Baibul a cikin shekara guda Janairu 4Farawa 7:1-241. Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Nuhu. “Shiga jirgin, kai da dukan iyalinka, gama na ga kai mai adalci ne a wannan zamani.2. Ka ɗauki bakwai na kowace iri tsabtaccen dabba tare da kai, namiji da ta mace, da kuma biyu na kowace dabba marar tsabta, namiji da ta mace,3. da kuma bakwai na kowane iri tsuntsu, namiji da ta mace, domin a bar kowane irinsu da rai a dukan duniya.4. Kwana bakwai daga yanzu zan aiko da ruwa a duniya yini arba’in da dare arba’in, zan kuma kawar da kowace halitta mai rai da na yi daga doron ƙasa.”5. Nuhu ya aikata duk abin da Ubangiji ya umarce shi.6. Nuhu yana da shekaru 106 ne sa’ad da aka yi ambaliya ruwa a duniya.7. Nuhu da matarsa da ’ya’yansa da matansu, suka shiga jirgi domin su tsira daga ruwa ambaliya.8. Biyu-biyu daga dabbobi masu tsabta da marasa tsabta, da tsuntsaye da kuma dukan halittu masu rarrafe a ƙasa,9. namiji da ta mace, suka zo wurin Nuhu, suka shiga jirgi, kamar yadda Allah ya umarce Nuhu.10. Bayan kwana bakwai kuwa ambaliya ruwa ta sauko a bisa duniya.11. A ranar sha bakwai ga wata na biyu, na shekara ta ɗari shida na rayuwar Nuhu, a ran nan sai dukan maɓuɓɓugai na manyan zurfafa suka fashe, tagogin sammai suka buɗe.12. Ruwa yana ta kwararowa bisa duniya, yini arba’in da dare arba’in.13. A wannan rana Nuhu tare da matarsa da ’ya’yansa maza, Shem, Ham da Yafet da matansu uku suka shiga jirgi.14. Tare da su kuwa, akwai kowane naman jeji bisa ga irinsa, da dukan dabbobin gida bisa ga irinsu, da kowace halitta mai rarrafe a ƙasa bisa ga irinta, da kowane tsuntsun gida da na jeji bisa ga irinsa, da dukan abu mai fiffike.15. Biyu-biyu na dukan halittu masu numfashi suka zo wurin Nuhu, suka shiga jirgi.16. Dabbobi da kowane abu mai rai da suka shiga ciki, namiji ne da ta mace, yadda Allah ya umarci Nuhu. Sa’an nan Ubangiji ya kulle jirgin daga baya.17. Kwana arba’in ambaliya ta yi ta saukowa a duniya, sa’ad da ruwa ya yi ta ƙaruwa sai ya yi ta ɗaga jirgin sama, ya kuwa tashi can bisa duniya.18. Ruwa ya taso, ya ƙaru ƙwarai a duniya, jirgin kuma ya yi ta yawo a bisa ruwa.19. Ruwa ya ƙaru ƙwarai a duniya, ya kuma rufe dukan duwatsu masu tsawo a ƙarƙashin sammai.20. Ruwan ya taso ya rufe duwatsu, zurfin ruwa daga duwatsun zuwa inda jirgin yake ya fi ƙafa ashirin.21. Kowane abu mai rai da yake tafiya a duniya ya hallaka, tsuntsaye, dabbobin gida, namun jeji, da dukan masu rarrafe waɗanda suke rarrafe a duniya, da kuma dukan mutane.22. Kome a busasshiyar ƙasa da yake numfashi a hancinsa ya mutu.23. Aka kawar da kowane abu mai rai, mutane da dabbobi da halittu masu rarrafe a ƙasa, da tsuntsayen sama a doron ƙasa, duka aka kawar da su daga duniya. Nuhu kaɗai aka bari da waɗanda suke tare da shi a cikin jirgi.24. Ruwa ya mamaye duniya har kwana ɗari da hamsin.Farawa 8:1-221. Amma Allah ya tuna da Nuhu da dukan namun jeji da dabbobin da suke tare da shi a cikin jirgi, ya kuma aika da wata iska ta hura dukan duniya, ruwan kuwa ya janye.2. Aka