Baibul a cikin shekara guda Janairu 2Farawa 3:1-241. To, maciji dai ya fi kowane a cikin namun jejin da Ubangiji Allah ya yi wayo. Ya ce wa macen, “Tabbatacce ne Allah ya ce, ‘Kada ku ci daga kowane itace a lambu’?”2. Macen ta ce wa macijin, “Za mu iya ci daga ’ya’ya itatuwa a lambun,3. amma Allah ya ce, ‘Kada ku ci daga ’ya’yan itacen da yake tsakiyar lambu, kada kuma ku taɓa shi, in ba haka ba kuwa za ku mutu.’ ”4. Maciji ya ce wa macen, “Tabbatacce ba za ku mutu ba.5. Gama Allah ya san cewa sa’ad da kuka ci daga itacen idanunku za su buɗe, za ku kuma zama kamar Allah, ku san abin da yake mai kyau da abin da yake mugu.”6. Sa’ad da macen ta ga ’ya’yan itacen suna da kyau don abinci, abin sha’awa ga ido, abin marmari kuma don samun hikima, sai ta tsinka ta ci, ta kuma ba da waɗansu wa mijinta wanda yake tare da ita, shi ma ya ci.7. Sa’an nan idanun dukansu biyu suka buɗe, suka kuma gane tsirara suke; saboda haka suka ɗinɗinka ganyayen ɓaure suka yi wa kansu sutura.8. Da mutumin da matarsa suka ji motsin Ubangiji Allah yana takawa a lambun a sanyin yini, sai suka ɓuya daga Ubangiji Allah a cikin itatuwan lambu.9. Amma Ubangiji Allah ya kira mutumin ya ce, “Ina kake?”10. Ya ce, “Na ji ka a cikin lambu, na kuwa ji tsoro gama ina tsirara, saboda haka na ɓuya.”11. Sai ya ce, “Wa ya faɗa maka cewa kana tsirara? Ko dai ka ci daga itacen da na umarce ka kada ka ci ne?”12. Mutumin ya ce, “Macen da ka sa a nan tare da ni, ita ta ba ni waɗansu ’ya’ya daga itacen, na kuwa ci.”13. Sai Ubangiji Allah ya ce wa matar, “Me ke nan kika yi?” Matar ta ce, “Macijin ne ya ruɗe ni, na kuwa ci.”14. Saboda haka Ubangiji Allah ya ce wa macijin, “Saboda ka yi haka, “Na la’anta ka cikin dukan dabbobi da kuma cikin dukan namun jeji! Daga yanzu rubda ciki za ka yi tafiya turɓaya kuma za ka ci dukan kwanakin rayuwarka.15. Zan kuma sa ƙiyayya tsakaninka da macen, tsakanin zuriyarka da zuriyarta. Zai ragargaje kanka, kai kuma za ka sari ɗiɗɗigensa.”16. Sa’an nan ya ce wa macen, “Zan tsananta naƙudarki ainun, da azaba kuma za ki haifi ’ya’ya. Za ki riƙa yin marmarin mijinki zai kuwa yi mulki a kanki.”17. Ga Adamu kuwa ya ce, “Saboda ka saurari matarka, ka kuma ci daga itacen da na ce, ‘Kada ka ci,’ “Za a la’anta ƙasa saboda kai. Da wahala za ka ci daga cikinta dukan kwanakin rayuwarka.18. Za tă ba ka ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya za ka kuwa ci ganyayen gona.19. Da zuffan goshinka za ka ci abincinka har ka koma ga ƙasa, da yake daga cikinta aka yi ka. Gama kai turɓaya ne, kuma ga turɓaya za ka koma.”20. Mutumin ya sa wa matarsa suna, Hawwa’u, gama za tă zama mahaifiyar masu rai duka.21. Ubangiji Allah ya yi tufafin fata domin Adamu da Hawwa’u, ya kuma yi musu sutura.22. Ubangiji Allah ya kuma ce, “To, fa, mutum ya zama kamar ɗaya daga cikinmu, ya san abin da yake mai kyau da abin da yake mugu. Kada a yarda yă miƙa hannunsa yă ɗiba daga itacen rai yă ci, yă kuma rayu har abada.”23. Saboda haka Ubangiji Allah ya kore shi daga Lambun Eden domin yă nome ƙasa wadda aka yi shi.24. Bayan da ya kori mutumin, sai ya sa kerubobi da takobi mai harshen wuta yana jujjuyawa baya da gaba a gabashin Lambun Eden don yă tsare hanya zuwa itacen rai.Farawa 4:1-261. Adamu ya kwana da matarsa Hawwa’u, ta kuwa yi ciki ta haifi Kayinu. Sai ta ce, “Da taimakon Ubangiji na sami ɗa namiji.”2. Daga baya ta haifi ɗan’uwansa, ta kuma ba shi suna