Baibul a cikin shekara guda Oktoba 25Irmiya 35:1-191. Ga maganar da ta zo wa Irmiya daga wurin Ubangiji a lokacin mulkin Yehohiyakim ɗan Yosiya sarkin Yahuda.2. “Ka tafi wurin iyalin Rekabawa ka gayyace su su zo a ɗaya daga cikin ɗakunan da suke gefe a gidan Ubangiji ka kuma ba su ruwan inabi su sha.”3. Sai na tafi don in kawo Ya’azaniya ɗan Irmiya, ɗan Habazziniya, da ’yan’uwansa da kuma dukan ’ya’yansa maza, dukan iyalin Rekabawa.4. Na kawo su cikin gidan Ubangiji, a cikin ɗakin ’ya’yan Hanan ɗan Igdaliya maza mutumin Allah. Ɗakin ne kusa da ɗakin fadawa, wanda yake bisa na Ma’asehiya ɗan Shallum mai tsaron ƙofa.5. Sai na ajiye ƙwarya cike da ruwan inabi da waɗansu kwaf a gaban iyalin Rekabawan na kuma ce musu, “Ku sha ruwan inabin.”6. Amma sai suka amsa suka ce, “Ba ma shan ruwan inabi, domin kakanmu Yehonadab ɗan Rekab ya umarce mu cewa, ‘Ko ku, ko zuriyarku kada ku sha ruwan inabi.7. Haka kuma ba za ku gina gidaje, ku dasa iri ko ku nome gonakin inabi ba; kada ku kasance da wani daga cikin waɗannan abubuwa, amma dole kullum ku zauna a tentuna. Ta haka za ku yi dogon rai a cikin ƙasar baƙuncinku.’8. Mun yi biyayya da kome da kakanmu Yehonadab ɗan Rekab ya umarce mu. Mu ko matanmu ko ’ya’yanmu maza da mata ba mu taɓa shan ruwan inabi ba9. ba mu kuma gina gidaje mu zauna a ciki ba ko mu yi gonakin inabi, gonaki ko hatsi ba.10. Mun yi rayuwarmu a cikin tentuna mun kuma yi biyayya ƙwarai da kowane abin da kakanmu Yehonadab ya umarce mu.11. Amma da Nebukadnezzar sarkin Babilon ya kawo wa ƙasan nan hari, sai muka ce, ‘Ku zo, dole mu tafi Urushalima don mu tsira daga Babiloniyawa da kuma sojojin Arameyawa.’ Saboda haka ne muke a Urushalima.”12. Sai maganar Ubangiji ta zo wa Irmiya cewa,13. “Ga abin da Ubangiji, Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa ka tafi ka faɗa wa mutanen Yahuda da kuma mutanen Urushalima cewa, ‘Ba za ku koyi darasi ku kuma yi biyayya da maganata ba?’ In ji Ubangiji.14. ‘Yehonadab ɗan Rekab ya umarci ’ya’yansa maza kada su sha ruwan inabi sun kuma kiyaye wannan umarni. Har yă zuwa yau ba sa shan ruwan inabi, domin sun yi biyayya da umarnin kakansu. Amma na yi muku magana sau da sau, duk da haka ba ku yi biyayya ba.15. Sau da sau na aika dukan bayina annabawa gare ku. Suka ce, “Kowannenku ya juyo daga mugayen hanyoyinsa ya sabunta ayyukansa; kada yă bi waɗansu alloli don yă bauta musu. Ta haka za ku zauna a cikin ƙasar da na ba ku da kuma kakanninku.” Amma ba ku saurara ba, ba ku kuwa ji ni ba.16. Zuriyar Yehonadab ɗan Rekab sun yi biyayya da umarnin da kakansu ya ba su, amma waɗannan mutane ba su yi mini biyayya ba.’17. “Saboda haka, ga abin da Ubangiji Allah Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, ‘Ku saurara! Zan kawo wa Yahuda da kuma kowane mutumin da yake zama a Urushalima kowace masifar da na ambata a kansu. Na yi musu magana, amma ba su saurara ba; na kira su, amma ba su amsa ba.’ ”18. Sai Irmiya ya ce wa iyalin Rekabawa, “Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, ‘Kun yi biyayya da umarnin kakanku Yehonadab kuka kuma kiyaye dukan umarnansa kuka yi kome bisa ga tsari.’19. Saboda haka, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, ‘Yehonadab ɗan Rekab ba zai taɓa rasa mutumin da zai yi mini hidima ba.’ ”Irmiya 36:1-321. A shekara ta huɗu ta Yehohiyakim ɗan Yosiya sarkin Yahuda, wannan magana ta zo wa Irmiya daga wurin Ubangiji cewa,2. “Ka ɗauki littafi ka rubuta dukan maganganun da na yi maka game da Isra’ila, Yahuda da kuma dukan sauran al’ummai daga lokacin da na fara maka magana a mulkin Yosiya har zuwa yanzu.3. Wataƙila sa’ad da mutanen Yahuda suka ji game da kowace masifar da na shirya in auka musu, kowa ya juya daga muguwar hanyarsa; sa’an nan in gafarta musu muguntarsu da kuma zunubinsu.”4. Saboda haka Irmiya ya kira Baruk ɗan Neriya, yayinda Irmiya yake fadar dukan waɗannan maganganun da Ubangiji ya faɗa masa, Baruk ya rubuta su a littafin.5. Sai Irmiya ya ce wa Baruk, “An hana ni, ba zan tafi haikalin Ubangiji ba.6. Saboda haka ka tafi gidan Ubangiji a ranar azumi ka karanta wa mutane daga littafin maganar Ubangiji da na shibta maka ka rubuta. Ka karanta su ga dukan mutanen Yahuda waɗanda suka zo daga garuruwansu.7. Wataƙila za su kawo kukansu a gaban Ubangiji, kowanne kuma ya juya daga muguwar hanyarsa, gama fushi da hasalar da Ubangiji ya furta a kan mutanen nan yana da girma.”8. Sai Baruk ɗan Neriya ya yi dukan abin da annabi Irmiya ya ce ya yi; a haikalin Ubangiji kuwa ya karanta maganar Ubangiji daga littafin9. A watan tara na shekara ta biyar ta Yehohiyakim ɗan Yosiya sarkin Yahuda, an yi shela a yi azumi a gaban Ubangiji ga dukan mutanen Urushalima da waɗanda suka zo daga garuruwan Yahuda.10. Daga ɗakin Gemariya ɗan Shafan magatakarda, wanda yake a fili na bisa a mashigin Sabuwar Ƙofar haikali, Baruk ya karanta wa dukan mutane a haikalin Ubangiji maganar Irmiya daga littafin.11. Sa’ad da Mikahiya ɗan Gemariya, ɗan Shafan, ya ji dukan maganar Ubangiji daga littafin,12. sai ya sauka zuwa ɗakin magatakarda a fada, inda dukan fadawa suke zaune, Elishama magatakarda, Delahiya ɗan Shemahiya, Elnatan ɗan Akbor, Gemariya ɗan Shafan, Zedekiya ɗan Hananiya, da dukan sauran fadawa.13. Bayan Mikahiya ya faɗa musu kome da ya ji Baruk ya karanta wa mutane daga littafin,14. sai dukan fadawan suka aiki Yehudi ɗan Netaniya, ɗan Shelemiya, ɗan Kushi, ya ce wa Baruk, “Ka zo tare da littafin da ka karanta wa mutane.” Saboda haka Baruk ɗan Neriya ya tafi wurinsu tare da littafin a hannunsa.15. Suka ce masa, “Zauna, ka karanta mana littafin.” Sai Baruk ya karanta musu littafin.16. Da suka ji dukan maganar, sai suka dubi juna a firgice suka ce wa Baruk, “Dole mu sanar da dukan maganan nan ga sarki.”17. Sa’an nan suka ce wa Baruk, “Faɗa mana yadda ka yi ka rubuta dukan wannan. Irmiya ne ya yi maka shibtar ta?”18. Baruk ya amsa ya ce, “I, shi ne ya faɗa mini dukan wannan magana, na kuwa rubuta su a takarda.”19. Sa’an nan fadawan suka ce wa Baruk, “Kai da Irmiya ku je ku ɓuya. Kada ku bari wani ya san inda kuke.”20. Bayan da suka ajiye littafin a ɗakin Elishama magatakarda, sai suka tafi wurin sarki a fili suka sanar da shi kome.21. Sai sarki ya aiki Yehudi ya kawo littafin daga ɗakin Elishama magatakarda ya kuma karanta wa sarki da kuma dukan fadawan da suke tsaye kusa da shi.22. A watan tara ne sarki kuwa yana zaune a gidansa na rani, wuta kuwa tana ci a kasko a gabansa.23. Duk sa’ad da Yehudi ya karanta sashi uku ko huɗu na littafin, sai sarkin ya sa wuƙa ya yanke su, ya zuba a wutar da take ci a kasko, da haka ya ƙone dukan littafin.24. Sai sarki da dukan masu yin masa hidima waɗanda suke jin maganan nan ba su firgita ba, balle su keta rigunansu.25. Ko da yake Elnatan, Delahiya da Gemariya sun roƙi sarki kada yă ƙone littafin, bai saurare su ba.26. A maimakon haka, sai sarki ya umarci Yerameyel ɗan sarki, Serahiya ɗan Azriyel da Shelemiya ɗan Abdeyel su kama Baruk marubuci da Irmiya annabi. Amma Ubangiji ya ɓoye su.27. Bayan sarki ya ƙone littafin da ya ƙunshi maganar da Baruk ya rubuta daga shibtar Irmiya, sai maganar Ubangiji ta zo wa Irmiya cewa,28. “Ka ɗauki wani littafi ka rubuta a kansa dukan maganar da littafi na farin ya ƙunsa, wanda Yehohiyakim sarkin Yahuda ya ƙone.29. Ka kuma faɗa wa Yehohiyakim sarkin Yahuda