Baibul a cikin shekara guda Oktoba 31Irmiya 47:1-71. Ga maganar Ubangiji da ta zo wa Irmiya annabi game da Filistiyawa kafin Fir’auna ya yaƙi Gaza.2. Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Dubi yadda ruwaye suna tasowa a arewa; za su zama kogi mai rigyawa. Za su malala a ƙasa da kuma a kan kome da yake cikinta, garuruwa da waɗanda suke zaune a cikinsu. Mutane za su yi kuka; dukan mazaunan ƙasar za su yi kururuwa3. da jin motsin takawar kofatan dawakai, da jin surutun kekunan yaƙin abokin gāba da motsin ƙafafunsu. Ubanni ba za su juye don su taimaki ’ya’yansu ba; hannuwansu za su yi laƙwas.4. Gama rana ta zo da za a hallaka Filistiyawa a kuma datse dukan waɗanda suka ragu waɗanda za su iya taimakon Taya da Sidon. Ubangiji yana gab da hallaka Filistiyawa, raguwa daga bakin tekun Kaftor.5. Gaza za tă aske kanta cikin baƙin ciki; Ashkelon zai yi shiru. Ya raguwar da suke zama a fili, har yaushe za ku tsattsage kanku?6. “Za ku yi kuka kuna cewa, ‘Wayyo, takobin Ubangiji sai yaushe za ka huta? Ka koma kubenka; ka huta, ka yi shiru.’7. Amma ta yaya zai huta sa’ad da Ubangiji ya umarta, sa’ad da ya umarta shi don yă faɗa wa Ashkelon da kuma bakin teku?”Irmiya 48:1-471. Game da Mowab. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, “Kaito ga Nebo, gama za tă lalace. Kiriyatayim za su kunyata a kuma kame ta; katagar za tă sha kunya ta kuma wargaje.2. Ba za a ƙara yabi Mowab ba; a Heshbon mutane za su shirya mata maƙarƙashiya. ‘Zo, mu tafi mu kawo ƙarshe ga wannan al’umma.’ Ke kuma, ya Madmen za ki yi shiru; takobi zai fafare ki.3. Saurari kuka daga Horonayim, kukan risɓewa mai girma da hallaka.4. Za a karye Mowab; ƙanananta za su yi kuka.5. Sun haura hanyar zuwa Luhit, suna kuka mai zafi yayinda suke tafiya; a hanyar da ta gangara zuwa Horonayim suna kuka a kan hallakar da aka ji.6. Ku gudu! Ku gudu don tserar da ranku; ku zama kamar kurmi a hamada.7. Da yake kun dogara ga ayyukanku da arzikinku, ku ma za a kwashe ku bayi, Kemosh zai tafi bauta, tare da firistocinsa da fadawansa.8. Mai hallakarwa zai aukar wa kowane gari, kuma ba wani garin da zai kuɓuta. Kwari zai lalace tudu kuma ya hallaka, domin Ubangiji ya faɗa.9. Ku sa gishiri a kan Mowab, gama za tă zama kango; garuruwanta za su zama kufai, ba mazauna a cikinsu.10. “La’ananne ne shi wanda yake sake a yin aikin Ubangiji! La’ananne ne wanda ya janye takobinsa daga zub da jini!11. “Mowab ta kasance cikin kwanciyar rai tun ƙuruciyarta, kamar ruwan inabin da aka bari lis, ba a juya daga tulu zuwa wani tulu ba ba tă tafi bauta ba. Saboda haka tana da ɗanɗanonta, kuma ƙanshinta bai canja ba.12. Kwanaki suna zuwa,” in ji Ubangiji, “sa’ad da zan aika da mutanen da za su tuntsurar da tuluna, su kuma zubar da ita waje. Za su bar tulunan ba kome a ciki su kuma farfashe tulunanta.13. Sa’an nan Mowab za tă ji kunyar Kemosh, yadda gidan Isra’ila ya ji kunya sa’ad da suka dogara ga Betel.14. “Yaya za ku ce, ‘Mu jarumawa ne, mutane masu ƙarfi a yaƙi?’15. Mowab za tă hallaka a kuma kai wa garuruwanta hari; samarinta kyawawa za su gangara cikin mayanka,” in ji Sarki, wanda sunansa Ubangiji Maɗaukaki ne.16. “Fāɗuwar Mowab ta yi kusa; bala’inta zai auku nan da nan.17. Yi kuka saboda ita, dukanku mazaunan kewayenta, duk waɗanda suka san shahararta; ku ce, ‘Dubi yadda sandan sarauta mai iko ya karye, dubi yadda sanda mai daraja ya karye!’18. “Sauko daga darajarku ku zauna a busasshiyar ƙasa, Ya