Baibul a cikin shekara guda Oktoba 20Irmiya 25:1-381. Magana ta zo wa Irmiya game da dukan mutanen Yahuda a shekara ta huɗu ta Yehohiyakim ɗan Yosiya sarkin Yahuda, wadda ta kasance shekara ta fari ta Nebukadnezzar sarkin Babilon.2. Saboda haka Irmiya annabi ya ce wa dukan mutanen Yahuda da dukan mazaunan Urushalima.3. Shekaru ashirin da uku, daga shekara ta goma sha uku ta Yosiya ɗan Amon sarkin Yahuda har zuwa wannan rana, maganar Ubangiji ta zo mini na kuma yi muku magana sau da sau, amma ba ku saurara ba.4. Ko da yake Ubangiji ya aika dukan bayinsa annabawa gare ku sau da sau, ba ku saurara ba, ba ku kuma kula ba.5. Sun ce, “Ku juye yanzu, kowannenku, daga mugayen hanyoyinku da mugayen ayyukanku, za ku kuwa iya zauna a ƙasar da Ubangiji ya ba ku da kuma kakanninku har abada abadin.6. Kada ku bi waɗansu alloli don ku bauta ku kuma yi musu sujada; kada ku tsokane ni in yi fushi da abin da hannuwanku suka yi. Sa’an nan ba zan kawo muku lahani ba.”7. “Amma ba ku saurare ni ba,” in ji Ubangiji, “kun tsokane ni da abin da kuka yi da hannuwanku, kuka kuma kawo lahani wa kanku.”8. Saboda haka Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Domin kun ƙi ku saurara ga maganata,9. zan kira dukan mutanen arewa da bawana Nebukadnezzar sarkin Babilon,” in ji Ubangiji, “zan kuma kawo su su yi gāba da wannan ƙasa da mazaunanta da kuma gāba da dukan al’ummai da suke kewaye. Zan hallaka su sarai in kuma mai da su abin bantsoro da abin dariya, za su kuma zama kufai har abada.10. Zan kawar da muryoyin farin ciki da murna daga gare su, muryoyin amarya da na ango, ƙarar dutsen niƙa da hasken fitila.11. Dukan wannan ƙasa za tă zama kango, kuma waɗannan al’ummai za su bauta wa sarkin Babilon shekaru saba’in.12. “Amma sa’ad da shekaru saba’in ɗin suka cika, zan hukunta sarkin Babilon da kuma al’ummarsa, ƙasar Babiloniyawa, saboda laifinsu,” in ji Ubangiji, “in kuma mai da ita kango har abada.13. Zan kawo wa wannan ƙasa dukan abubuwan na yi magana a kanta, dukan abubuwan da aka rubuta a wannan littafi, abubuwan da Irmiya kuma ya yi annabci a kan dukan al’ummai.14. Su kansu al’ummai da sarakuna masu yawa za su bautar da su; zan sāka musu bisa ga ayyukansu da aikin hannuwansu.”15. Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya faɗa mini, “Ka karɓi kwaf ruwan inabin nan na fushina a wurina, ka sa dukan al’umman da na aike ka gare su, su sha.16. Sa’ad da suka sha, za su yi ta tangaɗi su kuma yi hauka saboda takobin da zan aika a cikinsu.”17. Saboda haka na karɓi kwaf daga hannun Ubangiji na sa dukan al’ummai waɗanda ya aiko ni wurinsu su sha.18. Urushalima da garuruwan Yahuda, sarakunan da fadawanta, don su mai da su kufai da kuma abin bantsoro da ba’a da la’ana, yadda suke a yau;19. Fir’auna sarkin Masar, ma’aikatansa, fadawansa da dukan mutanensa,20. da dukan baƙin da suke can; dukan sarakunan Uz; dukan sarakunan Filistiyawa (waɗannan na Ashkelon, Gaza, Ekron da mutanen da aka bari a Ashdod);21. Edom, Mowab da Ammon;22. dukan sarakunan Taya da Sidon; sarakunan