Baibul a cikin shekara guda Oktoba 4Ishaya 59:1-211. Tabbatacce hannun Ubangiji bai kāsa yin ceto ba, kunnensa kuma bai kurmance da zai kāsa ji ba.2. Amma laifofinku sun raba ku da Allahnku; zunubanku sun ɓoye fuskarsa daga gare ku, saboda kada yă ji.3. Gama hannuwanku sun ƙazantu da jini, yatsotsinku kuma da alhaki. Leɓunanku suna faɗin ƙarairayi, harshenku kuma yana raɗar mugayen abubuwa.4. Babu wani mai ce a yi adalci; babu wani mai nema a dubi al’amarinsa da mutunci. Sun dogara a gardandamin banza suna ƙarairayi; suna ɗaukar cikin ɓarna, su haifi mugunta.5. Suna ƙyanƙyashe ƙwan kāsā su kuma saƙa yanar gizo-gizo. Duk wanda ya ci ƙwansu zai mutu, kuma sa’ad da ƙwan ya fashe, zai ƙyanƙyashe kububuwa.6. Yanar gizo-gizonsu ba amfani don tufa; ba za su iya rufuwa da abin da suka yi ba. Ayyukansu mugaye ne, ayyukan tā da hargitsi kuma suna a hannuwansu.7. Ƙafafunsu sukan gaggauta zuwa aikata zunubi; suna da saurin zub da jini. Tunaninsu mugaye ne; lalaci da hallaka sun shata hanyoyinsu.8. Ba su san hanyar salama ba; babu adalci a hanyoyinsu. Sun mai da su karkatattun hanyoyi; babu wanda zai yi tafiya a kansu ya sami salama.9. Saboda haka gaskiya ta yi nisa da mu, adalci kuma ba ya kaiwa gare mu. Muna neman haske, sai ga duhu; muna neman haske, sai muka yi ta tafiya cikin baƙin inuwa.10. Kamar makafi, sai lallubar bango muke yi, muna lallubawar hanyarmu kamar marasa idanu. Da tsakar rana muna tuntuɓe sai ka ce wuri ya fara duhu; cikin ƙarfafa, mun zama kamar matattu.11. Muna gurnani kamar beyar; muna ta ƙugi kamar kurciyoyi. Muna ta neman adalci amma ina; mun nemi fansa, amma yana can da nisa.12. Gama laifofinmu suna da yawa a gabanka, zunubanmu kuma suna ba da shaida gāba da mu. Laifofinmu kullum suna a gabanmu, muna kuma sane da laifofinmu,13. tawaye da mūsun Ubangiji, mun juye bayanmu ga Allahnmu, zugawa a yi zalunci da tayarwa, faɗin ƙarairayi da zukatanmu suka shirya.14. Saboda haka aka kau da yin gaskiya adalci kuma ya tsaya can da nesa; gaskiya ta yi tuntuɓe a tituna, sahihanci ba zai shiga ba.15. Gaskiya ta ɓace gaba ɗaya, kuma duk wanda ya guji mugunta zai zama ganima. Ubangiji ya duba bai kuwa ji daɗi cewa babu adalci ba.16. Ya ga cewa babu wani, ya yi mamaki cewa babu wanda zai shiga tsakani; saboda haka hannunsa ya aikata masa ceto, adalcinsa kuma ya raya shi.17. Ya yafa sulke a matsayin rigar ƙirji, da hulan kwanon ceto a kansa; ya sa rigunan ɗaukar fansa ya kuma nannaɗe kansa da kishi kamar a cikin alkyabba.18. Bisa ga abin da suka yi, haka za a sāka fushi a kan abokan gābansa ramuwa kuma a kan maƙiyansa; zai sāka wa tsibirai abin da ya dace da su.19. Daga yamma, mutane za su ji tsoron Ubangiji, daga mafitar rana kuma, za su girmama ɗaukakarsa. Gama zai zo kamar rigyawa mai tsananin gudu cewa numfashin Ubangiji zai tafi tare da shi.20. “Mai fansa zai zo Sihiyona, zuwa waɗanda suke cikin Yaƙub da suka tuba daga zunubansu,” in ji Ubangiji.21. “Game da ni dai, ga alkawarina da su,” in ji Ubangiji. “Ruhuna, wanda yake a kanka, da kuma maganata da na sa a bakinka ba za tă