Baibul a cikin shekara guda Oktoba 29Irmiya 43:1-131. Sa’ad da Irmiya ya gama faɗa wa mutane dukan maganar Ubangiji Allahnsu, duk abin da Ubangiji ya aike shi ya faɗa musu,2. Azariya ɗan Hoshahiya da Yohanan ɗan Kareya da dukan masu ɗaga kai suka ce wa Irmiya, “Kana ƙarya ne! Ubangiji Allahnmu bai aike ka ka ce, ‘Kada ku tafi Masar don ku zauna a can.’3. Amma Baruk ɗan Neriya yana zuga ka a kanmu don ka ba da mu ga Babiloniyawa, don su kashe mu ko su kai mu zaman bauta a Babilon.”4. Saboda haka Yohanan ɗan Kareya da dukan shugabannin sojoji da dukan mutane suka yi rashin biyayya ga umarnin Ubangiji da su zauna a ƙasar Yahuda.5. A maimako, Yohanan ɗan Kareya da dukan shugabannin sojoji suka kwashe raguwar Yahuda waɗanda suka dawo su zauna a ƙasar Yahuda daga dukan al’umman inda aka kora su.6. Suka kuma kwashe dukan maza, mata da yara da ’ya’yan sarki mata waɗanda Nebuzaradan shugaban matsaran sarki ya bari tare da Gedaliya ɗan Ahikam, ɗan Shafan, da Irmiya annabi da kuma Baruk ɗan Neriya.7. Saboda haka suka shiga Masar cikin rashin biyayya ga Ubangiji suka tafi har can Tafanes.8. A Tafanes maganar Ubangiji ta zo wa Irmiya cewa,9. “Yayinda Yahudawa suna kallo, ka ɗauki waɗansu manyan duwatsu tare da kai ka kuma binne su cikin yumɓu a tubalin dakalin ƙofar shiga fadar Fir’auna a Tafanes.10. Sa’an nan ka faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, zan aika wa bawana Nebukadnezzar sarkin Babilon, zan kuma sa kursiyinsa a kan waɗannan duwatsun da na binne a nan; zai fadada bukkar mulkinsa a bisansu.11. Zai zo ya yaƙi Masar, ya kawo mutuwa ga waɗanda aka ƙaddara musu mutuwa, zaman bauta ga waɗanda aka ƙaddara musu zaman bauta, da kuma takobi ga waɗanda aka ƙaddara su mutu ta takobi.12. Zai sa wuta wa haikalan allolin Masar; zai ƙone haikalansu yă kuma kwashe allolinsu bayi. Kamar yadda makiyayi yakan yafa mayafinsa kewaye da shi, haka zai yafa Masar kewaye da kansa ya kuma tashi a wurin babu abin da ya same shi.13. A can cikin haikalin rana a Masar zai rushe al’amudan duwatsu yă kuma ƙone haikalan allolin Masar.’ ”Irmiya 44:1-301. Wannan maganata zo wa Irmiya game da dukan Yahudawa masu zama a Masar ta Ƙasa, a Migdol, Tafanes da Memfis, da kuma a Masar ta Bisa.2. “Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila yana cewa kun ga masifa mai girmar da na kawo a kan Urushalima da kuma a kan dukan garuruwan Yahuda. A yau sun zama hamada da kuma kango3. saboda muguntar da suka aikata. Sun tsokane ni na yi fushi ta wurin ƙone turare da kuma ta wurin bauta wa waɗansu allolin da su ko ku ko kakanninku ba su taɓa sani ba.4. Sau da sau na aiki bayina annabawa, waɗanda suka ce, ‘Kada ku yi wannan abin ƙyama da na ƙi!’5. Amma ba su saurara ko su kasa kunne ba; ba su juye daga muguntarsu ko su daina ƙone turare wa waɗansu alloli ba.6. Saboda haka, fushina mai ƙuna ya fāɗo a kan garuruwan Yahuda da kuma titunan Urushalima na kuma mai da su kufai da suke a yau.7. “To, ga abin da Ubangiji Allah Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa don me kuka kawo irin masifa mai girma haka a kanku ta wurin warewa daga Yahuda maza da mata, yara da jarirai, kun kuma bar kanku babu raguwa?8. Me ya sa kuka tsokane ni in yi fushi saboda abin da hannuwanku suka yi, kuna ƙone turare wa waɗansu alloli a Masar, inda kuka zo don ku zauna? Za ku hallakar da kanku ku kuma mai da kanku abin la’ana da abin zargi da abin ba’a a cikin dukan al’umman duniya.9. Kun manta mugayen ayyukan kakanninku, da na sarakuna da sarauniyoyin Yahuda da mugayen ayyukanku, da na matanku a cikin Yahuda da kan titunan Urushalima?10. Har yă zuwa yau ba su ƙasƙantar da kansu ko su nuna bangirma, ko su kiyaye dokata da ƙa’idodin da na sa a gabanku da kakanninku ba.11. “Saboda haka ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa na ƙudura in aukar muku da masifa in kuma