Baibul a cikin shekara guda Oktoba 16Irmiya 17:1-271. “An rubuta zunubin Yahuda da alƙalamin ƙarfe, an rubuta da tsinin dutse, a kan allunan zukatansu da kuma a kan ƙahonin bagadansu.2. Har ’ya’yansu ma sun tuna bagadansu da ginshiƙan Asheransu kusa da itatuwa masu duhuwa da kuma a kan tuddai masu tsayi.3. Dutsena a ƙasar da dukiyarku na ƙasar da dukan arzikinku za a ba da su ganima, tare da masujadanku na kan tuddai, saboda zunubi ko’ina a ƙasarku.4. Saboda laifinku za ku rasa gādon da na ba ku. Zan bautar da ku ga abokan gābanku a ƙasar da ba ku sani ba, domin kun husata ni, zai kuwa ci har abada.”5. Ga abin da Ubangiji yana cewa, “La’ananne ne mutumin da yake dogara ga mutum, wanda ya dogara ga jiki don ƙarfi wanda kuma zuciyarsa ta juya wa Ubangiji baya.6. Zai zama kamar ɗan kurmi a ƙasar da take kango; ba za su ga arziki sa’ad da ya zo ba. Za su zauna a busassun wuraren hamada, a cikin ƙasar gishiri inda ba kowa.7. “Amma mai albarka ne mutumin da yake dogara ga Ubangiji, wanda ƙarfin halinsa yana daga Ubangiji.8. Za su zama kamar itacen da aka dasa kusa da ruwa wanda ya miƙa saiwoyinsa zuwa cikin rafi. Ba ya jin tsoro sa’ad da zafi ya zo; ganyayensa kullum kore suke. Ba shi da damuwa a shekarar fări ba ya taɓa fasa ba da ’ya’ya.”9. Zuciya ta fi kome ruɗu ta fi ƙarfin warkewa. Wa zai iya gane ta?10. “Ni Ubangiji nakan bincike zuciya in gwada tunani, don in sāka wa kowane mutum bisa ga halinsa, bisa ga ayyukansa.”11. Kamar makwarwar da ta kwanta a kan ƙwan da ba ita ta zuba ba haka yake da mutumin da ya sami arziki a hanyar da ba daidai ba. A tsakiyar rayuwarsa za su rabu da shi, a ƙarshe kuma zai zama wawa.12. Kursiyi mai daraja, da aka ɗaukaka tun daga farko, shi ne wuri mai tsarkinmu.13. Ya Ubangiji, sa zuciyar Isra’ila, duk waɗanda suka rabu da kai za su sha kunya. Waɗanda suka juya maka baya za a rubuta su a ƙura domin sun yashe Ubangiji, maɓulɓular ruwan rai.14. Ka warkar da ni, ya Ubangiji, zan kuwa warke; ka cece ni zan kuwa cetu, gama kai ne nake yabo.15. Sun riƙa ce mini, “Ina maganar Ubangiji take? Bari tă cika yanzu!”16. Ban gudu zaman mai yin maka kiwo ba; ka sani ban marmarin ranan nan ta masifa ba. Abin da ya fito daga leɓunana kuwa, a bayyane suke gare ka.17. Kada ka zama mini abin razana; kai ne mafakata a ranar masifa.18. Bari masu tsananta mini su sha kunya, amma ka kiyaye ni daga shan kunya; bari su tsorata, amma ka kiyaye ni da razana. Ka kawo musu ranar masifa; ka hallaka su da hallaka riɓi biyu.19. Ga abin da Ubangiji ya ce mini, “Ka je ka tsaya a ƙofar mutane, inda sarakunan Yahuda sukan shiga su fita; ka tsaya kuma a dukan sauran ƙofofin Urushalima.20. Ka ce musu, ‘Ku ji maganar Ubangiji, ku sarakunan Yahuda, da dukan mutanen Yahuda da dukan mazaunan Urushalima waɗanda suke bi ta waɗannan ƙofofi.21. Ga abin da Ubangiji yana cewa, ku yi hankali kada ku ɗauki kaya a ranar Asabbaci ko ku shigar da shi ta ƙofofin Urushalima.22. Kada ku fitar da kayan gidajenku ko ku yi wani aiki a ranar Asabbaci mai tsarki, yadda na umarci kakanni-kakanninku.23. Duk da haka ba su saurara ba, ba su kuwa mai da hankali ba; suka taurare ba su kuwa saurara ko su karɓi horo ba.24. Amma in kuka yi hankali kuka yi mini biyayya, in ji Ubangiji, ba ku kuwa shigar da kaya ta ƙofofi a ranar Asabbaci ba, amma kuka kiyaye ranar