rabu da bakinka ba, ko daga bakunan ’ya’yanka ba, ko kuwa daga bakunan zuriyarsu ba daga wannan lokaci zuwa gaba da kuma har abada,” in ji Ubangiji.Ishaya 60:1-221. “Ki tashi, ki haskaka, gama haskenki ya zo, ɗaukakar Ubangiji ya taso a kanki.2. Duba, duhu ya rufe duniya duhu mai kauri kuma yana bisa mutane, amma Ubangiji ya taso a kanki ɗaukakarsa kuma ya bayyana a bisanki.3. Al’ummai za su zo wurin haskenki, sarakuna kuma zuwa asubahin sabon yininki.4. “Ki ɗaga idanunki ki duba kewaye da ke. Duka sun tattaru suka kuma zo wurinki; ’ya’yanki maza daga nesa, ana kuma ɗaukan ’ya’yanki mata a hannu.5. Sa’an nan za ki duba ki kuma haskaka zuciyarki zai motsa ya kuma cika da farin ciki; za a kawo miki wadata daga tekuna, za a kawo miki arzikin al’ummai.6. Manyan ayarin raƙuma za su cika ƙasar, ƙananan raƙuma ke nan daga Midiyan da Efa. Daga Sheba kuma duka za su zo, suna ɗauke da zinariya da turare suna shelar yabon Ubangiji.7. Dukan garkunan Kedar za su taru a wurinki ragunan Nebayiwot za su yi miki hidima; za a karɓe su kamar hadayu a kan bagadenki, zan kuma darjanta haikalina mai ɗaukaka.8. “Su wane ne waɗannan da suke firiya kamar gizagizai, kamar kurciyoyi suna zuwa sheƙarsu?9. Babu shakka tsibirai suna dogara gare ni; jiragen Tarshish kuma su ne a gaba, suna kawo ’ya’yanki maza daga nesa, tare da azurfa da zinariya, domin su girmama Ubangiji Allahnki, Mai Tsarkin nan na Isra’ila, gama ya cika ki da daraja.10. “Baƙi za su sāke gina katangarki, sarakunansu kuma za su yi miki hidima. Ko da yake a cikin fushi na buge ki, da tagomashi zan yi miki jinƙai.11. Ƙofofinki kullum za su kasance a buɗe, ba za a ƙara rufe su da rana ko da dare ba, saboda mutane su kawo miki dukiyar al’ummai, sarakunansu za su kasance a gaba a jerin gwanon nasara.12. Gama al’umma ko masarautar da ba tă bauta miki ba, za tă hallaka; za tă lalace sarai.13. “Darajar Lebanon za tă zo wurinki, itatuwan fir da dai ire-irensu da kuma itatuwan saifires duka za su zo don su ƙayatar da wurina mai tsarki; zan kuma ɗaukaka wurin ƙafafuna.14. ’Ya’ya maza masu zaluntarku za su zo suna rusunawa a gabanki; dukan waɗanda suka rena ki za su rusuna a ƙafafunki su kuma ce da ke Birnin Ubangiji, Sihiyona na Mai Tsarkin nan na Isra’ila.15. “Ko da yake an yashe ki aka kuma ƙi ki, har babu wani da ya ratsa a cikinki, zan mai da ke madawwamiyar abar taƙama da kuma farin cikin dukan zamanai.16. Za ki sha madarar al’ummai a kuma shayar da ke da nonon sarauta. Sa’an nan za ki san cewa ni, Ubangiji, ni ne Mai Cetonki, Mai Fansarki, Mai Ikon nan na Yaƙub.17. A maimakon tagulla zan kawo zinariya, azurfa kuma a maimakon baƙin ƙarfe. A maimakon katako zan kawo tagulla, baƙin ƙarfe kuma a maimakon duwatsu. Zan sa salama ta zama gwamnarki adalci kuma mai mulkinki.18. Ba za a ƙara jin hayaniyar tashin hankali a ƙasarki ba, balle lalacewa ko hallaka a cikin iyakokinki, amma za ki kira katangarki Ceto ƙofofinki kuma Yabo.19. Rana ba za tă ƙara zama haskenki a yini ba, balle hasken wata ya haskaka a kanki, gama Ubangiji zai zama madawwamin