Baibul a cikin shekara guda Oktoba 7Ishaya 65:1-251. “Na bayyana kaina ga waɗanda ba su tambaye ni ba; ina samuwa ga waɗanda ba su neme ni ba. Ga al’ummar da ba tă kira bisa sunana ba, Na ce, ‘Ga ni, ga ni.’2. Dukan yini ina miƙa hannuwana ga mutane masu tayarwa, waɗanda suna tafiya a hanyoyin da ba su da kyau, suna bin tunaninsu,3. mutanen da suna cin gaba da tsokanata a fuskata, suna miƙa hadayu a gonaki suna ƙone turare a bagadan tubali;4. suna zama a kaburbura su kwana suna yin asirtattun ayyuka; suna cin naman aladu, tukwanensu kuma sun cika da nama marar tsabta;5. suna cewa, ‘Ku tsaya a can; kada ku yi kusa da ni, gama na fi ku tsarki!’ Irin mutanen nan hayaƙi ne a hancina, wuta kuma da take cin gaba da ci dukan yini.6. “Ga shi, yana nan a rubuce a gabana cewa ba zan ƙyale ba, zan yi cikakken ramuwa; zan yi ramuwa a cinyoyinsu7. saboda zunubanku da kuma zunuban kakanninku,” in ji Ubangiji. “Gama sun ƙone turare a kan duwatsu suka kuma ƙazantar da ni a kan tuddai, zan yi musu awo in zuba a cinyoyinsu cikakken ramuwa saboda ayyukansu na dā.”8. Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Kamar sa’ad da ruwan ’ya’yan itace yana samuwa a cikin tarin ’ya’yan inabi mutane kuma su ce, ‘Kada a lalace shi, har yanzu akwai abu mai kyau a ciki,’ haka nan zan yi a madadin bayina; ba zan hallaka su duka ba.9. Zan fitar da zuriyar Yaƙub, daga Yahuda kuma waɗanda za su mallaki duwatsuna; zaɓaɓɓun mutanena za su gāje su, a can kuma bayina za su zauna.10. Sharon zai zama wurin kiwo don shanu, Kwarin Akor kuma wurin hutun garkuna, domin mutanena da suke nemana.11. “Amma game da ku waɗanda kuka yashe Ubangiji kuka manta da dutsena mai tsarki kuwa, ku da kuka shimfiɗa tebur don sa’a kuka kuma cika darunan ruwan inabin da aka dama don Ƙaddara,12. zan ƙaddara ku ga kaifin takobi, dukanku kuma za ku sunkuya wa mai yanka; gama na yi kira amma ba ku amsa ba, na yi magana amma ba ku saurara ba. Kuka aikata mugunta a gabana kuka kuma zaɓi abin da ba na jin daɗi.”13. Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “Bayin za su ci, amma ku za ku ji yunwa; bayina za su sha, amma ku za ku ji ƙishi; bayina za su yi farin ciki amma ku za ku sha kunya.14. Bayina za su rera da farin cikin zukatansu, amma ku za ku yi kuka daga wahalar zuciya ku kuma yi kururuwa da karayar zuci.15. Za ku bar sunanku ga zaɓaɓɓuna yă zama abin la’antarwa; Ubangiji Mai Iko Duka zai kashe ku, amma ga bayina zai ba su wani suna.16. Duk wanda zai roƙi albarka a cikin ƙasar zai yi haka da gaskiyar Allah; wanda zai yi rantsuwa a cikin ƙasar zai rantse da gaskiyar Allah. Gama za a manta da wahalolin baya a kuma ɓoye su daga idanuna.17. “Ga shi, na halicci sabuwar sama da kuma sabuwar duniya. Abubuwa na dā za a manta da su, ba kuwa za a ƙara tuna da su ba.18. Amma ku yi murna ku kuma yi farin ciki har abada a abin da na halitta, gama zan halicci Urushalima ta zama abin murna mutanenta kuwa abin farin ciki.19. Zan yi farin ciki a kan Urushalima in kuma yi murna saboda mutanena; a can ba za a ƙara jin karar makoki da na kuka ba.20. “A cikinta ba za