Baibul a cikin shekara guda Oktoba 22Irmiya 29:1-291. Ga abin da yake cikin wasiƙar annabi Irmiya da ya aika daga Urushalima zuwa ga sauran dattawan da suka ragu a cikin masu zaman bauta da kuma zuwa ga firistoci, annabawa da kuma dukan sauran mutanen da Nebukadnezzar ya kwashe zuwa zaman bauta daga Urushalima zuwa Babilon.2. (Wannan ya faru bayan Sarki Yekoniya da mahaifiyar sarauniya, shugabannin fada da kuma dukan shugabannin Yahuda da Urushalima, gwanayen sana’a da masu sassaƙa suka tafi zaman bauta daga Urushalima.)3. Ya ba da wasiƙar ta hannun Eleyasa ɗan Shafan da Gemariya ɗan Hilkiya, waɗanda Zedekiya sarkin Yahuda ya aika wurin Sarki Nebukadnezzar a Babilon. Wasiƙar ta ce,4. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa ga dukan waɗanda aka kwashe zuwa zaman bauta daga Urushalima zuwa Babilon.5. “Ku gina gidaje ku zauna; ku dasa gonaki ku kuma ci abin da suka haifar.6. Ku yi aure ku kuma haifi ’ya’ya maza da mata; ku nemi mata wa ’ya’yanku maza, ku kuma ba da ’ya’yanku mata ga aure, saboda su ma za su haifi ’ya’ya maza da mata. Ku riɓaɓɓanya a can, kada ku ragu.7. Haka kuma, ku nemi zaman salama da cin gaba a birnin da aka kai ku zaman bauta. Ku yi addu’a ga Ubangiji saboda birnin, domin in ya ci gaba, ku ma za ku ci gaba.”8. I, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila yana cewa, “Kada ku bar annabawa da masu sihiri a cikinku su ruɗe ku. Kada ku saurari mafarkan da dā kuke ƙarfafa su su yi.9. Suna muku annabcin ƙarya da sunana. Ban aike su ba,” in ji Ubangiji.10. Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Sa’ad da shekaru saba’in suka cika a Babilon, zan zo muku in cika alkawarin alherina don in komo da ku zuwa wannan wuri.11. Gama na san shirye-shiryen da na yi muku,” in ji Ubangiji, “shirye-shiryen cin gaba ba na cutarwa ba, shirye-shiryen ba ku sa zuciya da kuma na nan gaba.12. Sa’an nan za ku kira gare ni ku zo ku kuma yi addu’a gare ni, zan kuwa ji ku.13. Za ku neme ni ku kuwa same ni sa’ad da kuka neme ni da dukan zuciyarku.14. Za ku same ni,” in ji Ubangiji, “zan kuma komo da ku daga bauta. Zan tattaro ku daga dukan al’ummai in sa ku inda na kore ku,” in ji Ubangiji, “zan kuma komo da ku zuwa wurin da na kwashe ku zuwa zaman bauta.”15. Za ku iya ce, “ Ubangiji ya tā da annabawa saboda mu a Babilon.”16. Amma ga abin da Ubangiji yana cewa game da sarki, wanda yake zaune a kursiyin Dawuda da kuma dukan mutanen da suka ragu a wannan birni, ’yan’uwanku waɗanda ba su tafi tare da ku zuwa zaman bauta ba.17. I, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, “Zan aika da takobi, yunwa da annoba a kansu zan kuma sa su zama kamar ɓaure marar amfani da suka yi munin da ba a iya ci.18. Zan fafare su da takobi, yunwa da annoba zan kuma sa su zama abin ƙyama ga dukan mulkokin duniya da kuma abin la’ana da abin bantsoro, abin dariya da abin reni, a cikin dukan al’umman da aka kore su zuwa.19. Gama ba su saurari maganata ba,” in ji Ubangiji, “maganar da na aika gare su sau da sau ta bayina annabawa. Ku kuma masu zaman bauta ba ku saurara ba,” in ji Ubangiji.20. Saboda haka, ku ji maganar Ubangiji, dukanku masu zaman bauta waɗanda na aika daga Urushalima zuwa Babilon.21. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa game da Ahab ɗan Kolahiya da Zedekiya ɗan Ma’asehiya, waɗanda suke muku annabcin ƙarya da sunana. “Zan ba da su ga Nebukadnezzar sarkin Babilon, zai kuwa kashe su a gaban idanunku.22. Saboda su, dukan masu zaman bauta daga Yahuda waɗanda suke a Babilon za su yi amfani da wannan la’ana cewa, ‘ Ubangiji ka yi da mu kamar Zedekiya da Ahab waɗanda sarkin Babilon ya ƙone da wuta.’23. Gama sun aikata munanan abubuwa a Isra’ila; sun yi zina da matan maƙwabtansu kuma da sunana suka yi ƙarya, waɗanda ban faɗa musu su yi ba. Na san wannan kuma ni shaida ne ga haka,” in ji Ubangiji.24. Faɗa