bakin teku a ƙetaren teku;23. Dedan, Tema, Buz da dukan waɗanda suke a manisantan wurare;24. dukan sarakunan Arabiya da dukan sarakunan baƙin da suke zama a hamada;25. dukan sarakunan Zimri, Elam da Mediya;26. da kuma dukan sarakunan arewa, nesa da kuma kusa, bi da bi, dukan mulkokin duniya. Bayan dukansu kuma, sai sarkin Sheshak ma yă sha.27. “Sa’an nan na faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa ku sha, ku bugu ku kuma yi amai, ku fāɗi, kada kuma ku ƙara tashi saboda takobin da zan aiko muku.’28. Amma in suka ki su karɓi kwaf ɗin daga hannunka su sha, ka faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa dole ku sha!29. Ga shi, na sa masifa tă yi aiki cikin birnin da ake kira da sunana, kuna gani za ku tafi ba hukunci? Ba za ku tafi ba hukunci ba, gama ina kawo wa dukan mazaunan duniya takobi, in ji Ubangiji Maɗaukaki.’30. “Yanzu ka yi annabcin dukan waɗannan maganganu a kansu ka kuma ce musu, “ ‘ Ubangiji zai yi ruri daga bisa; zai yi tsawa daga mazauninsa mai tsarki ya kuma yi ruri da ƙarfi a kan ƙasarsa. Zai yi ihu kamar waɗanda suke matsin ’ya’yan inabi, yi ihu a kan dukan waɗanda suke zaune a duniya.31. Hayaniya za tă taso har iyakar duniya, gama Ubangiji zai kawo tuhume-tuhume a kan al’ummai; zai kawo shari’a a kan dukan ’yan adam ya kuma kashe mugaye da takobi,’ ” in ji Ubangiji.32. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, “Duba! Masifa tana yaɗuwa daga al’umma zuwa al’umma; hadari mai girma yana tasowa daga iyakar duniya.”33. A lokacin waɗanda Ubangiji ya kashe za su kasance a ko’ina, daga wannan bangon duniya zuwa wancan. Ba za a yi kuka dominsu, ba za a tattara su don a binne ba, amma za su zama kamar juji da an tsiba a ƙasa.34. Ku yi kuka ku kuma yi makoki, ku makiyaya; ku yi ta birgima a ƙura, ku shugabannin garke. Gama lokacin da za a yanka ku ya zo; za ku fāɗi ku kuma farfasa kamar tukunyar yumɓu mai kyau.35. Makiyaya ba za su sami wurin da za su gudu su tafi ba, shugabannin garke ba za su sami wurin kuɓuta ba.36. Ji kukan makiyaya, kururuwan shugabannin garke, gama Ubangiji yana hallaka wurin kiwo.37. Rafi mai gudu a hankali zai zama kango saboda zafin fushin Ubangiji.38. Kamar zaki zai bar wurin ɓuyarsa, ƙasarsu kuma za tă zama kufai saboda takobin masu danniya da kuma saboda zafin fushin Ubangiji.Irmiya 26:1-241. A farkon sarautar Yehohiyakim ɗan Yosiya sarkin Yahuda, wannan magana ta zo daga wurin Ubangiji,2. “Ga abin da Ubangiji yana cewa, ka tsaya a filin gidan Ubangiji ka kuma yi magana ga dukan mutanen garuruwan Yahuda waɗanda suka zo sujada a gidan Ubangiji. Ka faɗa musu kome da na umarce ka; kada ka bar wata magana.3. Wataƙila su saurara kowanne kuma ya juyo daga mugun hanyarsa. Sa’an nan in yi juyayi in kuma janye masifar da nake shirin kawo a kansu saboda muguntar da suka aikata.4. Ka faɗa musu, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, in ba ku saurare ni, ku kuma bi dokata, wadda na sa a gabanku ba,5. in kuma ba ku saurari maganganun bayina annabawa, waɗanda na aika muku sau da sau ba (ko da yake ba ku saurara ba),6. to, sai in mai da gidan nan kamar Shilo, birnin nan kuma abin la’ana a cikin al’umman duniya.’ ”7. Firistoci, annabawa da dukan mutane suka ji Irmiya yana waɗannan maganganu a gidan Ubangiji.8. Amma da Irmiya ya gama faɗar wa dukan mutanen abin da Ubangiji ya umarce shi ya faɗa, sai firistoci, annabawa da dukan mutane suka kama shi suka ce, “Mutuwa za ka yi!9. Me ya sa ka yi annabci da sunan Ubangiji cewa wannan gida zai zama kamar Shilo, wannan birni kuma zai zama kango da hamada?” Sai duk mutane suka tattaru kewaye da Irmiya a cikin gidan Ubangiji.10. Da fadawan Yahuda suka ji haka, sai suka haura daga fada zuwa gidan Ubangiji suka zazzauna a wuraren zamansu a mashigin Sabuwar Ƙofar gidan Ubangiji.11. Sa’an nan firistoci da annabawa suka ce wa fadawan da dukan mutane, “Mutumin nan ya cancanci hukuncin kisa gama ya yi annabci gāba da wannan birni. Ku kun ji da kunnuwanku!”12. Sai Irmiya ya ce wa dukan fadawa da kuma dukan mutane, “ Ubangiji ya aiko ni in yi annabci gāba da wannan gida da wannan birni dukan abin da na faɗa.13. Yanzu sai ku gyara hanyoyinku da kuma ayyukanku ku yi biyayya da Ubangiji Allahnku. Sa’an nan Ubangiji zai yi juyayi ya kuma janye masifar da ya furta zai kawo a kanku.14. Game da ni dai, ina a hannuwanku; ku yi duk abin da kuka ga ya yi kyau, ya kuma dace a gare ku.15. Ku tabbata dai, cewa in kuka kashe ni, za ku jawo wa kanku alhakin jini marar laifi a kanku da a kan birnin nan da kuma a kan masu zama a cikinsa, gama a gaskiya Ubangiji ne ya aiko ni wurinku domin in faɗa muku dukan maganan nan a kunnuwanku.”16. Sai fadawa da dukan mutane suka ce wa firistoci da annabawa. “Wannan mutum bai yi abin da ya isa hukuncin kisa ba, gama ya yi magana da sunan Ubangiji Allahnmu.”17. Waɗansu daga cikin dattawan ƙasar suka zo gaba suka ce wa dukan taron jama’a,18. “Mika mutumin Moreshet, ya yi annabci a kwanakin Hezekiya sarkin Yahuda. Ya ce wa dukan mutanen Yahuda, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, “ ‘Za a nome Sihiyona kamar gona, Urushalima kuwa za tă zama tsibin juji, ƙwanƙolin dutsen haikali kuwa zai zama kurmi.’19. “Hezekiya sarkin Yahuda ko kuwa wani a Yahuda ya kashe shi? Ashe, Hezekiya bai ji tsoron Ubangiji ya nemi tagomashinsa ba? Ubangiji kuwa bai yi juyayi ya kuma janye masifar da ya furta zai kawo a kansu ba? Muna gab da jawo wa kanmu muguwar masifa!”20. (To, fa, Uriya ɗan Shemahiya daga Kiriyat Yeyarim wani mutum ne wanda ya yi annabci da sunan Ubangiji; ya yi annabci irin abu ɗaya gāba da wannan birni da wannan ƙasa yadda Irmiya ya yi.21. Da sarki Yehohiyakim da dukan fadawansa da ma’aikatansa suka ji wannan magana, sai sarki ya nemi a kashe shi. Amma Uriya ya ji wannan shiri sai ya gudu zuwa Masar don tsoro.22. Sarki Yehohiyakim ya aiki Elnatan ɗan Akbor zuwa Masar, tare da waɗansu mutane.23. Suka dawo da Uriya daga Masar suka kawo shi wurin Sarki Yehohiyakim, wanda ya kashe shi da takobi aka kuma jefar da gawarsa a makabartar talakawa.)24. Bugu da ƙari, Ahikam