Baibul a cikin shekara guda Oktoba 15Irmiya 15:1-211. Sai Ubangiji ya ce mini, “Ko da Musa da Sama’ila za su tsaya a gabana, zuciyata ba za tă komo ga mutanen nan ba. Ka kore su daga gabana! Su tafi!2. In kuma suka tambaye ka, ‘Ina za mu tafi?’ Sai ka faɗa musu, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, “ ‘Waɗanda aka ƙaddara ga mutuwa, ga mutuwa za su; waɗanda aka ƙaddara ga takobi, ga takobi za su; waɗanda aka ƙaddara ga yunwa, ga yunwa za su; waɗanda aka ƙaddara ga zaman bauta, ga zaman bauta za su.’3. “Zan aika musu da iri masu hallakarwa guda huɗu,” in ji Ubangiji, “takobi zai kashe, karnuka za su kwashe, tsuntsaye da namun jeji kuma su cinye su kuma hallaka.4. Zan sa su zama abin ƙyama ga dukan mulkokin duniya saboda abin da Manasse ɗan Hezekiya sarkin Yahuda ya aikata a Urushalima.5. “Wa zai ji tausayinki, ya Urushalima? Wa zai yi makoki dominki? Wa zai dakata ya tambayi lafiyarki?6. Kin ƙi ni,” in ji Ubangiji. “Ki ci gaba da ja da baya. Ta haka zan ɗibiya hannuwana a kanki in hallaka ki; ba zan ƙara nuna miki jinƙai ba.7. Zan sheƙe ki da abin sheƙewa a ƙofofin birnin ƙasar. Zan kawo baƙin ciki da hallaka a kan mutanena, gama ba su canja hanyoyinsu ba.8. Zan ƙara yawan gwaurayensu su fi yashin teku yawa. Da tsakar rana zan kawo mai hallakarwa a kan iyaye mata na samarinsu; farat ɗaya zan kawo musu wahala da razana.9. Mahaifiya ’ya’ya bakwai za tă suma ta ja numfashinta na ƙarshe. Ranarta zai fāɗi tun lokacin bai yi ba; za tă sha kunya a kuma wulaƙanta ta. Zan sa a kashe raguwa da takobi a gaban abokan gābansu,” in ji Ubangiji.10. Kaitona, mahaifiyata, da kika haife ni, mutumin da dukan ƙasa take faɗa take kuma gardama da shi! Ban ba da bashi ko in ci bashi ba, duk da haka kowa yana zagina.11. Ubangiji ya ce, “Tabbatacce zan cece ka don alheri; tabbatacce zan sa abokan gābanka su yi roƙo gare ka a lokacin masifa da kuma lokacin wahala.12. “Mutum zai iya karye ƙarfe ƙarfe daga arewa, ko tagulla?13. “Dukiyarku da arzikinku zan ba da su ganima, babu tara, saboda duka zunubanku ko’ina a ƙasar.14. Zan bautar da ku ga abokan gābanku a ƙasar da ba ku sani ba, gama fushina zai yi ƙuna kamar wuta da za tă yi ƙuna a kanku.”15. Ka gane, ya Ubangiji; ka tuna da ni ka kuma lura da ni. Ka yi mini ramuwa a kan masu tsananta mini. Cikin jimirinka, kada ka ɗauke ni; ka tuna yadda na sha zagi saboda kai.16. Sa’ad da maganganunka suka zo, na cinye su; suka zama abin farin ciki zuciyata kuma ta yi murna, gama ana kirana da sunanka, Ya Ubangiji Allah Maɗaukaki.17. Ban taɓa zauna a cikin ’yan tawaye ba, ban taɓa yi murna da su ba; na zauna ni kaɗai domin hannunka yana a kaina ka kuma sa na cika da haushi.18. Me ya sa wahalata ba ta ƙarewa mikina kuma ba ya warkuwa? Za ka zama mini kamar rafi mai yaudara ne, kamar maɓulɓulan da ta kafe ne?19. Saboda haka ga abin da Ubangiji yana cewa, “In ka tuba, zan maido da kai don ka bauta mini; in ka ambaci maganganu masu kyau, ba marasa kyau ba, za ka zama kakakina. Bari wannan mutane su juyo gare ka, amma kada ka juye gare su.20. Zan mai da kai katanga ga wannan mutane, katanga mai ƙarfi na tagulla; za su yi yaƙi da kai amma ba za su yi nasara a kanka ba, gama ina tare da kai don in kuɓutar in kuma cece ka,” in ji Ubangiji.21. “Zan cece ka daga hannuwan mugaye in ɓamɓare ka daga hannun marasa tausayi.”Irmiya 