a ƙara jin jariri ya rayu na ’yan kwanaki kawai ba, ko kuwa wani tsohon da bai cika kwanakinsa ba; duk wanda ya mutu yana da shekaru ɗari za a ce ya mutu a kurciya ne kawai; duk wanda bai kai ɗari ba za a ɗauka la’antacce ne.21. Za su gina gidaje su kuma zauna a cikinsu; za su yi shuki a gonakin inabi su kuma ci ’ya’yansu.22. Ba za su ƙara gina gidaje waɗansu kuma su zauna a cikinsu ba, ko su yi shuki waɗansu kuma su ci ba. Gama kamar yadda kwanakin itace suke, haka kwanakin mutanena za su kasance; zaɓaɓɓuna za su daɗe suna jin daɗin ayyukan hannuwansu.23. Ba za su yi wahala a banza ba ko su haifi ’ya’yan da aka ƙaddara da rashin sa’a; gama za su zama mutanen da Ubangiji ya yi wa albarka, su da zuriyarsu tare da su.24. Kafin su yi kira zan amsa; yayinda suke cikin magana zan ji.25. Kyarketai da ’yan raguna za su ci abinci tare, zaki kuma zai ci buɗu kamar yadda shanu suke yi, amma ƙura ce za tă zama abincin maciji. Ba za su ƙara cuci ko su yi ɓarna a kan dukan dutsena mai tsarki ba,” in ji Ubangiji.Ishaya 66:1-241. Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Sama kursiyina ce, duniya kuma matashin sawuna. Ina gidan da za ku gina mini? Ina wurin hutuna zai kasance?2. Ba hannuna ba ne ya yi dukan waɗannan abubuwa, ta haka suka kasance?” In ji Ubangiji. “Wannan mutum ne nake jin daɗi, shi da yake mai ƙasƙanci da kuma zuciyar yin tuba, yana kuma rawar jiki ga maganata.3. Amma duk ya miƙa hadayar bijimi yana kama da wanda ya kashe mutum, kuma duk wanda ya miƙa ɗan rago, kamar wanda ya karye wuyan kare; duk wanda ya miƙa hadaya ta gari yana kama da wanda ya yi sadakar jinin alade, kuma duk wanda ya ƙone turaren tuni, kamar wanda yake bauta gunki ne. Sun zaɓi hanyoyinsu, rayukansu kuma suna jin daɗin abubuwan banƙyamarsu;4. saboda haka ni ma zan aukar musu da masifa mai zafi in kuma kawo musu abin da suke tsoro. Gama sa’ad da na yi kira, ba wanda ya amsa, sa’ad da na yi magana, ba wanda ya saurara, Sun aikata mugunta a idona suka kuma zaɓa abin da ba na jin daɗi.”5. Ku ji maganar Ubangiji, ku da kuke rawar jiki ga maganarsa, “’Yan’uwanku da suke ƙinku, suna kuma ware ku saboda sunana, sun ce, ‘Bari a ɗaukaka Ubangiji, don mu ga farin cikinku!’ Duk da haka za su sha kunya.6. Ku ji wannan hayaniya daga birni, ku ji surutu daga haikali! Amon Ubangiji ne yana sāka wa abokan gābansa abin da ya dace da su.7. “Kafin naƙuda ya fara mata, ta haihu; kafin zafi ya zo mata, ta haifi ɗa.8. Wa ya taɓa jin irin wannan abu? Wa ya taɓa gani irin abubuwan nan? Za a iya ƙirƙiro ƙasa a rana ɗaya ko a haifi al’umma farat ɗaya? Duk da haka da zarar Sihiyona ta fara naƙuda sai ta haifi ’ya’yanta.9. Zan kai mace har haihuwa in kuma sa ta kāsa haihu?” In ji Ubangiji. “Zan rufe mahaihuwa sa’ad da lokacin haihuwa ya yi?” In ji Allahnku.10. “Ku yi farin ciki tare da Urushalima ku kuma yi murna saboda ita, dukanku waɗanda kuke ƙaunarta; ku yi farin ciki matuƙa tare da ita, dukanku waɗanda kuke makoki a kanta.11. Gama za ku tsotsa ku kuma ƙoshi da nonon ta’aziyyarta; za ku sha sosai ku kuma ji daɗin yalwarta.”12. Gama ga abin da