Baibul a cikin shekara guda Janairu 6Farawa 11:1-321. To, a lokacin, yaren mutanen duniya ɗaya ne, maganarsu kuma ɗaya ce.2. Yayinda mutane suke ta yin ƙaura zuwa gabas, sai suka sami fili a Shinar, suka zauna a can.3. Suka ce wa juna, “Ku zo, mu yi tubula, mu gasa su sosai.” Suka yi amfani da tubula a maimakon duwatsu, kwalta kuma a maimakon laka.4. Sa’an nan suka ce, “Ku zo, mu gina wa kanmu birni da hasumiyar da za tă kai har sammai, domin mu yi wa kanmu suna, don kada mu warwatsu ko’ina a doron ƙasa.”5. Sai Ubangiji ya sauko don yă ga birni da kuma hasumiyar da mutanen suke gini.6. Ubangiji ya ce, “Ga su, su jama’a ɗaya ce, su duka kuwa harshensu guda ne. Wannan kuwa masomi ne kawai na abin da za su iya yi, babu kuma abin da suka yi shirya yi da ba za su iya yi ba.7. Zo, mu sauka, mu rikitar da harshensu don kada su fahimci juna.”8. Saboda haka Ubangiji ya watsar da su daga wurin zuwa ko’ina a doron ƙasa, suka kuwa daina gina birnin.9. Shi ya sa aka kira birnin Babel, domin a can ne Ubangiji ya rikitar da harshen dukan duniya. Daga can Ubangiji ya watsar da su ko’ina a doron ƙasa.10. Wannan shi ne labarin Shem. Shekara biyu bayan ambaliya, sa’ad da Shem ya yi shekara 100, sai ya haifi Arfakshad.11. Bayan ya haifi Arfakshad, Shem ya yi shekara 500, ya haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.12. Sa’ad da Arfakshad ya yi shekara 35, sai ya haifi Shela.13. Bayan ya haifi Shela kuwa, Arfakshad ya yi shekara 403, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.14. Sa’ad da Shela ya yi shekaru 30, sai ya haifi Eber.15. Bayan ya haifi Eber, Shela ya yi shekara 403, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.16. Sa’ad da Eber ya yi shekaru 34, sai ya haifi Feleg.17. Bayan ya haifi Feleg, Eber ya yi shekara 430, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.18. Sa’ad da Feleg ya yi shekaru 30, sai ya haifi Reyu.19. Bayan ya haifi Reyu, Feleg ya yi shekara 209, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.20. Sa’ad da Reyu ya yi shekaru 32, sai ya haifi Serug.21. Bayan ya haifi Serug, Reyu ya yi shekara 207, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.22. Sa’ad da Serug ya yi shekaru 30, sai ya haifi Nahor.23. Bayan ya haifi Nahor, Serug ya yi shekara 200, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.24. Sa’ad da Nahor ya yi shekaru 29, sai ya haifi Tera.25. Bayan ya haifi Tera, Nahor ya yi shekara 119, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.26. Bayan Tera ya yi shekaru 70, sai ya haifi Abram, Nahor da Haran.27. Wannan ita ce zuriyar Tera. Tera ya haifi Abram, Nahor da Haran. Haran kuma ya haifi Lot.28. Yayinda mahaifinsa Tera yana da rai, Haran ya rasu a Ur ta Kaldiyawa, a ƙasar haihuwarsa.29. Abram da Nahor suka yi aure. Sunan matar Abram, Saira ne, sunan matar Nahor kuwa Milka; ita ’yar Haran ce, mahaifin Milka da Iska.30. Saira kuwa bakararriya ce, ba ta da yara.31. Tera ya ɗauki ɗansa Abraham, jikansa Lot ɗan Haran, da surukarsa Saira, matar