16:1-211. Sai maganar Ubangiji ta zo mini cewa,2. “Kada ka yi aure ka haifi ’ya’ya maza da mata a wannan wuri.”3. Gama ga abin da Ubangiji yana cewa game da ’ya’ya maza da matan da aka haifa a wannan ƙasa da kuma game da matan da suke iyayensu da suke mazan da iyayensu.4. “Za su mutu da muguwar cuta. Ba za a yi kuka dominsu ba, ba kuwa za a binne su ba, amma za a bar su a juji. Takobi da yunwa ne za su hallaka su, gawawwakinsu za su zama abincin tsuntsayen sararin sama da kuma namun jeji na duniya.”5. Gama ga abin da Ubangiji yana cewa, “Kada ka shiga gidan da akwai abincin makoki; kada ka tafi ka yi makoki ko ka nuna juyayi, domin na janye albarkata, ƙaunata da tausayina daga wannan mutane,” in ji Ubangiji.6. “Manya da ƙanana duka za su mutu a wannan ƙasa. Ba za a binne su ba, ba kuwa za a yi makokinsu ba, kuma ba wanda zai tsaga kansa ko ya aske kansa saboda su.7. Ba wanda zai ba da abinci don yă ta’azantar da waɗanda suke makoki saboda matattu, kai, ko saboda mahaifi ko mahaifiya ma ba kuwa wani da zai ba da abin sha don yă ta’azantar da su.8. “Kada kuma ka shiga gidan da ake biki ka zauna don ci da sha.9. Gama ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa a idanunka da kuma a kwanakinka zan kawo ƙarshen muryar farin ciki da murna da kuma muryoyin amarya da ango a wannan wuri.10. “Sa’ad da ka faɗa wa waɗannan mutane wannan duka suka kuma tambaye ka, ‘Me ya sa Ubangiji ya ƙaddara irin wannan babban masifa a kanmu? Wace mugunta muka yi? Wane zunubi muka aikata wa Ubangiji Allahnmu?’11. Sai ka ce musu, ‘Wannan ya zama haka domin kakanninku sun rabu da ni,’ in ji Ubangiji, ‘suka bi waɗansu alloli suka kuma bauta musu. Suka rabu da ni, ba su kuwa kiyaye dokata ba.12. Amma kun yi laifi fiye da kakanninku. Duba yadda kowannenku yana bin taurin muguwar zuciyarsa a maimakon yin mini biyayya.13. Saboda haka zan fitar da ku daga wannan ƙasa zuwa wata ƙasar da ku da kakanninku ba ku taɓa sani ba, a can kuwa za ku bauta wa waɗansu alloli dare da rana, gama ba zan nuna muku tagomashi ba.’14. “Amma fa, kwanaki suna zuwa,” in ji Ubangiji, “da mutane ba za su ƙara cewa, ‘Muddin Ubangiji yana raye, wanda ya fitar da Isra’ilawa daga Masar,’15. amma za su ce, ‘Muddin Ubangiji yana raye, wanda ya fitar da Isra’ilawa daga ƙasar arewa da kuma daga dukan ƙasashe da ya kora su.’ Gama zan komo da su zuwa ƙasar da na ba wa kakanninsu.16. “Amma yanzu zan aiko a kira masunta masu yawa su zo,” in ji Ubangiji, “za su kuma kama su. Bayan wannan zan aiko a kira mafarauta su zo, su farauce su daga kowane dutse da tudu da kuma daga kogwannin duwatsu.17. Idanuna suna a kan dukan hanyoyinsu; ba a ɓoye suke daga gare ni, kuma zunubansu ba a ɓoye suke a idanuna ba.18. Zan riɓaɓɓanya sakayyar da zan yi musu saboda muguntarsu da zunubinsu, domin sun ƙazantar da ƙasata da ƙazantattun gumakansu marasa rai, suka kuma cika abin gādona da gumakansu na banƙyama.”19. Ya Ubangiji, ƙarfina da katangana, mafakata a lokacin damuwa, gare ka al’ummai za su zo daga iyakokin duniya su ce, “Kakanninmu ba su mallaki kome ba sai allolin ƙarya, gumakan banza da ba su yi musu amfani ba.20. Mutane kan yi allolinsu ne? I, amma waɗannan ba alloli ba ne!”21. “Saboda haka zan koya musu a wannan lokaci zan koya musu ikona da ƙarfina. Sa’an nan za su sani cewa sunana Ubangiji ne.Zabura 118:21-2421. Zan