haskenki, Allahnki kuma zai zama ɗaukakarki.20. Ranarki ba za tă ƙara fāɗuwa ba watanki kuma ba zai ƙara shuɗewa ba; Ubangiji zai zama madawwamin haskenki, kwanakin baƙin cikinki za su ƙare.21. Sa’an nan dukan mutanenki za su zama masu adalci za su kuma mallaki ƙasar har abada. Su ne reshen da na shuka, aikin hannuwana, don nuna darajata.22. Mafi ƙanƙanta a cikinki za tă zama dubu, ƙarami zai zama al’umma mai girma. Ni ne Ubangiji, cikin lokacinsa zan yi haka da sauri.”Zabura 115:1-81. Ba gare mu ba, ya Ubangiji, ba gare mu ba amma ga sunanka yă sami ɗaukaka, saboda ƙaunarka da amincinka.2. Me ya sa al’ummai suke cewa, “Ina Allahnsu?”3. Allahnmu yana a sama; yana yin duk abin da ya ga dama.4. Amma gumakansu azurfa da zinariya ne, da hannuwan mutane suka yi.5. Suna da bakuna, amma ba sa magana, idanu, amma ba sa gani;6. suna da kunnuwa, amma ba sa ji, hanci, amma ba sa jin ƙanshi7. suna da hannuwa, amma ba sa iya taɓa kome, ƙafafu, amma ba sa iya tafiya; ba sa iya ce wani abu da maƙogwaronsu.8. Masu yinsu za su zama kamar su, haka kuma zai kasance da duk wanda ya dogara da su.Karin Magana 26:23-2323. Kamar kaskon da aka dalaye da azurfar da ba a tace ba haka leɓuna masu mugun zuciya.Afisawa 5:17-3317. Saboda haka kada ku zama wawaye, sai dai ku fahimci ko mene ne nufin Ubangiji.18. Kada ku bugu da ruwan inabi, wanda yake kai ga lalaci. A maimako haka, ku cika da Ruhu.19. Ku yi zance da juna cikin zabura, da waƙoƙi, da kuma waƙoƙin ruhaniya. Ku rera, ku kuma yi kiɗe-kiɗe a zuciyarku ga Ubangiji.20. Kullum ku dinga yin amfani da sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi, kuna gode wa Allah Uba a kome.21. Ku yi biyayya da juna saboda bangirmar da kuke nuna wa Kiristi.22. Matan aure, ku yi biyayya ga mazanku, kamar ga Ubangiji ne kuke yi.23. Gama miji shi ne kan mace, yadda Kiristi yake kai da kuma Mai Ceton ikkilisiya, wadda take jikinsa.24. To, kamar yadda ikkilisiya take biyayya ga Kiristi, haka ma ya kamata mata su yi biyayya ga mazansu cikin kome.25. Maza, ku ƙaunaci matanku, kamar yadda Kiristi ya ƙaunaci ikkilisiya, ya kuma ba da kansa dominta.26. Ya mai da ikkilisiya ta zama mai tsarki ta wurin ikon maganarsa, ya kuma tsabtacce ta ta wurin wanke ta da ruwa.27. Kiristi ya yi haka don yă miƙa wa kansa ikkilisiya mai ɗaukaka da kuma mai tsarki, marar aibi, marar tabo, da kuma marar lahani.28. Don haka, dole maza su ƙaunaci matansu kamar yadda suke ƙaunar jikunansu. Wanda yake ƙaunar matarsa, yana ƙaunar kansa ne.29. Gama ba wanda ya taɓa ƙin jikinsa, sai dai yă ciyar da shi, yă kuma kula da shi, kamar yadda Kiristi yake yi wa ikkilisiya,30. gama mu gaɓoɓin jikinsa ne.31. “Saboda haka mutum yakan bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, yă manne wa matarsa, su biyun su zama jiki ɗaya.”32. Wannan babban asiri ne, amma na ɗauke shi a matsayin kwatanci ne na Kiristi da ikkilisiya.33. Duk da haka, dole kowannenku yă ƙaunaci matarsa kamar yadda yake ƙaunar kansa, kuma dole matar tă yi biyayya ga mijinta. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.