Abram, tare kuwa suka bar Ur ta Kaldiyawa, don su tafi Kan’ana. Amma sa’ad da suka zo Haran sai suka zauna a can.32. Tera yi shekaru 205, ya kuma mutu a Haran.Farawa 12:1-201. Ubangiji ya ce wa Abram, “Tashi ka bar ƙasarka, da mutanenka, da iyalin mahaifinka, ka tafi ƙasar da zan nuna maka.2. “Zan mai da kai al’umma mai girma, zan kuma albarkace ka; zan sa sunanka yă zama mai girma, ka kuma zama sanadin albarka.3. Zan albarkaci duk wanda ya albarkace ka, in kuma la’anci duk wanda ya la’anta ka, dukan mutanen duniya za su sami albarka ta wurinka.”4. Saboda haka Abram ya tashi yadda Ubangiji ya faɗa masa; Lot ma ya tafi tare da shi. Abram yana da shekaru 75, sa’ad da ya tashi daga Haran.5. Abram ya ɗauki matarsa Saira da Lot ɗan ɗan’uwansa, da dukan mallakar da suka tattara, da kuma mutanen da suka samu a Haran, suka kama hanya zuwa ƙasar Kan’ana.6. Abram ya ratsa ƙasar har zuwa wurin babban itace na More a Shekem. A lokacin Kan’aniyawa suna a ƙasar.7. Ubangiji ya bayyana ga Abram ya ce, “Ga zuriyarka ne zan ba da wannan ƙasa.” Saboda haka Abram ya gina bagade a can ga Ubangiji, wanda ya bayyana gare shi.8. Daga can, ya ci gaba zuwa wajen tuddai a gabashin Betel ya kafa tentinsa, Betel yana yamma, Ai, kuma a gabas. A can ya gina bagade ga Ubangiji ya kuma kira bisa sunan Ubangiji.9. Sa’an nan Abram ya tashi ya ci gaba da tafiya zuwa wajen Negeb.10. To, a lokacin, an yi yunwa a ƙasar, sai Abram ya gangara zuwa Masar don yă zauna a can na ɗan lokaci, domin yunwa ta yi tsanani.11. Yayinda yana gab da shiga Masar, sai ya ce wa matarsa Saira, “Na sani ke kyakkyawar mace ce.12. Sa’ad da Masarawa suka ganki, za su ce, ‘Wannan matarsa ce.’ Za su kuwa kashe ni, su bar ki da rai.13. Saboda haka ki ce ke ’yar’uwata ce, domin ta dalilinki a mutunta ni, a kuma bar ni da rai.”14. Sa’ad da Abram ya isa Masar, Masarawa suka ga cewa Saira kyakkyawa mace ce ƙwarai.15. Sa’ad da fadawan Fir’auna suka gan ta kuwa, sai suka yabe ta wajen Fir’auna, aka kuwa kawo ta cikin fadarsa.16. Ya mutunta Abram sosai saboda ita, Abram kuwa ya mallaki tumaki da shanu, da jakuna maza da mata, da bayi maza da mata, da kuma raƙuma.17. Amma Ubangiji ya wahalar da Fir’auna da gidansa da cututtuka masu zafi saboda Saira, matar Abram.18. Saboda haka Fir’auna ya kira Abram ya ce, “Me ke nan ka yi mini? Me ya sa ba ka faɗa mini cewa ita matarka ce ba?19. Don me ka ruɗe ni cewa, ‘Ita ’yar’uwata ce,’ har na ɗauke ta tă zama matata? To, ga matarka. Ɗauke ta ka tafi.”20. Sa’an nan Fir’auna ya yi wa mutanensa umarni a kan Abram, suka kuwa sallame shi tare da matarsa da kuma dukan abin da yake da shi.Zabura 4:1-31. Ka amsa mini sa’ad da na kira gare ka, Ya Allahna mai adalci. Ka ba ni sauƙi daga wahalata; ka ji tausayina ka kuma ji addu’ata.2. Har yaushe, ya ku mutane za ku mai da ɗaukakata abin kunya? Har yaushe za ku ƙaunaci ruɗu ku nemi allolin ƙarya?3. Ku san cewa Ubangiji ya keɓe masu tsoron Allah wa kansa; Ubangiji zai ji sa’ad da na yi kira gare shi.Karin Magana 