Baibul a cikin shekara guda Oktoba 21Irmiya 27:1-221. A farkon sarautar Zedekiya ɗan Yosiya sarkin Yahuda, wannan magana ta zo wa Irmiya daga Ubangiji.2. Ga abin da Ubangiji ya ce mini, “Ka yi karkiyar itace da maɗaurai ka ɗaura a wuyanka.3. Sa’an nan ka aika da saƙo zuwa wurin sarakunan Edom, Mowab, Ammon, Taya da Sidon ta bakin jakadu waɗanda suka zo Urushalima wurin Zedekiya sarkin Yahuda.4. Ka ba su saƙo wa iyayengijinsu su ce, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, “Ku faɗa wa iyayengijinku wannan.5. Da ikon mai ƙarfi da kuma hannuna da na miƙa na yi duniya da mutanenta da kuma dabbobin da suke ciki, na ba da ita ga duk wanda na ga dama.6. Yanzu zan ba da dukan ƙasashenku ga bawana Nebukadnezzar sarkin Babilon; zan sa namun jeji ma su bauta masa.7. Dukan al’ummai za su bauta masa da ɗansa da kuma jikansa har sai har lokacin ƙasarsa ya kai; sa’an nan al’ummai masu yawa da kuma manyan sarakuna za su kasance a ƙarƙashinsa.8. “ ‘ “Amma fa, duk al’umma ko mulkin da bai bauta wa Nebukadnezzar sarkin Babilon ba bai kuwa rusunar da wuyarsa ga karkiyarsa ba, zan hukunta wannan al’umma da takobi, yunwa da annoba, in ji Ubangiji, har sai na hallaka ta ta wurin hannunsa.9. Saboda haka kada ku saurari annabawanku, masu dubanku, masu fassarar mafarkanku, bokayenku ko masu maitancinku waɗanda suke ce muku, ‘Ba za ku bauta wa sarkin Babilon ba.’10. Suna muku annabcin ƙaryar ne kawai da za tă kau da ku daga ƙasarku; zan kore ku za ku kuwa hallaka.11. Amma duk al’ummar da ta rusuna da wuyarta a ƙarƙashin karkiyar sarkin Babilon ta kuma bauta masa, zan bar al’ummar ta zauna a ƙasarta ta noma ta, ta kuma zauna a can, in ji Ubangiji.” ’ ”12. Na ba da wannan saƙo guda ga Zedekiya sarkin Yahuda. Na ce, “Ka rusunar da wuyanka a ƙarƙashin sarkin Babilon; ka bauta masa da kuma mutanensa, za ka kuwa rayu.13. Me ya sa kai da mutanenka za ku mutu saboda takobi, yunwa da annoba waɗanda Ubangiji ya yi barazana wa duk al’ummar da ba za tă bauta wa sarkin Babilon ba?14. Kada ku saurari maganganun annabawa waɗanda suke ce muku, ‘Ba za ku bauta wa sarkin Babilon ba,’ gama annabcin ƙarya suke muku.15. ‘Ban aike su ba,’ in ji Ubangiji. ‘Suna annabcin ƙarya ne da sunana. Saboda haka, zan kore ku za ku kuwa hallaka, da ku da kuma annabawan da suke muku annabci.’ ”16. Sai na ce wa firistoci da dukan waɗannan mutane, “Ga abin da Ubangiji yana cewa, kada ku saurari annabawan da suke cewa, ‘Ba daɗewa ba za a komo da kayan gidan Ubangiji daga Babilon.’ Suna muku annabcin ƙarya ne.17. Kada ku saurare su. Ku bauta wa sarkin Babilon, za ku kuwa rayu. Don me wannan birni zai zama kufai?18. In su annabawa ne da gaske suna kuma da maganar Ubangiji, bari su roƙi Ubangiji Maɗaukaki ya sa kada a kwashe kayayyakin da suka ragu a gidan Ubangiji da kuma a cikin fadar sarkin Yahuda da kuma cikin Urushalima a kai Babilon.19. Gama ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa game da ginshiƙai, kwatarniya, da dakalai, da sauran kayayyaki da aka