mazaunan Diyar Dibon, gama shi mai hallaka Mowab zai haura a kanku zai kuma lalace biranenku masu kagarai.19. Ku tsaya a bakin hanya ku duba, ku da kuke zama a Arower. Ku tambayi mutumin da yake gudu da macen da take tserewa, tambaye su, ‘Me ya faru?’20. An kunyata Mowab, gama ta wargaje. Ku yi kuka ku kuma tā da murya! Ku yi shela kusa da Arnon cewa an hallaka Mowab.21. Hukunci ya zo wa tudu, zuwa Holon, Yahza da Mefa’at,22. zuwa Dibon, Nebo da Bet-Dibilatayim,23. zuwa Kiriyatayim, Bet-Gamul da Bet-Meyon,24. zuwa Keriyot da Bozra zuwa dukan garuruwan Mowab, nesa da kusa.25. An karye ƙahon Mowab; an karye hannunta,” in ji Ubangiji.26. “Ku bugar da ita domin ta tayar wa Ubangiji. Bari Mowab tă yi ta birgima a cikin amanta; bari tă zama abin dariya.27. Isra’ila ma bai zama abin dariya a gare ki ba? Ba a kama shi cikin ɓarayi, har kaɗa kai na ba’a kike yi a duka sa’ad da kike magana game da shi?28. Ku bar garuruwanku ku zauna a cikin duwatsu, ku da kuke zama a Mowab. Ku zama kamar kurciyar da take sheƙarta a bakin kogo.29. “Mun ji labarin girman kan Mowab mun ji alfarma girmankanta da kumburinta girmankanta da fariyarta da renin zuciyarta.30. Na san alfarmanta amma a banza ne,” in ji Ubangiji, “kuma taƙamarta ba ya cimma kome.31. Saboda haka zan yi kuka a kan Mowab gama dukan Mowab zan yi kuka, Zan yi gurnani don mutanen Kir Hareset.32. Zan yi kuka saboda kai, yadda Yazer ya yi kuka Ya kuringar Sibma. Rassanki sun kai har teku; sun kai har tekun Yazer. Mai hallakarwa ya fāɗo a kan ’ya’yan itatuwanku da kuma inabinku da suka nuna.33. Farin ciki da murna su ɓace daga lambunan itatuwa da kuma gonakin Mowab. Na dakatar da malalar ruwan inabi daga wurin matsi; ba wanda zai matse su da ihun farin ciki. Ko da yake akwai sowa sowar ba ta farin ciki ba ce.34. “Muryar kukansu na tashi daga Heshbon zuwa Eleyale da Yahaz, daga Zowar har zuwa Horonayim da Eglat Shelishiya, gama har ruwan Nimrim ma sun bushe.35. A Mowab zan kawo ƙarshen waɗanda suke miƙa hadayu a masujadan kan tudu suna kuma ƙone turare ga allolinsu,” in ji Ubangiji.36. “Saboda haka zuciyata na makoki don Mowab kamar busa; tana makoki kamar busa saboda mutanen Kir Hareset. Arzikin da suka samu ta ƙare.37. An aske kowane kai aka kuma yanke kowane gemu aka kuma sa wa kowane kwankwaso rigar makoki.38. A kan dukan rufi a Mowab da kuma a dandalin jama’a babu wani abu sai kuka gama na karye Mowab kamar tulun da babu mai so,” in ji Ubangiji.39. “Duba yadda aka ragargazar ta ita! Duba yadda suke kuka! Duba yadda Mowab ta juya bayanta da kunya! Mowab ta zama abin ba’a abin tsoro ga dukan waɗanda suke kewaye da ita.”40. Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Ga shi! Gaggafa tana firiya zuwa ƙasa, tana shimfiɗa fikafikanta a kan Mowab.41. Za a ci Keriyot a kuma kame kagarai. A wannan rana zukatan jarumawan Mowab za su zama kamar zuciyar macen da take naƙuda.42. Za a hallakar da Mowab a matsayin al’umma domin ta tayar wa Ubangiji.43. Razana da rami da tarko suna jiranku, Ya mutanen Mowab,” in ji Ubangiji.44. “Duk wanda ya gudu daga razana zai fāɗa cikin rami, duk wanda ya haura daga rami zai fāɗa cikin tarko; gama zan kawo wa Mowab shekarar hukuncinta,” in ji Ubangiji.45. “A ƙarƙashin Heshbon masu gudun hijira suna tsaye ba mai taimako, gama wuta ta mutu daga Heshbon, harshen wuta daga tsakiyar Sihon; ta ƙone goshin Mowab, ƙoƙon kai na ’yan tayarwa masu surutu.46. Kaitonki, ya Mowab! Mutanen