hallaka dukan Yahuda.12. Zan ɗauke raguwar Yahuda waɗanda suka ƙudurta su je Masar su zauna a can. Duk za su hallaka a Masar; za su mutu ta wurin takobi ko su mutu da yunwa. Daga ƙarami zuwa babba, za su mutu ta wurin takobi ko yunwa. Za su zama abin zarge da abin tsoro, abin la’ana da abin ba’a.13. Zan hukunta waɗanda suke zama a Masar da takobi, yunwa da annoba, yadda na hukunta Urushalima.14. Babu wani daga raguwar Yahuda wanda ya tafi Masar da zai kuɓuta ko ya tsira har ya komo zuwa ƙasar Yahuda, wadda za su yi marmari su komo su zauna; babu wani da zai komo sai dai ’yan gudun hijira.”15. Sai dukan mazan da suka san cewa matansu suna ƙone turare wa waɗansu alloli, tare da dukan matan da suke a nan babban taro, da kuma dukan mutanen da suke zama a Masar ta Ƙasa da ta Bisa, suka ce wa Irmiya,16. “Ba za mu saurari saƙon da ka yi mana magana a sunan Ubangiji ba!17. Lalle za mu aikata duk abin da muka ce za mu yi. Za mu ƙone turare ga Sarauniyar Sama za mu kuma miƙa hadayun sha gare ta kamar dai yadda mu da kakanninmu, sarakunanmu da fadawanmu muka yi a garuruwan Yahuda da kuma kan titunan Urushalima. A lokacin muna da abinci a yalwace muna kuma da arziki ba mu kuma da wata damuwa.18. Amma tun da muka daina ƙone turare ga Sarauniyar Sama da kuma miƙa mata hadayun sha, muka rasa kome muna ta mutuwa ta wurin takobi da yunwa.”19. Matan suka ƙara da cewa, “Sa’ad da muka ƙone turare ga Sarauniyar Sama muka kuma miƙa mata hadayun sha, mazanmu ba su san muna yin waina kamar siffarta muna kuma miƙa mata hadayun sha ba?”20. Sai Irmiya ya ce wa dukan mutanen, maza da mata, waɗanda suke ba shi amsa,21. “ Ubangiji bai tuna ya kuma yi tunani game da turaren da aka ƙone a garuruwan Yahuda da kan titunan Urushalima wanda ku da kakanninku, sarakunanku da fadawanku da mutanen ƙasar ba ne?22. Sa’ad da Ubangiji bai iya jurewa da mugayen ayyukanku da kuma abubuwa banƙyama da kuka aikata ba, sai ƙasarku ta zama abin la’ana da kufai babu mazauna yadda yake a yau.23. Domin kun ƙone turare kuka kuma yi wa Ubangiji zunubi ba ku kuma yi masa biyayya ko ku kiyaye dokarsa ko ƙa’idodinsa ko farillansa ba, wannan masifa ta aukar muku, yadda yanzu kuka gani.”24. Sai Irmiya ya ce wa dukan mutane, har da mata, “Ku saurari maganar Ubangiji, dukanku mutanen Yahuda a Masar.25. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa ku da matanku kun nuna ta wurin ayyukanku abin da kuka yi alkawari sa’ad da kuka ce, ‘Lalle za mu yi abin da muka yi alkawari na ƙone turare da kuma miƙa hadayun sha ga Sarauniyar Sama.’ “To, sai ku ci gaba, ku aikata abin da kuka yi alkawari! Ku cika alkawarinku!26. Amma ku ji maganar Ubangiji, dukan Yahudawan da suke zama a Masar, ‘Na rantse da sunana,’ in ji Ubangiji, ‘cewa babu wani daga Yahuda wanda yake zama a ko’ina a Masar zai ƙara kira bisa sunana ko ya rantse ya ce, “Muddin Ubangiji Mai Iko Duka yana raye.”27. Gama ina lura da su don lahani, ba alheri ba; mutanen Yahuda da suke a Masar za su hallaka ta wurin takobi da yunwa sai dukansu sun hallaka.28. Waɗanda suka kuɓuta wa takobi suka komo zuwa ƙasar Yahuda daga Masar za su zama kima kawai. Sa’an nan dukan raguwar Yahuda waɗanda suka zo don su yi zama a Masar za su san maganar wane ne za tă tabbata, tawa ko tasu.29. “ ‘Wannan zai zama alama a gare ku cewa zan hukunta ku a wannan wuri,’ in ji Ubangiji, ‘saboda ku san cewa barazanata ta lahani a kanku tabbatacce za tă cika.’30. Ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Zan bayar da Fir’auna Hofra sarkin Masar ga abokan gābansa waɗanda suke neman ransa, kamar yadda na ba da Zedekiya sarkin Yahuda ga Nebukadnezzar sarkin Babilon, abokin gāban da ya nemi ransa.’ ”Zabura 119:97-10497. Kash, ga yadda nake ƙaunar dokarka! Ina tunani a kanta dukan yini.98. Umarnanka suna sa in zama mai hikima fiye da abokan gābana, gama kullum suna tare da ni.99. Ina da ganewa sosai fiye da dukan malamaina, gama ina tunani a kan farillanka.100. Ina da ganewa fiye da dattawa, gama ina biyayya da farillanka.101. Na kiyaye ƙafafuna daga kowace muguwar hanya domin in yi biyayya da maganarka.102. Ban rabu da dokokinka ba, gama kai da kanka ne ka koya mini.103. Ɗanɗanon maganarka akwai zaki, sun ma fi zuma zaki a bakina!104. Na sami ganewa daga farillanka; saboda haka ina ƙin kowace hanyar da ba daidai ba.Karin Magana 28:3-33. Mai mulkin da ya danne talakawa yana kama da ruwan saman da ya lalatar da hatsi.2 Timoti 2:1-261. Kai kuma, ɗana, ka yi ƙarfi cikin alherin da yake cikin Kiristi Yesu.2. Abubuwan da ka ji na faɗa a gaban shaidu masu yawa kuwa ka danƙa wa amintattun mutane waɗanda su ma za su iya koya wa waɗansu.3. Ka jure wa shan wahala tare da mu kamar soja mai kyau na Kiristi Yesu.4. Ba wanda yake aikin soja da zai sa kansa a sha’anin mutumin da ba ya aikin soja, domin yakan so yă gamshi wanda ya ɗauke shi soja.5. Haka ma, in wani ya yi gasa a matsayi shi ɗan wasa ne, ba ya sami rawanin nasara, sai in ya yi gasar bisa ga dokoki.6. Manomi mai aiki sosai ya kamata yă zama na fari wajen samun rabon amfanin gona.7. Ka yi tunani a kan abin da nake faɗi, gama Ubangiji zai ba ka ganewa cikin dukan wannan.8. Ka tuna da Yesu Kiristi, wanda aka tā da shi daga matattu, zuriyar Dawuda, wanda shi ne bisharata,9. wadda nake shan wahala har ga daurin sarƙa kamar mai laifi. Amma Maganar Allah ba a daure take ba.10. Saboda haka nake jure kome saboda zaɓaɓɓu, domin su ma su sami ceton da yake cikin Kiristi Yesu, tare da madawwamiyar ɗaukaka.11. Ga wata magana tabbatacciya, “In muka mutu tare da shi, za mu rayu tare da shi;12. in muka jimre, za mu yi mulki tare da shi. In muka yi mūsunsa, shi ma zai yi mūsunmu;13. in ba mu da aminci, shi dai mai aminci ne, domin shi ba zai iya mūsun kansa ba.”14. Ka riƙa tuna masu da haka, ka kuma gama su da Allah, kada su yi jayayya a kan maganganu, don ba ta da wani amfani, sai ɓad da masu ji kawai take yi.15. Ka yi iyakacin ƙoƙarinka ka gabatar da kanka a gaban Allah a matsayin wanda aka amince da shi, ma’aikaci wanda ba shi da dalilin jin kunya wanda kuma yake fassara kalmar gaskiya daidai.16. Ka yi nesa da maganganun banza na rashin tsoron Allah, gama waɗanda suka mai da hankali ga yin waɗannan za su ƙara zama marasa tsoron Allah.17. Koyarwarsu za tă bazu kamar ruɓaɓɓen gyambo. A cikinsu akwai Himenayus da Filetus,18. waɗanda suka bauɗe daga gaskiya. Suna cewa tashin matattu ya riga ya faru, suna kuma ɓata bangaskiyar waɗansu.19. Duk da haka, ƙaƙƙarfan tushen nan na Allah yana nan daram, an hatimce shi da wannan rubutu, “Ubangiji ya san waɗanda suke nasa,” da kuma, “Duk wanda ya bayyana yarda ga sunan Ubangiji, to, dole yă yi nesa da aikata mugunta.”20. A babban gida akwai kayayyakin da ba na zinariya da na azurfa kaɗai ba, amma har da na katako da na yumɓu ma; waɗansu domin hidima mai daraja waɗansu kuwa domin hidima marar daraja.21. In mutum ya tsabtacce kansa daga na farkon zai zama kayan aikin hidima mai daraja, mai amfani ga Maigida, kuma shiryayye domin yin kowane aiki mai kyau.22. Ka yi nesa da mugayen sha’awace-sha’awace na ƙuruciya, ka kuma bi adalci, bangaskiya, ƙauna da kuma salama, tare da waɗanda suke kira ga Ubangiji daga zuciya mai tsabta.23. Kada wani abu yă haɗa ka da gardandamin banza da wofi, domin ka san yadda suke jawo faɗa.24. Bai kamata bawan Ubangiji yă zama mai neman faɗa ba; a maimako, dole yă nuna alheri ga kowa, mai iya koyarwa, mai haƙuri kuma.25. Waɗanda suke gāba da shi kuwa dole yă yi musu gargaɗi cikin hankali, da fata Allah zai sa su tuba su kai ga sanin gaskiya,26. su kuma dawo cikin hankulansu su kuɓuta daga tarkon Iblis, wanda ya sa suka zama kamammu don su aikata nufinsa. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.