Ubangiji ya faɗa, “Zan fadada salama gare ta kamar kogi, wadatar al’ummai kuma kamar rafi mai gudu; za ku tsotsa a kuma riƙe ku a hannunta ku kuma yi wasa a gwiwoyinta.13. Kamar yadda uwa takan ta’azantar da ɗanta haka zan ta’azantar da ku; za ku kuma ta’azantu a Urushalima.”14. Sa’ad da kuka ga wannan, zuciyarku za tă yi farin ciki za ku kuma haɓaka kamar ciyawa; za a sanar da hannun Ubangiji ga bayinsa, amma za a nuna wa maƙiyansa fushinsa.15. Ga shi, Ubangiji yana zuwa da wuta, kuma kekunan yaƙinsa suna kama da guguwa; zai sauko da fushinsa da zafi, tsawatawarsa kuma da harsunan wuta.16. Gama da wuta da kuma takobi Ubangiji zai yi hukunci a kan dukan mutane, kuma yawanci za su kasance waɗanda Ubangiji zai kashe.17. “Waɗanda suka tsarkake suka kuma tsabtacce kansu don su je lambu, suna bin wannan da yake tsakiya waɗannan da suke cin naman aladu da ɓeraye da waɗansu abubuwan banƙyama, za su sadu da ƙarshensu tare,” in ji Ubangiji.18. “Ni kuwa, saboda ayyukansu da kuma tunaninsu, ina dab da zuwa in tattara dukan al’ummai da harsuna, za su kuma zo su ga ɗaukakata.19. “Zan kafa alama a cikinsu, zan kuma aika waɗansu da suka tsira zuwa al’ummai, zuwa Tarshish, zuwa Libiya da Lidiya (sanannun ’yan aika), zuwa Tubal da kuma Girka, da kuma zuwa manisantan tsibirai da ba su taɓa jin labarin sunana ba ko su ga ɗaukakata. Za su yi shelar ɗaukakata a cikin al’ummai.20. Za su kuma dawo da dukan ’yan’uwanku, daga dukan al’ummai, zuwa dutsena mai tsarki a Urushalima kamar hadaya ga Ubangiji, a kan dawakai, a kekunan yaƙi da wagonu, da kuma a kan alfadarai da kuma raƙuma,” in ji Ubangiji. “Za su kawo su, kamar yadda Isra’ilawa suke kawo hadayun hatsi, zuwa haikalin Ubangiji a cikin tsabtatattun kore.21. Zan kuwa zaɓa waɗansunsu kuma su zama firistoci da Lawiyawa,” in ji Ubangiji.22. “Kamar yadda sabuwar duniya da sabuwar sama za su tabbata a gabana,” in ji Ubangiji, “haka sunanku da zuriyarku za su tabbata.23. Daga wannan sabon wata zuwa wancan, kuma daga wannan Asabbaci zuwa wancan, dukan mutane za su zo su rusuna a gabana,” in ji Ubangiji.24. “Za su kuma fita su ga gawawwakin mutanen da suka yi mini tayarwa; tsutsotsin da suke cinsu ba za su taɓa mutuwa ba, balle wutar da take ƙona su ta mutu, za su kuma zama abin ƙyama ga dukan mutane.”Zabura 116:1-41. Ina ƙaunar Ubangiji, gama ya ji muryata; ya ji kukata ta neman jinƙai.2. Domin ya juye kunnensa gare ni, zan kira gare shi muddin ina da rai.3. Igiyoyin mutuwa sun shaƙe ni, wahalar kabari sun zo a kaina; na cika da wahala da ɓacin rai.4. Sai na kira ga sunan Ubangiji na ce, “Ya Ubangiji, ka cece ni!”Karin Magana 26:28-2828. Harshe mai faɗin ƙarya yana ƙin waɗanda yake ɓata musu rai, daɗin baki kuma yakan aikata ɓarna.Filibbiyawa 2:1-301. In kuna da wata ƙarfafawa daga tarayya da Kiristi, in da wata ta’aziyya daga ƙaunarsa, in da wani zumunci da Ruhu, in da juyayi da tausayi,2. to, sai ku sa farin cikina yă zama cikakke ta wurin kasance da hali ɗaya, kuna ƙauna ɗaya, kuna zama ɗaya cikin ruhu da kuma manufa.3. Kada ku yi kome da sonkai ko girman kai, sai dai cikin