bar su a birnin nan,20. waɗanda Nebukadnezzar sarkin Babilon ya kwashe sa’ad da ya kame Yekoniya ɗan Yehohiyakim sarkin Yahuda zuwa zaman bauta daga Urushalima zuwa Babilon tare da dukan manyan mutanen Yahuda da Urushalima,21. I, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila yana cewa game da abubuwan da aka bari a gidan Ubangiji da kuma a cikin fadar sarkin Yahuda da Urushalima,22. ‘Za a kwashe su zuwa Babilon a can kuwa za su kasance sai ranar da na neme su,’ in ji Ubangiji. ‘Sa’an nan zan komo da su in maido da su wannan wuri.’ ”Irmiya 28:1-171. A wata na biyar na wannan shekara, shekara ta huɗu, a farkon sarautar Zedekiya sarkin Yahuda, sai annabi Hananiya ɗan Azzur, wanda ya fito daga Gibeyon, ya zo wurina a gidan Ubangiji a gaban firistoci da kuma dukan mutane,2. “Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila ya ce, ‘Zan karya karkiyar sarkin Babilon.3. Cikin shekaru biyu zan komo da dukan kayayyakin gidan Ubangiji da Nebukadnezzar sarkin Babilon ya kwashe daga wannan wuri ya kai Babilon.4. Zan kuma komo da Yekoniya ɗan Yehohiyakim sarkin Yahuda da kuma dukan sauran masu zaman bauta daga Yahuda waɗanda suka tafi Babilon,’ in ji Ubangiji, ‘gama zan karya karkiyar sarkin Babilon.’ ”5. Sai annabi Irmiya ya amsa wa annabi Hananiya a gaban firistoci da kuma dukan mutane waɗanda suke tsaye a gidan Ubangiji.6. Ya ce, “Amin! Ubangiji yă sa yă zama haka! Ubangiji yă cika maganar da ka yi annabci ta wurin komo da kayayyakin gidan Ubangiji da kuma dukan masu zaman bauta zuwa wannan wuri daga Babilon.7. Duk da haka, ka saurari abin da zan faɗa a kunnenka da kuma a kunnen duka mutane,8. Daga farko fari annabawan da suka riga ka da ni sun yi annabcin yaƙi, masifa da annoba a kan ƙasashe masu yawa da kuma manyan mulkoki.9. Amma annabin da ya yi annabcin salama shi za a ɗauka a matsayin wanda Ubangiji ya aika in har abin da ya furta ya zama gaskiya.”10. Sai annabi Hananiya ya cire karkiya daga wuyar annabi Irmiya ya karya ta,11. ya ce a gaban dukan mutane, “Ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘A haka zan karya karkiyar Nebukadnezzar sarkin Babilon daga wuyan dukan al’ummai a cikin shekaru biyu.’ ” Da wannan, annabi Irmiya ya yi tafiyarsa.12. Ba a daɗe ba bayan annabi Hananiya ya karya karkiya daga wuyan annabi Irmiya, sai maganar Ubangiji ta zo wa Irmiya cewa,13. “Je ka faɗa wa Hananiya cewa, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, ka karya karkiyar katako, amma a wurinsa za ka sami karkiyar ƙarfe.14. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa zan sa karkiyar ƙarfe a wuyan dukan waɗannan al’ummai don in sa su bauta wa Nebukadnezzar sarkin Babilon, za su kuwa bauta masa. Zan ma sa shi ya mallaki namun jeji.’ ”15. Sa’an nan annabi Irmiya ya ce wa annabi Hananiya, “Ka saurara, Hananiya! Ubangiji bai aike ka ba, duk da haka ka lallashe wannan al’umma su dogara ga ƙarya.16. Saboda haka, ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Ina shirin kawar da kai daga fuskar duniya. A wannan shekara za ka mutu, domin ka yi wa’azin tawaye a kan Ubangiji.’ ”17. A wata na bakwai na wannan shekara, annabi Hananiya ya mutu.Zabura 119:33-4033. Ka koya mini Ya Ubangiji, don in bi ƙa’idodinka; sa’an nan zan kiyaye su har ƙarshe.34. Ka ba ni ganewa, zan kuwa kiyaye dokarka in kuma yi biyayya da ita da dukan zuciyata.35. Ka bi da ni a hanyar umarnanka, gama a can zan sami farin ciki.36. Ka juye zuciyata wajen farillanka ba wajen riba ta sonkai ba.37. Ka juye idanuna daga abubuwa marasa amfani; ka kiyaye raina bisa ga maganarka.38. Ka cika alkawarinka ga bawanka, saboda a ji tsoronka.39. Ka kawar da shan kunyar da nake tsoro, gama dokokinka nagari ne.40. Ina marmarin farillanka ƙwarai! Ka kiyaye raina cikin adalcinka.Karin Magana 27:18-1818. Duk wanda ya lura da itacen ɓaure, zai ci ’ya’yansa, kuma duk wanda ya lura da maigidansa za a girmama shi.2 Tessalonikawa 3:1-181. A ƙarshe, ’yan’uwa, ku yi mana addu’a domin saƙon Ubangiji yă yi saurin bazuwa a kuma girmama shi, kamar yadda yake a wurinku.2. Ku kuma yi addu’a yadda za a cece mu daga mugayen mutane masu mugunta, gama ba kowa ba ne yake da bangaskiya.3. Ubangiji mai aminci ne, zai ƙarfafa ku, yă kuma tsare ku daga mugun nan.4. Muna da tabbaci cikin Ubangiji cewa kuna bin umarnai da muka yi muku, za ku kuma ci gaba da yin abubuwan da muka umarta.5. Bari Ubangiji yă bi da zukatanku ga ƙaunan nan ta Allah da kuma jimirin nan na Kiristi.6. A cikin sunan Ubangiji Yesu Kiristi, muna muku umarni, ’yan’uwa, da ku kiyaye kanku daga kowane ɗan’uwa mai zaman banza da ba ya rayuwa bisa ga koyarwar da kuka karɓa daga wurinmu.7. Gama ku kanku kun san yadda ya kamata ku bi gurbinmu. Ba mu yi zaman banza sa’ad da muke tare da ku ba,8. ba mu kuwa ci abincin kowa ba tare da ba mu biya ba. A maimakon haka, mun yi aiki dare da rana, muna fama muna wahala kuma don kada mu nawaita wa waninku.9. Mun yi wannan, ba don ba mu da ’yancin karɓar irin taimakon nan ba ne, sai dai domin mu zama gurbin da za ku bi.10. Ko ma a sa’ad da muke tare da ku, mun ba ku wannan umarni cewa, “In mutum ya ƙi yin aiki, kada a ba shi abinci.”11. Mun ji cewa waɗansunku suna zaman banza. Ba sa aikin kome; sai shisshigi kurum.12. Irin waɗannan mutane muna ba da umarni muna kuma gargaɗe su cikin Ubangiji Yesu Kiristi su natsu su kuma nemi abincin da suke ci.13. Game da ku kuma ’yan’uwa, kada ku gaji da yin abin da yake daidai.14. In wani bai yi biyayya da umarninmu a wannan wasiƙa ba, sai fa ku lura da shi. Kada ku haɗa kai da shi, don yă ji kunya.15. Duk da haka kada ku mai da shi abokin gāba, sai dai ku gargaɗe shi a matsayin ɗan’uwa.16. Yanzu, bari Ubangiji mai salama kansa yă ba ku salama a kowane lokaci da kuma a ta kowace hanya. Ubangiji yă kasance tare da ku duka.17. Ni, Bulus, nake rubuta wannan gaisuwa da hannuna, wannan ce shaida a kowace wasiƙata, haka nake rubutu.18. Alherin Ubangijinmu Yesu Kiristi yă kasance tare da ku duka. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.