yi maka godiya, domin ka amsa mini; ka zama mai cetona.22. Zabura Dutsen da magina suka ƙi ya zama mai amfani;23. Ubangiji ne ya yi haka, kuma abu mai daraja ne a idanunmu.24. Wannan ita ce ranar da Ubangiji ya yi; bari mu yi farin ciki mu kuma yi murna a cikinta.Karin Magana 27:10-1010. Kada ka manta da abokinka da kuma abokin mahaifinka, kuma kada ka tafi gidan ɗan’uwanka sa’ad da masifa ta same ka, gara ka je wurin maƙwabci na kusa da ka je wurin ɗan’uwan da yake da nisa.1 Tessalonikawa 2:1-201. Kun sani, ’yan’uwa, cewa ziyararmu a gare ku ba tă zama a banza ba.2. Mun riga mun sha wahala, aka kuma zage mu a Filibbi, kamar yadda kuka sani, amma da taimakon Allahnmu muka yi ƙarfin hali muka sanar muku bishararsa duk da matsananciyar gāba.3. Gama roƙon da muke yi bai fito daga kuskure ko munafunci ba, ba kuwa ƙoƙari muke yi mu yaudare ku ba.4. A maimako haka, muna magana ne kamar mutanen da Allah ya amince yă danƙa musu amanar wannan bishara. Ba ma ƙoƙari mu gamshi mutane sai dai Allah, mai auna zukatanmu.5. Kun san ba ma taɓa yin daɗin baki ko mu yi ƙoƙarin kasance da halin kwaɗayin da muke ɓoyewa, Allah shi ne shaidarmu.6. Ba ma neman yabo daga wurin mutane, ko a gare ku, ko ga waɗansu. A matsayinmu na manzannin Kiristi da mun so, da mun nawaita muku,7. amma muka kasance masu sauƙinkai a cikinku, kamar yadda mahaifiya take lura da ƙananan ’ya’yanta.8. Muka ƙaunace ku ƙwarai har muka ji daɗin bayyana muku, ba bisharar Allah kaɗai ba amma har rayukanmu ma, domin kun zama ƙaunatattu a gare mu.9. Ba shakka kuna iya tunawa, ’yan’uwa, famarmu da kuma wahalarmu; mun yi aiki dare da rana don kada mu zama nauyi wa wani yayinda muke muku wa’azin bisharar Allah.10. Ku shaidu ne, haka ma Allah, na yadda muka yi zaman tsarki, adalci da kuma marar aibi a cikinku, ku da kuka ba da gaskiya.11. Gama kun san cewa mun bi da kowannenku yadda mahaifi yakan yi da ’ya’yansa,12. muna ƙarfafa ku, muna ta’azantar da ku, muna kuma gargaɗe ku ku yi rayuwar da za tă cancanci Allah, wanda ya kira ku zuwa mulkinsa da kuma ɗaukakarsa.13. Muna kuma gode wa Allah ba fasawa domin, sa’ad da kuka karɓi maganar Allah, wadda kuka ji daga gare mu, kun karɓe ta ba kamar maganar mutane ba, sai dai kamar yadda take, maganar Allah wadda take aiki a cikinku ku da kuka ba da gaskiya.14. Gama ku, ’yan’uwa, kun zama masu koyi da ikkilisiyoyin Allah a Yahudiya waɗanda suke cikin Kiristi Yesu. Kun sha wahala a hannun mutanen ƙasarku kamar yadda ikkilisiyoyin nan ma suka sha a hannun Yahudawa,15. waɗanda suka kashe Ubangiji Yesu da annabawa suka kuma kore mu. Ba sa yin aikin da Allah yake so, masu gāba ne kuwa da dukan mutane16. suna ƙoƙarin hana mu yin magana ga Al’ummai don kada su sami ceto. Ta haka kullum suke ƙara tara tsibin zunubansu. Fushin Allah ya aukar musu a ƙarshe.17. Amma, ’yan’uwa, sa’ad da aka raba mu da ku na ɗan lokaci (a jiki, ba a tunani ba), daga cikin marmarinmu mai tsanani mun yi duk abin da muke iya yi mu gan ku.18. Gama mun so mu zo wurinku, tabbatacce ni, Bulus, na yi ƙoƙari sau da sau, amma Shaiɗan ya hana mu.19. Gama mene ne begenmu, farin cikinmu, ko kuma rawanin da zai zama mana abin ɗaukaka a gaban Ubangijinmu Yesu sa’ad da ya dawo? Ba ku ba ne?20. Tabbatacce, ku ne ɗaukakarmu da kuma farin cikinmu. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.