom.Zabura 9:6-106. Lalaci marar ƙarewa ya cimma abokan gābanmu, ka tuttumɓuke biranensu; yadda ma ba aka ƙara tunaninsu.7. Ubangiji yana mulki har abada; ya kafa kujerarsa don shari’a.8. Zai hukunta duniya da adalci; zai yi mulkin mutane cikin gaskiya.9. Ubangiji shi ne mafakan waɗanda ake danniya, mafaka a lokutan wahala.10. Waɗanda suka san sunanka za su dogara da kai, gama kai, Ubangiji, ba ka taɓa yashe waɗanda suke nemanka ba.Karin Magana 3:27-3027. Kada ka ƙi yin alheri ga duk wanda ya dace, sa’ad da kana iya yin haka.28. Kada ka ce wa maƙwabcinka “Ka yă dakata sai gobe,” idan kana iya taimakonsa yanzu.29. Kada ka shirya kome da zai cuci maƙwabcinka, wanda yake zama da aminci kusa da kai.30. Kada ka zargi mutum ba dalili, sa’ad da bai yi laifi ba.Mattiyu 12:22-5022. Sai aka kawo masa wani bebe kuma makaho mai aljani, Yesu kuwa ya warkar da shi, har ya iya magana ya kuma sami ganin gari.23. Dukan mutane suka yi mamaki, suka ce, “Wannan Ɗan Dawuda ne kuwa?”24. Amma da Farisiyawa suka ji haka, sai suka ce, “Ahab, da Be’elzebub sarkin aljanu ne kaɗai, wannan mutum yake fitar da aljanu.”25. Yesu kuwa ya san tunaninsu sai ya ce musu, “Duk mulkin da yake gāba da kansa zai lalace, kuma duk birni ko gidan da yake rabe gāba da kansa ba zai ɗore ba.26. In Shaiɗan yana fitar da Shaiɗan, ai, ya rabu yana gāba da kansa ke nan. Yaya kuwa mulkinsa zai ɗore?27. In kuwa ta wurin Be’elzebub nake fitar da aljanu, to, ta wa mutanenku suke fitar da su? Saboda haka, su ne za su zama alƙalanku.28. Amma in ina fitar da aljanu ta wurin Ruhun Allah ne, to, fa, mulkin Allah ya zo muku ke nan.29. “Ko kuwa, yaya wani zai iya shiga gidan mai ƙarfi yă ƙwace masa kaya ba tare da ya fara daure mai ƙarfin nan tukuna ba? Sa’an nan zai iya washe gidansa.30. “Wanda ba ya tare da ni, yana gāba da ni ne, kuma wanda ba ya taya ni tarawa, watsarwa yake yi.31. Saboda haka ina gaya muku, za a gafarta wa mutane kowane zunubi da kuma saɓo, amma saɓo game da Ruhu, ba za a gafarta ba.32. Duk wanda ya zargi Ɗan Mutum, za a gafarta masa, amma duk wanda ya zargi Ruhu Mai Tsarki, ba za a gafarta masa ba, ko a wannan zamani ko a zamani mai zuwa.33. “Itace mai kyau, yakan ba da ’ya’ya masu kyau. Itace marar kyau kuma, yakan ba da ’ya’ya marasa kyau. Itace dai, da irin ’ya’yansa ne ake gane shi.34. Ku macizai, ta yaya ku da kuke mugaye za ku iya magana kirki? Gama daga baki, mutum yakan faɗi abin da yake cikin zuciya.35. Mutumin kirki yakan fito da abubuwa masu kyau daga ajiyar da aka a yi cikinsa, mugun mutum kuwa yakan fito da mugayen abubuwa daga cikin muguntar da aka yi ajiya a cikinsa.36. Amma ina gaya muku cewa mutane za su ba da lissafi a ranar shari’a a kan kowace kalmar banza da suka faɗa.37. Gama ta wurin kalmominka za a kuɓutar da kai, kuma ta wurin kalmominka za a hukunta ka.”38. Sa’an nan waɗansu Farisiyawa da malaman dokoki suka ce masa, “Malam, muna so mu ga wata alama mai banmamaki daga gare ka.”39. Sai ya amsa ya ce, “Mugaye da masu zinan zamanin nan suna neman wata alama mai banmamaki! Amma babu wadda za a nuna musu, sai dai alama ta annabi Yunana.40. Gama kamar yadda Yunana ya yi yini uku da kuma dare uku a cikin wani babban kifi, haka Ɗan Mutum zai yi yini uku da kuma dare uku a cikin ƙasa.41. Mutanen Ninebe za su tashi a ranar shari’a tare da wannan zamani, su kuwa hukunta shi; don sun tuba saboda wa’azin Yunana, yanzu kuwa ga wanda ya fi Yunana girma a nan.42. Sarauniyar Sheba za tă tashi a ranar shari’a tare da wannan zamani, tă kuwa hukunta shi; don ta zo daga ƙarshen duniya, ta saurari hikimar Solomon, yanzu kuwa ga wanda ya fi Solomon girma a nan.43. “Sa’ad da mugun ruhu ya fita daga mutum, yakan bi wuraren da ba ruwa yana neman hutu, ba ya kuwa samu.44. Sa’an nan yakan ce, ‘Zan koma gidan da na bari.’ Sa’ad da ya iso, ya tarar da gidan ba kowa a ciki, shararre, kuma a kintse.45. Sai yă je yă ɗebo waɗansu ruhohi bakwai da suka fi shi mugunta, su kuwa zo su shiga su zauna a can. Ƙarshen mutumin nan fa zai fi farkonsa muni. Haka zai zama ga wannan mugun zamani.”46. Yayinda Yesu yake cikin magana da taron, sai ga mahaifiyarsa da ’yan’uwansa tsaye a waje, suna so su yi magana da shi.47. Wani ya ce masa, “Mahaifiyarka da ’yan’uwanka suna tsaye a waje, suna so su yi magana da kai.”48. Ya amsa masa ya ce, “Wace ce mahaifiyata, su wane ne kuma ’yan’uwana?”49. Sai ya miƙa hannu wajen almajiransa ya ce, “Ga mahaifiyata da kuma ’yan’uwana.50. Ai, duk wanda yake aikata nufin Ubana wanda yake cikin sama, shi ne ɗan’uwana da ’yar’uwata da kuma mahaifiyata.” Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.