Baibul a cikin shekara guda Oktoba 13Irmiya 11:1-231. Ga maganar da ta zo wa Irmiya daga wurin Ubangiji.2. “Ka saurari zancen wannan alkawari ka kuma faɗe su ga mutanen Yahuda da kuma waɗanda suke zaune a Urushalima.3. Ka faɗa musu cewa ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila yana cewa, ‘La’ananne ne wanda bai kula da zancen alkawarin nan ba,4. zancen da na umarci kakanni-kakanninku sa’ad da na fitar da su daga Masar, daga cikin tanderun narkewar ƙarfe.’ Na ce, ‘Ku yi mini biyayya ku kuma aikata kowane abin da na umarce ku, za ku kuwa zama mutanena, ni kuwa zan zama Allahnku.5. Sa’an nan zan cika rantsuwar da na yi wa kakanni-kakanninku, da zan ba su ƙasa mai zub da madara da kuma zuma’ ƙasar da kuka mallaka a yau.” Sai na amsa na ce, “Amin, Ubangiji.”6. Sai Ubangiji ya ce mini, “Ka yi shelar dukan maganan nan a biranen Yahuda da titunan Urushalima duka cewa, ‘Su saurari zancen alkawarin nan, su aikata.7. Daga lokacin da na fitar da kakanni-kakanninku daga Masar har yă zuwa yau, na gargaɗe su sau da sau, ina cewa, “Ku yi mini biyayya.”8. Amma ba su kasa kunne ko su saurara ba, a maimako, sai suka bi taurinkai na mugayen zukatansu. Saboda haka na kawo musu dukan la’anonin alkawarin da na riga na umarce su, su bi amma ba su kiyaye ba.’ ”9. Sa’an nan Ubangiji ya ce mini, “Akwai maƙarƙashiya a cikin mutanen Yahuda da waɗanda suke zaune a Urushalima.10. Sun koma ga zunuban kakanni kakanninsu, waɗanda suka ƙi su saurari maganata. Suka bi waɗansu alloli don su bauta musu. Da gidan Isra’ila da kuma gidan Yahuda duk sun take alkawarin da na yi da kakanni kakanninsu.11. Saboda haka ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Zan kawo masifa a kansu wadda ba za su iya tsere mata ba. Ko da yake suna kuka gare ni, ba zan saurare su ba.12. Garuruwan Yahuda da mutanen Urushalima za su tafi su yi kuka ga allolin da suke ƙona wa turare, amma ba za su taimake su ba sam sa’ad da masifar ta auku.13. Kuna da alloli masu yawa yadda kuke da garuruwa, ya Yahuda; kuma bagadan da kuka yi don ƙona turare wa allahn nan Ba’al abin kunya sun yi yawa kamar titunan Urushalima.’14. “Kada ka yi addu’a domin wannan mutane ko ka miƙa wani roƙo ko kuka dominsu, domin ba zan saurara ba sa’ad da suka kira gare ni a lokacin ƙuncinsu.15. “Mene ne ƙaunatacciyata take yi a haikali da yake ta yin ƙulle-ƙullen mugayen makircinta tare da mutane masu yawa? Tsarkakar nama zai iya kawar da hukuncinki? Sa’ad da kike yin muguntarki sa’an nan ki yi farin ciki.”16. Ubangiji ya kira ki itacen zaitun mai inuwa kyakkyawa mai ’ya’ya masu kyau. Amma da ƙugin babbar hadari zai cinna masa wuta, rassansa za su kakkarye.17. Ubangiji Maɗaukaki, wanda ya dasa ki, ya furta miki masifa, domin gidan Isra’ila da kuma gidan Yahuda sun aikata mugunta suka kuma tsokane ni in yi fushi ta wurin ƙona wa Ba’al turare.18. Domin Ubangiji ya bayyana mini maƙarƙashiyarsu, na santa, gama a wannan lokaci ya nuna mini abin da suke yi.19. Na kasance kamar ɗan rago marar faɗa wanda aka kai mayanka; ban gane cewa sun ƙulla mini maƙarƙashiya, suna