Habila. Sa’ad da suka yi girma sai Habila ya zama makiyayin tumaki, Kayinu kuwa ya zama manomi.3. Ana nan sai Kayinu ya kawo waɗansu amfanin gona a matsayin hadaya ga Ubangiji.4. Amma Habila ya kawo mafi kyau daga ’ya’yan fari na garkensa. Ubangiji ya yi farin ciki da sadakar da Habila ya kawo,5. amma bai yi farin ciki da sadakar da Kayinu ya kawo ba. Saboda haka Kayinu ya ji fushi sosai, fuskarsa kuma ta ɓace.6. Sai Ubangiji ya ce wa Kayinu, “Don me kake fushi? Don me fuskarka ta ɓace?7. Da ka yi abin da yake daidai, ai, da ka sami karɓuwa. Amma tun da ba ka yi abin da ba daidai ba, zunubi zai yi fakonka don yă rinjaye ka kamar naman jeji. Yana so yă mallake ka, amma tilas ka rinjaye shi.”8. To, Kayinu ya ce wa ɗan’uwansa Habila, “Mu tafi gona.” Yayinda suke a gona, sai Kayinu ya tasar wa Habila ya buge shi ya kashe.9. Sai Ubangiji ya ce wa Kayinu, “Ina ɗan’uwanka Habila?” Sai Kayinu ya ce, “Ban sani ba, ni mai gadin ɗan’uwana ne?”10. Ubangiji ya ce, “Me ke nan ka yi? Saurara! Ga jinin ɗan’uwanka yana mini kuka daga ƙasa.11. Yanzu, kai la’ananne ne, an kuma kore ka daga ƙasa wadda ta buɗe bakinta ta shanye jinin ɗan’uwanka daga hannunka.12. In ka nome ƙasa, ba za tă ƙara ba ka hatsinta ba. Za ka kuma zama mai yawo barkatai a duniya.”13. Kayinu ya ce wa Ubangiji, “Horon nan ya sha ƙarfina.14. Ga shi, yau kana kori na daga ƙasar, zan zama a ɓoye daga fuskarka, zan kuma zama mai yawo barkatai, duk wanda ya same ni kuwa zai kashe ni.”15. Amma Ubangiji ya ce masa, “Ba haka ba ne! Duk wanda ya kashe Kayinu, za a ninƙa hukuncinsa har sau bakwai.” Sa’an nan Ubangiji ya sa wa Kayinu alama don duk wanda ya same shi kada yă kashe shi.16. Saboda haka Kayinu ya yi tafiyarsa ya rabu da Ubangiji, ya je ya zauna ƙasar Nod a gabashin Eden.17. Kayinu ya kwana da matarsa, ta kuwa yi ciki, ta haifi Enok. A lokacin Kayinu yana gina birni, sai ya sa wa birnin sunan ɗansa Enok.18. Aka haifa wa Enok Irad, Irad kuma ya haifi Mehujayel, Mehujayel kuma ya haifi Metushayel, Metushayel kuma ya haifin Lamek.19. Lamek ya auri mata biyu, ana ce da ɗaya Ada, ɗayan kuma Zilla.20. Ada ta haifi Yabal, shi ne mahaifi waɗanda suke zama a tentuna, suna kuma kiwon dabbobi.21. Sunan ɗan’uwansa Yubal, shi ne mahaifin dukan makaɗan garaya da masu hura sarewa.22. Zilla ma ta haifi ɗa, Tubal-Kayinu, shi ne wanda ya ƙera kowane iri kayan aiki daga tagulla da kuma ƙarfe. ’Yar’uwar Tubal-Kayinu ita ce Na’ama.23. Wata rana, Lamek ya ce wa matansa, Ada da Zilla, “Ku saurara, matan Lamek, ku ji maganata. Na kashe wani saboda ya yi mini rauni, na kashe wani saurayi saboda ya ji mini ciwo.24. Idan za a rama wa Kayinu har sau bakwai, lalle za a rama wa Lamek sau saba’in da bakwai ke nan.”25. Sai Adamu ya sāke kwana da matarsa, ta haifi ɗa, aka kuma ba shi suna Set, gama ta ce, “Allah ya ba ni wani yaro a madadin Habila, tun da yake Kayinu ya kashe shi.”26. Set ma ya haifi ɗa, ya kuma kira shi Enosh. A lokaci ne, mutane suka fara kira ga sunan Ubangiji.Zabura 2:1-61. Me ya sa ƙasashe suke haɗa baki mutane kuma suke ƙulla shawarwarin banza?2. Sarakunan duniya sun ɗauki matsayi masu mulki sun taru gaba ɗaya suna gāba da Ubangiji da kuma Shafaffensa.3. Suna cewa, “Bari mu tsittsinke sarƙoƙinsu, mu kuma ’yantar da kamammu daga kangin bautar Allah.”4. Mai zama a kursiyi a sama yana dariya; Ubangiji yana musu ba’a.5. Sa’an nan ya tsawata musu cikin fushinsa ya kuma