cewa, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, ka ƙone wancan littafin ka kuma ce, “Don me ka rubuta a cikinsa, cewa lalle sarkin Babilon zai zo ya hallaka wannan ƙasa, zai kashe mutum duk da dabba?”30. Saboda haka, ga abin da Ubangiji yana cewa game da Yehohiyakim sarkin Yahuda. Ba zai kasance da wani wanda zai zauna a kan gadon sarautar Dawuda ba; za a jefar da gawarsa ta sha zafi da rana da dare kuma ta sha matsanancin sanyi.31. Zan hukunta shi da kuma ’ya’yansa da masu hidimarsa saboda muguntarsu; zan kawo kowace masifar da na furta a kansu da kuma waɗanda suke zama a Urushalima da na Yahuda, domin sun ƙi su saurara.’ ”32. Sai Irmiya ta ɗauko wani littafi ya ba wa Baruk ɗan Neriya marubuci, kuma yayinda Irmiya yake shibtawa, Baruk ya rubuta a littafin dukan maganar da take a littafin da Yehohiyakim sarkin Yahuda ya ƙone. Ya kuma ƙara ire-iren maganganun nan a kansu.Zabura 119:65-7265. Ka yi wa bawanka alheri bisa ga maganarka, ya Ubangiji.66. Ka koya mini sani da kuma hukunci mai kyau, gama na gaskata a umarnanka.67. Kafin in sha wahala na kauce, amma yanzu ina biyayya da maganarka.68. Kai nagari ne, kuma abin da kake yi yana da kyau; ka koya mini ƙa’idodinka.69. Ko da yake masu fariya sun shafe ni da ƙarairayi, na kiyaye farillanka da dukan zuciyata.70. Zukatansu sun yi tauri da kuma marasa tausayi amma ina farin ciki a dokarka.71. Ya yi kyau da na sha wahala don in koyi ƙa’idodinka.72. Doka daga bakinka ya fi mini daraja fiye da azurfa da zinariya guda dubu.Karin Magana 27:22-2222. Ko da ka daka wawa a turmi, kana daka shi kamar hatsi da taɓarya, ba za ka fid da wauta daga gare shi ba.1 Timoti 4:1-161. Ruhu a sarari ya faɗa cewa a kwanakin ƙarshe waɗansu za su watsar da bangaskiya su bi ruhohi masu ruɗu da kuma abubuwan da aljanu suke koyarwa.2. Irin koyarwan nan tana zuwa ne daga waɗansu munafukai maƙaryata, waɗanda aka yi wa lamirinsu kaca-kaca.3. Suna hana mutane yin aure suna kuma umarce su kada su ci waɗansu irin abinci, waɗanda Allah ya halitta don waɗanda suka gaskata suka kuma san gaskiya, su karɓa da godiya.4. Gama duk abin da Allah ya halitta yana da kyau, kada kuma a ƙi kome in dai an karɓe shi da godiya,5. domin an tsarkake shi ta wurin maganar Allah da kuma addu’a.6. In ka nuna wa ’yan’uwa waɗannan abubuwa, za ka zama mai hidima mai kyau na Kiristi Yesu, wanda aka goya cikin gaskiyar bangaskiya da kuma koyarwa mai kyau wadda ka bi.7. Ka kiyaye kanka daga tatsuniyoyi na rashin tsoron Allah da labaru banza na tsofaffin mata; a maimako, ka hori kanka ga zama mai tsoron Allah.8. Gama horon jiki yana da amfani, amma tsoron Allah yana da amfani ga kowane abu, yana da albarka ga rai na yanzu da kuma rai mai zuwa.9. Wannan magana tabbatacciya ce wadda ta cancanci cikakkiyar karɓa.10. Saboda wannan kuwa muke wahala da kuma fama, domin mun sa begenmu ga Allah mai rai, wanda yake Mai Ceton dukan mutane, musamman na waɗanda suka ba da gaskiya.11. Ka umarta ka kuma koyar da waɗannan abubuwa.12. Kada ka bar wani yă rena ka domin kai matashi ne, sai dai ka zama gurbi ga masu bi cikin magana, cikin rayuwa, cikin ƙauna, cikin bangaskiya da kuma cikin zaman tsarki.13. Kafin in zo, ka ci gaba da karanta wa mutane Nassi, da yin wa’azi, da kuma koyarwa.14. Kada ka yi sakaci da baiwarka, wadda aka ba ka ta wurin saƙon annabci sa’ad da ƙungiyar dattawa suka ɗibiya hannuwa a kanka.15. Ka yi ƙwazo cikin waɗannan batuttuwa; ka ba da kanka gaba ɗaya gare su, don kowa yă ga ci gabanka.16. Ka kula da rayuwarka da kuma koyarwarka da kyau. Ka daure a cikinsu, domin in ka yi, za ka ceci kanka da kuma masu sauraronka. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.