toshe maɓuɓɓugan zurfafa da ƙofofin ambaliyar sammai, ruwan sama kuma ya daina saukowa daga sarari.3. Ruwan ya janye a hankali daga ƙasa. A ƙarshen kwanaki ɗari da hamsin ɗin, ruwan ya ragu.4. A rana ta goma sha bakwai ga watan bakwai, jirgin ya sauka a duwatsun Ararat.5. Ruwan ya ci gaba da janyewa har watan goma. A rana ta fari ga watan goma kuwa ƙwanƙolin duwatsun suka bayyana.6. Bayan kwana arba’in, sai Nuhu ya buɗe tagar jirgin da ya yi,7. ya saki hankaka. Hankaka ya yi ta kai da kawowa har sai da ruwa ya shanye a duniya.8. Sai ya saki kurciya don yă ga in ruwan ya janye daga doron ƙasa.9. Amma kurciyar ba tă sami inda za tă sa ƙafafunta ba gama akwai ruwa a dukan doron ƙasa, saboda haka ta komo wurin Nuhu a jirgi. Ya miƙa hannunsa ya ɗauko kurciyar ya shigar da ita wurinsa a cikin jirgi.10. Ya ƙara jira kwana bakwai, sai ya sāke aiken kurciyar daga jirgi.11. Sa’ad da kurciya ta komo wurinsa da yamma, sai ga ɗanyen ganyen zaitun da ta tsinko a bakinta! Sa’an nan Nuhu ya san cewa ruwa ya janye daga duniya.12. Ya ƙara jira kwana bakwai, sai ya sāke aiken kurciyar, amma a wannan ƙaro ba tă komo wurinsa ba.13. A rana ta fari ga wata na fari wanda Nuhu ya cika shekaru 601, ruwa ya shanye a ƙasa. Sai Nuhu ya buɗe murfin jirgin, ya ga cewa doron ƙasa ya bushe.14. A ran ashirin da bakwai ga wata na biyu, ƙasa ta bushe ƙaƙaf.15. Sa’an nan Allah ya ce wa Nuhu,16. “Fito daga jirgin, kai da matarka da ’ya’yanka maza da matansu.17. Ka fitar da kowane iri halitta mai rai da take tare da kai waje, tsuntsaye, dabbobi, da dukan halittu masu rarrafe a ƙasa, don su yi ta haihuwa, su yi yawa, su ƙaru a duniya.”18. Sai Nuhu ya fito tare da matarsa da ’ya’yansa maza da matan ’ya’yansa,19. da kowace irin dabba, da kowane mai rarrafe, da kowane irin tsuntsu, da kowane irin abu da yake tafiya a bisa duniya, suka fito daga jirgi daki-daki bisa ga irinsu.20. Sai Nuhu ya gina bagaden hadaya ga Ubangiji, ya ɗiba waɗansu dabbobi da tsuntsaye masu tsabta, ya yi hadaya ta ƙonawa da su a kan bagaden.21. Da Ubangiji ya ji ƙanshi mai daɗi, sai ya ce a zuciyarsa, “Ba zan ƙara la’anta ƙasa saboda mutum ba, ko da yake dukan tunanin zuciyar mutum mugu ne tun yana ƙarami. Ba kuwa zan ƙara hallaka dukan halittu masu rai, kamar yadda na yi ba.22. “Muddin duniya tana nan, lokacin shuki da na girbi, lokacin sanyi da na zafi, lokacin damina da na rani, dare da rana ba za su daina ba.”Zabura 3:1-41. Ya Ubangiji, abokan gābana nawa ne! Su nawa suke gāba da ni!2. Da yawa suna magana a kaina suna cewa, “Allah ba zai cece shi ba.”3. Amma kai ne garkuwa kewaye da ni, ya Ubangiji; ka ba ni ɗaukaka ka kuma ɗaga kaina.4. Ga Ubangiji na yi kuka mai ƙarfi, ya kuwa amsa mini daga tudunsa mai tsarki.Karin Magana 1:20-2220. Hikima tana kira da ƙarfi a kan titi, tana ɗaga muryarta a dandalin taron jama’a;21. tana kira da ƙarfi a kan tituna masu surutu, tana yin jawabinta a hanyoyin shiga gari.22. “Har yaushe ku da kuke marasa azanci za ku ci gaba a hanyoyinku marasa azanci? Har yaushe ku