Kemosh sun hallaka; an kai ’ya’yanki maza daurin talala ’ya’yanki mata zaman bauta.47. “Duk da haka zan maido da wadatar Mowab a kwanaki masu zuwa,” in ji Ubangiji. A nan hukuncin Mowab ya ƙare.Zabura 119:113-120113. Na ƙi mutane masu baki biyu, amma ina ƙauna dokarka.114. Kai ne mafakata da garkuwata; na sa zuciyata a maganarka.115. Ku rabu da ni, ku masu aikata mugunta, don in kiyaye umarnan Allahna!116. Ka raya ni bisa ga alkawarinka, zan kuwa rayu; kada ka bari a gwale sa zuciyata.117. Ka riƙe ni za a kuma cece ni; kullayaumi zan ɗauka ƙa’idodinka da muhimmanci.118. Ka ki dukan waɗanda suka kauce daga ƙa’idodinka, gama yaudararsu banza ne.119. Dukan mugayen duniya ka zubar kamar datti; saboda haka nake ƙaunar farillanka.120. Naman jikina na rawan jiki don tsoronka; na cika da tsoron dokokinka.Karin Magana 28:5-55. Mugaye ba su san gaskiya ba, amma waɗanda suke neman Ubangiji sun santa sosai.2 Timoti 4:1-221. A gaban Allah da kuma Kiristi Yesu, wanda zai yi wa masu rai da matattu shari’a, saboda kuma bayyanuwarsa da mulkinsa, ina ba ka umarni.2. Ka yi wa’azin Maganar Allah, ka zama a shirye a kullum, ko da zarafi, ko babu zarafi, ka yi gyara, ka kwaɓe, ka kuma ƙarfafa, da matuƙar haƙuri da koyarwa cikin natsuwa.3. Gama lokaci yana zuwa da mutane ba za su jure da sahihiyar koyarwa ba. A maimako, don cimma burinsu, za su taro wa kansu malamai masu yawa, domin su faɗi abin da kunnuwansu masu ƙaiƙayi suke so su ji.4. Za su juye kunnuwansu daga gaskiya zuwa ga jin tatsuniyoyi.5. Amma kai, ka natsu cikin kowane hali, ka jure shan wahala, ka yi aikin mai bishara, ka cika dukan ayyukan hidimarka.6. Gama an riga an tsiyaye ni kamar hadaya ta sha, kuma lokacin tashina ya yi.7. Na yi fama mai kyau, na gama tseren, na riƙe bangaskiya.8. Yanzu kuwa an ajiye mini rawanin adalci, wanda Ubangiji, Alƙali mai adalci zai ba ni a ranan nan ba kuwa ni kaɗai ba, amma ga duk waɗanda suka yi marmarin bayyanuwarsa.9. Ka yi iyakacin ƙoƙarinka ka zo wurina da sauri,10. gama Demas, saboda ƙaunar wannan duniya, ya yashe ni ya tafi Tessalonika. Kirssens ya tafi Galatiya, Titus kuwa ya tafi Dalmatiya.11. Luka ne kaɗai yake tare da ni. Ka nemi Markus ku zo tare, domin yana da amfani a gare ni cikin hidimata.12. Na aiki Tikikus zuwa Afisa.13. Sa’ad da za ka dawo, ka zo mini da alkyabbar da na bari a wurin Karbus a Toruwas, da kuma naɗaɗɗun littattafaina, tun ba ma fatun nan masu rubutu ba.14. Alekzanda maƙerin ƙarafan nan ya yi mini mugunta ƙwarai. Ubangiji zai sāka masa saboda abin da ya yi.15. Kai ma sai ka lura da shi, domin ya yi gāba sosai da saƙonmu.16. A lokacin da na kāre kaina da farko, ba wanda ya goyi bayana, sai ma kowa ya yashe ni. Ina fata ba za a lasafta wannan laifi a kansu ba.17. Amma Ubangiji ya tsaya tare da ni, ya kuma ba ni ƙarfi, don ta wurina a yi cikakkiyar shelar saƙon har Al’ummai duka su ji. Aka kuma cece ni daga bakin zaki.18. Ubangiji zai cece ni daga kowane mugun hari yă kuma kai ni mulkinsa na sama lafiya. A gare shi ɗaukaka ta tabbata har abada abadin. Amin.19. Ka gai da Firiskila da Akwila da iyalin Onesiforus.20. Erastus ya dakata a Korint, na kuma bar Turofimus cikin rashin lafiya a Miletus.21. Ka yi iyakacin ƙoƙarinka ka iso nan kafin damina. Yubulus yana gaishe ka, haka ma Fuden, Lainus, Kalaudiya da kuma dukan ’yan’uwa.22. Ubangiji yă zama tare da ruhunka. Alheri yă zama tare da ku. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.