1:28-3328. “Sa’an nan za su kira gare ni amma ba zan amsa ba; za su neme ni amma ba za su same ni ba.29. Da yake sun ƙi sani ba su kuwa zaɓi tsoron Ubangiji ba,30. da yake ba su karɓi shawarata ba suka kuwa yi kunnen ƙashi ga tsawatata,31. za su sami sakayyar abubuwan da suka yi su kuma ƙoshi da sakayyar makircinsu.32. Gama rashin hankalin marasa azanci zai kashe su, rashin kulawar wawaye kuma zai hallaka su;33. amma duk wanda ya saurare ni, zai zauna lafiya yă kuma kasance da rai kwance, ba tare da tsoron lahani ba.”Mattiyu 5:27-4827. “Kun dai ji an faɗa, ‘Kada ka yi zina.’28. Amma ina gaya muku, duk wanda ya dubi mace, sa’an nan ya yi sha’awarta a zuci, ya riga ya yi zina ke nan da ita a zuciyarsa.29. In idonka na dama yana sa ka yin zunubi, ƙwaƙule shi ka yar. Zai fiye maka ka rasa ɗaya daga cikin gaɓoɓin jikinka, da a jefa jikinka ɗungum a cikin jahannama ta wuta.30. In kuma hannunka na dama yana sa ka yin zunubi, yanke shi ka yar. Zai fiye maka ka rasa ɗaya daga cikin gaɓoɓin jikinka, da a jefa jikinka ɗungum a cikin jahannama ta wuta.31. “An kuma faɗa, ‘Duk wanda ya saki matarsa, dole yă ba ta takardar saki.’32. Amma ina gaya muku, duk wanda ya saki matarsa in ba a kan laifin zina ba, ya sa ta zama mazinaciya ke nan, kuma duk wanda ya auri macen da mijinta ya sake, shi ma yana zina ne.33. “Har wa yau dai kun ji an faɗa wa mutane a dā, ‘Kada ka karya alkawarinka, sai dai ka cika alkawaran da ka yi wa Ubangiji.’34. Amma ina gaya muku, Kada ku yi rantsuwa sam, ko da sama, domin kursiyin Allah ne;35. ko da ƙasa, domin matashin ƙafafunsa ne; ko kuma da Urushalima, domin birnin Babban Sarki ne.36. Kada kuma ka rantse da kanka, domin ba za ka iya mai da ko gashi ɗaya yă zama fari ko baƙi ba.37. Abin da ya kamata ku ce kawai, shi ne, I, ko A’a. Abin da ya wuce haka kuwa daga wurin Mugun nan yake.38. “Kun dai ji an faɗa, ‘Ido domin ido, haƙori kuma domin haƙori.’39. Amma ina gaya muku, Kada ku yi tsayayya da mugun mutum. In wani ya mare ka a kumatun dama, juya masa ɗayan ma.40. In kuma wani yana so yă yi ƙararka yă ƙwace rigarka, to, ba shi mayafinka ma.41. In wani ya tilasta ka yin tafiya mil ɗaya, to, tafi tare da shi mil biyu.42. Ka ba wa duk wanda ya roƙe ka abu, kada kuma ka hana wa wanda yake neman bashi daga gare ka.43. “Kun dai ji an faɗa, ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka, ka kuma ƙi abokin gābanka.’44. Amma ina gaya muku, ku ƙaunaci abokan gābanku kuma ku yi wa waɗanda suke tsananta muku addu’a,45. don ku zama ’ya’yan Ubanku na sama. Shi yakan sa ranarsa ta haskaka a kan mugaye da masu kirki; yakan kuma sako ruwan sama a bisa masu adalci da marasa adalci.46. In masoyarku kawai kuke ƙauna, wace lada ce gare ku? Ko masu karɓar haraji ma ba haka suke yi ba?47. In kuwa kuna gai da ’yan’uwanku ne kaɗai, me kuke yi fiye da waɗansu? Marasa bin Allah ma ba haka suke yi ba?48. Saboda haka sai ku zama cikakku, yadda Ubanku na sama yake cikakke. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.