tawali’u, ku ɗauki waɗansu sun fi ku.4. Bai kamata kowannenku yă kula da sha’anin kansa kawai ba, sai dai yă kula da sha’anin waɗansu ma.5. A cikin dangantakarku da juna, ya kamata halayenku su zama kamar na Kiristi Yesu.6. Wanda, ko da yake cikin ainihin surar Allah yake, bai mai da daidaitakansa nan da Allah wani abin riƙewa kam-kam ba,7. amma ya mai da kansa ba kome ba, yana ɗaukan ainihin surar bawa, aka yi shi cikin siffar mutum.8. Aka kuma same shi a kamannin mutum, ya ƙasƙantar da kansa ya kuma zama mai biyayya wadda ta kai shi har mutuwa, mutuwar ma ta gicciye!9. Saboda haka Allah ya ɗaukaka shi zuwa mafificin wuri ya kuma ba shi sunan da ya fi dukan sunaye,10. don a sunan Yesu kowace gwiwa za tă durƙusa, a sama da a ƙasa da kuma a ƙarƙashin ƙasa,11. kowane harshe kuma yă furta cewa Yesu Kiristi Ubangiji ne, don ɗaukakar Allah Uba.12. Saboda haka, ya abokaina ƙaunatattu, kamar yadda kullum kuke biyayya ba kawai sa’ad da ina nan ba, amma yanzu da ba na nan tare da ku, ku ci gaba da yin ayyukan cetonku da tsoro da kuma rawan jiki,13. gama Allah ne yake aiki a cikinku, don ku nufa ku kuma aikata bisa ga nufinsa mai kyau.14. Ku yi kome ba tare da gunaguni ko gardama ba,15. don ku zama marasa abin zargi, sahihai ’ya’yan Allah, waɗanda ba su da laifi, a zamanin mutane karkatattu, kangararru, waɗanda kuke haskakawa a cikinsu kamar fitilu a duniya16. kuna kuwa cin gaba da riƙe maganar rai domin in yi taƙama a ranar Kiristi cewa ban yi gudu ko fama a banza ba.17. Amma ko da ana tsiyaye jinina kamar hadaya ta sha a kan hadaya da kuma hidimar da take fitowa daga bangaskiyarku, ina murna ina kuma farin ciki da ku duka.18. Haka ma ya kamata ku yi murna ku kuma yi farin ciki tare da ni.19. Ina sa rai a cikin Ubangiji Yesu cewa zan aika da Timoti zuwa gare ku ba da daɗewa ba, don ni ma in ji daɗi sa’ad da na ji labarinku.20. Ba ni da wani kamar sa, wanda yake da ainihin sha’awa a zaman lafiyarku.21. Gama kowa yana lura da al’amuran kansa ne kawai, ba na Kiristi Yesu ba.22. Amma, ai, kun san darajar Timoti yadda muka yi bautar bishara tare, kamar ɗa da mahaifinsa.23. Saboda haka, ina sa rai, in aike shi da zarar na ga yadda abubuwa suke a nan.24. Ni kuma ina da tabbaci a cikin Ubangiji cewa zan zo ba da daɗewa ba.25. Amma ina gani ya dace in aika da Afaforiditus, ɗan’uwana, abokin aikina da kuma abokin famana, wanda kuma yake ɗan saƙonku, wanda kuka aika domin yă biya mini bukatuna.26. Gama yana marmarin ganinku duka ya kuma damu domin kun ji cewa ya yi rashin lafiya.27. Ba shakka ya yi rashin lafiya, har ya kusa mutuwa. Amma Allah ya nuna masa jinƙai, ba shi kaɗai ba amma har da ni ma, don yă rage mini baƙin ciki kan baƙin ciki.28. Saboda haka na yi niyya ƙwarai in aike shi wurinku, don sa’ad da kuka sāke ganinsa za ku yi murna, ni kuma in rage damuwa.29. Ku marabce shi cikin Ubangiji da farin ciki mai yawa, ku kuma girmama mutane irinsa,30. domin ya kusa yă mutu saboda aikin Kiristi, ya yi kasai da ransa don yă cikasa taimakon da ba ku iya yi mini ba. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.