cewa, “Bari mu lalatar da itacen duk da ’ya’yansa; bari mu datse shi daga ƙasar masu rai, har da ba za a ƙara tunawa da sunansa ba.”20. Amma, ya Ubangiji Maɗaukaki, kai da kake yin shari’a da adalci kake gwada zuciya da kuma tunani, ka sa in ga sakayyar da za ka yi musu, gama a gare ka na danƙa maganata.21. “Saboda haka ga abin da Ubangiji yana cewa game da mutanen Anatot, waɗanda suke neman ranka suna kuma cewa, ‘Kada ka yi annabci da sunan Ubangiji in ba haka za ka mutu a hannunmu’22. saboda haka ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, ‘Zan hukunta su. Samarinsu za su mutu ta wurin takobi, ’ya’yansu maza da mata kuwa ta wurin yunwa.23. Babu raguwar da za a bar musu, domin zan kawo masifa a kan mutanen Anatot a shekarar hukuncinsu.’ ”Irmiya 12:1-171. Kullum kai mai adalci ne, ya Ubangiji, sa’ad da na kawo ƙara a gabanka. Duk da haka zan yi magana da kai game da shari’arka. Me ya sa mugaye suke nasara? Me ya sa dukan maciya amana suke zama ba damuwa?2. Ka dasa su, sun kuwa yi saiwa; sun yi girma suna ba da ’ya’ya. Kullum sunanka yana a bakinsu amma kana nesa da zuciyarsu.3. Duk da haka ka san ni, ya Ubangiji; kana ganina ka kuma gwada tunanina game da kai. Ka ja su kamar tumakin da za a yanka! Ka ware su don ranar yanka!4. Har yaushe ƙasar za tă kasance busasshiya ciyawar kowane fili ta bushe? Domin waɗanda suke zaune cikinta mugaye ne, dabbobi da tsuntsaye sun hallaka. Ban da haka ma, mutane suna cewa, “Ba zai ga abin da yake faruwa da mu ba.”5. “In ka yi tsere da mutane a ƙafa suka kuma gajiyar da kai, yaya za ka yi gasa da dawakai? In ka yi tuntuɓe a lafiyayyiyar ƙasa, ƙaƙa za ka yi a kurmin Urdun?6. ’Yan’uwanka, iyalinka har su ma sun bashe ka; sun tā da kuka mai ƙarfi a kanka. Kada ka amince da su, ko da yake suna faɗa maganganu masu kyau game da kai.7. “Zan yashe gidana, in rabu da gādona; Zan ba da wadda nake ƙauna a hannuwan abokan gābanta.8. Gādona ya zama mini kamar zaki a kurmi. Yana mini ruri; saboda haka na ƙi shi.9. Ashe, gādona bai zama mini kamar dabbare dabbaren tsuntsu mai cin nama da sauran tsuntsaye masu cin nama suka kewaye shi da faɗa ba? Tafi ka tattaro dukan namun jeji; ka kawo su su ci.10. Makiyaya masu yawa za su lalace gonar inabina su tattake gonata; za su mai da gonata mai kyau kango marar amfani.11. Za tă zama kango, busasshiya da kuma kango a gabana; ƙasar duka za tă zama kango domin ba wanda ya kula.12. A kan dukan tsaunukan nan na hamada masu hallakarwa za su zo, gama takobin Ubangiji zai ci daga wannan iyaka ƙasa zuwa wancan; ba wanda zai zauna lafiya.13. Za su shuka alkama, su girbe ƙayayyuwa; za su gajiyar da kansu, ba za su kuwa sami kome ba. Saboda haka ku sha kunyar abin da kuka girbe saboda zafin fushin Ubangiji.”14. Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Game da dukan mugayen maƙwabtana waɗanda suka ƙwace gādon da na ba wa mutanena Isra’ila kuwa, zan tumɓuke su daga ƙasashensu zan kuma tumɓuke gidan Yahuda daga cikinsu.15. Amma bayan na tumɓuke su, zan sāke jin tausayi in komo da kowannensu zuwa gādonsa da kuma ƙasarsa.16. In kuma suka koyi al’amuran mutanena sosai suka kuma yi rantsuwa da sunana, suna cewa, ‘Muddin Ubangiji yana raye’ kamar yadda sun taɓa koya wa jama’ata yin rantsuwa da Ba’al, sa’an nan za su kahu a cikin jama’ata.17. Amma duk al’ummar da ba tă saurara ba, zan tumɓuke ta ɗungum in kuma hallaka ta,” in ji Ubangiji.Zabura 118:10-1410. Dukan al’ummai sun kewaye ni, amma a cikin sunan Ubangiji na hallaka su.11. Sun kewaye ni a kowane gefe, amma a cikin sunan Ubangiji na hallaka su.12. Sun rufe ni kamar ƙudan zuma, amma suka mutu nan da nan kamar ƙayayyuwa masu cin wuta; a cikin sunan Ubangiji na hallaka su.13. An ture ni baya na kusa fāɗuwa, amma Ubangiji ya taimake ni.14. Ubangiji ne ƙarfina da waƙata; ya zama mai cetona.Karin Magana 27:8-88. Kamar tsuntsun da ya ɓace daga sheƙarsa haka yake da mutumin da ya bar gidansa.Kolossiyawa 4:1-181. Masu bayi, ku riƙe bayinku da kyau da kuma daidai, domin kun san cewa ku ma kuna da Ubangiji a sama.2. Ku nace da yin addu’a, kuna zaman tsaro da kuma godiya.3. Ku kuma yi mana addu’a, mu ma, don Allah yă buɗe ƙofa saboda saƙonmu, don mu iya yin shelar asirin Kiristi, wanda saboda shi nake cikin sarƙoƙi.4. Ku yi addu’a yadda zan yi shelarsa, yadda ya kamata.5. Ku zama masu hikima a yadda kuke ma’amala da waɗanda suke ba masu bi ba; ku kuma yi amfani da kowane zarafi.6. Bari maganarku kullum ta zama da ladabi da kuma daɗin ji, domin ku san amsar da ta dace ku ba wa kowa.7. Tikikus shi ne ƙaunataccen ɗan’uwan nan, wanda ya yi aiki da aminci a hidimar Ubangiji tare da mu, zai kuwa faɗa muku dukan labari game da ni.8. Ina aikansa shi a gare ku musamman domin ku san yadda muke, yă kuma ƙarfafa muku zuciya.9. Yana zuwa tare da Onesimus, ƙaunatacce da kuma amintaccen mai bin nan, wanda yake ɗaya daga cikinku. Za su gaya muku dukan abin da yake faruwa a nan.10. Aristarkus yana a kurkuku tare da ni. Yana gaishe ku, haka ma Markus, wanda kakansa ɗaya ne da Barnabas. (Shi ne na riga na yi magana a kansa, na ce muku in ya zo, ku karɓe shi hannu biyu-biyu.)11. Yesu, wannan da muke kira Yustus, shi ma yana gaisuwa. Waɗannan ne kaɗai Yahudawa masu bi a cikin abokan aikina saboda mulkin Allah. Sun kuma zama da taimako a gare ni.12. Efafaras naku, mai hidimar Kiristi Yesu, yana gaisuwa. Kullum yana addu’a dominku sosai, don ku san cikakken abin da Allah yake so ku yi don kuma ku yi shi cikakke.13. Na tabbatar muku, cewa yana aiki ƙwarai dominku da kuma domin waɗanda suke a Lawodiseya da Hiyerafolis.14. Luka ƙaunataccen likitan nan, da kuma Demas suna gaishe ku.15. Ku miƙa gaisuwata ga ’yan’uwan da suke a Lawodiseya, musamman ga Nimfa da kuma ikkilisiyar da take taru a gidanta.16. Bayan an karanta muku wannan wasiƙa, ku tabbata an karanta ta kuma a ikkilisiyar Lawodiseyawa; ku ma ku karanta wasiƙar da ta zo daga Lawodiseya.17. Ku faɗa wa Arkiffus yă tabbata ya ƙarasa aikin da ya karɓa cikin Ubangiji.18. Ni Bulus ne nake rubuta muku wannan gaisuwa da hannuna. Ku tuna da sarƙoƙina. Alherin Allah yă kasance tare da ku. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.