wa Shemahiya mutumin Nehelam,25. “Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa ka aika da wasiƙu da sunanka ga dukan mutane a Urushalima, zuwa ga Zefaniya ɗan Ma’asehiya firist da kuma ga sauran firistoci. Ka ce wa Zefaniya,26. ‘ Ubangiji ya naɗa ka firist a wurin Yehohiyada don ka lura da gidan Ubangiji; ya kamata ka sa kowane mahaukaci wanda yake yi kamar annabi cikin turu da kuma a kangi.27. To, me ya sa ba ka tsawata wa Irmiya daga Anatot, wanda yana ɗauka kansa annabi a cikinku ba?28. Ya aiko mana da saƙonsa a Babilon cewa zai ɗauki lokaci ƙwarai. Saboda haka ku gina gidaje ku zauna; ku dasa gonaki ku kuma ci abin da suka haifar.’ ”29. Zefaniya firist kuwa, ya karanta wasiƙar annabi Irmiya.Irmiya 30:1-241. Ga maganar da ta zo wa Irmiya daga Ubangiji.2. “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, yana cewa, ‘Ka rubuta a cikin littafi dukan maganganun da na yi maka.3. Kwanaki suna zuwa,’ in ji Ubangiji, ‘sa’ad da zan komo da mutanena Isra’ila da Yahuda daga bauta in kuma maido da su ga ƙasar da na ba wa kakanninsu mallaka,’ in ji Ubangiji.”4. Ga kalmomin Ubangiji da ya yi game da Isra’ila da Yahuda,5. “Ga abin da Ubangiji yana cewa, “ ‘Ana jin kukan tsoro, razana, ba salama ba.6. Ku tambaya ku ji. Namiji zai iya haifi ’ya’ya? To, me ya sa kuke ganin kowane mai ƙarfi da hannuwansa a kwankwaso kamar mace mai naƙuda, kowace fuska ta koma fari?7. Kaito, gama wannan rana za tă zama mai girma! Babu kamar ta. Zai zama lokacin wahala wa Yaƙub, amma za a cece shi daga cikinta.8. “ ‘A wannan rana,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki, ‘Zan karya karkiya daga wuyansu zan kuma cire musu kangi; baƙi ba za su ƙara bautar da su ba.9. A maimakon haka, za su bauta wa Ubangiji Allahnsu Dawuda sarkinsu kuwa, wanda na tayar musu.10. “ ‘Saboda haka kada ka ji tsoro, ya Yaƙub bawana; kada ka karai, ya Isra’ila,’ in ji Ubangiji. ‘Tabbatacce zan cece ka daga wuri mai nesa, zuriyarka daga ƙasar zaman bautansu. Yaƙub zai sami salama da zaman lafiya, kuma ba wanda zai sa ya ji tsoro.11. Ina tare da kai zan kuma cece ka,’ in ji Ubangiji. ‘Ko da yake na hallakar da dukan al’umma gaba ɗaya a inda na warwatsa ku, ba zan hallaka ku gaba ɗaya ba. Zan hore ku amma da adalci kaɗai; ba zan ƙyale ku ku tafi gaba ɗaya ba hukunci ba.’12. “Ga abin da Ubangiji yana cewa, “ ‘Mikinku marar warkewa ne, raunin da kuka ji ya sha ƙarfin warkarwa.13. Babu wanda zai yi roƙo saboda damuwarku, ba magani domin mikinku babu warkarwa dominku.14. Dukan abokanku sun manta da ku; ba su ƙara kulawa da ku. Na buge ku kamar yadda abokin gāba zai yi na kuma hukunta ku yadda mai mugunta zai yi, domin laifinku da girma yake zunubanku kuma da yawa suke.15. Me ya sa kuke kuka a kan mikinku, wahalarku da ba ta da magani? Domin laifinku da girma yake da kuma zunubanku masu yawa na yi muku waɗannan abubuwa.16. “ ‘Amma duk wanda ya cinye ku za a cinye shi; dukan abokan gābanku za su tafi zaman bauta. Waɗanda suka washe ku su ma za a washe su; dukan waɗanda suka mai da ku ganima su ma zan mai da su ganima.17. Amma zan mayar muku da lafiya in kuma warkar da mikinku,’ in ji Ubangiji, ‘domin ana ce da ku yasassu, Sihiyona wadda ba wanda ya kula da ita.’18. “Ga abin da Ubangiji yana cewa, “ ‘Zan mayar da wadatar tentin Yaƙub in kuma ji tausayin wuraren zamansa; za a sāke gina birnin a kufansa, fadar kuwa za tă tsaya a wurin da ya dace da ita.19. Daga gare su waƙoƙi za su fito na godiya da kuma sowa ta farin ciki. Zan riɓaɓɓanya su, ba za su kuwa ragu ba; zan kawo musu ɗaukaka, ba kuwa za a ƙasƙanta su ba.20. ’Ya’yansu za su kasance kamar a kwanakin dā jama’arsu kuma za su kahu a gabana; zan hukunta duk wanda ya zalunce su.21. Shugabansu zai zama ɗaya daga cikinsu; mai mulkinsu zai taso daga cikinsu. Zan kawo shi kusa zai kuma zo kusa da ni, gama wane ne zai miƙa kansa don yă yi kusa da ni?’ In ji Ubangiji.22. ‘Saboda haka za ku zama mutanena, ni kuwa in zama Allahnku.’ ”23. Ga shi, hadarin Ubangiji zai fasu cikin hasala, iskar guguwa mai hurawa a kan kawunan mugaye.24. Fushi mai zafi na Ubangiji ba zai kawu ba sai ya cika manufofin zuciyarsa gaba ɗaya. A kwanaki masu zuwa za ku gane wannan.Zabura 119:41-4841. Bari ƙaunarka marar ƙarewa ta zo gare ni, ya Ubangiji, cetonka bisa ga alkawarinka;42. sa’an nan zan amsa wa masu cin mutuncina, gama na dogara ga maganarka.43. Kada ka ƙwace maganarka daga bakina, gama na sa zuciyata a dokokinka.44. Kullayaumi zan yi biyayya da dokokinka, har abada abadin.45. Zan yi ta yawo a sake gama na nemi farillanka.46. Zan yi maganar farillanka a gaban sarakuna ba kuwa za a kunyata ni ba,47. gama ina farin ciki da umarnanka saboda ina ƙaunarsu.48. Na ɗaga hannuwana ga umarnanka, waɗanda nake ƙauna, ina kuma tunani a kan ƙa’idodinka.Karin Magana 27:19-1919. Kamar yadda ruwa kan nuna yadda fuska take, haka zuciyar mutum kan nuna irin mutumin.1 Timoti 1:1-201. Bulus, manzon Kiristi Yesu ta wurin umarnin Allah Mai Cetonmu da kuma na Yesu Kiristi begenmu,2. Zuwa ga Timoti ɗana na gaske cikin bangaskiya. Alheri, jinƙai da kuma salama daga Allah Uba da Kiristi Yesu Ubangijinmu, su kasance tare da kai.3. Kamar yadda na gargaɗe ka sa’ad da zan je Makidoniya, ka zauna can Afisa domin ka umarci waɗansu mutane kada su koyar da ƙa’idodin ƙarya nan gaba4. ko su ba da kansu ga tatsuniyoyi da ƙididdigar asali marar iyaka. Waɗannan suna kawo faɗa a maimakon aikin Allah wanda yake ta wurin bangaskiya.5. Maƙasudin wannan umarnin dai ƙauna ce, wadda take zuwa daga zuciya mai tsabta da lamiri mai kyau da kuma sahihiyar bangaskiya.6. Waɗansu sun bauɗe daga waɗannan al’amura, suka koma ga maganganu marasa ma’ana.7. So suke su zama malaman doka, ba tare da fahimtar abin da suke faɗa ba, balle abubuwan da suke ta nacewa a kai.8. Mun san cewa doka tana da kyau in an yi amfani da ita yadda ya kamata.9. Mun kuma san cewa an yi doka ba domin masu adalci ba sai dai masu tawaye, da marasa biyayya, da marasa bin Allah, da masu zunubi, da marasa tsarkaka, da masu saɓon Allah, da masu kashe iyaye maza da mata, da masu kisankai,10. da masu zina da kuma da maza masu kwana da maza, ko mata masu kwana da mata, da masu cinikin bayi da masu ƙarya da kuma masu shaidar ƙarya, da kuma duk wani abin da ya saɓa wa sahihiyar koyarwa,11. da take bisa ga bishara mai ɗaukaka ta Allah mai albarka, wadda ya danƙa mini.12. Na gode wa Kiristi Yesu Ubangijinmu, wanda ya ba ni ƙarfi, saboda ya amince da ni, har ya sa ni aikinsa.13. Ko da yake a dā ni mai saɓo da mai tsanantawa da kuma mai rikici ne, aka nuna mini jinƙai saboda na yi haka cikin jahilci ne da kuma rashin bangaskiya.14. An zubo mini alherin Ubangijinmu a yalwace, tare da bangaskiya da ƙaunar da take cikin Kiristi Yesu.15. Ga wata magana tabbatacciya wadda ta cancanci cikakkiyar karɓa. Kiristi Yesu ya zo duniya domin ceton masu zunubi, wanda nake mafi muni a cikinsu.16. Amma saboda wannan dalilin ne aka nuna mini jinƙai domin ta wurina, mafi zunubi duka, Kiristi Yesu yă iya bayyana matuƙar haƙurinsa a matsayin misali ga waɗanda za su gaskata shi su kuma sami rai madawwami.17. Bari girma da ɗaukaka su tabbata har abada abadin ga Sarki madawwami, wanda ba ya mutuwa, wanda ba a ganinsa, wanda kuma shi ne kaɗai Allah! Amin.18. Timoti, ɗana, na ba ka wannan umarni bisa ga annabce-annabcen da aka yi a dā game da kai, domin ta wurin binsu ka iya yin yaƙi mai kyau,19. kana riƙe da bangaskiya da kuma lamiri mai kyau. Gama waɗansu mutane, saboda ƙin kasa kunne ga lamirinsu, suka lalatar da bangaskiyarsu.20. Cikinsu kuwa akwai Himenayus da Alekzanda, waɗanda na miƙa ga Shaiɗan don su horo su bar yin saɓo. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.