masu ba’a za ku yi ta murna cikin ba’arku wawaye kuma ku ƙi ilimi?Mattiyu 4:1-251. Sa’an nan Ruhu ya kai Yesu cikin hamada don Iblis yă gwada shi.2. Bayan ya yi azumi yini arba’in da kuma dare arba’in, sai ya ji yunwa.3. Sai mai gwajin ya zo wurinsa ya ce, “In kai Ɗan Allah ne, ka ce wa duwatsun nan su zama burodi.”4. Yesu ya amsa ya ce, “A rubuce yake cewa, ‘Ba da abinci kaɗai mutum yake rayuwa ba, sai dai da kowace kalmar da take fitowa daga bakin Allah.’ ”5. Sai Iblis ya kai shi birni mai tsarki, ya kai shi can wuri mafi tsayi duka na haikali.6. Ya ce, “In kai Ɗan Allah ne, yi tsalle ka sauka ƙasa. Gama a rubuce yake, “ ‘Zai umarci mala’ikunsa game da kai, za su tallafe ka da hannuwansu, don kada ka buga ƙafarka a kan dutse.’ ”7. Yesu ya amsa masa ya ce, “A rubuce yake kuma cewa, ‘Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.’ ”8. Har wa yau, Iblis ya kai shi bisa wani dutse mai tsawo sosai, ya nunnuna masa dukan mulkokin duniya da darajarsu.9. Ya ce, “Zan ba ka dukan wannan, in za ka durƙusa ka yi mini sujada.”10. Sai Yesu ya ce masa, “Rabu da ni, Shaiɗan! Gama a rubuce yake, ‘Yi wa Ubangiji Allahnka sujada, shi kaɗai kuma za ka bauta wa.’ ”11. Sa’an nan Iblis ya bar shi, mala’iku kuwa suka zo suka yi masa hidima.12. Da Yesu ya ji labari cewa an kulle Yohanna a kurkuku, sai ya koma zuwa Galili.13. Ya bar Nazaret, ya je ya zauna a Kafarnahum, wadda take a bakin tafki wajen Zebulun da Naftali14. don a cika abin da aka faɗa ta bakin annabi Ishaya cewa,15. “Ƙasar Zebulun da ƙasar Naftali, da kuke a hanyar zuwa tekun Galili, a ƙetaren Urdun, wannan yankin Galili ta Al’ummai,16. mutanen da suke zama cikin duhu sun ga babban haske; haske kuma ya haskaka a kan waɗanda suke zama a inuwar mutuwa.”17. Tun daga wannan lokaci, Yesu ya fara wa’azi yana cewa, “Ku tuba, gama mulkin sama ya yi kusa.”18. Da Yesu yana kan tafiya a bakin Tekun Galili, sai ya ga waɗansu ’yan’uwa guda biyu, Siman wanda ake kira Bitrus da ɗan’uwansa Andarawus. Suna jefa abin kamun kifi a tafki, gama su masunta ne.19. Sai Yesu ya ce, “Zo, ku bi ni, ni kuwa zan mai da ku masu jan mutane zuwa wurina.”20. Nan da nan suka bar abin kamun kifinsu suka bi shi.21. Da ya ci gaba daga nan, sai ya ga waɗansu ’yan’uwa guda biyu, Yaƙub ɗan Zebedi da ɗan’uwansa Yohanna. Suna cikin jirgin ruwa tare da mahaifinsu Zebedi, suna shirya abin kamun kifinsu. Yesu ya kira su,22. nan take suka bar jirgin ruwan da mahaifinsu suka kuwa bi Yesu.23. Yesu ya zazzaga dukan Galili, yana koyarwa a cikin majami’unsu, yana wa’azin labari mai daɗi na mulkin sama, yana kuma warkar da kowace cuta da rashin lafiyar mutane.24. Labarinsa ya bazu ko’ina a Suriya, mutane kuwa suka kawo masa dukan waɗanda suke fama da cututtuka iri-iri, da waɗanda suke da zafin ciwo, da masu aljanu, da waɗanda suke masu farfaɗiya, da shanyayyu, ya kuwa warkar da su.25. Taron mutane mai yawa daga Galili, Dekafolis, Urushalima, Yahudiya da kuma yankin hayin Urdun suka bi shi. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.