Asabbaci da tsarki ba tare da yin wani aiki a cikinta ba,25. sa’an nan sarakuna da suke zama a kursiyin Dawuda za su shiga ta ƙofofin wannan birni tare da fadawansu. Su da fadawansu za su shiga a kan kekunan yaƙi da kuma a kan dawakai, mutanen Yahuda suna musu rakiya tare da waɗanda suke zaune a Urushalima, wannan birni kuwa za tă kasance da mazauna har abada.26. Mutane za su zo daga garuruwan Yahuda da ƙauyukan kewaye da Urushalima, daga iyakar Benyamin da gindin tuddan yamma, daga ƙasar tudu da kuma Negeb, suna kawo hadayun ƙonawa da hadayun gari, sadakokin turare da na godiya zuwa gidan Ubangiji.27. Amma in ba ku yi mini biyayya ba, ba ku kiyaye ranar Asabbaci da tsarki ba, kuka ɗauki wani kaya yayinda kuke shiga ƙofofin Urushalima a ranar Asabbaci, to, sai in cinna wa ƙofofin Urushalima wutar da ba a iya kashewa, tă cinye kagaranta.’ ”Irmiya 18:1-231. Ga maganar da ta zo wa Irmiya daga wurin Ubangiji.2. “Ka gangara zuwa gidan mai ginin tukwane, a can zan ba ka saƙona.”3. Sai na gangara zuwa gidan mai ginin tukwane, na gan shi yana aiki a na’urar ginin tukwanen.4. Amma tukunyar da yake ginawa ta lalace a hannuwansa, sai mai ginin tukwanen ya sāke gina wata tukunya dabam, yana gyara ta yadda ya ga dama.5. Sai maganar Ubangiji ta zo mini cewa,6. “Ya gidan Isra’ila, ashe, ba zan yi da ku yadda mai ginin tukwanen nan yake yi ba?” In ji Ubangiji. “Kamar yumɓu a hannun mai ginin tukwane, haka kuke a hannuna, ya gidan Isra’ila.7. A duk lokacin da na yi shela cewa za a tumɓuke, a kakkarya a kuma hallaka wata al’umma ko mulki,8. in wannan al’ummar da na yi wa gargaɗi ta tuba daga muguntarta, sai in janye in kuma fasa kawo mata masifar da na yi niyya aukar mata.9. In kuma wani lokaci na yi shela cewa za a gina wata al’umma ko mulki a kuma kafa ta,10. in ta yi mugunta a gabana ba tă kuwa yi mini biyayya ba, sai in janye alherin da na yi niyya in yi mata.11. “Yanzu fa, sai ka faɗa wa mutanen Yahuda da waɗanda suke zaune a Urushalima, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa ga shi! Ina shirya muku masifa ina ƙirƙiro dabara a kanku. Saboda haka ku juya daga mugayen hanyoyinku, kowannenku, ku canja hanyoyinku da kuma ayyukanku.’12. Amma za su amsa su ce, ‘Ba amfani. Za mu ci gaba da shirye-shiryenmu; kowannenmu zai bi taurin muguwar zuciyarsa.’ ”13. Saboda haka ga abin da Ubangiji yana cewa, “Ku tattambaya a cikin al’ummai. Wa ya taɓa jin irin wannan abu? Budurwa Isra’ila ta yi mugun abu mafi banƙyama.14. Dusar ƙanƙarar Lebanon ta taɓa rabuwa da kan duwatsun Lebanon? Ruwan mai sanyinsa daga rafuffukansa masu nesa sun taɓa daina gudu?15. Duk da haka mutanena sun manta da ni; sun ƙone turare wa gumaka marasa amfani, waɗanda suka sa su tuntuɓe a al’amuransu a hanyoyin dā. Sun sa suka yi tafiya a ɓarayin hanyoyi a hanyoyin da ba a gina ba.16. Ƙasarsu za tă zama kufai, abin reni har abada; dukan waɗanda suka wuce za su yi mamaki su kaɗa kai.17. Kamar iska daga gabas zan warwatsa su a gaban abokan gābansu; zan juya musu bayana, ba zan nuna musu fuskata ba a ranar masifarsu.”18. Suka ce, “Zo mu shirya wa Irmiya maƙarƙashiya; gama koyarwar doka da firist ya yi ba za tă ɓace ba, haka ma shawara daga mai hikima da kuma magana daga annabawa. Saboda haka ku zo, mu fāɗa masa da harsunanmu kada mu saurari wani abin da zai faɗa.”19. Ka