Baibul a cikin shekara guda Janairu 28Fitowa 5:1-231. Daga bisani sai Musa da Haruna suka tafi wurin Fir’auna suka ce, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, ‘Bari mutanena su tafi domin su yi mini biki a hamada.’ ”2. Fir’auna ya ce, “Wane ne Ubangiji da zan yi biyayya da shi, har in bar Isra’ila su tafi? Ban san Ubangiji ba, kuma ba zan bar Isra’ila su tafi ba.”3. Sai suka ce, “Allah na Ibraniyawa ya sadu da mu. Yanzu bari mu ɗauki tafiyar kwana uku cikin hamada domin mu miƙa hadaya ga Ubangiji Allahnmu, don kada yă buga mu da annoba ko takobi.”4. Amma sarkin Masar ya ce wa, “Musa da Haruna, don me kuke hana mutane yin aikinsu? Ku koma wurin aikinku!”5. Sa’an nan Fir’auna ya ce, “Ga shi mutane sun yi yawa a ƙasar Masar, ku kuma yanzu kuna so ku hana su yin aiki.”6. A wannan rana Fir’auna ya ba da wannan umarni wa shugabannin masu gandu,7. “Kada ku ƙara ba wa mutanen ciyawar tattaka domin su yi tubula, bari su tafi su tattara tattaka da kansu.8. Ku kuma bukace su su yi tubula daidai yawan tubalin da suka saba yi, kada ku rage. Ragwaye ne, shi ya sa suke kuka cewa, ‘Bari mu tafi mu yi hadaya ga Allahnmu.’9. Ku sa waɗannan mutane su yi aiki mai tsanani sosai, don kada su sami zarafin kasa kunne ga maganganun ƙarya.”10. Sai shugabannin masu aikin gandu suka fita suka gaya wa mutanen Isra’ila, “Ga abin da Fir’auna ya ce, ‘Ba zan ƙara ba ku tattaka ba.11. Ku tafi ku nemo wa kanku tattaka duk inda za ku samu, amma ba za a rage aikinku ba ko kaɗan.’ ”12. Saboda haka mutane suka warwatsu ko’ina a Masar domin tattara bunnun da za su yi amfani da su, maimakon tattaka.13. Shugabannin gandu suka dinga matsa musu suna cewa, “Ku cika aikin da aka bukace ku na kowace rana kamar yadda kuke yi sa’ad da kuke da tattaka.”14. Manyan Isra’ilawa waɗanda shugabannin gandun Fir’auna suka naɗa, suka sha dūka, aka kuma yi musu tambayoyi ana cewa, “Don me ba ku cika yawan tubula na jiya da na yau kamar yadda kuka saba ba?”15. Sai manyan Isra’ila masu bi da aikin gandu suka tafi wurin Fir’auna suka yi roƙo suna cewa, “Don me kake yi wa bayinka haka?16. Ba a ba wa bayinka tattaka, duk da haka ana ce mana, ‘Ku yi tubula!’ Ana wa bayinka dūka, amma fa laifin na mutanenka ne.”17. Fir’auna ya ce, “Ku ragwaye ne! Shi ya sa kuke cewa, ‘Bari mu tafi mu yi hadaya wa Ubangiji.’18. Ku ɓace yanzu daga nan, ku koma wurin aikinku. Ba za a ba ku tattaka ba, kuma dole ku fid da tubula kamar yadda kuka saba.”19. Manyan Isra’ilawa da suke bi da aikin gandu suka gane cewa sun shiga uku, sa’ad da aka gaya musu, “Ba za ku rage yawan tubulan da aka bukace ku ku yi na kowace rana ba.”20. Da suka bar Fir’auna, sai suka sadu da Musa da Haruna suna jira su sadu da su,21. sai suka ce, “Bari Ubangiji yă duba, yă kuma hukunta ku! Kun maishe mu abin ƙyama ga Fir’auna da bayinsa, kuka kuma sa musu takobi a hannunsu don su kashe mu.”22. Musa ya koma wurin Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji, don me ka kawo wahala a kan mutanen nan? Abin da ya sa ka aiko ni ke nan?23. Gama tun da na tafi wurin Fir’auna, na yi masa magana da sunanka, sai ya fara gasa wa mutanen nan azaba, ba ka kuma ceci mutanenka.”Fitowa 6:1-301. Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Yanzu za ka gan abin da zan yi da Fir’auna. Zan sa shi dole yă bar su su tafi, har ma yă iza ƙyeyarsu don su bar ƙasarsa!”2. Allah ya kuma ce wa Musa, “Ni ne Ubangiji.3. Na bayyana ga Ibrahim, ga Ishaku da kuma ga Yaƙub a matsayin Allah Maɗaukaki, amma sunan nan nawa Ubangiji, ban bayyana kaina a gare su ba.4. Na kuma kafa alkawari da su don in ba su ƙasar Kan’ana, inda suka yi zaman baƙunci.5. Ban da haka ma, na ji nishe-nishen Isra’ilawa, waɗanda Masarawa suka bautar, na kuma tuna da alkawarina.6. “Saboda haka, ka ce wa Isra’ilawa, ‘Ni ne Ubangiji, zan kuma fitar da ku daga bauta ta Masarawa. Zan ’yantar da ku daga zama bayinsu, da ƙarfina zan fanshe ku, in kawo hukunci mai zafi a kansu, don in cece ku.7. Zan ɗauke ku tamƙar mutanena, in kuma zama Allahnku. Sa’an nan za ku sani Ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga wahalar Masarawa.8. Zan kuwa kawo ku a ƙasar da na rantse da hannun da na ɗaga sama, cewa zan ba wa Ibrahim, wa Ishaku, da kuma wa Yaƙub. Zan ba da ita gare ku gādo. Ni ne Ubangiji.’ ”9. Musa ya faɗa wa Isra’ilawa wannan magana, amma ba su kasa kunne a gare shi ba, don ɓacin rai saboda tsananin aikin bauta.10. Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa,11. “Koma ka ce wa Fir’auna sarkin Masar, yă bar Isra’ilawa su fita daga ƙasarsa.”12. Amma Musa ya ce wa Ubangiji, “In Isra’ilawa ba su ji ni ba, yaya Fir’auna zai ji ni, da yake ina magana da ƙyar?”13. Ubangiji ya yi magana da Musa da Haruna game da Isra’ilawa da Fir’auna sarkin Masar, ya umarce su su fitar da Isra’ilawa daga Masar.14. Waɗannan su ne shugabannin iyalansu. ’Ya’yan Ruben maza ɗan farin Isra’ila su ne, Hanok da Fallu, Hezron da Karmi. Waɗannan su ne dangin Ruben.15. ’Ya’yan Simeyon maza su ne, Yemuwel, Yamin, Ohad, Yakin, Zohar da Sha’ul ɗan mutuniyar Kan’ana. Waɗannan su ne dangin Simeyon.16. Waɗannan su ne sunayen ’ya’yan Lawi maza bisa ga abin da aka rubuta, Gershon, Kohat da Merari. Lawi ya yi shekara 137.17. ’Ya’yan Gershon maza, bisa ga dangi su ne, Libni da Shimeyi.18. ’Ya’yan Kohat maza, su ne, Amram, Izhar, Hebron da Uzziyel. Kohat ya yi shekara 133.19. ’Ya’yan Merari maza, su ne, Mali da Mushi. Waɗannan su ne dangin Lawi bisa ga abin da aka rubuta.20. Amram ya auri ’yar’uwar mahaifinsa Yokebed, wadda ta haifa masa Haruna da Musa. Amram ya yi shekara 137.21. ’Ya’yan Izhar maza, su ne, Kora, Nefeg da Zikri.22. ’Ya’yan Uzziyel maza, su ne, Mishayel, Elzafan da Sitri.23. Haruna ya auri Elisheba, ’yar Amminadab, ’yar’uwar Nashon, sai ta haifa masa Nadab da Abihu, Eleyazar da Itamar.24. ’Ya’yan Kora maza, su ne, Assir, Elkana da Abiyasaf. Waɗannan su ne dangin Kora.25. Eleyazar ɗan Haruna, ya auri ɗaya daga cikin ’yan matan Futiyel, sai ta haifa masa Finehas. Waɗannan su ne shugabannin iyalan Lawi, dangi, dangi.26. Wannan Haruna da Musa ne, waɗanda Ubangiji ya yi musu magana ya ce, “Ku fitar da Isra’ilawa daga Masar ɓangare-ɓangare.”27. Su ne suka yi magana da Fir’auna sarkin Masar game da fitar da Isra’ilawa daga