Baibul a cikin shekara guda Oktoba 18Irmiya 21:1-141. Magana ta zo wa Irmiya daga Ubangiji sa’ad da Sarki Zedekiya ya aiki Fashhur ɗan Malkiya da firist Zefaniya ɗan Ma’asehiya gare shi. Suka ce masa,2. “Yanzu ka roƙi mana Ubangiji saboda Nebukadnezzar sarkin Babilon yana kawo mana yaƙi. Wataƙila Ubangiji zai yi mana waɗansu abubuwa banmamaki kamar a lokacin baya don yă janye daga gare mu.”3. Amma Irmiya ya amsa musu ya ce, “Ku faɗa wa Zedekiya cewa,4. ‘Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, yake cewa ina shirin juya kayan yaƙin da suke a hannuwanka a kanka, waɗanda kake amfani don ka yaƙi sarki Babilon da kuma Babiloniyawa waɗanda suka kewaye katangar birnin, zan kuwa tsiba kayan yaƙinka a tsakiyar birnin nan.5. Ni da kaina zan yi yaƙi da kai da miƙaƙƙen hannu mai ƙarfi cikin fushi da hasala mai girma.6. Zan kashe waɗanda suke zaune a wannan birni, mutane da dabbobi za su kuwa mutu da muguwar annoba.7. Bayan wannan, in ji Ubangiji, zan ba da Zedekiya sarkin Yahuda, fadawansa da kuma mutanen wannan birni waɗanda suka tsira daga annoba, takobi da kuma yunwa, ga Nebukadnezzar sarkin Babilon da kuma ga abokan gābansu waɗanda suke neman ransu. Zai kashe su da takobi; ba zai ji tausayinsu ko ya yi musu jinƙai ko ya yi juyayinsu ba.’8. “Bugu da ƙari, ka faɗa wa mutanen cewa, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, ga shi na sa a gabanku hanyar rai da hanyar mutuwa.9. Duk wanda ya zauna a wannan birni zai mutu ta takobi, yunwa ko annoba. Amma duk wanda ya fita ya miƙa kansa ga Babiloniyawa waɗanda suka kewaye ku zai rayu; zai kuɓutar da ransa.10. Na ƙudura in yi wa wannan birni lahani ba alheri ba, in ji Ubangiji. Za a ba da shi a hannuwan sarki Babilon, zai kuwa hallaka shi da wuta.’11. “Ban haka ma, ka faɗa wa gidan sarauta na Yahuda cewa, ‘Ku saurari maganar Ubangiji;12. Ya gidan Dawuda ga abin da Ubangiji yana cewa, “ ‘Ku yi gaskiya kowace safiya; ku kuɓuta daga hannun mai danniya wannan da aka yi wa fashi in ba haka ba hasalata za tă sauka ta kuma ci kamar wuta saboda muguntar da kuka aikata za tă ci babu wanda zai kashe ta.13. Ina gāba da ku, mazaunan Urushalima, ku da kuke zama a bisa wannan kwari kan dutsen da yake a fili, in ji Ubangiji ku da kuke cewa, “Wa zai iya yaƙe mu? Wa zai iya shiga mafakarmu?”14. Zan hukunta ku gwargwadon ayyukanku, in ji Ubangiji. Zan sa wuta a kurminku da za tă cinye kome da yake kewaye da ku.’ ”Irmiya 22:1-301. Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Ka gangara zuwa fadan sarkin Yahuda ka yi shelar wannan saƙo a can ka ce,2. ‘Ka ji maganar Ubangiji, ya sarkin Yahuda, kai da kake zaune kan gadon sarautar Dawuda, kai, da fadawanka da mutanenka waɗanda suke shiga ta waɗannan ƙofofi.3. Ga abin da Ubangiji yana cewa, ka yi abin da yake gaskiya da kuma daidai. Ka kuɓutar da wannan da aka yi masa ƙwace daga hannun mai zaluntarsa. Kada ka yi abin da ba daidai ba ko ka cuci baƙo, maraya ko gwauruwa, kuma kada ka zub da jini marar laifi a wannan wuri.4. Gama in ka lura da bin waɗannan umarnai, to, sarakunan da suke zaune a gadon sarautar Dawuda za su shiga ta ƙofofin wannan fada, suna hawan kekunan yaƙi da dawakai, fadawansu da mutanensu suna musu rakiya.5. Amma in ba ku kiyaye waɗannan umarnai ba, in ji Ubangiji, na rantse da kaina cewa wannan fada za tă zama kufai.’ ”6. Gama ga abin da Ubangiji yana cewa game da wannan fadar sarkin Yahuda, “Ko da yake kina kamar Gileyad a gare ni, kamar ƙwanƙolin Lebanon, tabbatacce zan maishe ki hamada, kamar garuruwan da ba mazauna.7. Zan aika da mai hallakarwa a kanki, kowane mutum da makamansa, za su kuma yayyanka gumaguman al’ul na ki masu kyau su jefa su cikin wuta.8. “Mutane daga al’ummai da yawa za su ratsa cikin wannan birni su kuma tambayi juna suna cewa, ‘Me ya sa Ubangiji ya yi haka da wannan babban birni?’9. Amsar kuwa za tă zama, ‘Domin sun keta alkawarin Ubangiji Allahnsu, suka yi sujada suka kuma bauta wa waɗansu alloli.’ ”10. Kada ku yi kuka domin sarkin da ya mutu ko ku yi makoki saboda rashinsa; a maimako, ku yi kuka mai zafi saboda wanda aka kai zaman bauta, domin ba zai ƙara dawowa ba ko ya ƙara ganin ƙasarsa ta haihuwa.11. Gama ga abin da Ubangiji yana cewa game da Shallum ɗan Yosiya, wanda ya gāji mahaifinsa a matsayin sarkin Yahuda amma bai bar wurin nan ba, “Ba zai ƙara dawowa ba.12. Zai mutu a inda suka kai shi zaman bauta; ba zai ƙara ganin wannan ƙasa ba.”13. “Kaiton wanda ya gina gidansa ta hanyar rashin adalci, ɗakunansa na sama kuma ta hanyar rashin gaskiya, yana sa mutanen ƙasarsa suna aiki a banza ba ya biyansu wahalarsu.14. Yana cewa, ‘Zan gina wa kaina babban fada da manyan ɗakuna.’ Ta haka sai ya yi musu manyan tagogi ya manne musu al’ul ya yi musu ado kuma da ruwan ja.15. “Wannan zai mai da kai sarki ne in kana da al’ul a kai a kai? Mahaifinka bai kasance da abinci da abin sha ba? Ya yi abin da yake gaskiya da kuma daidai saboda haka kome ya kasance da lafiya da shi.16. Ya kāre muradin matalauta da mabukata, ta haka kome ya tafi masa daidai. Ba abin da ake nufi da ba san ni ke nan ba?” In ji Ubangiji.17. “Amma idanunka da zuciyarka sun kahu kawai a kan ƙazamar riba, da a kan zub da jinin marar laifi da kuma a kan danniya da zalunci.”18. Saboda haka ga abin da Ubangiji yana cewa game da Yehohiyakim ɗan Yosiya sarkin Yahuda, “Ba za su yi kuka dominsa ba, ‘Kaito, ɗan’uwana! Kaito, ’yar’uwata!’ Ba za su yi kuka dominsa ba, ‘Kaito, maigidana! Kaito, darajarsa!’19. Za a binne shi kamar jaki za a ja shi a ƙasa a jefar a bayan ƙofofin Urushalima.”20. “Ka haura zuwa Lebanon ka yi kuka, bari a ji muryarka a Bashan, yi kuka daga Abarim, gama an murƙushe dukan abokanka.21. Na ja maka kunne sa’ad da kake zama lafiya, amma sai ka ce, ‘Ba zan saurara ba!’ Wannan halinka ne tun kana matashi; ba ka yi mini biyayya ba.22. Iska za tă koro dukan makiyayanka abokanka kuma za su tafi zaman bauta. Sa’an nan za ka sha kunya a kuma walaƙanta ka saboda dukan muguntarka.23. Kai da kake zama a ‘Lebanon,’ kai da kake sheƙa a gine-ginen al’ul za ka yi nishi sa’ad da zafi ya auka maka, zafi kamar na mace mai naƙuda!24. “Muddin ina raye,” in ji Ubangiji, “ko kai, Yehohiyacin ɗan Yehohiyakim sarkin Yahuda, ka zama zoben hatimin dama a hannuna na dama, zan kwaɓe ka.25. Zan ba da kai ga waɗanda suke neman ranka, waɗanda kake tsoro, ga Nebukadnezzar sarkin Babilon da kuma ga Babiloniyawa.26. Zan jefar da kai da mahaifiyar da ta haife ka zuwa wata ƙasa, inda babu ɗayanku da aka haifa a wurin, a can kuma za ka mutu.27. Ba za ka ƙara dawo ƙasar da kake marmarin dawowa ba.”28. Wannan mutum Yehohiyacin ne da aka rena, fasasshen tukunya, abin da babu wanda yake so? Me ya sa za a jefar da shi da ’ya’yansa a jefar da su a ƙasar da ba su sani ba?29. Ya ke ƙasa, ƙasa, ƙasa, ki ji maganar Ubangiji!30. Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Ka rabu da wannan mutum sai ka ce marar ’ya’ya, mutumin da ba zai yi nasara a rayuwarsa ba, gama babu zuriyarsa da za tă yi nasara babu wani da zai zauna a kursiyin Dawuda ko ya ƙara yin mulkin Yahuda.”Zabura 119:9-169. Yaya matashi zai kiyaye hanyarsa da tsabta? Sai ta yin rayuwa bisa ga maganarka.10. Na neme ka da dukan zuciyata; kada ka bar ni in kauce daga umarnanka.11. Na ɓoye maganarka a cikin zuciyata don kada in yi maka zunubi.12. Yabo ya tabbata gare ka, ya Ubangiji; ka koya mini ƙa’idodinka.13. Da leɓunana na ba da labarin dukan dokokin da suka fito bakinka.14. Na yi farin ciki da bin farillanka yadda mutum yakan yi farin ciki da arziki mai yawa.15. Na yi tunani a kan farillanka na kuma lura da hanyoyinka.16. Na yi murna a cikin ƙa’idodinka; ba zan ƙyale maganarka ba.Karin Magana 27:14-1414. In mutum ya albarkaci maƙwabcinsa da murya mai ƙarfi da sassafe, za a ɗauka shi a matsayin la’ana.1 Tessalonikawa 5:1-281. To, ’yan’uwa, game da lokuta da ranaku, ba ma bukata mu rubuta muku,2. gama kun sani sarai cewa ranar Ubangiji za tă zo kamar ɓarawo da dare.3. Yayinda mutane suke cewa, “Akwai salama da zaman lafiya,” hallaka za tă auko musu farat ɗaya, kamar yadda naƙuda take kama mace mai ciki, ba za su kuwa tsira ba.4. Amma ku, ’yan’uwa, ba kwa cikin duhu da wannan rana za tă zo muku ba zato kamar ɓarawo.5. Dukanku ’ya’yan haske ne da kuma ’ya’yan rana. Mu ba mutanen dare ko na duhu ba ne.6. Saboda haka fa, kada mu zama kamar saura, waɗanda suke barci, sai dai mu zama masu tsaro da masu kamunkai.7. Gama masu barci, da dad dare suke barci, masu sha su bugu kuwa, da dad dare suke buguwa.8. Amma da yake mu na rana ne, bari mu zama masu kamunkai, sanye da bangaskiya da ƙauna kamar sulke, begen cetonmu kuma kamar hular kwano.9. Gama Allah bai naɗa mu don mu sha fushi ba, sai dai mu sami ceto ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi.10. Ya mutu saboda mu domin, ko muna a faɗake ko muna barci, mu kasance tare da shi.11. Saboda haka ku ƙarfafa juna ku kuma gina juna, kamar dai yadda kuke yi.12. To, muna roƙonku, ’yan’uwa, ku girmama waɗanda suke aiki sosai a cikinku, waɗanda suke bisanku cikin Ubangiji da kuma waɗanda suke yin muku gargaɗi.13. Ku riƙe su da mutunci sosai cikin ƙauna saboda aikinsu. Ku yi zaman lafiya da juna.14. Muna kuma gargaɗe ku, ’yan’uwa, ku gargaɗe waɗanda suke zaman banza, ku ƙarfafa masu raunanar zuciya, ku taimaki marasa ƙarfi, ku yi haƙuri da kowa.15. Ku tabbata cewa kada kowa yă rama mugunta da mugunta, sai dai kullum ku yi ƙoƙarin yin wa juna alheri da kuma dukan mutane.16. Ku riƙa farin ciki kullum;17. ku ci gaba da yin addu’a;18. ku yi godiya cikin kowane hali, gama wannan shi ne nufin Allah dominku cikin Kiristi Yesu.19. Kada ku danne aikin Ruhu.20. Kada ku rena annabci,21. amma ku gwada kome, ku riƙe abin da yake mai kyau,22. ku ƙi kowace mugunta.23. Bari Allah da kansa, Allah na salama, yă tsarkake ku sarai. Bari dukan ruhunku, ranku, da kuma jikinku su zama marar aibi a dawowar Ubangijinmu Yesu Kiristi.24. Wannan wanda ya kira ku mai aminci ne zai kuwa aikata.25. ’Yan’uwa, ku yi mana addu’a.26. Ku gaggai da dukan ’yan’uwa da sumba mai tsarki.27. Na gama ku da Ubangiji ku sa a karanta wannan wasiƙa ga dukan ’yan’uwa.28. Alherin Ubangijinmu Yesu Kiristi yă kasance tare da ku. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.