saurare ni, ya Ubangiji ka ji abin da masu zargina suke cewa!20. Ya kamata a sāka wa alheri da mugunta? Duk da haka sun haƙa mini rami. Ka tuna cewa na tsaya a gabanka na kuma yi magana a madadinsu don ka janye fushinka daga gare su.21. Saboda haka ka kawo wa ’ya’yansu yunwa; ka miƙa su ga ikon takobi. Bari matansu su zama marasa ’ya’ya da gwauraye; bari a kashe mazansu, a kuma kashe samarinsu da takobi a yaƙi.22. Bari a ji kuka daga gidajensu sa’ad da ka kawo masu hari a kansu farat ɗaya, gama sun haƙa rami don su kama ni suka kuma kafa tarko wa ƙafafuna.23. Amma Ya Ubangiji, ka san duk maƙarƙashiyarsu, na neman su kashe ni. Kada ka gafarta musu laifofinsu ko ka shafe zunubansu daga gabanka. Bari a tumɓuke su a gabanka; ka yi da su sa’ad da kake fushi.Zabura 118:25-2925. Ya Ubangiji, ka cece mu; Ya Ubangiji, ka ba mu nasara.26. Mai albarka ne shi mai zuwa cikin sunan Ubangiji. Daga gidan Ubangiji muna sa muku albarka.27. Ubangiji shi ne Allah ya kuma sa haskensa ya haskaka a kanmu. Da kwanoni a hannunmu, muka shiga jerin gwanon biki ku kai su ƙahoni na bagade.28. Kai ne Allahna, zan kuwa yi maka godiya; kai ne Allahna, zan kuwa ɗaukaka ka.29. Ku gode wa Ubangiji, gama nagari ne shi; ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.Karin Magana 27:11-1211. Ka zama mai hikima, ɗana, ka kuma faranta mini zuciya; zan iya amsa kowace irin suƙar da wani zai yi mini.12. Mai basira kan hango hatsari ya kuma kauce, marar azanci zai yi ta kutsa kai ciki, daga baya ya yi da na sani.1 Tessalonikawa 3:1-131. Saboda haka da muka kāsa daurewa, sai muka ga ya fi kyau a bar mu a Atens mu kaɗai.2. Muka aiki Timoti, wanda yake ɗan’uwanmu da kuma abokin aikin Allah a cikin yaɗa bisharar Kiristi, don yă gina ku yă kuma ƙarfafa ku cikin bangaskiyarku,3. don kada kowa yă raunana ta wurin waɗannan gwaje-gwajen. Kun sani sarai cewa an ƙaddara mu don waɗannan.4. Gaskiyar ita ce, sa’ad da muke tare da ku, mun sha gaya muku cewa za a tsananta mana. Haka kuwa ya faru, kamar dai yadda kuka sani.5. Saboda wannan, sa’ad da ban iya jimrewa ba, sai na aika domin in sami labarin bangaskiyarku, da fata kada yă zama mai jarraban nan ya riga ya jarrabce ku, ƙoƙarinmu kuma yă zama banza.6. Amma ga shi yanzu Timoti ya dawo mana daga wurinku ya kuma kawo labari mai daɗi game da bangaskiyarku da kuma ƙaunarku. Ya faɗa mana yadda kullum kuke da tunani mai kyau a kanmu, yadda kuke marmari ku gan mu, kamar dai yadda mu ma muke marmari mu gan ku.7. Saboda haka ’yan’uwa, cikin dukan damuwarmu da tsananinmu an ƙarfafa mu game da ku saboda bangaskiyarku.8. Gama yanzu tabbatacce muna da rai, da yake kuna nan tsaye daram a cikin Ubangiji.9. Wace irin godiya ce za mu yi wa Allah saboda ku a kan dukan farin cikin da muke da shi a gaban Allahnmu ta dalilinku?10. Dare da rana muna addu’a da himma domin mu sāke ganinku, mu kuma ba ku abin da kuka rasa a bangaskiyarku.11. Yanzu bari Allahnmu da Ubanmu kansa da kuma Ubangijinmu Yesu yă shirya mana hanya mu zo wurinku.12. Ubangiji yă sa ƙaunarku ta ƙaru ta kuma yalwata ga juna da kuma ga kowa, kamar yadda tamu take muku.13. Bari yă ƙarfafa zukatanku har ku zama marasa aibi da kuma tsarkaka a gaban Allahnmu da Ubanmu sa’ad da Ubangijimmu Yesu ya dawo tare da dukan tsarkakansa. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.