Masar, wannan Musa da Haruna.28. Ana nan, sa’ad da Ubangiji ya yi magana da Musa a Masar,29. ya ce masa, “Ni ne Ubangiji. Sai ka faɗa wa Fir’auna sarkin Masar kome da na faɗa maka.”30. Amma Musa ya ce wa Ubangiji, “Ni mai nauyin baki ne, ina magana da ƙyar, ƙaƙa Fir’auna zai kasa kunne gare ni?”Zabura 16:7-117. Zan yabi Ubangiji, wanda yake ba ni shawara; ko da dare ma zuciyata kan koya mini.8. Kullum nakan sa Ubangiji a gabana. Gama yana a hannun damana, ba zan jijjigu ba.9. Saboda haka zuciyata tana murna harshena kuma yana farin ciki; jikina kuma zai zauna lafiya,10. domin ba za ka yashe ni a kabari ba, ba kuwa za ka bar Mai Tsarkinka yă ruɓa ba.11. Ka sanar da ni hanyar rai; za ka cika ni da farin ciki a gabanka, da madawwamin jin daɗi a hannun damarka.Karin Magana 5:7-147. Yanzu fa, ’ya’yana, ku saurare ni; kada ku juye daga abin da nake faɗa.8. Ku yi nesa da hanyarta, kana ku je kusa da ƙofar gidanta,9. don kada ku ba da ƙarfi mafi kyau ga waɗansu da kuma shekarunku ga wani marar imani,10. don kada baƙi su yi biki a kan dukiyarku wahalarku ta azurta gidan wani mutum dabam.11. A ƙarshen rayuwarku za ku yi ta nishi, sa’ad da namanku da jikinku suka zagwanye.12. Za ku ce, “Me ya sa na ƙi horo! Me ya sa zuciyata ta ƙi gyara!13. Ban yi biyayya da malamaina ba ko in saurari masu koyar da ni.14. Na zo gab da hallaka gaba ɗaya a tsakiyar dukan taron.”Mattiyu 18:21-3521. Sai Bitrus ya zo wurin Yesu ya yi masa tambaya ya ce, “Ubangiji, sau nawa zan yafe wa ɗan’uwana sa’ad da ya yi mini zunubi? Har sau bakwai?”22. Yesu amsa ya ce, “Ina gaya maka, ba sau bakwai ba, amma sau saba’in da bakwai.23. “Saboda haka, mulkin sama yana kama da wani sarki wanda ya so yă yi ƙididdigar dukiyarsa da take a hannun bayinsa.24. Da ya fara ƙididdigar, sai aka kawo masa wani wanda yake bin bashin talenti dubu goma.25. Da yake bai iya biya ba, sai maigida ya umarta a sayar da shi da matarsa da yaransa da kuma duk abin da yake da shi, a biya bashin.26. “Bawan ya durƙusa a gabansa. Ya yi roƙo ya ce, ‘Ka yi mini haƙuri, zan biya ka ƙaf.’27. Maigidan bawan ya ji tausayinsa, ya yafe masa bashin, ya kuma sake shi.28. “Amma da wannan bawa ya fita, sai ya gamu da wani abokin bautarsa wanda yake binsa bashin dinari ɗari. Sai ya cafke shi, ya shaƙe shi a wuya yana cewa, ‘Biya ni abin da nake binka!’29. “Wannan abokin bautarsa ya durƙusa ya roƙe shi, ‘Ka yi mini haƙuri, zan biya ka.’30. “Amma ya ƙi. A maimako, sai ya je ya sa aka jefa shi a kurkuku, har yă biya bashin.31. Sa’ad da sauran bayin suka ga abin da ya faru, abin ya ɓata musu rai ƙwarai, sai suka tafi suka faɗa wa maigidansu dukan abin da ya faru.32. “Sai maigidan ya kira wannan bawa. Ya ce, ‘Kai mugun bawa, na yafe duk bashin da nake binka domin ka roƙe ni.33. Ashe, bai kamata kai ma ka ji tausayin abokin bautarka yadda na yi maka ba?’34. Cikin fushi, maigidan ya miƙa shi ga ma’aikatan kurkuku su gwada masa azaba, har yă biya dukan bashin da ake binsa.35. “Haka Ubana da yake cikin sama zai yi da kowannenku, in ba ku yafe wa ’yan’uwanku daga zuciyarku ba.” Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.