razanar da su cikin hasalarsa, yana cewa,6. “Na kafa Sarkina a kan kursiyi a kan Sihiyona, dutsena mai tsarki.”Karin Magana 1:8-98. Ɗana, ka saurari umarnin mahaifinka kada kuma ka ƙyale koyarwar mahaifiyarka.9. Za su zama kayan ado don su inganta ka da kuma sarƙar wuya don su yi wa wuyanka ado.Mattiyu 2:1-231. Bayan an haifi Yesu a Betlehem, a Yahudiya, a zamanin Sarki Hiridus, sai waɗansu Masana, daga gabas suka zo Urushalima2. suka yi tambaya suka ce, “Ina shi wanda aka haifa sarkin Yahudawa? Gama mun ga tauraronsa a gabas mun kuwa zo ne domin mu yi masa sujada.”3. Da Sarki Hiridus ya ji wannan, sai hankalinsa ya tashi haka ma na dukan Urushalima.4. Bayan ya kira dukan manyan firistoci da malaman dokoki na mutane wuri ɗaya, sai ya tambaye su inda za a haifi Kiristi.5. Suka amsa suka ce, “A Betlehem ne, cikin Yahudiya, gama haka annabin ya rubuta.6. “ ‘Amma ke Betlehem, a cikin ƙasar Yahuda, ba ke ce mafi ƙanƙanta a cikin masu mulki a Yahuda ba, gama daga cikinki mai mulki zai zo, wanda zai zama makiyayin mutanena Isra’ila.’ ”7. Sai Hiridus ya kira Masanan nan a ɓoye, yă gano daga wurinsu daidai lokacin da tauraron ya bayyana.8. Sai ya aike su Betlehem ya ce, “Ku je ku binciko a hankali game da yaron nan. Da kun same shi, sai ku kawo mini labari nan da nan, domin ni ma in je in yi masa sujada.”9. Bayan sun saurari sarki, sai suka kama hanyarsu, tauraron da suka gani a gabas kuwa yana tafe a gabansu, sai da ya kai inda yaron yake.10. Da suka ga tauraron, sai suka yi farin ciki ƙwarai.11. Suka shiga gidan, suka kuwa ga yaron tare da mahaifiyarsa Maryamu. Suka durƙusa har ƙasa, suka yi masa sujada. Sa’an nan suka kunce dukiyarsu, suka miƙa masa kyautai na zinariya da na turare da na mur.12. Bayan an gargaɗe su cikin mafarki kada su koma wurin Hiridus, sai suka koma ƙasarsu ta wata hanya dabam.13. Bayan sun tafi, sai mala’ikan Ubangiji ya bayyana ga Yusuf a mafarki ya ce, “Tashi, ka ɗauki yaron da mahaifiyarsa, ku gudu zuwa Masar. Ku zauna a can sai na gaya muku, gama Hiridus zai nemi yaron don yă kashe.”14. Sai Yusuf ya tashi, ya ɗauki yaron da mahaifiyarsa da dad dare suka tafi Masar,15. inda ya zauna har sai da Hiridus ya mutu. Ta haka kuwa aka cika abin da Ubangiji ya faɗa ta bakin annabin cewa, “Daga Masar na kira ɗana.”16. Da Hiridus ya gane cewa Masanan nan sun yi masa wayo, sai ya husata ƙwarai, ya yi umarni cewa a karkashe dukan ’yan yara maza da suke a Betlehem da kewayenta, daga masu shekara biyu zuwa ƙasa, bisa ga lokacin da ya sami labarin daga Masanan nan.17. Sai abin da aka faɗa ta bakin annabi Irmiya ya cika, cewa,18. “An ji murya a Rama, tana kuka da makoki mai tsanani, Rahila ce take kuka domin ’ya’yanta, an kāsa ta’azantar da ita, don ba su.”19. Bayan Hiridus ya mutu, sai mala’ikan Ubangiji ya bayyana ga Yusuf a mafarki a Masar,20. ya ce, “Tashi, ka ɗauki yaron da mahaifiyarsa ku tafi ƙasar Isra’ila, domin waɗanda suke neman ran yaron sun mutu.”21. Sai ya tashi, ya ɗauki yaron da mahaifiyarsa suka tafi ƙasar Isra’ila.22. Amma da ya ji Arkelawus ne yake mulki a Yahudiya a matsayin wanda ya gāji mahaifinsa Hiridus, sai ya ji tsoron zuwa can. Bayan an gargaɗe shi a mafarki, sai ya ratse zuwa gundumar Galili,23. ya je ya zauna a wani garin da ake kira Nazaret. Ta haka aka cika abin da aka faɗa ta bakin annabawa cewa, “Za a ce da shi Banazare.” Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.