ɗan Shafan ya goyi bayan Irmiya, saboda haka ba a ba da shi ga mutane don su kashe shi ba.Zabura 119:25-3225. An kwantar da ni ƙasa cikin ƙura; ka kiyaye raina bisa ga maganarka.26. Na ba da labari hanyoyina ka kuma amsa mini; ka koya mini ƙa’idodinka.27. Bari in gane koyarwar farillanka; sa’an nan zan yi tunani a kan abubuwan banmamakinka.28. Raina ya gaji da baƙin ciki; ka ƙarfafa ni bisa ga maganarka.29. Ka kiyaye ni daga hanyoyin ruɗu; ka yi mini alheri ta wurin dokokinka.30. Na zaɓi hanyar gaskiya; na sa zuciyata a kan dokokinka.31. Na riƙe farillanka kankan, ya Ubangiji; kada ka sa in sha kunya.32. Ina gudu a kan hanyar umarnanka, gama ka ’yantar da zuciyata.Karin Magana 27:17-1717. Kamar yadda ƙarfe kan wasa ƙarfe haka mutum kan koyi daga mutum.2 Tessalonikawa 2:1-171. Game da dawowar Ubangijinmu Yesu Kiristi da game da tattara mu gare shi, muna roƙonku, ’yan’uwa,2. kada ku yi saurin jijjiguwa ko kuwa hankalinku yă tashi ta wurin wani annabci, rahoto ko wasiƙar da an ce daga wurinmu ne, cewa ranar Ubangiji ta riga ta zo.3. Kada ku bar wani yă ruɗe ku ko ta yaya, gama wannan rana ba za tă zo ba sai an yi tawayen nan an kuma bayyana mutumin tawayen nan, mutumin da aka ƙaddara ga hallaka.4. Zai yi gāba yă kuma ɗaukaka kansa a bisa kome da ya shafe sunan Allah, ko kuma ake yi wa sujada, domin yă kafa kansa a haikalin Allah, yana shelar kansa a kan shi Allah ne.5. Ba ku tuna ba cewa sa’ad da nake tare da ku nakan gaya muku waɗannan abubuwa?6. Yanzu kuwa kun san abin da yake hana shi, wannan yana faruwa ne don a bayyana shi a daidai lokaci.7. Gama ikon asirin tawaye ya riga ya fara aiki; sai dai wannan da yake hana shi zai ci gaba da yin haka sai an kau da shi.8. Sa’an nan za a bayyana mai tawayen, Ubangiji Yesu kuwa zai hamɓare shi da numfashin bakinsa yă kuma hallaka shi da darajar dawowarsa.9. Zuwan mai tawayen nan zai zama ta wurin aikin Shaiɗan da aka bayyana cikin kowane irin ayyukan banmamaki, alamu da abubuwan banmamaki na ƙarya,10. da kuma cikin kowace irin muguntar da take ruɗin waɗanda suke hallaka. Sun hallaka ne domin sun ƙi su ƙaunaci gaskiya don su sami ceto.11. Saboda haka Allah zai aiko musu da babban ruɗu don su gaskata ƙarya12. don kuma a hukunta dukan waɗanda ba su gaskata gaskiyar ba sai dai suke jin daɗin mugunta.13. Amma dole kullum mu gode wa Allah dominku, ’yan’uwa waɗanda Ubangiji ya ƙaunace, domin daga farko Allah ya zaɓe ku don a cece ku ta wurin aikin tsarkakewar Ruhu da kuma ta wurin gaskatawa da gaskiya.14. Ya kira ku ga wannan ta wurin bishararmu, don ku sami rabo a cikin ɗaukakar Ubangijinmu Yesu Kiristi.15. Saboda haka fa, ’yan’uwa, sai ku tsaya daram ku riƙe koyarwar da muka miƙa muku, ko ta wurin maganar baki ko kuma ta wurin wasiƙa.16. Ubangijinmu Yesu Kiristi kansa da kuma Allah Ubanmu, wanda ya ƙaunace mu kuma ta wurin alherinsa yă ba mu madawwamiyar ƙarfafawa da kyakkyawar bege,17. yă ƙarfafa zukatanku yă kuma gina ku cikin kowane aikin nagari da kuma magana. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.